Showing 27001 words to 30000 words out of 68203 words

Chapter 10 - JARABTA 1 TO END Book Complete Document hausa novels by Maman Abdul Shakur--.txt

M Shakur   

29 Dec 2024

8283

her once haka dawani thief ya kwace mata jaka and daga nan I think mun sake haduwa twice ko I think, ashema sisters neku, Kinga ko Allah ma wants me to marry u tunda har yasa nasan yar uwarki" tashi tayi tsaye tace "bye" da sauri shima ya tashi yace "but I don't wanna go now" hawaye ne yacika idonta tadan kalleshi sanan ta dauke kai, ahankali yace "okay I will go, Plz don't cry" dan matsowa yayi ya tsaya a gabanta ya mika mata chocolate din yay murmushi yace "u have to eat it before i go" bakinta yakai hakan yasa ta kawad dakai, tsayawa yay yana nazarin fuskarta kaman something is wrong ahankali yace "Are you okay?" murmushi tayi tadan bude baki hakan yasa yay wani murmushi daya bayyana fararen teeth dinshi yasaka mata chocolate din abaki ta gutsiri kadan sanan ya cire yana murmushi, dadan sauri tabar wajen murmushi yayi saida yaga tai sama sanan yafita daga dakin tareda kai sauran chocolate din bakinshi.
Ahankali ta bude dakinsu jikinta yay mugun sanyi ganin Farida tsaye a tsakar dakin idanunta sunyi jajir alamun taci kuka, ahankali ta maida kofar ta rufe ta shigo dakin tace "Faree wlh ban.." hannu Farida ta daga mata tace "banason naji komi daga gareki" nuna kanta tayi in so much pain tace "nizaki yaudara? Ni Islam ur own blood, ur only sister, daga nace yaje ya taimaka miki ranan a school shikenan har kin nunama su Abba shi aka samuku rana ko" share hawayen daya zubo mata tayi tace "no wonder ko waya zakiyi dashi bakiyi agabana, ko dazuma bayi kika gudu sabida karnaji mekuke cewa, duk idan nai maganar shi saidai kiyita cemin na manta dashi, na shareshi, my God u fooled me Islam" sosai Islam ke kuka tana girgiza kai tace "bahaka bane wlh" ta matso kusa da ita zata tabata wani tsawa Farida ta daka mata tace " don't touch me you cheat! Mara Imani, mai bakin hali, trusting and liking u sune biggest mistake din danayi arayuwata wlh, mai bakin hali kawai kamar uwarta" tsayar da kukan datake tayi ta kalleta tace "Faree dan Allah karki kara zagin min mama kinga tariga tamutu ba kyau" nunata Farida tai da yatsa tace "an zagadin, ance uwarki kika biyo da wanan bakin halin" mari Islam ta kaimata abaki hakan yasa Farida ta taba bakinta jini tagani hakan yasa wani zuciya ya dauketa da haushin kwace mata superman datayi ta chakume Islam, da sauri Islam data mugun tsorata dan ganin idanun Farida ta rike hanun Farida inda ta chakumeta tace "yakuri dan Allah bada gangan na mareki ba" buga Islam tayi da bango, Islam tai wani wahalallen kara, duk iya karfin ta takasa ture Farida, kara Fizgo Islam tayi daga bangon tawani nakata akasa kan center carpet din tsakiyar dakin ta finciko gashin Islam tanaja, azaban da Islam taji yasa ta dana mata cizo a hannu da sauri Farida tasaki gashin nata tana duba hanunta, azabure Islam tamike zata gudu waje Farida ta tadiyota da kafa jikake dimm tafadi tai kara, Farida da zuciya tariga ta debeta ga shaidan daketa zugata tai kan Islam tahau ruwan cikinta tana kima kaman ta sami kayan wanki, da kyar Islam ta iya kai hannu tana kokarin kama gaban rigar ta.
[6/18, 10:30 PM] Maman Jedda: *JARABTA*


