Showing 33001 words to 36000 words out of 68203 words

Chapter 12 - JARABTA 1 TO END Book Complete Document hausa novels by Maman Abdul Shakur--.txt

M Shakur   

29 Dec 2024

8274

share mata hawayen datake ya girgiza mata kai yace "is okay, stop crying Baby" ture hanunshi tadanyi ganin yanda Farida ke kallonsu ahankali yace "bari nadan baku wuri to" yadan matso da bakinshi wurin kunnenta yace "zanje gida, but idan nadawo zamu cigaba daga inda muka tsaya" dan tureshi tayi tana kallon fuskar Farida murmushi yay ya saketa sanan ya kalli Farida ahankali yace "make your self at home bari naje gidanmu bye" tunda yake maganan takasa dauke idonta akanshi, fita yay yana kallon fuskar Islam ya rufo musu kofa.


Rungumeta Islam tasakeyi sanan taja hannunta suka zauna akan kujera tana kallon fuskarta tace "Faree da gaske kin yafemin dan Allah?" dan murmushi Farida tayi tace "how about nadafa miki wanan sweet Indomie dana ke miki agida kici kawai dan ki yadda komi yawuce awurina" cike da murna Islam tace "to tashi muje mu dafa" ta mike tsaye harda jan hanun Farida tashi Farida tayi tace "ki zauna abinki, nizan dafa miki gawayata nan ki karanta Soyayyar mu yau Fati Teejay tai posting" da sauri ta karbi wayar sabida tana mugun son littatafan faty, Farida ta kalleta tace "inane kitchen din? " nunamata tayi da hannu tareda kwanciya dan ta karanta novel din, Farida tajuya ta shiga kitchen din, Indomie biyu ta ciro da Kwai tafara dafawa, komawa tayi ta kulle kofar kitchen din sanan tadawo gaban gas din ahankali ta bude jakarta ta ciro sniper tabare ledan tabude sanan ta zuba acikin ruwan Indomie, tai maza tai grating attarugu da yawa da albasa ta zuba aruwan sabida ya kashe warin sniper, saida tagama dafa Indomie dayay mugun kyau a indo ga egg agefe ta bare sanan taje gaban fridge ta dauko sabon exotic dayay sanyi sosai ta bude ragowan sniper ta zuba aciki ta jijjiga sosai sanan tahada komi a tray tadau fork da glass cup tasaka sanan wurgar da goran sniper a bin dake kitchen din, tadawo tadau tray tabude kofa tafito falon, table taja ta ijiye mata tace "tashi tashi kici" ta mika hannu ta karbi wayarta takoma ta zauna wurin ringing tone ta shiga ta danna hakan yasa wayar tai kara ta mike da sauri ta kalli Islam da ita take kallo tace "Abba nakirana bari natafi zaikaini airport ne saisa yake kirana nadawo" Islam tadan tabe fuska tace "to Indomie mufa bazaki tsaya muciba" hararan ta tayi tana murmushi tace "sabida nai missing flight dina ko" tashi Islam tayi tsaye da sauri Farida ta maida ita ta zauna tace "dalla kekuma sai Indomie yahuce, I cook it with luv so kici da kyau bye" murmushi Islam tayi tace "Allah kiyaye hanya, I love you Faree bye" fita Farida tai daga dakin tana daga mata hannu.
Komawa Islam tayi ta kwanta ta lumshe ido danji tayi hankalin ta ya kwanta yanda Farida tadena fushi da ita, jin kamshin indomie ya ishi hancin ta yasa ta tashi ta zauna fork ta dauka ta debo ahankali takai bakinta dan yatsine fuska tayi tana tunawa tace "kaman wari warin kalanzir" hadiye wa tayi dan ba karamin dadi Indomie yayi ba, ahankali ta sake debo na biyu takai bakinta hadiye wa tayi tana yatsine fuska tace "kodai akwai kalanzir agidan nanne" exotic din ta dauka ta jijjiga sanan tabude ta zuba a glass cup takai bakin ta tana sha, cire cup din tayi tana jujjuyawa tana shinshina jikin cup din, kodai hancin tane kejin warin kalanzir dinan tasake tambayan kanta, sanyin da exotic din yayi yasa takarashe kwankwadewa ta ijiye cup din, sanan ta tashi taje gaban TV tai plugging ta kunna, remote ta dauka tasaka zee world sanan tadawo ta zauna akan kujera takara daukan fork tadebo Indomie zatakai bakine taji cikinta yadanyi wani irin kara tareda tsukewa kadan, dan zabura tayi tareda yamutse fuska but tagama period mekuma cikinta ke haka, batare data kawo komi ba takara kai Indomie bakin ta ta hadiye da kyar, tashi tayi tana shahshafa cikinta sabida yanda taji kaman hanjinta na vibrating.
[6/23, 1:42 PM] Maman Jedda: *JARABTA*




