Showing 12001 words to 15000 words out of 68203 words

Chapter 5 - JARABTA 1 TO END Book Complete Document hausa novels by Maman Abdul Shakur--.txt

M Shakur   

29 Dec 2024

8286

yabama Khaleel dariya, cup din shayin ya ijiye yadau one slice bread ya shafa cheese spread dake dakinsu yaci, da tissue ya share baki yay murmushi jin Goggo da Yusuf nata daru yadau wallet dinshi yasa a aljihun bayan wandon shi yafita daga dakin.
Wani babban barbing saloon yaje aka mai aski da gyaran fuska ba karamin kyau yayiba sanan yabiya kudin yabar shagon, ganin he is running out of fuel gashi baida enough cash atare dashi yasa yay parking agaban wani ATM ganin akwai 2 people infront of him yasa ya tsaya ya jingina da motar shi yana kallon titi, ihu yaji hakan yasa ya juya da sauri, wata yarinya yagani ta fashe da kuka tana nuna wani guy dake gudu ga jakar ta a hanunshi tana cewa barawo ya kwacemin jakana.
[6/11, 9:19 AM] Maman Jedda: *JARABTA*




Maman Abd Shakur


14...
Tashi tayi tazo gabanshi da sauri, hawayen dake zubo mata ta share cikin muryan kuka tace "please help, ya kwance min jakana, credentials dina and everything are inside" baice mata komiba ya koma cikin mota ya kunna motar yabi guy din daketa gudu yana kokarin shiga wani layi gaban shi yasha da mota ya fito da sauri Guy din yajuya zai kara guduwa, taku biyu yay ya riko guy din ranshi abace da daga hannu zai wanka mai mari da sauri yaron yabashi jakar yace "dan Allah mallam kayakuri wlh yunwa yasa nai hakan, kayakuri dan darajan Allah" shiru yayi dan yaron yabashi tausayi duka duka bazai wuce 22 ba, anatse yace "idan kanajin yunwa kamata yayi kaje kafita ka nemi aiki kasamu kaci abinci stealing daukar abun wasu ba kyau, hakki zai bika" wallet dinshi yaciro daga aljihun bayan wando ragowan cash din dayake dashi yaciro yabashi sanan yabashi card din Abba yace "kaje address din company nan zansa abaka aiki kaji" tsugunnawa yayi yaron yanamai godiya murmushi yamai yace "tashi katafi don't worry" daidai lokacin ta iso wajen dan tun dazu take tsaye tana kallon abinda yafaru. Tafiya yaron yayi shikuma Khaleel ya mika mata jakar tareda bude mota ya shiga, yana kokarin tada motar ne tace "thank you so much, am grateful, ammm by the way am Farida Maikano and you?" dago kanshi yayi ya kalleta sai alokacin ma ya lura da fuskarta black beauty ce yarinyar tana sanye da doguwar riga na lace orange dakeda rantsin baki, ta yana black gyale akanta, murmushi tasake mai tace "u really help me wlh credentials dina duka suna ciki nagode ko" murmushi yadan mata batare dayace komiba ya kunna motar zai tafi da sauri takara matsowa jikin motar kaman zatai kuka tace "baka fadamin name dinka ba and u are going is dat fair?" murmushi yasake mata ganin yanda takeda surutu sai ta tunamai da Ihsan ahankali yace "just call me MK" kaman mai tunanin tace "MK, MK Mk?" tasake kallonshi alamu tambaya ahankali yace "zaki iya kirana Muhammad" murmushi tamai tace "wow MK nafiso, Muhammad na tsofaffi ne" murmushi yasake yi dan dukta cikashi da surutu yace "bye" girgiza kai tayi tace "please dan tsaya kaji dan Allah" Jakarta ta bude taciro wani memo ta rubuta number ta da sauri ta yagi paper ta mikamai tace "please please ka kirani this is my number kaji, dan Allah" ajiye mai tayi ajikinshi ganin yaki miko hanunshi sanan tamai bye, tafiya yayi haka tabi motar da kallo baki abude saida motar yabace sanan tace "gosh he's so handsome, jibi muscles dinshi bumbum, awwwn my superman" Ta wani lumshe ido.
[6/12, 1:16 AM] Maman Jedda: *JARABTA*