Maman Abd Shakur


40 & 41


Wani mugun kallo ya watsama Faridan batare daya damu da maganan mutanen wajen ba ya juya zai tafi, kafarshi Islam ta rike gam gam tareda daura fuskarta akan gwuiwar shi tafashe da mugun kuku harda shesheka tace "bakace kana sona ba, inhar kanasona son gaskiya, so sabida Allah to ka yarda ka auri Farida, dan girman Allah do it for me" fincike kafarshi yayi yakara juyawa zai tafi da sauri tabishi da gwuiwa ta kama kafarshi again gam sanan ta dago kai ta kallai suka hada ido, ahankali ta saki kafarshi tahada hannayenta tace "inhar kanasona da gaske, ka aure ta karta kashe kanta, yar uwata ce bazan taba yafema kaina ba idan wani abu yasa metaba, dan darajan Allah am begging you" yanda take kuka tana rokanshi yasa ya tsugunna ya dagota sama kallon cikin idonta yay yace "stop crying" ahankali ta tsayar da kukan tana kallon fuskarshi yace "abinda kikeso kenan na auri Farida?" Ya tambayeta "jama'a zataci shinkafar fa" da sauri Islam ta juya ganin Farida na kokarin kai shinkafar bakinta ta daga hannu tace "stop, stop Faree ya yarda, zai aureki" kallon ta Farida tayi sanan ta kalli Khaleel din tana goge hawaye, Islam ta kallai tace "please tell her ka yarda" yadade yana kallon fuskar Islam din kafin ahankali ya juyo ya kalli Faridan da kyar ya iya cewa "yea na yarda I will marry u" murmushi Islam tayi tana goge hawayen dataji ya zubo mata, Farida takara goge hawayen dasuka ki dena zuba tace "and kayarda dazaran na sakko zamuje gida direct ku fadama Abba kun yarda" yadade yana kallon fuskar ta sanan yace "yea, now come down" yasa hannu ya danne mata ladder, murmushi Farida tayi ta kabar da shinkafar rice din dake hanunnata tafara sakkowa saida ta sakko kasa ta fada jikinshi ta rungumeshi tana kuka sosai tace "I love you so much Mk, wlh Ina mugun sonka, Allah ya jarabceni da sonka, I love you my superman" ihu mutanen wajen sukeyi suna tafi da sauri Islam ta sanya hijabin ta tarufe fuskarta jin kuka yazo mata sosai, da sauri ta juya zatabar wajen karaf taji anrike hanunta hakan yasa ta dago da rinannun idanunta taga Khaleel ne wanda Farida ta shige jikinshi tana kuka yana kallon kwayar idonta, fizge hanunta tayi da gudu tabar wajen tai bakin titi Keke napep ta tare ta shiga ciki tacemai suje sosai take kuka mai Keke na tambayan ta lpy.


Cireta daga jikinshi yayi batare daya kalli fuskarta ba yace "mutafi" yana gaba tana biye dashi suka karasa har wajen motar ya shiga itama ta bude gaba ta shiga sai murmushi take tana kallon fuskarshi kaman yau tafara ganinshi, kunna motar yayi sukabar wajen, a kofar gida suka ganta zaune akan bencin mai gadi, parking yayi suka fito ta kalli Farida tace "dama kunake jira mutafi wurin Abban" da sauri ta bude gate ta shiga batare data kalleshi shiba Farida ta kallai tace "muje my superman" Atare suka shiga cikin gidan direct falon Abba sukayi suka shiga da sallama, yana zaune tareda Mum dake tayashi arranging some business papers. Daga Abba har Mum din binsu sukai da kallo ganin yanayin idanun yaran nasu.


