Showing 48001 words to 51000 words out of 68203 words

Chapter 17 - JARABTA 1 TO END Book Complete Document hausa novels by Maman Abdul Shakur--.txt

M Shakur   

29 Dec 2024

8276

Abba yay daga dakin dan kiran abokin nashi kan maganan ambulance flight din hakan yasa Mum ta fuskanci su Abba ahankali cike da girmamawa tace "Alaji dan Allah kitayani rokon shi ya yay hakuri ya yafema Farida tadawo gida, bata dawani uba daya wuce shi, ina zataje yau kwana uku kenan daga yau ta kwana agidan wanan kawa gobe agidan waccan, nasan tai babban kuskure wanan abun datama yar uwarta amma tai nadama wlh sai neman gafara take, kaga yahanata tama shigo dakin nan balle tanemi gafarrar yar uwartata, dan Allah kuyakuri kuyafe mata Alhaji, yarinta da rashin hankali sukasa ta aikata wanan mummunar abin" takarashe maganan tana matse kwalla, ajiyar zuciya Abban Khaleel ya sauke yace "in sha Allah zamu mai magana, gaskiya hukuncin yay tsauri, ai hannunka baya rubewa ka yanke kayar korarta daga gida zai iya jefata cikin wani halakar, tunda dai tai nadama ta yarda tai kukkure ai shikenan komi ya wuce, ita kuma Allah yabata lafiya" yay maganar yana kallon fuskar Islam dake bacci abinta akan cinyar Ammi. Fita sukayi daga dakin hakan yasa Anty Hindu ta zubama Mum wani irin mugun harara, dauke kai Mum tayi tana goge ido.


Washegari wuraren 10 suka shigo airport din, bangaren private jet terminals suka tafi, sukai parking mota suka fiffito, yana sanye cikin kananan kaya Jean da t-shirt fara, yafito da Islam dake wheelchair Anty Hindu ta shiryata cikin light kayan kanti pink skirt da riga, an samata hula, tsugunnawa yay agaban ta yamata peck a kumatu tareda share mata wuya da soft towel sabida yanda miyau yabata mata jiki yay murmushi yace "you will be fine kinji wife" tashi tsaye yay ganin su Abba da kowa sun fiffito, Yusuf kuma ya gunguro akwatinan guda biyu, tafiya duk suka fara shikuma yana turata har suka kai gaban jirgin da sauri nurses din cikin jirgin suka sauko daukar ta sukayi awani gado suka shiga da ita ciki Ihsan ta rungume Ammi tana daga musu hannu ta shiga, murmushi Abban Islam yay yace "Allah maka Albarka Muhammad, kaje Allah ya kiyaye hanya Allah kaiku lpy" ahankali yace "Ameen" Ya rungume Ammin shi sosai fuskar shi ta shafa sanan tace "take care of my two daughters kanajina ko" gyada mata kai yayi sanan ya daddaga musu hannu yajuya ya shiga cikin jirgin sukuma su Abba sukabar filin jirgin, ahankali jirgin ke tafiya harya daga.
Kan kujeran dake kusa da ita ya zauna hanunta yarike yakai kirjinshi ya rungume yana kallon fuskarta, dayar hanun kuma yana shahshafa goshin ta dashi, kadan kadan take bude ido tana kallonshi har bacci yay gaba da ita.