Maman Abd Shakur

15 &16


ATM gallery din yakoma yaciro cash sanan yawuce gida.
Wuraren 4 suka shigo gidan, dawani irin gudu Farida taje ta fada jikin Mum tace "oyoyo Mummy na mundawo" murmushi Mum tayi tace "wanan murnan na lafiya ne" ta kalli Islam dake kokarin bude bottle water tasha dan kishi takeji tace "Ya school din Islam hope kunbama Olayinka credentials dinku danace" gyada mata kai Islam tayi sanan takafa goran abaki, tashi daga jikin Mum Farida tayi tace "Mum yunwa nakeji sosai" tai hanyar kitchen taji andaka mata tsawa "my friend will you leave there! wuce sama kije kafara wanka ki canza kayan jikin ki kafin kinemi abinci, yara duk anbi anbata su" takarashe maganan tana huhhura hanci tana kallon Mum dako daga kai batayi ba, saima marking scripts din dake gabanta da takeyi, turo baki Farida tayi ta juyo tai stairs hakama Islam tabi bayan ta sum sum sukazo suka wuce ta sukai dakinsu.
Dakinsu suka shiga duk ransu abace, suka zauna akan gado, murmushi Farida tayi tafada jikin Islam tace "no Anty Hindun nan bazan bari tai running mood dina yauba am so so happy" baki a sake Islam ke kallonta irin lafiyan ki lau, dariya tayi sosai sanan tasa hannu ta Fizgo Islam suka fada kan gadon a kwance tace "Islam yau I met my superman, wlh Islam yanada mugun kirki, kinsan nasauka daga mota a bakin ATM ba ke Bala ya wuce dake school ba, shine fa bayan naciro kudi wani barawo ya fizge jakana ya gudu, haba saiga giant huge gallant superman dina ya kwatomin jakan, and ko, baima barawon komiba saima kyauta dayamai ya bashi card wai yazo address din zai bashi aiki" ajiyar zuciya ta sauke tace "Sis kingan shi wlh kyakkyawane sosai, black arab, gashida kirki, he is so cute" ba karamin mamaki abin yabama Islam ba tace "Auwal dinki fa Faree?" tsaki taja tace "please karki karamin maganan shi nidai" murmushi tasake yi sanan ta bude ido ta kalli Islam daketa kallonta cike da mamaki tace "gist me jor dazu ina hall Fahad yakirani wai yanaso yazo gida kin hanashi, mesa kika hanashi yazo yaga Dad?" kaman zatai kuka ta tashi tana zage zip din sket din dake jikinta na material tace "kinga Anty Hindu tazo banason anything dazaisa tasani agaba wlh banason masifar ta" da sauri Farida tace "to shikenan saiki hanashi zuwa?" turo baki tayi batace komiba ta zame sket din ta ninke, tashi Farida tayi tace "shikenan karki gayamin gaskiya zurfin ciki saiya miki illa wataran" tai hanyar bayi da sauri ta rike hanunta hawayen datake kokarin boyewa ne yadan zubo da sauri ta share cike da damuwa Farida tace "talk to me Islam" ahankali ta zauna abakin gado tissue ta dauko ta share fuskar ta sanan tace "yasami wani job offer ne a Dubai kuma in two months time akace yay resuming yafara aiki, shine yake damuna yanaso yazo gida ya gaida su Dad, shiwai so yake muyi aure yatafi dani chan, so yake ai auren nan da 2 months, and because nace karyazo shine yaketa fushi jiya ko kirana baiyiba text kawai yamin jiya wai yatafi Abuja yin some papers zai dawo ran monday" "and all this while baki fadamin ba kikai shiru tun jiya nake lura dake kaman abu nadamin ki nadaiyi shiru, wai mesa kike hakane why are you my sister idan nima zaki dingamin zurfin cikine" girgiza kai tayi ahankali tace "am sorry Faree bansan tayaya zan fara fadan miki bane" hugging dinta Farida tayi ta shafa kanta tace "stop crying" share fuskan tayi sanan ta saketa ahankali tace "tun muna SS3 kuke soyayya da Fahad, baki taba bari yazo gidaba kibarshi yazo yaga Dad koma mezai faru ya faru" girgiza kai tayi tace "yanzu fa muka fara University sai kawai nai maganan aure, Anty Hindu da Dad zasuce dama aure nakeso maisa nabari ya kashe min kudi a school, am scared" tureta Farida tayi tace "banza kekika sani sabida tsoro zakije kiyi asaran love dinki, bari naje I will tell mum" tai hanyar kofa da sauri Islam tarike mata hannu tace "dan Allah karki fadama Mum, we will sort it out ran monday idan ya dawo, zance yafara aikin tukunna nan gaba sai muyi auren" sosai ta mugun bama Farida tausayi hakan yasa tace "okay shikenan amma karki bari abin yaja muku matsala" gyada mata kai tayi tadanyi murmushi sanan ta wuce bathroom da gudu jin Anty Hindu ta kwalla musu kira.


