Showing 78001 words to 81000 words out of 133269 words

Chapter 27 - Dan Makaho Complete Document by Biebee Isa--.txt

28 Dec 2024

13075

ta kawar da kanta kamar bata ganta ba.


Yesmin da murmushi tace “Labiba, ki gaisheni” da sauri Labiba ta kalleta, ta san cewa wannan ta girmeta nesa ba kusa ba, a k’alla zata bata shekaru 7 ko 8 chan kasan murya tace “Ina kwana” K’amshi ta murmusa har ta samo answer tambayarta, tace “Lafiya lau, aiki kikeyi ne?” Uhm kawai tace, murmushi ta sake mata tace “oya ayi aiki da kyau kar mama tayi fada” bata jira me labiba zatace ba ta juya ta shigewanta dakin Zaid.


In ran Labiba yayi dubu ya baci, bata kin mutane, ranta sai yayi kuri yake baci, amma sosai Yesmin ta bata mata rai, haka kurum take jin haushinta, ta dade tsaye da roba a hannu, abunda yafi bata haushi shine ganin Yesmin ta shiga dakin Zaid, kamar ta janyota ta daba mata wuka takeji, zuciyarta Zafi Zafi zafi, kishi kishi kishi.


Yesmin na shiga dakin Zaid ta danne kirjinta, zuciyarta kamar ya fito, tabbas yarinyar nan na son Zaid, ta karanto son Zaid a idanunta, tambayar shine Shin Zaid na Sonta? Waigawa tayi ta kalli Zaid da ke sheme kan Gado, da alama ko asuba beyi ba, kuma duk ta k’are ya banki shegiyar wato World jiya da daddare ba ta san sadda ta daka mata duka a baya ba.


Kamar jira yake yayi firgigit ya tashi ganinta Yamutsutsuke idanunshi, hararshi tayi tace “bakayi sallah ba” yace “Uhm” ta sake galla mai uwar harara tace “ai sai ka tashi kaje kayi” sum sum ya wuce toilet ta samu wuri ta zauna zuciyarshi cike da tunanin Labiba, sai da yayo wanka kafin ya dauro alwala, ya shigo ya kalli gabas yayi asuba.
Ya kallota yafe “ina kwana yas yas kamshi”
Ba ta iya fushi dashi tace “ka kwana ladiya?” Yace “Alhamdulilah” tace “munyi breakfast na san ba zaka ci Abincin cikin gida ba shiyasa ban diba ma ba”.


Murmushi yayi yace “zan hada da kaina” tace “ni yanzu kankia zaka rakani”.
Yace “yadai?”
Tace “lafiya lau, kayana zan kwaso, wai yajin aiki ake”.
Yace “to daga yajin aiki sai a kwaso kaya?”
Tace “to zaman me zamuyi?”
Yace “ku kuma haka kuke?
Tayi daria tace “nidai mu tafi”.
Yace “Okay barin yi breakfast”
Tace “muje mu siya a crispy sai mu wuce”
Yace “Okay muje”
“Wai kai baka da kaya ne sai wannan jallabiyan”
Yace “Yesmmmin mu tafi”
Dariya tayi tayi gaba ya bi bayanta tare da rufo dakin.


A kan idonta suka fito suka tafi, hawaye masu dimi suka ziyarci idanunta.
Jin motsin Aunty Asee ya sa ta goge hawayenta da sauri.
“Baban Amirah be aiko ba?”
Labiba tace “eh wai be kai ga aikowa ba”.
Okay.
Ba da dadea ba sai ga yaro da cefane daga kasuwa
Labiba ta amsa ta gyara kayan miya ta yi blending.
Aunty Aseeyah ta taimaka ta.
Bayan Azahar sun gama tuwo miyan ogu da yaji stock fish da ganda ”
Aunty Aseey tace “maza ki shiga kiyi wanka”.


Labiba tayi wanka tayi alwala, bayan tayi sallah ta shirya cikin wani Swiss Lace black and red.
Ta na cikin shiri Jawad ya kirata yace ya shigo Katsina zai yi Sallah a Masallacin matafiya da ke dandagoro sai ya karaso.


Da kwatance Jawad ya iso Gidansu Labiba, be sha wahala ba don sun taba zuwa Tudun Matawalle da yayyinshi, har k’ofar gida Jawad yayi parking.
Ta fito don tarbanshi.
Sam be ganeta ba, wani irin kyau ta kara, hotunan da take turo mishi kwata kwata basuyi kama da ita a bayyane ba, sai gani yayi ganin da yayi mata a farko bata kai haka kyau ba, MashaAllah, tsarki ya tabbata ga sarkin da ya k’agi wannan hallitar.