Karfe 6 na yamma suka sauka jirginsu ya sauka a UK saukowa sukayi aka shigar dasu motar ambulance din datazo daukan su aka tafi dasu asibitin, har lokacin hanunta na sakale cikin nashi yana kallon fuskarta dan bacci takeyi har yanzu, suna kaiwa hospital din doctors suka karbeta akai ciki da ita sanan suka zauna, wayarshi ya ciro ya chanza line zuwa old Sim dinshi na UK yana chanza wa ya kunna wayar yay dailing wani number bayan sunyi magana ya kashe ko 10min ba'ayi ba wani bature dan yaro dabazai wuce 20 ba yazo jakunkunan su ya amsa sanan yacemai ta harshe turenci yakaimai gida sanan ya bashi kudi yaron yatafi, Ihsan ta kallai tace "Ya waye shi" murmushi yamata yace "wani yarone tun Ina school na sanshi, errand boy ne, yanada kirki" tashi yayi yace "lemme get something for you" restaurant yaje coffee kadai ya siyoma kanshi ita kuma yasaimata snacks sanan yadawo yabata ya zauna, Dr Omprakash ne yafito yakirashi hakan yasa ya bishi office, murmushi Om yamai ya mikamai hannu suka kashe sanan ya nunamai kujera yace "ka zauna" zama yayi sanan Om yace "I have good news" dan murmushi yayi tareda sauke ajiyar zuciya ya gyara zama Om yace "zata warke, yanzu dai for now step by step zamu dinga daukan treatment dinta, target dinmu na farko bakinne which for sure zata warke, we will be able to stop d drooling and kumburin komi zai dawo daidai sabida tasamu ta dinga shan maganin dazai warkar da intestine nata tasamu tana mikewa, den daganan ne zamu fara duba abinda ke hanata magana inma any damage ne za'ayi surgery komi ya dawo daidai in sha Allah" ajiyar zuciya ya sauke tareda mikamai hannu yace "thank you so much Dr" murmushi yayi yace "zaka iya zuwa ka ganta kasan 7 ake koran visitors and kasan hospital dinan ba'a bari kowa ya kwana da patient, so jeka ganta kafin 7 tayi" murmushi yay yatashi yafita daga dakin. Ahankali ya bude dakin datake ciki, wata nurse yagani tana saka mata safa akafa an chanza mata kaya zuwa kayan asibitin gaishe dashi nurse din tayi sanan tafita, karasowa jikin gadon yayi yaja kujera ya zauna ya daura kanshi akan cinyarta yana kallon fuskar ta.
[6/26, 4:58 PM] Maman Jedda: *JARABTA*




Maman Abd Shakur


61 & 62


Yafi minti biyu ahaka sanan ya saketa ahankali yana kallon fuskar ta dan taki yarda su hada ido, murmushin gefen baki yayi sanan yadau teddy yarike tareda rikemata hannu daya yace "let's go" ahankali ahankali take tafiya yana binta ahaka har suka fita daga dakin hasken wuta bau data gani awajen yasa ta daga dayar hanunta taka kokarin kare fuskarta dan tadade rabonta da haske, sai kakkauda kai take, daukarta kawai taji yayi hakan yasa ta kalleshi afirgice, gira daya ya dagamata hakan yasa tadanyi murmushi tamaida kanta ta kwantar akan kirjinshi, ahaka ya dinga tafiya yana kallon fuskar ta harya fito da ita sanan yasata acikin mota Ihsan nata musu dariya sanan ya koma ciki asibitin ya karbo magungunan yafito ya shiga gaban motar mai motar ya tada suka tafi, sai kallonta yake ta madubin kanta ta daura akan shoulder Ihsan dake nunama ta wani game datake bugawa, ajiyar zuciya yadan sauke sanan ya maida kanshi yana kallon hanya. Agaban gidan su mai taxi yay parking Ihsan ta fito tabude mata kofa ahankali ta fito ta tsaya satan kallonshi karaf suka hada ido yana kokarin bama mai taxi kudi da sauri tadan dauke kai kaman bashi take kalloba, akwatin su Ihsan taciro daga bayan mota shikuma ya karaso wajen zai dauketa ta girgiza mai kai kaman zatai kuka, hannunta ya rike yasa key yabude kofar suka shiga ciki, ko ina agyare tsaf tsaf sai kamshin room freshener dakin keyi, dakinshi ya bude ya shigar da ita Ihsan kuma tawuce dakinta. Akan makeken gadon dake dakin dayaci zanin gado fari da bargo fari ya zaunar da ita sanan ya kunna na'urar dake sanya daki dumi sabida sanyin garin, bayi ya wuce ya shiga ya dauro alwala jin ana kiran sallan magrib dan anguwan akwai massallaci, fitowa yayi daga bayin yana kokarin warware hanun rigar jikinshi daya nannade sabida alwala dayay ya kalleta yace "bari naje massallaci, kema tashi kije kidauro alwala ki salla" fita yay dadan saurin jin antada, a kitchen yaga Ihsan na kokarin dafa abinci hanyar fita daga dakin yay yace "kibar girkin nan zan taho da takeaway" kashe gas din Ihsan tayi ta wuce dakinta dayin salla dama wlh tagaji.