Gaban Abba Islam taje ta tsugunna ahankali tace "Abba dan Allah kahada Farida da Khaleel aure bada niba please Abba, don't ask me why amma dan Allah kahada su aure ni banaso" tunda take maganan Khaleel yay folding hanunshi akirji yana kallonta idanunshi sunyi jaa, with so much confusion Abba ya kalleta sanan ya kalli Farida da Khaleel dake tsaye sanan yadawo da kallonshi ga Islam yace "wai meke faruwa ne Ummi, wanan wace irin magana ne kikazomin dashi haka, meke faruwa?" gyara zama Mum tayi tace "Alaji zan fadama" dan shiru tayi tana kallon fuskar Islam sanan ta kalli Alhajin tace "ni dama ban fadamaka bane sabida banason kaga kaman na tsangwami Islam ne, ka tuna fadan da ita da Farida sukayi kwanakin baya, to ashewai Islam ce bayan Farida tagama bata labarin soyayyar ta da Khaleel shine Islam taje ta kwacema Farida dake son Khaleel sosai Khaleel" shiru Abba yayi yana nazarin maganar Mum sanan ya kalli Islam yace "haka abin yake Ummi?" ahankali ta gyada kai ganin yanda Abba ke kallonta yasa tace "am sorry Abba" batare daya kalleta ba yakira Farida, ahankali Farida tazo gabanshi ta tsugunna Abba yace "haka zancen yake?" gyada kai tayi sanan tace "Abba inason Khaleel sosai shine ta kwacemin shi" tafashe da kuka tareda daura kanta akan cinyar Abba, shiru Abba yayi sanan ya kalli Islam ahankali yace "kinason Khaleel ko baki sonshi, tell me the truth?" ahankali ta juya ta kalli Khaleel da ita yake kallo sanan ta kalli Mum data jeho mata wani uban hararan, kallon Abba tayi sanan ta girgiza kai tana kokarin hadiye kukan dake zuwan mata tace "a'a bana sonshi" da sauri Abba yace "dama kinyi hakane dan ki bakan tama yar uwarki rai ko?" da sauri ta girgiza kai, dago kai Abba yayi ya nunama Khaleel kujera, kasa zama yay akujeran ya zauna akasa, ahankali Abba yace "Wakake so cikin su wazaka aura? Banason tauyema kowa hakkin sa, yaran zamanin nan kuncika matsala wlh, ka fadamin gaskiya Khaleel wakake so acikin su wazaka aura?" kallon Islam yayi hadamai hannu tayi sanan ta girgixamai kai tana hawaye da sauri ya dauke kai, ya kalli Farida dake kallonshi kirjinta na bugawa idanunta sun cicciko da hawaye ahankali yace" "Farida" murmushi Abba yayi yace "shikenan Allah Sanya albarka, Allah muku albarka dukan ku saikaje ka sanar da iyayenka" Ahankali yatashi yafita daga dakin, sauka yayi yafita daga gidan ya shiga mota ya daki sit din motar yafi sau dari, wani bakin ciki mara misultuwa yaji yanaji da kyar ya iya tuka kanshi yakai gida.


Abba ya kalli Islam yace "mesa kika aikata irin abin nan Islam?" Mum tace "Alaji bawanan ma kadai ba da Farida tamata magana shine fa takifa mata mari ranan harda fasamata baki, haba haka ake abu a duniya, daga yar uwarki tabaki labarin saurayin ta saikibi takasa kije ki kwace mata shi, kasan shi namiji wawane hala saisa lokacin ya biyemata ya yarda har aka turo, yanzu dai alhaji tunda komi yay daidai basaika hukuntata ba nariga na yafemata, faridama ta yafe mata shikenan magana ta wuce a cigaba da shagulgulan biki zamu aurar da ya" Ahankali Abba ya sauke ajiyan zuciya yace "hakane kutashi kutafi" fita sukayi daga dakin Farida ta bangajeta ta shige dakin Mum binta tai da kallo kafin ta wuce dakinsu a daddafe ta fada gado taci kukanta tai bacci.


Manya manyan hajiyoyi masu gyaran jiki Mum ta daukoma Farida nan fa aka fara gyara amarya ciki da waje idan kunga Farida en tai mugun kyau bakin fatarta har kara walkiya take, ko tak baya hadata da Islam idan Islam zata wuni tana mata magana bazata kulata ba hakan yasa kullum Islam na daki, Maman Miemie nema idan tazo aiki takan dan kawomata Miemie ta dauketa suyita wasa, Khaleel bai kara zuwaba, Farida bata damuba tunda wani zubin yanadan picking call dinta suyi magana daya biyu ya katse.


Yau saura sati daya biki yaune aka kawo akwatin Farida saitin goma sha biyar, su Umma da Mujiba datai kini kini da rai dawasu kawayen sune suka kawo inda Mum da kawayenta lecturers suka tarbesu akaci akasha, akasha guda, dazasu tafi aka basu tukuici. Da daddaren ranan Anty Hindu tadawo daga dubai da kayayyakin daki data siyo anata murna Koda Islam tazo gaishe ta kallonta tayi daga sama har kasa tace "ke ciwo kikayine haka wanan rama" murmushi tayi tace "eh amma naji sauki" tsaraba Anty Hindu tabata sanan ta wuce dakinsu ta kwanta.