Takowa tayi cike da murmushi tace “Assalam Alaikum Jay, barka da zuwa Katsina ta dikko dakin kara” kasa amsata yayi sai murmushin da yake cizga baki zuwa wuy, da hannun ta mishi Alama da Bismillah.


Tayi gaba, ya bita a baya kamar rak’umi da akala, har suka shiga gidan da Sallama, kasancewar ba wuta parlon akwai zafi ya sa ta shimfida musu babban darduma a waje.
Zama yayi suka gaisa sosai. Labiba ta shiga daki tace ma Aunty Asiya su fito su gaisa.
Hijab dinta ta saka suka fito tare, cike da girmamawa Jawad ya gaidata, ta tambayesu ya ya bar su Umma ya amsa da Alhamdulilah. Ciki ta shiga Labiba taje kitchen ta gabatar mai da Abinci a kan tray.


Serving dinshi tayi, Jawad baya cin tuwo, amma yau sai da ya bude ciki ya ci tuwon nan mulmula daya da rabi, zobo da ya fara sha sai da ya shane kofi ya kuma kara, anya baby ba Aunty Aseey tayi abincin nan ba?
Dariya tayi tace “ ta taimaka min da kwashe tuwo da tukawa, amma ni nayi miyana nayi sobona”.
Dariya yayi yace “amma abincin yayi dadi sosai, baby wallahi kin k’ara kyau”
Hannu ta sa ta rufe fuskarta.
Binta kawai yake da mayattaten kallo, be iya surutu ba, be da hayaniya, sai ya zamana ma in ta ga kallon yayi yawa sai ta tambayeshi ina kaza ko ya kaza?.


Jawad miskili ne, kallon kallo da murmushi yafi firan su yawa, suna zaune aka kira Laasar tace “muyi sallah ko?” Yace “eh k’asaru zanyi, amma yanzu zan tafi gidan Baban Usman sai naje na gaida Grannynmu sai naje masauki, anjima zan dawo na gaida Yaya”.
Murmushi tayi tace “to shikenan”
Aunty Asiya ta fito ya mata Sallama, Labiba ta rakashi har bakin Mota.
Tsayawa sukayi suna kallon juna suna murmushi.


Motarta ta danno layin, tun daga nesa ya hango ta tana yashe hak’ora kamar audaga, ita ko kamshi tukinta takeyi ba tare da ta san meke going ba, waigawan da zatayi taga jikin Zaid na kyarma a tsorace ta taka birki tace “Zaid are you Okay?” Kasa magana yayi amma jikinshi ba inda baya rawa, idonshi kan su, Yesmin ta maida idonta kan inda yake kallo.


Kallo daya ta masu ta gano Labiba ce, ta kalli Zaid da ke tafasa a ranta tace menene haka? Kishi kenan?.


Tuni Zaid ya fita daga motar ya nufesu, tafiya yake be san inda yake jefa kafanshi ba, wani abu Jay yace mata da ya sata daria sosai tana kallon gabas ta hango Zaid da ya tunkarosu kamar wani zaki, cikinta ya bada kululu, gabanta ya fadi, jawad ya juya mai baya be san me ke tunkaroshi ba, Labiba kam tsoro da fargaba sun mamayeta, bata san me zaiyi ba, nan take ta tuna karon Yan Bencin Eskaley da AbuSideeq basu kwashe da kyau ba, har yau bataji daga Abu Sideeq ba, tsoro ya sake mamayeta, tuni zufa ya keto mata, ganin yanayin Labiba ya sa Jawad saurin juyawa ga abunda take kallo.
Hango wani yayi ya tunkarosu kamar namijin zaki...
“Me ke shirin faruwa?”


#1love
#DM
#anatare
#FWASonSo
#nagode


Biebee Isa
[14/03 9:35 pm] Biebie: DAN MAKAHO 😉


BABI NA ASHIRIN DA BIYU 2⃣2⃣
(ZANCE 👫 )


"Me kake shirin yi? Meke kake tunani Zaid? Menene haka?" Tambayoyin da ke zuwa mai a kai kenan, daf da su ya tsaya chak, yana kallonsu daya bayan daya kafin ya dawo da kallonshi ga Yesmin da tayi saurin shan gabanshi tare da fadin "Sweetheart, saurin me kake haka?".
Bakinshi ya mai nauyi da k'yar yace "bakomai, dama so nake na rigaki shiga Gida".
Hannunta ta sagala ana shi ta jashi tace "nak'i wayon mu shiga a tare".
Yace "motar fa?"
Tace "na rufeta".


