Showing 24001 words to 27000 words out of 68203 words
Chapter 9 - JARABTA 1 TO END Book Complete Document hausa novels by Maman Abdul Shakur--.txt
cikin sanyin murya yace "is it paining you?" gyada kai tayi tana yarfe hannu tana hurawa batare data dago kaiba dan gabaki dayan hankalin ta nakan ciwon, dago kai tayi da sauri ta kalleshi da katon bandejin dake goshinta da sauri ta saukar da rigarta ta rufe kafafun ta, dan murmushi yayi sanan ya zauna abakin gadon yana fuskan ta hararan shi tayi tace "waikai duk inda nake sekazo, tracker kake amfani dashi ne? Wlh ko kafita daga dakin nan kona kirama Abbana nahadaka dashi komame zai faru ya faru" murmushi yasake yi sanan yace "how are you feeling now?" dauke kai tayi ta turo baki, sosai yake kallonta sake juyo dakai tayi ta kalleshi tace "wai bazaka fitaba sai su Abbana sunzo, okay bari na kirasu" bude baki tayi zatai ihu yadaura hannu akan lips dinshi alamun tai shiru, kasa magana tayi kaman wacce yama magic saima dauke kai datayi daga kallon dayake mata jitake kaman ta makeshi, hanunshi yasa a aljihun wandon shi yaciro wayarta ya mika mata juyowa tayi tana ganin wayarta ta karba da sauri akuma dan rude tace "a ina kasamo wayata?" baice komiba yatashi tsaye yana kallonta yace "waye My heartbeat" da sauri ta kallai sanan ta harareshi tareda murguda mai baki tace "meruwan ka and kafita daga nan" kallon cikin idonta yayi yace "well I told him karya sake kiranki because am ur husband to be" kwalalo ido tai ta kalleshi da so much pain a idanunta tace "Fahad din nawa ka fadanma haka?" gyada mata kai yayi yace "yes" azuciye ta juya tana waige waige pillow dake bayanta ta raruma ta jefamai da duka karfin ta ya chafe yana murmushi har saida hakoranshi suka bayyana daidai lokacin Anty Hindu da Abba suka shigo, Abba yace "Ummi Khaleel din kike bugama pillo mutumin daya taimakeki dabadan shiba da Allah kadai yasan mezai sameki" da sauri ta kalli fuskarshi, dan murmushi yamata sanan ya tako yadan duka ya ijiye filon abayanta ahankali yace "I will come and check you tomorrow, I love you" yay maganar ta yanda ita kadai zata iyaji ya juyo ya Kalli Abba da Anty Hindu yace "Abba saida safen ku" addu'a sosai da godiya Abba da Anty Hindu sukamai sanan ya juya zai fita daga dakin dan waigowa yay ya kalleta daidai lokacin itama tadan dago kai suka hada ido hannu yadaga mata alamun bye, kawad dakai tai da sauri murmushi kwance kan fuskarta.
[6/17, 6:38 PM] Maman Jedda: Novels
*JARABTA*
Maman Abd Shakur
32 & 33
Kaman mai rada yace "I love you so much, zuciya ta bazata iya jure rashin kiba, nasan baki sanni ba but please give me a chance, ina sonki sosai" dan hawaye taji ya gangaro mata, girgiza mata kai yayi ahankali yace "will u marry me please" dan lumshe ido tayi tareda dagamai kai maganar Anty Hindu dataji tawaje ya mai do da ita hankalin ta da sauri ta tashi ta zauna ta kawad dakai kirjinta na bugawa sosai tashi tsaye yayi shima yana kallon fuskarta, bude kofa Anty Hindu tayi ta shigo ita da Dr, dubata Dr yayi sanan yace "Hajiya babu wata matsala, nan da yan kwana biyu yan ciwukan nan zasu warke zaku iya tafiya" Anty Hindu tace "to nagode Dr, bari nakira Bala yazo ya dauke mu" da sauri Khaleel yace "basaikin kirashi ba nina kaiku Hajiya" yay maganar yana kallon fuskar Islam da har yanzu taki kallonshi, "to shikenan, ke tashi mutafi" ahankali ta mike tsaye tadau Hijabin ta tasaka shiya fara fita sai ita da Anty Hindu dasuka fito suna biye dashi abaya kofar baya ya bude musu suka shiga sanan yarufe sanan yakoma gaba yabude motar ya shiga ya kunna yafara driving har suka fita daga hospital din, ta mirror gaban mota yaketa kallonta amma taki dago kai saima wasa da yatsun ta da taketayi, har cikin compound ya shiga dasu suka fiffito da sauri tai cikin gida dan bataso su sake hada ido, Anty Hindu ce tamai godiya cike da fara'a da addu'a sanan ya kunna mota yafita daga gidan.