Washegari da safe Abba yafita da wurin kasancewar yanada aiki, Mum ce ta turo akwatinan Farida ta shigo dasu dakin Anty Hindu one by one tace "ga akwatin Farida nan Anty?" kallonta Anty Hindu tayi cike da mamaki tace " Farida Kuma wace Faridan?" kama haba Mum tayi tace "au Abban su bai fadamiki ba, ai Anty Kwai ne yafashe gaskiya ta futa, ashe fadan nan da yaran nan sukayi kan Khaleel ne, wai Islam kwacema Farida Khaleel fa tayi, shine da kanshi Khaleel din yay tattaki yazo yafadi ma Abba shifa Farida yakeso ba Islam ba" tunda take maganar Anty Hindu ke kallonta tace "Khaleel din yace hakan" "eh" murmushi Mum tayi tace "ga akwatin ki duba kisa mana albarka" tabe baki Anty Hindu tayi tace "nayafe fitanmun dasu daga daki" tabe baki mum tayi tafita dasu tana kunkuni tace "yar bakin ciki kawai" sosai Anty Hindu taji ranta ya baci da zancen, wanan wani irin abune.


Family Khaleel kodaya fadan musu abinda ke kasa basu wani damuba kasancewa sunsan Faridan dama.
Yau thursday da kyar Yusuf ya tirsasa Khaleel yatashi suje gidan su kaima Farida kudin fati, da wasu yan abubuwa, da kyar yatashi ya shirya dan wlh bayason yamaje gidan balle yamaga Islam shiryawa yay cikin shadda Light brown shadda daya mugun amsan shi ba karamin kyau kayan sukamai ba sai uban kamshi yake, fara tsayawa sukayi sukai isha'i sanan suka tafi.
Farida taci uban lalle dan gobene walima tasanya wata atampa da tasha uban stones, kallon Sameer dake kusa da ita tayi ganin kiran Khaleel ya shigo wayarta tace "jeka cemusu su shigo falo Ina zuwa" fita yay da gudu, ta zauna agaban mirro tana shafa hoda.


Ahankali take sakkowa daga stairs sanye da doguwar riga na atampa jada baki ta daura gyale black akai, so take taje kitchen ta dafa Indomie kamshin turaren dataji yasa ta daga kai hada ido sukayi daidai suna shigowa falon hanunshi rike da Sameer tsayawa yay chak yana kallonta hakan yasa Yusuf ya Kalli inda yake kallo, da sauri takarasa sakkowa ta shiga kitchen, jingina tai da fridge ta dafe kirjinta jin wani abu ya tsayamata awuya, tayi kusa 20 sec ahaka sanan ta shiga store ta dauko Indomie guda daya da egg daya tafito, kamshin turaren shi taji da sauri ta daga kai ta kallai suka hada ido ganin ya kulle kofar kitchen din yasa ta ijiye kwan da Indomie akan fridge tajuya da sauri ta bude kofar dazai satada da backyard tafita, babu haske sosai a backyard din dan kwan fitilar wajen ya mutu hasken wata ne kawai ke haska wajen, tafiya ta soma yi da sauri zata zaga, hanunta taji ankama da sauri ta juyo fizgota yayi da karfi fuskarshi a daure yasata abango yana wani irin kallon fuskar ta, ahankali yake matsowa har ya matso kusa da ita sosai wanda gab din tsakanin su baifi tsawon yatsa ba dan tanajin saukar numfashin shi, sosai kirjinta ke bugawa hakan yasa ta kawad da kanta gefe, ahankali yakai hannu ya kama habarta ya juyo da kanta kin kallonshi tayi ta saukar da idanunta kasa, hanunshi daya ya daura a bangon wajen dayan kuma na habar ta murya chan kasa yace "look at me, kin kasa kallonane sabida kinsan u are forcing me to do dis?" sosai kirjinta ke bugawa, lumshe ido yayi sanan ya budesu akanta ahankali yace "bakyacin abinci ko, look at your neck" yasa hannu yana shafa kashin wuyarta buge hanunshi tayi hanun nata ya kama da sauri yadan matse hakan yasa tai yar kara tana yatsine fuska yace "it hurt ko?" gyadamai kai tayi, dan murmushi yayi yace "zuciya hurt more than this sau dubu dabara sabida abinda kika sata tayi" yakarashe maganan tareda sakin hanunta yana nuna mata zuciyar shi da yatsa, dan shiru yayi yana kallon fuskar ta dan har yanzu taki yarda suhada ido, hannu yakai yarike habarta yadaga kanta kaman mai rada yace "kinfiso na auri yar uwarki ina dawainiya da sonki araina ko" shiru tamai, kasa daurewa yayi ahankali yahada goshin su yana kallon idonta, hakan yasa itama ta dago idanunta dasuka cika da hawaye ta kallai bakinshi taga yay motsi yace "I love you Islam" fashewa tai da kuka sosai, hannu yakai ya share hawayen dake zubowa batare daya cire forehead dinshi daga nata ba, ahankali ya saukar da yatsar tashi akan lips dinta, shafa su yayi yana kallon idonta, hannunta tasa ta bigemai hannu, lumshe ido yayi ya maida fuskar shi ta gefen kunnenta ta, goga mata sajen shi akumatun ta yayi wani yarrr tajj yabi kowani gashin fatarta sabida yanda gashin sajen suka tattaba fatar, kokarin tureshi tafara yi hakan yasa ya cigaba da gangaro da sajen nashi har wajen lips dinta, ahankali ya juyo da kanshi daidai ta wajen hakan yasa lips dinshi yahadu da nata.