Da sallama ya turo kofar dakin ya shigo yana kallonta ganin ko motsawa batayi daga inda yabarta ba, maida kofar yay yarufe yakaraso cikin dakin yazo kusa da ita stool din gaban mirror yajawo ya ijiye agabanta yazauna akai, hanunshi yakai yafara warware vail din kanta anatse yace "kinyi sallan?" girgiza mai kai tayi, karasa warware gyalen yayi ya ciro ya ijiye akan gadon yasa hannu yadaga habarta hakan yasa ta kallai murya chan kasa yace "kingaji ko?" gyadamai kai tayi akasalance dan batada karfi ko kadan, kafarta ya dauko ya daura kan cinyarshi yace "sorry, dazaran kinci abinci zaki sami karfi" takalmin ya cire ya ijiye akasa sanan ya dauko dayar kafar ya daura akan cinyarshi ya cire takalmin yana kallonta, ahankali ya ijiye kafar akasa sanan ya mike tsaye ya dauketa tadan tsorata dan bata zaci ita zai dauka ba hakan yasa kirjinta yabuga tana zazzaro idanun tana kallonshi atsorace, murmushi yamata sanan yajuya yay hanyar bayi da ita batare daya dena kallonta ba itama haka, Karan bude kofa dataji ne yasa ta janye idanunta daga nashi tai maza ta juya bayi taga ya shiga da ita, akan wani irin kujeran datagani abayin kaman bishiya ya zaunar da ita sanan yahada ruwa a bathtub maidan zafi sabida sanyin da akeyi sanan yadau goran sabulu ya tsayaya a ruwan ya rufe ya maida ya ijiye, wani irin kamshi ne ya gauraye duka bayin tashi yayi yadawo inda take zaune ya mikar da ita tsaye hannu yadaura akan sweater jikinta yana kallon fuskar ta yace "zokiyi wanka zakiji dadin jikinki" kokarin cire mata sweater yake hakan yasa ta daura hanunta akan nashi tana girgiza mai kai kaman zatai kuka, mayar da hanunta kasa yayi sanan ya karasa cire mata sweater ya wurga kan laundry basket da sauri ta tsugunna ta rungume kanta duka jikinta na rawa sabida shimi kadai ce ajikin nata, ahankali shima ya tsugunna ya shafa kitson kanta daya soma tsufa yace "bakiso kiyi wankan nekuma?" da sauri ta dagamai kai, dan murmushi yasake yi yace "okay tashi am going" juyawa yayi yafara tafiya hakan yasa ta mike tsaye tana goge yar kwallan daya zubo daga kai tayi suka hada ido da sauri ta tsugunna tana kakkare gaban rigar ta, dariya yay yajuya yafita I daga bayin, dadduma ya shinfida mata sanan ya bude wardrobe wani light half gown iya cinya haka yaciro mata mai spaghetti hand jane rigar tanada tauchi sosai dan cotton ce, yadauko mata hijabi da plain zani dan ta daura tai salla ya ijiye mata sanan ya kalli agogo ganin takwas da kwata yasa yafita daga dakin dan zuwa massallaci.