Maman Abd Shakur


43 & 44


Parking Abba yay yafuto yazagayo ta inda take ya budemata kofa, tama kasa tashi tana mamaki mekuma sukeyi anan ga Khaleel, inane ma nan, hannu Abba ya mikomata yace "sakko" ahankali ta sakko da kafarta dake sanye cikin flat shoe dinta black, maida kofar Abba yay yarufe sanan yafara tafiya tana biye dashi abaya dan dukar dakai kadan Khaleel yayi yace "sannu da zuwa Abba" murmushi Abba yamai ya shiga gaba Abba da Islam na biye dashi abaya ya bude musu kofa suka shiga wani babban falo dayasha kujeru ash color ansa labulaye masu kyau baki da ash, dakin sai kamshi yake ga sanyin ac dayakara karama dakin dadi, ga babban tv bango dake aiki saidai babu kara, zama Abba yay akan kujera har lokacin yana rike da hanunta ya zaunar da ita a gefenshi, karasa shigowa Khaleel yayi yaje zai zauna akasa Abba ya nunamai dayan gefenshi ahankali yazo ya zauna yanadan satan kallon fuskar Islam wacce kanta ke kasa.


Gyara murya Abba yayi sanan yafara da addu'oi ya kalli Islam yasa hannu yaciro bandir din yan dubu daidai a aljihunshi ya ijiye akan jikinta yace "Ummi ga sadakin kinan, dazu aka daura aurenki da Khaleel" da sauri ta dago kai ta kalli Abba jikinta har bari yake murmushi Abba yamata yace "nariga nasan komi, yanzu dai abinda nakeso dake shine kibi mijinki sau da kafa karki manta aljannarki na karkashin kafarshi, Koda wasa karki batama mijinki rai ki kasance mace mai addini, ibada hakuri da jarumta dakuma tsafta, har mahaifiyarki ta koma ga Allah bazan iya tuna randa ta taba batamin raiba" murmushi yadanyi sanan ya mike tsaye, ahankali Khaleel ya mike, hannu Abba yasa ya dagota sanan yarike hannunta ya kamo na Khaleel yasaka hanunta aciki ya Kalli Khaleel yace "ga amanar yata nan nabaka Muhammad ka kular min da ita, Allah ya baku zaman lpy Allah ya albarkaci auren, Abban ka yacemin ran Sunday zaku wuce Abujan ko" Ahankali yace "eh Abba sati daya kawai zamuyi anan" murmushi Abba yay yace "to shikenan ubangiji Allah ya kiyaye yakuma baku zaman lpy ka kular min da amanata na yarda da tarbiyanka Khaleel" murmushi yay yace "in sha Allah Abba" "to masha Allah nabarku lpy" yajuya zai tafi sai alokacin taji wani mugun kuka yazo mata fizge hanunta tayi daga hannu Khaleel da gudu taje ta rungume Abba tabaya tana kuka sosai tace "Abba dan Allah karka tafi kabarni, dan Allah" dan juyowa Abba yayi danba karamin karyarmai da zuciya tayi ba, ahankali ya dagota ya sharemata fuskar tareda sumbatar goshin ta ya girgiza mata kai yace "ai auren kenan Ummi, kiyakuri kinji dole natafi ki zauna da mijinki, haka iyayenmu duk aka musu, take care daughter" alamu Abba yamai da hannu ya riketa hakan yasa ya rikota Abba yajuya yatafi, sosai tafashe da kuka harda majina tureshi tayi ta zube a wajen tana kuka.




