Showing 39001 words to 42000 words out of 68203 words
Chapter 14 - JARABTA 1 TO END Book Complete Document hausa novels by Maman Abdul Shakur--.txt
superman dinta yasaimata yabata ahankali tace "menama Islam haka datamin irin wanan abu? Mesa nakasa cire sonshi araina why, please God inaso na manta dashi please" share da kwallan daya zubomata tayi tadau smoothie zatakai baki da sauri ta ijiye ta kife kanta akan table din tana wani irin kuka mai cinrai, "hey is everything okay" dago kai tayi suka hada ido da Yusuf dake sanye cikin sport wears hanunshi rike da cold bottle water, share ido tayi ta juya da sauri ta duba ko suna tareda superman dinta ne taga shikadai ne, juyoda kai tayi ta harari Yusuf tace "wat are you doing here?" kujera Yusuf yaja ya zauna yana kallon fuskarta yace "nothing banmasan kebace" tashi tsaye tayi tajuya zata bar wajen dan wani irin haushin Yusuf takeji da sauri yabita juyowa tai cike da masifa tace "kadena bina harda kai aka hadu aka yaudaran, Islam Islam" takira sunanta saikuma tajuya tafita daga wajen da sauri jin wani kukan ke zuwan mata suna fita Yusuf yasha gabanta yace "hear me out, kidena blaming sister ki wlh batada laifi, Allah kuwa trust me" bakin gyalen ta tasa akan fuskar ta tafashe dawani kukan, jitake kaman zuciyata zai fashe, ba karamin tausayin ta Yusuf yaji tabashi ba ya tsaya kawai yana kallonta da kyar tai shiru ta kalli Yusuf da rinannu idonta tace "koma menene at least for d sake of ni yar uwartace, tasan yanda nake sonshi saitaki auren shiko" ta dago kai ta kalli Yusuf tace "kataba son wata?" girgiza mata kai yayi alamun a'a hakan yasa tadanyi murmushi tace "bazaka taba iya gane wat am going through ba, Islam" tasake kiran sunan Islam tana wani irin dafa kirjinta da sauri tajuya tabar wajen akan bakin titi ta tare napep ta shiga tana goggoge ido da bakin gyale. Sosai Yusuf yaji jikinshi yay sanyi wanan wani irin sone, yanda take haukan son Khaleel dinan shikuma haka yake haukan son Islam, oh Allah kayaye ma wanan baiwar naka wanan son maso wanin, ahankali ya juya ya shiga ciki.
Islam dai sai gyaran jiki ake mata in and out, Goggo yanzu kulle kofa take idan baka kwankwasa ka fadi sunanka ba bazata taba budewa ba duk dan kar Khaleel ya ganta take wanan.
Dayake yau asabar yasa anata shirye shirye kowa na hada kayanshi dan gobe zasu tafi, Wuraren 11 Khaleel yafito daga part dinsu yana sanye da jeans black da blue t-shirt mai gajeren hannu, fuskar nan tashi adaure har wata yar raman dole yayi sabida rashin ganin Islam, dakin Ammi yayi yasameta zaune kusa da Dad datake hadama tea gaishe su yayi suka amsa, Dady ne yace "mekake so son" kallon fuskar Ammi yayi hakan yasa ta dauke kai ahankali yace "dama Dady inaso Ammi tasa Islam muje ta tayani hada kayan mune nachan gidan tunda gobe zamu tafi" Dady ya Kalli Ammi yace "kiramai matarshi tazo sutafi ta tayashi mana" Mum zatai magana Daddy yace "ki kirata nace banson jin komi" murmushi Khaleel yayi hakan yasa Ammi ta watsamai harara sanan ta wuce tafita tai dakin Goggo saida tai magana sanan Goggo tabude ta shigo Islam dake sanye da riga da sket nawani soft material mint green dake zaune rike da wayar Ihsan tana karanta wani novel tace "dauko Hijab dinki kizo Islam" ajiye wayar tayi tadau hijab Goggo tace "ina zata?" "Kiranta Alaji yake" black hijab tadaura akan kayan tabi bayan Ammi har falo, tunda ta shigo yake kallonta ganin yanda fatarta har wani kyalli take takara haske, dudda tasaka hijabi bai hanashi ganin yanda tawani kara cikowa ba tai fresh like honey wine, gaida Abba tayi cikeda girmamawa tana kallon Khaleel ta gefen ido dudda tadanyi kewanshi amma taki Koda kallonshi balle ta gaidashi, Abba ya nuna mata Khaleel yace "kuje kuhado kayanku na dayan gidan dan gobe da safe zamu tafi" ahankali