Tun jiya da daddare duk ringing din da wayar ta zaiyi da gudu take dubawa taga ko bakuwar number ne amma duk wayanda tasani ne, babu sallan dazatayi da bazatai addu'a Allah yasa ya kirata ba, ko bayi zata shiga wayar na hanunta dan Karya kira yaga baa dagaba. Koyau da safe data tashi saida tai mafarkin shi hakan yasa tana bude ido ta duba wayarta bataga any miss call ba tsaki taja duk ranta adagule.
Batai niyyar zuwa Saturday lecture da aka samusu ba amma sabida yanda duk taji batajin dadin komi ne yasa ta tashi tai wanka ta shirya cikin wani brown Abaya da aka bishi da stones ba karamin kyau yamata ba gyale ta yana akai Islam dake nannade cikin bargo tace "ina zaki?" turare ta fesa sanan tadau jaka ta kalli Islam tace "inada Saturday lecture ne, bye baby girl" ahankali Islam tace "bye" tafita tayi dakin Mum ta shiga tamata sallama sanan tafito Bala driver ne ya dauketa suka fita, jakar ta tabude tasake ciro wayar ganin har yanzu babu miss call yasa ta ijiye wayar akan cinyar ta ta dafe kai dan bakaramin daci taji zuciyar ta namata ba, sun kusa kaiwa school ta tuna bata dauko calculator ba sabida bakin ciki gashi calculation course zasuyi hakan yasa tacema Bala "malam Bala please danyi parking agaban super market dinan bari nasiyo abu" gaban wani babban super market Bala yay parking purse dinta da waya kawai ta riko tafito ta shiga ciki, bangaren littatafai taje nan taga calculator ta dauka, wajajen su ice-cream tayi tadanyi tsaki maybe zata dan rage zafi da ice-cream din, fridge din tabude ta ciro ice-cream ta juyo zata tafi wajen biya kaman ance ta daga kai ta hango Khaleel tareda Yusuf sunci sky blue shadda gizna da aka musu dinki half jumper ga wata hula kube sun kafa akai sai kace zasuje biki suna kwasan su snacks da littafi dan zasuje ma Fa'iza visit a boarding school ne. Wani irin farin ciki ne ya lullube zuciyar ta ajiye abubuwan tayi a kanta din accounter tace "am coming" da sauri tai wajen su da murmushi akan fuskarta tace "Hi MK" Yusuf ne yafara juyowa saikuma Khaleel daya dago kai ya kalleta yana kokarin tuna fuskar, kamar zatai kuka ta kalli Khaleel tace "shine baka is kirani bako MK" sai alokacin ya tunata, dan murmushi yay yace "how you?" har cikin ranta takejin muryar shi da yanda yay maganan tace "fine" Yusuf ta kalla sanan ta kalli Khaleel din tace "dan uwanka neko" gyada mata kai yayi Yusuf ta kalla tace "ina yini" cikeda fara'a yace "Lpy Lau sis, yasu Mum nd Dad" purse din hanunta taketa wasa da igiyan sanan tace "suna lpy" dan kallon Khaleel dake kokarin dauko gwangwanin Milo tayi tace "shine baka kirani bako MK" ajiye milon yay a cart sanan yace "sorry battery na was flat jiya ne saisa" murmushi tamai har cikin zuciya sanan tace "okay" Yusuf ne yace "how about nabaki number shi dan ya iya mantuwa kina ganinshi haka, incase ya manta baikirakiba sai kimai flashing ko" kama rigar Yusuf yayi tabaya yanda bazatai ganiba hanunshi Yusuf ya bige ya shiga karanto mata number tana saving sanan ta kallesu tace "okay kayana nachan bye" ta daga musu hannu cike da fara'a, bye suka mata sanan tawuce tatafi, turashi Yusuf yayi yace "at least be a gentle man kabiya mata kudin abinda tasiya" zaiyi magana Yusuf yakara tureshi hakan yasa yajuya yatafi badan son ranshi ba, murmushi Yusuf yay ya dunkule hannu ya saki a iska yace "yess".
ATM card taciro tana shirin biya da POS ya mika nashi, ahankali ta kalli gefenta ganin shine yasa wani dadi ya lullubeta, samata akai a leda aka bata ta karba sanan ta juyo cike da dan kunya tace "thank you, am going to school karnai latti, bye" hannu yadaga mata yana mata calm murmushi dake melting heart tai hanyar fita security ya bude mata kofan.
[6/12, 1:16 AM] Maman Jedda: *JARABTA*