Farida takira Khaleel yayi sau goma baya dauka, daga bayama saitaga bata iya kiranshi dan kaman ma yay adding dinta a black list, mutanen dazasu kai Amarya sun gaji da jira suka fara watsewa dai dai yarage daga Mumy sai wasu kawayen ta guda biyu da ita Faridan dake sanye da lapaya ajiki duk tai sukusuku gabanta sai faduwa take idanun nan sun fiffito waje.


Shigowan Abba yasa Mum da Farida suka mike batare daya kallesu ba yace "kusame ni afalo na" yay gaba suna biye dashi abaya, zama yay a babban kujeran shi ya nuna musu waje, kofa Anty Hindu ta bude ta shigo dakin cike da murmushi ta kalli Abba tace "harka kaita kadawo?" gyada mata kai yayi tareda cire hular dake kanshi ya ijiye a saman kan kujera Mum ce tace "Alaji naga kana cire hulane, kiran mutanen nan fa yakamata kayi azo atafi da amarya wanan wani irin abune, ko sai gobe zasuzo ne" wani irin kallo Abba yamata sanan yace "ai anriga ankai amarya tun dazu" batare daya sake kallon Mum da fuskarta ya nuna alamun tambaya ba yacema Farida "zonan" tashi tayi jikinta a sanyaye taje gaban Abba ta zauna, ahankali yasa hannu a aljihun shi yaciro ticket din makka dakuma car key yabama Farida yana murmushi yace "kinga wayan nan duk nakine mota sabuwa, ga ticket din makka wanda ranan lahadi mai zuwa jirginku zai daga ko Faridan babanta" murmushi tama Abba tace "nagode Abba" gyara zama Abba yayi yace "Farida yanda nake sonki haka nakeson Ummi, saisa nake kokarin yin adalci atsakaninku, kinsan hadarin auran mijin dabaya sonka kuwa? Ai yaro kodan gidan kirki ne inhar baya sonka gwara ka hakura dan duk yanda zuciyar shi take dole saiya cutar dakai dan zuciyar nan dakike gani bata da Kashi Farida, ko yayyinki maza Abdallah da Ibrahim wlh bazan taba bari su auri wacce basaso ba sabida nasan zasu cutar da itane" ajiyar zuciya ya sauke sanan ya dafa kanta kaman yanda ake lallashin yaro yace "Farida nariga nasan komi, Khaleel bake yakeso ba Islam yakeso saisa nahada auren shi da ita bawai da wani abu ba, saidan shine abu mafi alkairi agareki, amma yanzu ga ticket dinki idan kinje Umarah kiyi addu'a in sha Allah mijinki na nan zuwa, and Koda banma hadasu aure bayau one way or d other saiya aureta dan Matar mutum kabarin sa, kiyakuri kinji karki bari komi ya tsaya miki arai, aure lokaci ne, wani rashin alherine kinji" gyadama Abba kai tayi tana hawaye, Mummy da duk ranta ya dagule yanzu mezatace ma kawayen ta ta kalli Abba tace "gaskiya Alhaji anzuba sonkai awajen nan, kirikiri shikenan kanuna kafison Islam, yarinya tama Farida kwacen saurayi Kuma ka auramata ha..." tsawa Anty Hindu tamata tace "kwace saurayin gidan ubanwa eh? To bari kiji jiya yaron nan saida na aika aka kiramin shi bayan kun watse kun tafi walimar ku, har cikin falon nan na Abba ya shigo saida nasa shi yafadiman gaskiya, ni tun bayau ba nasan Islam yakeso, Islam yafara haduwa da a garin nan, sanan maganar so baitaba hadashi da Farida ba daga taimako ta likemai, ai har labarin haukan datayi nacin shinkafar bera saida nasamu" takalli Farida dawani mugun ido tace "ba shinkafar beraba ko taliyar bera ce kije kisiyo kici dan uwaki kezaki mutu kafira kinji ko walakiri ya narkeki ehe mara hankali kawai" da gudu Farida ta tashi tafita daga dakin tana kuka, tsaki mum taja tamike tabi bayan yarta, Anty Hindu ta kalli Abba tace "tana dawowa daga Umarah kanemi Yaron kirki mumata aure kafin tajawo mana abin kunya tunda dai zuciyar uwarta ta dauko" ta wuce tafita daga dakin tana masifa, Abba ya girgiza kai wanan yayar tashi hmmm ba'a cewa komi.