Tafi minti sha biyar a ruwan zafin dan ba karamin dadi yamata ba rabon datai wanka me kyau haka ai tama manta, saida tagama sanan tafito ahankali tana dan daddafa bango towel din data gani fari sai kamshi yake ta dauka ta dauro tadan bude kofa kadan ganin baya dakin yasa tafito, ahankali tadan tsugunna tadau rigar data gani akan dudduma tasaka ba karamin kyau rigar yamata ba bayi takoma ta ijiye towel din sanan tafito ta daura zanin tasaka hijabi tai salla magrib da Isha tadan dade zaune sanan ta tashi ta cire hijabin da zanin ta ijiye gaban madubi taje ta zauna dan mai takeso ta shafa jin jikinta yawani bushe kayau, mai ta dauka ta tsiyaya ahannu ta shafa a fuska, hannun rigar tadan saukar sabida tashafa man akafada daukar man tayi ta tsiyaya ahannu tafara shafawa akafadan hannun dataji akan nata yasa ta dago kai da sauri danko kadan bataji shigowan shi dakin ba, dawowa ta gabanta yayi tareda ijiye hannayen nata yana kallon fuskar ta, saukar da nata kasa tayi sabida wani irin kunya dataji tanaji gashi yawani cika mata ido, daukar man yayi batare dayace mata komi ba yakai kan kafadar nata ya tsiyaya kadan sanan ya ijiye, slowly yakai hanunshi ya daura akan kafadar da sauri ta kulle runtse idanunta gam sabida yanda sanyin hanunshi yamata wani irin shocking ajiki, gently yake massaging man all over shoulder har zuwa cikin bayanta hakan yasa tadan matso gaba tareda dan juyar dakai sabida yanda takeji, fito da hanun yayi daga bayan yasake daukar man ya shafa mata a hannayen ta, kafarta ya dauka ya daura akan kafarshi yadan ja rigar zuwa sama kadan jin shiru baifara shafaman ba yasa tadan bude ido ta kallai hada ido sukayi hakan yasa ta mayar da nata ta rufe tareda daura hanunta akan rigarta ta rike sosa, man ya dauko ya tsiyaya akan cinyar yasa hannu ya shafa mata man harya gama ya mayar ya dauko dayan ma yay haka sanan ya ijiye, numfashin shi dataji gab da fuskarta yasa tasake bude ido kadan takallai da sauri ta mayar ta rufe ganinshi gab da ita yanamata wani irin kallo kirjinta sai bugawa yake sosai, saukar bakinshi dataji akan nata yasa tai baya luuuu zata fadi da sauri ya riketa tareda sakin bakin ya dangwali dogon hancin ta yace "fear fear, muje kici abinci kisha magani" ahankali tabude ido ta kallai makemai kafada tayi sanan ta juyar dakai tamai pointing hijabin ta dake kan dadduma alamun yabata, yiyayi kaman bai gane metake nufi ba ya mikar da ita tsaye da sauri ta labe abayan shi tana tattabe baki kaman zatai kuka ta rike rigar shi gam tana turashi da dayar hannun, dariya yayi yafara tafiya tana rike dashi abayan shi haryakai jikin gado, tray daya ajiye na abinci dayayo musu ya daga batare daya juyoba yace "to zauna kici abincin, ni am going outside ma basai kinsa hijabin ba" fitowa tayi daga bayanshi ta zauna tana kallon fuskarshi tray ya ijiye kusa da ita batare daya kalleta ba sanan ya dauko maganin dazata sha ya ballo mata ya mikamata karba tayi sanan tadau ruwan goran dake kan tray din tana kokarin budewa kasawa tayi sabida batada karfi ko kadan hakan yasa ta mikamai batare daya kalletaba ya karba ya budemata sanan ya mikamata shan maganin tayi hakan yasa yajuya yafita daga dakin, dakin Ihsan ya shiga ya tarar tana bacci ga takeaway dataci tabarshi awajen girgiza kai yayi kawai ya kwashe sanan ya kashe mata wuta yarufo mlata kofar.
Yadade yana magana da Ammi saida yagama ya kwanta akan kujeran yana kallon news a CNN wurare 11 yatashi ya kashe tv tareda rufe kofa sanan yawuce ciki, dakinsu ya shiga akan gado ya ganta kwance hakan yasa yawuce bayi yay wanka yaduro alwala yafito jallabiya ya saka yadawo gaban mirror ya feshe jikinshi da turare karan turaren ne yatada ita daga baccin datafara kadan ta bude ido ta kallai dadduma dataga ya shimfida yahau kai yasa ta sake lumshe ido tareda gyara kwanciya abinta tacigaba da bacci.