Afalo taga Farida ta zauna taci uban tagumi tsakanin jiya da yau duk tai zuru zuru tana ganin ta ta taso da gudu ta rungumeta tsam tsam sakinta tayi ta kalli fuskarta tace "sannu Islam ya jikin?" dariya ma tabama Islam hakan yasa tai dan dariya tace "ke dalla am fine ciwo fa kawai naji, Ina Mum?" jiki a sake tace "tana daki" tace "bari naje na gaishe ta" sama tayi saida ta gaida Mum tamata ya jiki sanan ta wuce dakinsu bayi ta shiga tai wanka da ruwa mai dumi sanan ta fito, light kaya tasa tazo ta kwanta akan gado dan bacci takeso tayi ta lumshe ido, fuskar Khaleel tagani yana mata murmushi da sauri ta bude ido tajuya dayan gefen tasake lumshe ido tuna sanda ta daura fuskar ta akan hanunshi tayi, bude ido tayi da sauri ta tashi ta zauna tareda jan uban tsaki dan mugun haushin kanta takeji tayaya ma tai hakan wat was wrong with her, waya ta dauka tasake dailing number Fahad bai dauka ba, message ne ya shigo wayar ta bude bakuwar number ce hakan yasa ta bude "I love you so much. Khaleel" wirgi tai da Wayan akan gado tareda yin tsaki "mutum sai shegen naci anaci"
Misalin 9 na dare Yusuf ya shigo part dinsu ya sameshi yana zaune yana daddana waya gefenshi kuma tea ne daketa kamshin su citta, zama Yusuf yay kusa dashi yadau tea ya kurbe hakan yasa ya kalleshi batare dayace komiba, murmushi Yusuf yayi yay gyatsa sanan yace "idan ma masifa zakamin naji amma kafara zuwa Abba na kiranka" filon dake kan kujeran yadau ka ya naka mishi akai sanan yabar dakin. Sallama yayi ya shiga dakin Abban, shi kadai ne sanye da farar jallabiya idanunshi acikin medicated glass yana karanta littafin addu'oi samin waje yay ya zauna akasa. Saida Abba yagama sanan yarufe ya ijiye gefe ya kalleshi yace "Son" "Na'am Abba" Abba ya gyara murya yace "ahh dama magana nakeso nai dakai kan yar abokina, nafison naji daga gareka ne dan mahaifinta yacemin yayarshi tace kun dan dade da sanin juna dan har gidan su kajema" shiru yadanyi yana nazarin fuskar Khaleel din sanan yace "kana sonta ne?" sosai yaji kunyar maganan Abba hakan yasa yadanyi murmushi yana sosa keya, dan dariya Abba yayi yace "a'a to to to, wanan murmushi haka Khaleel ta eh ce ko" dan gyada kai yayi kanshi akasa Abba yace "to masha Allah dama nariga nai magana da mahaifinka ran sati zaizo sai muje nema maka auran ta, banason awani nisanta bikin sabida dazaran anyi auren kukadan yimana kwana biyu anan saika koma bakin aikin ka ko" gyada ma Abba kai yayi Abba yay murmushi yace "saura dan uwanka yanzun nan nagama dashi nabashi wata daya idan Bai fito da mataba nizan nema mai" dariya Khaleel yayi wanan karan, Abba yace "tashi katafi Allah muku albarka".