tace "to daddy" fita Khaleel yayi batare daya kalleta ba hakan yasa tabi bayanshi kirjinta nadan bugawa, mota ya shiga hakan yasa ta bude gaban motar ta shiga ta zauna tarufe, kunna motar yayi suka fita daga gidan su aranta tace "nan da nanne bazai iya zuwa da kafaba, lazy fellow" horn yay mai gadinsu yabude yay parking yafito ya shiga ciki saida tai kusan 2min a motan sanan tafito jiki duk asake, ahankali ta bude kofar ta shiga falon, da kyar ta iya daga kafa takai tsakiyar falon ta tsaya ganin bata ganshi ba, tabaya taji anrungumeta hakan yasa saida tai yar kara sabida tsoro, tsamtsam ya rungumeta yakawo kanshi ta wurin kunnenta yace "I miss you" juyo da ita yay yakai hanunshi yay cupping fuskarta ya kalli cikin idonta yace "did you miss me" dan murmushi tai sabida yanda yay maganan ta dauke kai, zama yay ya daurata akan cinya yana kallon fuskarta yace "waye lazy fellow?" adan rude ta kallai ta dafe kirji, ganin yanda yake kallonta yasa ta tashi da guda tana dariya tai hanyar bedroom tace "bafa dakai nakeba" harta zauna akan gado taji yabude dakin da gudu ta tashi zata shiga bayi ya rikota tabaya tareda cire hijabin jikinta ya matseta yana kallon idonta yace "Wana kama?".
[6/23, 2:07 PM] Maman Jedda: *JARABTA*
Maman Abd Shakur
49 & 50
Dan dariya taji yazo mata, kawad dakai tayi sanan tace "sorry" ahankali, kamo hanunta yay ya zauna akan gado ya daurata akan jikinshi yana kallon fuskarta murya chan kasa yace "did you miss me?" daura kanta tayi akan hanunta akunyace tace "uhm" bakinta tarufe da sauri dan wlh batasan lokacin da maganan yafito ba, hade kansu yay wuri daya ya hade hannayenshi biyu ta bayanta yana dan jijjigata akan kafarshi, murya chan kasa yace "banjiki da kyau ba" dan dago kai tayi ta kalleshi suka hada ido batare data cire idonta daga kanshi ba ta sanya hanunta ta baya ta bige hanunshi ta tashi da gudu ta tsaya abakin kofa sanan ta juyo ta kallai ta gyadamai kai kaman yanda yara suke sanan tace "yea I miss yhu" bude kofa tai tafita da gudu tai kwanciyan ta afalo akan dogon kujera tareda daura filon kan kujeran akan fuskarta. Alamun tahowar mutum dataji yasa tadan zame filon kadan daga kan fuskarta ta kalleshi maida filon tayi da sauri ganin sun hada ido kirjinta na bugawa sosai, zama yay ya dauki kafafun ta ya daura akan cinyarshi yana mata waiwayi akafa, motsi ta dingayi tareda kara rike filon ta danne fuskarta aciki, jin bakinshi datayi akan babbar yatsar kafarta yasa taji wani yarr batasan lokacin data saki filon yafadi akasa ba, kasa daure yanda yake sarrafa yatsun nata yake ta mirgina ta kifa tareda daga kafafun nata sama hakan yasa sket dinta yay kasa kafafun suka bayyana ta lumshe ido tana cuccusa fuskar ta acikin kujera, ahankali ya kamo kafafun ya kwantar sanan ya kwanto ta bayanta yakai bakinshi saitin kunen yakira sunanta "Islaaam" yanda yaja sunan yasa takasa daurewa saida tabude idanunta dasuka kankance ta kallai, tashi yay ya zauna ya sanya hannu ya dagota itama ta zauna tana lumlumshe ido, hanunta yakama yarike gam ahankali yace "ina sonki dayawa Islam please don't ever leave me, I love you sama da yanda kike tunani, u know something" kai ta girgiza mai tareda kwantar da kanta kan kafadar shi, kanshi ya daura akan goshin ta yasanya hannayen shi yay cuddling nata very tight sanan yadan sauke ajiyar zuciya yace "are you fine?" gyada mai kai tayi, ahankali yasake sauke ajiyar zuciya yace "nai mafarkin kine jiya saisa nasa Abba yace kiboyini nan, I just wanted to know idan kina lpy" lumshe ido tayi akan kafadar nashi tana kara shakan kamshin dayakeyi datake mugun so cikin siririyar muryarta tace "mafarkin mekayi?" murmushi yay tareda kissing forehead dinta yace "it doesn't matter now, all I want you to know is I love you very much Islam" da sauri ta maida kanta