Wuce su sukayi suka shige Gida, da Jawad da Labiba suka bi bayansu da ido kafin suka juyo suna kallon juna. Jawad mamakin abunda ya faru yanzu yakeyi, zai iya rantsewa da Allah cewa wannan tunkarosu yayi, wurinsu ya nufo, to ya akayi ya chanza akalan abun? Menene haka? Ya kalli Labiba da sauri ta girgiza mai kai! Da yake wani miskili ne be tsawaita abun ba sai yace ta shiga gida zai dawo anjima.


Da yake a k'agare take da sauri ta juya ta shige Gida. Jawad ya kira wasu Almajirai biyu ya bude booth yace su kwashe kayan da ke ciki su kai cikin gidan chan, jiki na rawa suka kwaso kayyayakin cikin booth.
Ya basu 200 sabuwa dal, sai da ya ga shigan su kafin ya shige motarshi ya mata key zuwa Gidan k'anin Babanshi Baba Usman.


Isan Zaid da Yesmin BoysQuaters yayi daidai da shigowar yara dauke da kaya nik'inik'i suna shela "Sallam Alaikum wai ance gashi a ba Labiba".
Dakatawa Zaid yayi daka shiga daki ya ga Labiba tayi wuf ta fito ta nufa yaran tace "wai inji wa?" Hade baki sukayi sukace "wani ne a waje a mota".
Labiba ta bude baki tace "tohhhh" karban ledar tayi yaran su ka fita a guje tana waigawa ta hade ido da Zaid da Yesmin, wani mugun kallo ta karanta a Idanuwan Zaid.


Ganin tafasan da Zaid yakeyi ne ya sa Yesmin riko hannunshi ta jashi zuwa dakinshi, labiba tsaye tayi nan ta bisu da idon da ya cika fal da hawaye.
Muryan Aunty Asee taji ta na cewa "mai muka samu?" Da sauri ta mayar da hawayenta ta mik'a mata ledar tare da shigewa daki ta bar Auntyn tsaye a tsakar Gida, Auntyn bata dau komai ba ta biyota baya tare da zazage ledojin kan Gado.


Leda daya kayan Zak'i ne kama daga Chocolates ne kalakala da biscuits cookies irin wanda taga ana talla a MBC2, dayar ledar kuma kayan shafa ne da turaruka masu k'amshi kala kala sai atamfar da taga an rubuta Juilius Holland sai wani Leshi.


A tare suka kalli juna ganin kayan da ke zube kan Gado, Labiba ta budi baki tace "wannan irin kaya da yawa haka? Anya Aunty zan karba kuwa? Gaskia bari ya dawo Anjima zan mayar mai" Aunty tace "uhm uhm, kayan sunyi yawa ga tsada kuma, bari dai yayanki ya dawo a gwada mai, duk mai yace hakan zaayi".
Labiba ba tace komai ba, Aunty Asee ta dauki chocolate diary milk ta fita tare da barin Labiba a daki ita kadai.


Kallonshi kawai takeyi, yana zaune sai ajiyar zuciya yake sauke lokaci zuwa lokaci.
Sosai ta tsura mishi ido, sai da ya lura da kallon da take mishi ya dawo dubanta.
Yesmin tace "KISHI kenan?"
Zaid ya murje idonshi na hagu yace "bangane ba"
K'amshi tace "ba zaka gane ba, ni ai nagane"
"Son yarinyar chan kake"
Borin kunya ya fara "So? Wace yarinya? Ni bansan me kike magana akai ba".
Yesmin ta yi wani murmushi mai takaici tace "ni na san maganar da nikeyi ai, kana son yarinyar chan, ka ganta tsaye da wani, zuciyanka na maka zafi, ranka na baci, bakinka na rawa, kishinta kakeyi".
A hankali yace "I dont know what you are talking about Yas".
Mik'ewa tayi tsaye ba tare da ta kalleshi ba tace "Bari inje Gida" ta fita.
Kiran sunanta yayi "Yesmin"
Ba ta juyo ba, bata tsaya ba ta bace wa ganinsa, bai da k'arfin bin bayanta, bai da karfin dawowa da ita, in shi a matsayinshi na Namiji yaji haka, ita ya take ji? God, me zaiyi yaji dadi? World kawai ya dauko ya zuk'e k'ulli uku yayi shameshame kan Gado.