Ahankali ya tsugunna agabanta yadaura hannayen shi akan gwuiwarta ta turemai hannu cike da masifa, murmushi yamata yace "stop crying to kinji" make kafada tayi ta cigaba da kukan ta, murmushi yamata yace "okay" tashi tsaye yayi ya cire babbar rigar shi ya zauna agabanta ya lankwashe kafa yay tagumi yana kallon yanda take kukan, hararan shi tayi sanan ta janyo hular hijabin ta tacigaba da kukan, dan dariya yayi ya sanya hannayen shi biyu ya maida hijabin baya hakan ya bayyana fuskar ta, turo baki tayi ta daga hannu kaman yanda yaro yake idan zai daki mutum tana kuka, murmushi yayi ya sanya hannayen shi ya rike kunenshi tareda langabar dakai ahankali yace "am sorry plzzzzzzz" kawad da kanta tayi tacigaba da gunjin kukan ta, ahankali yadawo ta inda fuskarta yake murya chan kasa yace "please stop crying ya isa haka, zomuje kiyi wanka let's have dinner" yay maganan yana rikemata hannu, fizge hanunta tayi tace "bazan yiba" murmushi yasake yi ganin masifa takeji yau, matsowa yasake yi kusa da ita yakai bakinshi saitin kunnenta ahankali yace "oh are u shy? Okay bari ni naje nafara yi" kin kallonshi tayi saima goge goge hawayen datake yi, ahankali ya mike tsaye yawuce ya shiga wani yar corridor dazai sadashi da bedroom din, tashi tayi tsaye da kyar jin yanda cikinta ke ciwo waige waige ta dinga yi kozata ga wani abu dazata iya rubutu dashi, akan dining table ta hango wani leda dataga an rubuta thanks for coming ajiki, dama ya taho dashi ne danyabama mai gadi, budewa tayi taga memo da byro da goran bottle water da duk anrubuta sunanta da nashi ajiki, memo ta dauka da byro dan tsaki tayi dan wlh Allah yagani bayanda zatayi yine bude marfin byro tayi sanan ta rubuta "please I, I, please I need pad" sosai taji wani irin kunya nakamata ajiye byro tayi akan dining din sanan ta dawo cikin falon, ajiye memo tayi kusa da wayarshi tabar page din datai rubutun abude yanda dazaran yazo zai gani, ta koma kan kujeran ta kwanta tana tunanin gida da Farida.
Alamun tafiyar shi dataji yasa ta lumshe ido da sauri yana sanye da farin jallabiya sai kamshi yake, shigowa falon yay yana kallon fuskarta ganin memo kusa da wayarshi yasa yakarasa wajen dan yasan babu komi akan kujeran daya shiga ciki, daukan memo yayi ya duba, dago kai yay ya kalleta yana murmushi, daukan key din motar shi yayi dake kan center table da wallet dinshi yasa a aljihun ahankali yazo gaban kujeran datake ya tsugunna ba karamin bugawa kirjinta yayi ba jin ya daura hanunshi akan nata data daura akan cikinta yana shafa fatar hanun nata, dayar hanunshi kuma a saman kan hijabin ta ahankali yace "am coming bari naje nasiyo miki" dan dukowa yayi yamata peck a kumatu ya mike tsaye yana kallon yanda jikinta ke rawa murmushi yayi yafita daga dakin.
Abunku da GRA gabaki daya shagunan duksun kulle tsaki yayi yadau wayarshi sako yaturama Ihsan kanwarshi sanan yay kwana yadawo, agaban gidansu yay parking dayake tsakanin gidan da inda akakai Islam baifi gida uku bane tsakani, yana zaune a car Ihsan ta bude gate tafito sanye da Hijab hanunta rike da Leda tana kallon fuskar Khaleel tana murmushi, daure fuska yayi ya mikamata hannu tasaka mai tana dan dariya ciki ciki tace "ka gaisheta Ya Khaleel" harara ya zuba mata yace "nidan aiken kine" eh din tace taruga da gudu tashiga cikin gida murmushi yay ya kunna mota yabar wajen yay horn agaban gidansu mai gadi ya budemai yay parking motar yafito, bude kofa yay dayar sallama tana kwance inda yabarta idanunta a lumshe takowa yay inda ya barta ya ijiye ledan a gefe ahankali yakai hanunshi waist