Sheshekan kuka datake ji yasa ta farka cikin tsakiyar daren nan, ahankali ta mika hannu ta kunna wutar dakin hakan yasa baccin idonta ya washe sosai, wawwaigawa tayi bataga kowa akasa ba hakan yasa ta sakko daga gadon, Farida tagani ke kuka a kwance da sauri tahau matattakalan bonk din tahau kan gadon ta dago ta, ta zaunar da ita takai hannu arude ta taba wuyan ta tace "baki da lafiya ne?" girgiza kai Farida tayi tana goggoge hawayen dake zubowa kaman an bude famfo, komawa tayi zata kwanta Islam tariko hanunta tace "talk to me please, problem shared is problem solved" fadawa tayi jikin Islam tafashe dawani irin kuka harda shesheka hakan yakara ruda Islam ta kankameta tace "Faree konaje na taso Mum ne?" girgiza kai Farida tayi ahankali tace "wlh Islam ina mugun sonshi, son da bazan iya kwatanta miki ba, amma kwata kwata bama ya daukan wayana yanzu, baya kulani na rasa yanda zanyi da kaina" kama fuskarta Islam tayi tace "listen listen kidena kuka kinata wahala shi baimasan kinayi ba, ki manta dashi jor, kanme zakizo kina wahala, ki manta dashi" girgiza kai tayi tace "bazan iyaba, I tried but nakasa I love my superman so much Islam bazaki gane bane" shiru Islam tayi cike da tausayin ta ahankali tace "to kinfada mai kina sonshi?" girgiza kai tai alamun a'a, tace "to duk randa kika sake ganinshi kinfada mai am sure zaisoki back" murmushi tadanyi ahankali tace "thank you Islam" kwantar da ita Islam tayi sanan ta kwanta agefen ta sukaja bargo suka kashe wutan dakin.
Gabaki dayan su suka hadu suna aiki a kitchen sabida Abba yace zaiyi baki sha daya zasuzo, Farida ta rame har Abba saida ya tambaye ta meke damunta tace bakomi Wuraren goma suka gama aka zuzzuba abincin a hadaddun kuloli, sanan kowa yawuce daki danyin wanka.
Suna shiga daki Farida ta kulle kofar su hadda sa sakata sanan ta kalli Islam dake kokarin cire kaya tace "kinsan me mommy tacemin?" girgiza kai Islam tayi tace "cewa tayi wai aurenki fa za'a zo nema yau" sosai taji kirjinta yabuga dum! Farida tace "kinsan dama baki bani labarin yanda kuka karasa da Fahad ba dama kin yarda yaturo ne?" arude ta girgiza kai tace "cemai fa nayi sainayi magana da Mummy, baifadamin zai turo ba and kona kirashi baya picking fa rabona damagana dashi tun Ina hospital" dariya Farida tayi harda kama ciki tace "yamin daidai, gwarama daya turo kinadai ji Abba yace mungama school dinan zai xhanza mana wanine, to mezaki zauna kiyi har next year, wlh nima dazaran na sasanta da superman dina aure zamuyi abunmu na cigaba da school din a dakina" tsaki Islam tayi ta ijiye wayar tace "kinga yaki picking ko" gwalo Farida tayi tace "ke dalla chan ki kyaleshi idan aka samuku rana yau ai automatic soyayya ce zata wani kara kulluwa" harara ta wurgamata tasake dariya tareda yin wurin kofa tace "kinga bari naje na debo mana abincin mu a flask dan dazaran iyaye sunzo bamu sake sauka kasa ina zasuga Amarya kafin aure" takalmi ta dauka ta jefamata da sauri tafita daga dakin tana dariyan shakiyanci rabon datai dariya haka harta manta.
Wuraren sha daya da rabi suka iso Babban Khaleel da Baban Eesha sai Kuma Abba da wasu abokana yen shi biyu duk sunci manyan kaya, da kanshi baban Islam yamusu iso nan suka zazzauna afalo ana gaishe gaishe kafin Mum da Anty Hindu da Maman Miemie suka fito aka gaggaisa sanan aka gabatar musu da abinci sukaci suka sha sanan aka fara magana. Basu boyema Baban Islam komi akan Khaleel ba ba karamin tausayin shi yajiba, nan ya yarda ya amince yabasu Islam yace ai tun randa Anty Hindu tafada mai yatura a kamai binciken halin shi Alhamdulillah duk yan anguwa sunce mutumin kirki ne ga zuwa massallaci. Aka fara maganan sa rana wata biyu yace amma Abba ya roki alfarma abarshi wata daya sabida suna son Yaron yakoma bakin aiki ya dade rabonshi da aiki nan baban Islam ya yarda, Baban Eesha ne yafita ya shigo ga jakunkunan gorori mai gadi ya tayashi dauka da su sweet nan aka ijiye dubu dari kudin nagani Ina so Anty Hindu tawani saki guda. Bayan anyi finalizing everything aka rufe taron da addu'a sanan suka wuce massallaci danyin sallan azahar dagangan suna dawowa suka tafi murmushi akan fuskar kowa.