Maman Abd Shakur


17...
Hararan shi Yusuf yayi daya dawo yace "shine ko abani labari, who is she?" dan yatsine fuska yayi yace "a girl I met yesterday" da sauri Yusuf yace "and??" tsayawa da tafiya Khaleel yayi ya kalleshi yace "and wat, nace jiya muka hadu I just helped her out ne da wani guy ya kwace jakarta shikenan" murmushi Yusuf yay suka cigaba da tafiya chan yace "she is nice" ahankali yace "yea ga shegen surutu ba" dariya Yusuf yayi batare daya kara cewa komiba sukaje suka biya kudin kayan sanan suka wuce school dinsu Faiza.
Tsabagen farin cikin daya mamaye zuciyar ta batamasan me aketayi a class ba dan murmushi kawai take tana kara kallon special number Khaleel datai saving da my superman.


Haka tai wasting 4 hours lecture dinan tunanin Khaleel barinma yanda yawani zo ya mika ATM card yabiya kudin nanne yafi tsumata.
Koda daddare Islam bacci tayi ta barta ido biyu sabida jira take Khaleel ya kirata ganin har 11 bai kirata ba yasa ta dialing number shi har tagama ringing bai dauka ba, sake kira tayi nanma bai daukaba wani iri taji sosai ahankali ta ijiye wayar taja bargo ta kwanta ta rufe ido da kyar bacci ya dauketa.


"Goggo jikan ki yay kawa fa" ajiye maficin datake fifita musu wani dan kasko data daura ruwan shayi akai anan tsakiyar falon ta tayi tace "kai da gaske Yusufa" kallon Khaleel dayay kaman bejishi ba yayi yace "gashi nan ki tambaye shi, wlh Goggo yarinyar badai hankali ba, ai in sha Allah watarana zan kawo miki ita ki ganta" sosai Goggo taji dadi, batace komiba ta sauke shayin daketa uban kamshi ta zuzzuba musu a cup, dauka yayi yay sipping kadan sanan ya ijiye saida yadanyi sanyi sanan ya dauka ya shanye ya goge baki ya tashi ya Kalli Yusuf yace "zanje Gym" kafin Goggo takirashi yafita daga dakin da sauri dan bayason surutun su, part dinsu ya wuce ya shirya cikin kayan gym, wata gym singlet ne dake kama jiki mai ruwan toka tadan budemai kirji sosai yasaka, sai dogon wandon shimin, yasa sport shoe na Nike, yadau wani dan madaidaicin towel ya daura akafada yadau car key da wayar shi, da sport bottle dake cike da warm water na glucose and lime yafita.