Tana a daki taji Sallaman Yayanta, shimfida matarshi ta mai a waje ta gabato mai da Abinci, yana ci yana santin dadi chan yace "ba dai bak'on Abuja ya tafi ba" Aunty Assy ta bashi amsa da "zai dawo bayan Isha'i" yace "ya dai ci tuwo ko?" Tayi daria tace "yaci kam".
Daga waje taji Aunty Aseey na cewa "Labiba firdo ma Yayanki tsaraban Jawad".


Sai da ta bata lokaci kafin ta fita jiki a sanyaye "Yaya sannu da zuwa" tsokanarta ya fara yi ta rufe fuska tana daria, bubbude mai kayan Aunty Aseey tayi tace "ka dai ga abun Arziki shine Labiba ke cewa sunyi yawa ko za ta mayar" yace "Aseeyah ba rokonshi akayi ba ai, ko rokonshi kikayi?" Da sauri ta girgiza kai yace "to kinga, abunda zaayi, in yazo anjima, zan yi magana dashi, zan tambayeshi in dagaske yakeyi aure ya kawoshi, tun wuri zan turashi chan gurin su Baba, kar ki manta Alkawarin da nama Baba cewa da kin samu Miji zakiyi aure, kema da amincewarki na da kin samu Miji zaki tsaida Karatu, to in dagaske yake tunda yazo har gida to yaje chan Asalinki ya nemi aurenki ba mu son dogon soyayyan zamani".


Tunda ya fara magana ta sadda kanta k'asa ta ji zuciyarta na wani irin zugi, Aure? Aure? Da wani ba Zaid ba? Ya Illahi. Sai da ta tabbatar yayan ya gama magana ba tare da tace komai ba ta tashi ta shigewarta daki, Aunty Asee ta k'ara da cewa kasan amincewar Yanmata masu kunya shine tashi ba tare da sunce komai ba".
Yayan ya murmusa yace "MashaAllahu, bari dai yazo muji".


Jawad kam yana barin Gidansu Labiba ya wuce Gidan Uncle Usman gidan 'kanin babanshi, Aisha tace "Ya Jawad fa tun dazun ka iso sai yanzu muke ganinka?" Antisco tace "sai da yaje ya ci girkin diyata" Jawad yayi murmushi yace "kyaleta Antisco, so take na fara ganinta kafin naje na ga matata?" Aisha tayi shewa tace "Allah ya baku hakuri yaya, shegia Besty an samu Miji a sama" harara ya zabga mata yace "wallahi ki kayi wasa sai na ma Yaya Majeed budurwa" hararar ta rama tace "shi kuma makaho baya iya budurwa da kanshi sai ka mashi?" Antisco dai tayi ta daria, sai da ya huta kafin yaje gidan Kakansu ya gaidasu kafin ya tafi masauki, yayi sallahr Maghrib ya jira Isha'i kafin ya kira Labiba yace gashi nan zuwa.


Tunda ta bar Gidan Alhaji Ali Zaki ta koma gida ta kulle knta a daki take ta riskar kuka, ranta a jagule, ta isa gida cike da tashin hankali, yanayin da ta gani a tare da Zaid dazu, yanayin da ta dade take buri ta ganinshi a ciki amma a dalilinta, ta dade tana mafarkin Zaid na Kishinta, Zaid na shiga yanayi a dalilinta, Sai gashi yau a gaban idonta Zaid ya shiga yanayi ta kan ‘yar karamar yarinya da take aji 1, yau Zaid dinta ke kishin wata ba ita, Allah ka kawo mata sauk’i, Allah ya yaye mata wannan damuwa nata, Allah ya iyakance mata Son maso wanin da takeyi, rannan taci kuka har ta gaji.
Er Rabi ta sameta tana kuka sosai hankalinta a tashe take tambayarta waye ya sa ta kuka, wani mai gangancin ne ke sanya tilon diyarta kuka.
Tarayota gabaki daya tayi jikinta tace “Baby me ya sameki? Me aka miki? Waya tabaki?”.


Da kyar ta samu tayi magana, “Mummy Zaid ba ya sona, ba ya sona Mummy, duk son da nake mishi be sona sai wata yarinya wanda da kyar ta kai shekara 17 a duniya, mummy ni Zaid zai ma haka? Bayan duk abunda na mishi?”.
Tuni Er Rabi ta shiga huci kamar Zaki tace “donuwar Dan Makaho ke zai ma haka? Don har yanzu na barshi yana jan numfashi a doron kasa, saboda kene fa baby, saboda ke, amma har yana iya yaudararki? Ya zabi watan ki? Lallai Dan Makaho, wannan shine babbar kuskuren da ka tafka a rayuwa, sa yesmin kuka shine ajalinka”.