*JARABTA*
Maman Abd Shakur
34 & 35
Aika Mum yayi takirasu zama sukayi su biyun afalon Abba yay gyaran murya yace "burin kowani uban ne yaga yarshi ta sami miji dan mutunci yaro mai hankali da addini da hikima, to Alhamdulillahi Ummi nariga namiki miji wanda kika sanshi sosai Muhammad Khaleel" ba karamin bugawa kirjinta yayi ba har saida ta dago kai ta kalleshi ya cigaba yace "mun riga mun gama magana da iyayen shi, an saka rana sati hudu, bayan biki zankudan yi kwana biyu anan yola sanan ku wuce Abuja sabida ya koma aiki, idan kinada any abu dakike so ki fadama Mummy ku sai asiyo miki" Ya gyara zama ya kalli Farida akunyace ta labe abayan Islam tace "Abba nima kwanan nan zan fito da nawa" murmushi kawai Abba yayi yace "Faridan Abba kenan to Masha Allah, Allah nuna mana ku tashi kutafi" atare suka fito daga dakin Farida ta kalleta tadan zaro ido tace "ke waye kuma Muhammad Khaleel nazaci Fahad ne ya turo?" kasa magana tayi sabida wasu hawayen bakin ciki da suka zubomata da gudu ta bude kofar dakinsu ta shiga ta zauna akan gado, Farida ta zauna akusa da ita tace "waye Muhammad Khaleel din?" kwallan daya dan zubomata ta share tace "wani ne fa datunda muka hadu duk inda naje saiya bini kaman maye, yace yana sona ni banason shifa Fahad dina nakeso" Farida tace "to mesa baki fadama Abba baki sonshi ba?" turo baki tayi ahankali tace "kasawa nayi wlh kaman antushe min baki" murmushi kawai Farida tayi tace "lemme not waste my saliver akanki dan ga sonshi nan kuri aidonki, nidai duk randa yazo I will love to meet him o" tashi tayi fuuuu ta dau wayarta ta shiga bayi ta rufe tai dailing number shi harya gama ringing bai dagaba saida ya katse ya kirata back cikeda tsiwa tace "nace ina sonka ne dazaka tura gidanmu?" murmushi yayi sanan yay magana ahankali yace "ai basai kince kina sonaba wife, gangar jikin ki, rohin ki, murmushin ki, kwayar idanunki sun riga suncemin suna sona so mezan jira? Yau dayake fada kikeji shine harda kirana bayan idan nakira ki u don't pick" rasa abinyi tayi hakan yasa ta fashe mai da kuka dan dariya yayi kafin ya sassauta murya yace "please don't cry, how about gobe nazo na lallasheki da kaina" tsayar da kukan tayi tace "Allah inkazo gidanmu saina cirema kafafu" wanan Karan dariya yayi sosai, shiru tadanyi tana sauraron yanda sautin dariyar nashi ke fita kaman Karya dena, dan shiru yayi kaman yasan meke zuciyar ta yace "you like how I laugh, na cigaba?" da sauri ta kashe wayar tana dan murmushi bude kofar tayi tafito daga bayin Farida ta harareta tace "kai Islam keko, kina so kina iskanci hegiya pretender" dauke kai Islam tayi kaman bataji taba tazo zata zauna akan gado filo Farida ta naka mata hakan yasa ta fada gado tana dariya ita kanta mamakin kanta take to Mesa tama kasa fushi.