"hey" taji yana shafamata fuska ahankali ta bude idonta dasuke cike da bacci saidai bata iya ganinshi sabida duhun daya cika dakin, hanunshi taji akan cikinta yana shafawa cikin wata irin murya dabata saba jinshi daitaba yace "ina kemiki ciwon aciki koya dena duka?" dagamai kai tayi, ahankali taji yajawota jikinshi bedside lamp ya kunna amma saiya mayar da wutan zuwa dim sanan yajuyo dakai ya kalleta ganin tanason ta kwace kanta yace "kin tuna ranan dakika ce Ya Khaleel I love you" murmushi tayi sabida yanda yay maganar was funny, kara jawota jikinshi yayi yahade kanshi da nata yana kallon fuskarta murya chan kasa yace "kin tuna?" dan murmushi tayi ta janye kanta daga nashi taja bargo ta rufe fuskarta, bargon ya fizge hakan yasa tai yunkuri zata juya da sauri yarikota hakan yasa ta kallai shima ita yake kallo sunkai kusan 3min ahaka ita tafara janye nata idon daga kanshi ta juyamai baya taja bargon tarufa dashi harkai sabida idonshi namata wani iri, shima bargon yaja ya rufa dashi harkai birkitota yay tajuyo tana facing dinshi yanda taga idanunshi sun chanza launi ne yasa ta maza zata juya rikota yayi tareda matso da kanshi saitin fuskarta ahankali yay whispering "I love you Islam, bari nadan baki wani labari" kawai saukar bakinshi taji akan nata tun tana zaton irin dai normal light light kiss din daya saba matane sai taji nayau daban ne, wani irin kissing dinta yake kaman yasami abinci hakan yasa tafara kokarin kwace kanta but rashin karfin dake tattare da ita bai barta ba, sosai ya shiga mata wasu irin wasanni dake birkita ta hakan yasa jikinta yafara rawa, hanunshi acikin rigar ta yasa tafara kokarin tashi dan matseta yay kadan ahankali yace "labari zan baki wife relax".
[6/27, 7:33 PM] Maman Jedda: *JARABTA*




Maman Abd Shakur


63 & 64


Wani irin hot romance yake mata kaman wani mayunwaci, sosai take kuka kaman zata shide hawaye ko kaman anbude pampo hakan yasa ya saketa tareda tashi ya zauna abakin gadon yafi minti biyar ahaka sanan yatashi ya shiga bathroom, da sauri tadau rigarta daya yar akasa ta saka tasakko daga gadon hartana neman faduwa tafita daga dakin da sauri, dakin Ihsan ta shiga ta kunna wuta kan gadon tahau ta kwanta agefen Ihsan dake bacci taja bargo ta lulluba kirjinta nabugawa sosai kaman zai fito.


Yadan dade a bathroom din daga baya yafito daure da dan towel a kwankwaso hanunshi Kuma rike da karami yana goge fuskarshi daga kai yay ya kalli gadon ganin batanan yasa yafita daga dakin falo yafara zuwa ganin bata wurin yawuce dakin Ihsan hangota dayay kan gado kusa da Ihsan tawani lullube da bargo har lokacin jikinta bai dena rawaba yasa yadan saki karamin murmushi maida kofar yay yarufe musu yakoma dakinshi.


Ihsan ce tafara tashi ganin Islam kusada ita yasa abin yabata mamaki tashi tai ta shiga bayi ta fito daure da alwala sanna ta tashi Islam din tace "jekiyi alwala" Ahankali ta tashi daga kan gadon ta shiga bayi Ihsan kuma takabbarta salla, bayan ta idar tai azkar sannan tafita danta daura musu breakfast afalo suka hadu da Khaleel sanye da jallabiya yadan dafe kanshi da sauri tace "Ya Khaleel bakada lpy ne" dan yatsine fuska yayi sanan yace "just headache" "ayya sorry, Ya Khaleel inaso natafi fa ance munada test a school next tommorow" zama yay akan kujera tareda jinginar da kanshi yace "maisa yanzu kike fadamin to" komawa tayi cikin kitchen din tabude drawer tace "nima jiya da daddare wata course mate dina take fadamin damuke chatting" dan girgiza kanshi yayi jin yanda ciwon ke damun shi yace "okay bari naduba in akwai flight yau da daddare ko gobe saina miki booking" tashi yay daga kan kujeran ya shiga ciki kofar dakinsu ya bude ganinta akan dadduma yasa ya shiga dakinsu laptop ya dauko yafara searching flight to Nigeria luckily yasami wanda zai tashi yau by 10 nadare dan babu gobe shiya mata booking sanan ya ijiye laptop din akan kujeran yatashi yahau kan gado yaja bargo yadan rufe kafanshi so yake yay bacci sabida yanda kanshi ke kwankwasa cikin kankanin lokaci bacci yay gaba dashi.
Sanye da hijabin Ihsan tafito ahankali tabude kofar ta shiga dakin nasu ta mayar ta rufe kadan kadan take tafiya ganin bacci yakeyi, wajen wardrobe taje ta bude

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login