Wlh kun daman saisa namuku typing. Gaskiya Naga Farida tafi fans, lol.
I love guys.
[6/22, 7:53 AM] Maman Jedda: *JARABTA*




Maman Abd Shakur


47 & 48


Yakamo hanunta yarike gam yana yar dariya, turo baki tace "kasaken" make mata kafada yayi yaja hanunta har gaban wardrobe, wani madaidaicin black hijab yaciro ya warware yasaka mata sanan yarike mata hannu ya kalleta yace "banason ana kallon mu goody bag dina muje naraka ki" akunyace ta dauke kai, tare suka fita daga dakin suna zuwa dining tafara kokarin kwace hanunta sabida mutanen datagani su kusan five ga manyan kuloli kusan 5 dasuka ajiye a tsakar falon, kin sakinta yay ahaka suka shigo falon, kasa daina kallonta su Ihsan sukayi, tana tsaye agefenshi tadan kallesu tace "ina kwanan ku" manyan matan guda biyune suka amsa da lpy lau, harara ya watsama su Ihsan yace "ku baku iya gaisuwa bane" atare suka taso sukazo inda take tsaye Ihsan ta mika mata hannu tace "ni sunana Ihsan his sister, welcome to our family" ahankali tai murmushi ta bata hannu, Ilham ma tace "sunana Ilham welcome to the family" murmushi tamata tace "thank you" Fa'iza ma tace "nice Fa'iza welcome and u are very very cute wlh" murmushi tai tace "thank you" hanunta Ihsan tarike tace "ga masu lalle nan mum tace amiki idan angama za'a kaiki chan family house ne, muje afara yimiki sai muyi dishing abinci kiyi breakfast ko" gyada musu kai tayi sukaja hanunta hakan yasa yasaketa, dan juyowa tai ta kallai tai raurau da ido, girgiza mata kai yayi alamun no, ya kalli Ihsan yace "ku kullan min da ita kuma, ko kuda karku bari ya tabata, bari naje" hanun yadaga mata alamun bye kunya taji yakamata ta dauke kai da sauri su Ihsan sunata mata dariya. Harara ya balla musu sanan ya juya yafita daga dakin yana kallon fuskar ta.
Lalle aka fara zizara mata, daya nayin na hannuwa dayar kuma na kafafu, Ihsan ta debo abinci tana bata abaki, Ilham kuma da Fa'iza sun kwanta akasa suna bata labarin Khaleel suna tafawa suna ihu, bakaramin tunamata da Farida sukayi ba, sosai taji tana kewan yar uwan nata da kyar ta iya tahana kanta yin kukan. In less than awa daya lallen ya bushe da aka mata sabida sanyin ac dakuma fanka dasuka kunna, wankewa akayi ba karamin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login