Wani tsalle Yesmin tayi ta duro gaban Mamarta tana haki tace “Mummy, wallahi aa, kar ki sake, kar ki taba yin wani abun da zai taba min Zaid, kar ki sake wallahi, wallahi ki ka taba Zaid wallahi daidai yake da rasani, Mummy kikayi ma Zaid wani abu ba zan taba yafe miki ba kuma sai na kashe kaina”.


Da sauri Er Rabi ta girgiza kai tace “aa baby, ba ma zai kai ga haka ba, ina kokarin kare matabanki da cin mutuncin da ya miki, ba zan dauka ba, ba zan iya dauka naga ana saki kuka ba Yesmin”.
“Mummy ina mugun son zaid fiye da kaina, rayuwana na cikin garari in har Zaid ya mutu ko ya bace, ba zan iya rayuwa babu shi ba, shine farincikina, Mummy ina sonshi fiye da rayuwa da kanta”.


Kalaman Yesmin sun fara ba Er Rabi tsoro, tana tsoron irin mutuwar son da diyarta ke ma mak’iyin aminiyarta, wannan lokacine da zata zabi farincikin diyarta ko kuma na aminiyarta.
Lallashin Yesmin ta fara yi, da k’yar ta samu tayi shiru, tace “zan baki wani kwalli, ki shafa in zakije gidan Shafaatu, da kin hada ido da shi, zai ji duk duniya bai da abunda yake so sama dake, zai so ki fiye da uwar da ta haifeshi”.


Yesmin tayi murmushi tace “Mummy, bana bukatar irin wannan Son daga gun Zaid, ba na son kazamar soyayya irin wanna, bana son kyamataccen so irin wannan, bana so Zaid ya so ni ta hanyar nan, ina So Zaid ya so ni daga zuciyarshi, da niyyarshi da yardanshi, Mummy Zaid ne farincikina, farincikina shine farincikinshi, in kuma kina son ki ganni cikin farinciki kar ki sake yi ma Aunty Shafaa aiki a kanshi, shi kuma farincikinshi itace Labiba? To bari a samo mishi farincikinshi” magana Yesmin kawai takeyi kamar baa hayyacinta ba.


Er Rabi kallon diyarta kawai takeyi cike da tsoro, fargaba da mamaki, ya zaayi diyarta ta ma wani mahaluki irin wannan Son? Ta yaya? Kuka yazo mata da sauri ta fita daga dakin Yesmin ta rufe tana fargaban rasa diyarta.


Lokacin da Jawad ya iso Gidan Mallam Muhammad ba wuta a Gidan, kuma basu da Generator, amma gidan babu duhu saboda hasken Gidan Alhaji Zaki ya shigo tsakar Gidan, ga kuma farin wata, ga kuma rechargeable lantern.
Yaya Muhammad ya tarbe Jawad don Labiba na cikin daki Aunty Aseey ta tsareta kan sai ta chanza wanka da kwalliya, to tayi wankan shafa takeyi.


Zaune suke a kan Carpet daya, Yaya Muhammad yace “Mallam Jawad ka ga Gidan sai duhu, sai hakuri” kan Jawad dai a k’asa shi bai ma san me zaice ba, yo shi ina ruwanshi da gidansu tunda yarinya yake so?.
Baban Amira yace “Yaya sunanka? Kuma kai dan ina ne?”
Jawad ya hadiya kafin yace “Sunana Jawad Abu Shamsu, ni ne na uku a gidanmu, ina da yayyi biyu da k’anwa daya, iyayena ‘yan Unguwar Alkali ne a nan garin amma muna Abuja zaune, ina aiki a wani Company kuma ina bussiness”.


Baban Amira ya jinjina kai yace “Mallam Jawad naji tak’aiceccen tarihinka, to an dai san wata alakar mace da namiji wanda ba muharamai ba bai wuce aure ba, amma duk da haka ina son ji daga bakinka, mai ke tafe da kai? Meye k’udurinka a kan kanwata Labiba?”.


Jawad yace “Ni Sonta nakeyi da aure, kuma na ma gaya ma Mamana”. Baban Amira ya murmusa daga jin shi ya san akwai shagwaba a tattare da shi Auta ne, yace “Yaron Mama, Mama za ta maka aure yanzu?” Murmushi yayi don

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login