"ke Farida, Farida, wai bataji nane" tana zaune a dining itada Islam suna hira taji Anty Hindu na kwala mata kiran nan kaman ana yaki, da sauri ta tashi tana amsawa, sama tayi tai sallama tabude dakin Anty Hindu dake zaune da Dad suna magana, kudi Anty Hindu ta mika mata tace "ki kira bala ya kaiki inda nake siyo fruit a kasuwa yasan wajen kisiyo, babu fruits agidannan yau" karban kudin tayi tajuya tafita daga dakin, dayake tariga tai wanka tunda sassafe yasa Hijab dinta kawai ta dauko da wayarta ta sakko, dining tazo tasami Islam na taya Mum yanka kubewa ta kalli Mum tace "Mumy Anty Hindu ta aikeni kasuwa plz Islam tarakani" Mum ta kalli Islam tace "zaki?" gyada kai tayi "tashi kutafi to, amma kuyi sauri" da gudu Islam tai sama Hijab ta dauko milk daya kai mata gwuiwa tadaura akan atampa dayake jikinta tabita suka fita waje bala ya dauke su suka tafi. Suna zaune a motar takara dailing number Khaleel saida wayar ta kusa katsewa ya dauka, ajiyar zuciya ta sauke mai kara har saida Islam ta kalleta, dawani irin calm voice tace "good morning Mk" ahankali yace "ya kk" murmushi tayi daya bayyana fararen hakoran ta tace "Alhamdulillah" "gud" yafada tareda yin shiru itama shiru tayi, hayaniyar dataji ata bangaren shi ne yasa tace "ina kake haka da ake hayaniya sosai?" wlh kawai dan bayason wulakanci ne saisa amma dis girl is really disturbing him, kaman bazaiyi magana ba chan dai yace "gym" da sauri tace "wani gym?" shiru yayi hakan yasa ta kalli wayar ganin yana kan line har yanzu yasa ta mayar kunne tace "hello are you there" batare daya amsa ba yace "infinity gym, bye gat to go now" Ya katse wayar. Bala ta kalla tace "dan Allah Bala dan kaini infinity gym" da sauri Islam ta kalleta tace "ba kasuwa aka aikemu ba" yarfe hannu sama tayi tace "dalla forget kasuwa, I wanna see my superman face tukun" tabe baki Islam tayi ta juya ta cigaba da kallon hanya, agaban wani babban building da aka rubuta infinity gym ajiki bala yay parking. Hannu Islam ta daura akan kirjinta sabida yanda taji yana bugawa.
[6/13, 8:48 AM] Maman Jedda: *JARABTA*




Maman Abd Shakur


18...


Bude motar Farida tayi ta zagayo ta bangaren Islam ta bude kofar tace "zomuje ku gaisa da superman dina" girgiza kai Islam tayi tace "sabida Anty Hindu ta hadamu ta mana rashin mutunci ko, nidai ban kudin Bala ya kaini na siyo" wani dadi ne ya kama Farida takama kumatun Islam taja sanan tamata peck tace "luv u Islam dina, idan kun siyo ko, kubiyo ku daukeni saimu koma tare" karban kudin Islam tayi tareda mata murmushi taja kofan motar ta rufe sanan ta kalli Farida yanda take washe baki yasa tace "at least adan rufe bakin ko ta superman" murguda baki tayi sanan tajuya security dake bakin wajen ya budemata ta shiga tana waige waige, babban wajene da sanyin ac ya cika ko ina, bangare daya gym ne sai dayan bangaren da ake saida any type of fruit salad da smoothies and fresh veggies da coffee. Waige waige tadinga dan wajen da dan mutane ga wani calm music dake tashi kadan kadan, hangoshi tayi akan treadmill machine yana gudu, karasawa wajen tayi ta zaga ta gabanshi ta tsaya ahankali tace "good morning Mk" saida yadanji tsoro daya ganta agaban shi kaman anjehota daga sama, wanan wace irin yarinya ne, murmushi kawai yamata batare dayace komiba yacigaba da gudu abinshi, wasa takama yi da bakin hijabin ta fuskar ta yay wani iri, yanda take wasa da bakin hijabin saiya tunamai da Eesha, ahankali yasa hannu ya kashe machine din sanan yadau towel dake kan kafadar shi ya share zufan dayayi sanan ya sakko yadan wuce ta ya dauko dumbell yadawo ya zauna akan kujera, kujeran dake kusa dashi ya nuna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login