dinta hakan yasa ta firgita ta bude ido da sauri tareda ture hanunshi, murmushi yamata yasaketa sanan yadau ledan yabata ahankali ta karba tareda kawad dakai, hanunta ya kama yace "to tashi kije ciki kiyi wankan" uhn tace tareda turemai hannu folding hannayen yay a kirji ya tsaya yana kallonta ganin gabaki daya duk a tsorace take yasa yay hanyar kitchen yace "am going to the kitchen, jekiyi wankan ki" saida taga ya shiga kitchen din sanan ta wuce hanyar dataga yabi dazu, daki dayane tak a corridor hakan yasa ta bude dakin ta shiga babban gadone royal yaci hadadden zanin gado, sai wardrobe din bango sai yar center carpet a tsakiyar dakin kofar bathroom din tagani yabari abude ta wuce ta shiga tarufe. Takai kusan 10min atsaye tana tunane tunane wai yanzu shikenan haka dama ake aure, shikenan ta auri wanda Farida ke mugun so bayan tai rantsuwa bazata taba auren shiba yanzu ya hukuncin rantsuwarta?.
Jiki asanyaye tacire hijabi da doguwar rigar ta ijiye a gefe sanan tafara wanka, sai bayan tagama wankan tarasa yanda zatayi gashi ko kaya daya bata dashi kuma doguwar rigan yadan yi staining balle tamaida, hijabin ta dauka tasaka sanan tadan bude kofa kadan ta leka dakin hada ido sukayi daidai yana ijiye tray din abinci akan drawer dan murmushi yay ya dauke kai ganin she's so uncomfortable, batare daya kalleta ba yace "am coming" ajiye tray din yayi yakoma gaban wardrobe ya bude wani dan madaidai cin akwati ya dauko ya kawomata nan gaban bayi ya ijiye batare daya kalleta ba ganin ya zauna abakin gado ya juya mata baya yana daddana waya yasa ta tsugunna ta bude akwatin wani doguwan rigan bacci ta dauko mai dan mutunci da undies sanan tadan dago kai ta kallai ganin baya kallonta yasa ta koma bayi da gudu ta shirya tass, rashin sabulu wanki yahanata wanke doguwar rigan, folding tayi tafito daga bayin sanye da hijabi ta tsugunna tasa rigan acikin akwatin sanan ta rufe ta daga akwatin tsaye, ahankali take tafiya tazo zata wuceshi ta fita da sauri dan wani irin tsoro taji tanaji yanda daga ita sai shi agidan nan, hanunta ya riko ya janyota ya daurata akan kafarshi da sauri ta mike tsaye jikinta har rawa yake, tashi shima yay tsaye yasa hannu ya yaye hijabin ta yacire ya wurga kan gadon da sauri tasa hannu tana kakkare gaban rigan kanta akasa duk jikinta na rawa, ahankali taji yakamo hanun yasaka hanunshi cikin nata ya zaunar da ita abakin gadon ya dauko tray din abincin ya zauna kusa da ita dan har jikin su na gogan juna, lafiyayyen fried rice ne da kaji sai cold exotic drink da bottle water ga magani data gani agefe, baice mata komiba ya debo rice din a spoon yakai bakinta girgiza kai tayi jikinta har baribari yakeyi tace "zan zanci dakaina" hannunta ta mika zata karbi spoon din ganin yanda hanunta ke rawa yasa ya ijiye spoon din ahankali ya daura hanun nashi akan nata yakai dayan hanun kumatunta yakira sunanta ahankali "Islaam, Hey relax is me" bata kalleshi ba, spoon din yasake dauka yadebo rice din yakai bakinta very calm yace "please" Ahankali ta bude bakinta kadan yasa mata taci da kyar ta iya tai 5 spoon sanan tace "am okay" bayason yatakura ta hakan yasa yadau maganin dake tray ya ballo kwara biyu yabata yana murmushi yace "for d stomach" Ya nuna cikin ta kawad dakai tayi ta karba yadau ruwa ya bata tasha tana yatsine fuska, tashi tayi tai hanyar kofa zata fita batare daya kalleta ba yace "kizo ki kwanta anan idan nagama cin abinci nixan kwana a falon" dan kallon fuskarshi tayi ganin baya kallonta kokarin debo rice

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login