Wuraren biyar na yamma yazo yana sanye da shadda mai ruwan toka sai kamshi yake, Anty Hindu tasa aka shigo dashi saida suka gaisa sanan tabar falon sama taje tasami Farida da Islam zaune tace "ke tashi ki xhanza kayan jikin nan naki Khaleel yazo" ganin Anty Hindu ta tsaya masu akai yasa ta tashi shiryawa tayi cikin simple brown material da akai mata doguwar riga ta daura milk color hijab din gida daya tsaya mata acinya tadan shafa hoda tasa lipgloss tadan fesa turaren Posess sanan ta kalli Farida tace "zomuje ki ganshi fa" girgiza kai tayi tace "ke haka akeyi jeku fara gaisawa tukun anjima zanzo" fita Islam tai daga dakin. Shigowa falon tayi batare data kalleshi ba ta wuce kujeran 2 sitter dake kusa da kujeran daya zauna ta zauna tana gyaggyara hijabin jikinta. Ahankali yataso yazo ya zauna akan kujeran datake ya fuskanceta yana kallon fuskar ta batare dayace komiba, dan dago kai tayi ta kallai, hararan shi tayi sanan ta turo baki tace "katashi kabarmana gidan mu" make mata kafada yayi hakan yasa ta dauke kai da sauri dan wani iri taji, ahankali kaman mai rada yace "I miss you ummina" dan dago kai tayi suka hada ido hakan yasa tasake dauke kai, tagumi yay ya cigaba da kallon ta kaman yau yafara ganin ta, batare data juyoba tace "stop looking at me" girgiza kai yayi yace "I can't" juyowa tayi tace "kabar mana gidanmu kuma" girgiza kai yasake yi yace "I can't" juyowa tayi cike da masifa tace "ninace ina sonka ne dazaka tura aje wurin Abban mu" Ahankali yace "but I love u" yay maganar murmushi kwance kan fuskarshi, ahankali yace "Are you angry with me?" hararan shi tayi ganin yamaida ita wawiya, hannu yasa a aljihun rigar shi yaciro chocolate bude chocolate din yayi yadan matso kusa da ita ya Kalli fuskar ta yace "kinsan ance chocolate na mantar da mutum fushin dayake yi ko" yay maganar yana kallon kwayar idonta...
Ahankali Farida ke sakkowa daga stairs sanye da hijab harta shigo falon, numfashin ta taji yana neman barin kirjinta ganin Superman dinta da Islam suna wani irin kallon juna...
Cikinsu babu wanda ya lura da Farida, kallonshi Islam tayi sanan ta kalli chocolate din daya bude yana miko mata make kafada tayi tace "I don't want" dan matsowa yay kadan ya sassauta murya kaman me lallaba yaro yace "plzzzzzzz" yanda yaja plz din haka tajishi har cikin ranta ahankali ta mika hannu zata karba girgiza kai yayi batare dayay magana ba ya nuna mata bakinta da yatsa yace "haaa" wai mutumin nan magic yake minne dudda yanda taso tahana kanta kasawa tayi ahankali ta bude bakinta kadan, murmushi yayi yakai chocolate din bakinta yana kallon fuskarta Islam! Farida takira sunanta dawani irin murya da tunda suke bata tabajinta dashi ba, adan rude ta juyo dan yanda Farida takira sunanta saida ta firgita shima ita ya kalla, gyara zama yay sanan yace "Hi how u?" dan wlh yamanta sunan ta, da kyar ta iya kakalo murmushi tace "fine" murmushi yamata sanan yace "don't tell me u two are sisters" Ya kalli Islam sanan ya kalleta ya nuna Islam yace "itace dama Islam din dakike ta bani labari" gyada mai kai tayi tana kokarin danne hawayen dake barazanar zubomata, yay murmushi yana wani irin kallon Islam kaman ya cinye ta yace "I see" dan murmushi tamai sanan tace "bye" tajuya tafara tafara hawa stairs, tashi Islam tayi zata bita dawani irin murya yace "ina zaki My Ummi, we are not done yet baki karbi Chocolate dinba" wani irin hawaye ne mai zafi ya zuboma Farida da sauri sauri tai tawuce dakinsu jin yanda Superman kema Islam muryar dabata sanshi da ita ba, dama yanama magana haka?.
Zama Islam tai ahankali ta kallai dauke kai tayi sanan tace "dama ka San Farida ne?" gyada kai yayi yace "yea I helped