kirjinshi tareda lumshe ido sabida yanda yakesa takejin kunya, ahankali yaciro kanta daga kirjinshi yana wani irin kallon fuskarta bude ido tayi kadan ta kallai da sauri ta kankame idon ganin ita yakema wani irin kallo, saukar bakinshi dataji akan lips dinta bazato ba tsammani yasa ta bude ido da sauri tana kokarin kwace bakin matseta yay ajikinshi yana mata wani irin zazzafan kiss, hanunshi taji abayanta yana shashafawa batare daya raba bakin nasuba zip din rigarta taji yaja kasa kokarin tashi tai daga jikinshi hakan yabashi damar cire rigar da kyau ya ijiye gefe, kankame idonta tayi sosai cike da kunya ganin yanda yake kallonta, ahankali yasaki bakinta da idanunshi dasuka soma ja yana kallon yanda take kakkare kirjin da hanunta, hanunta yakama yanadan murmushi yana wani irin kallonta ganin yanda taki bude ido, jin hanunshi akan bra dinta yasa tadanyi ihu ta shige jikinshi sosai jikinta na rawa ta fashe da kuka tace "please sto... " bai bari takarasa maganar ba yasake hade bakinsu wuri daya ya kwantar dasu akan kujeran ya shiga wasa da ita da zafi zafi gashi yaki bata daman yin magana hawaye kadai take iya zubarwa, bude kofa akayi aka shigo dakin kai tsaye hakan yasa ya dago kai tareda maida Islam bayanshi itama bude ido tai atsorace jin anshigo dakin tai lamo abayan shi duka hannayenta nakan kirjinshi dan rungumoshi tai tabayan, daure fuska yay tamau yace "mekika zoyi anan?" yana maganan ne tareda daukar rigar Islam dake kan kujeran yana bata da sauri ta karba ta saka, kasa cire ido tai akanshi ganin cikakken kirjinshi gawasu six packs dasukai layi gwanin ban sha'awa, jijiyoyi sun fiffito a muscle dinshi "mekekazo yi agidan mu nace?" Ya daka mata tsawa hakan yasa Islam tadan leko da kanta daga bayanshi bayan tagama saka rigar bakinta har rawa yake tace "Faa.. Faree" wani irin kuka ne da kishi yakawo ma Farida wuya da kyar ta iya kakalo murmushi tace "am sorry nazo gidan ku bada izinin kuba, dama damaa" takasa karashe maganan sabida wani irin kuka dataji yazo mata, da sauri Islam ta sakko daga kan kujeran zataje wajenta riketa yayi yasa hannun shi abayanta ya zuge mata zip din rigar, hakan yasa Farida taji wani sabon kuka yazo mata da kyar ta share idonta tace "dama nazo na roki gafarar kune akan duk abinda nayimuku, zan tafi Umara gobe, anjima zan tafi Abujama, so I just tot nazo sabida mu shirya, shine nace Bala yakawo ni tunda yace yasan gidan yataba kawo Anty Hindu" takarashe maganan tana kuka dan takasa daurewa yanda tagansu yasa taji kirjinta namata zafi, fizge jikinta Islam tayi daga nashi taje da gudu ta rungume Faridan hakan yasa ta fashe da kuka sosai tace "Islam am sorry, please kiyafe min abubuwan dana miki kinji kema naji Anty Hindu tana cewa gobe zaku tafi ko please forgive me" girgiza mata kai tayi tace "am sorry too Faree, please kiyafe min" girgiza kai Farida tayi tace "bakimin komiba, please kiyakuri da duk abinda nayi" tai maganan tana kallon Khaleel, rigarshi dake kan kujera yadauka ya saka sanan yazo wajen kamo Islam yay ya share mata hawayen datake ya girgiza mata kai yace "is okay, stop crying Baby" ture hanunshi tadanyi ganin yanda Farida ke kallonsu ahankali yace "bari nadan baku wuri to" yadan matso da bakinshi wurin kunnenta yace "zanje gida, but idan nadawo zamu cigaba daga inda muka tsaya" dan tureshi tayi tana kallon fuskar Farida murmushi yay ya saketa sanan ya kalli Farida ahankali yace "make your self at home bari naje gidanmu bye" tunda yake maganan takasa dauke idonta akanshi, fita yay yana kallon fuskar Islam ya rufo musu kofa.
Rungumeta Islam tasakeyi sanan taja hannunta suka zauna akan kujera tana kallon fuskarta tace "Faree da gaske kin yafemin dan Allah?" dan murmushi Farida tayi tace "how about nadafa miki wanan sweet Indomie dana ke miki agida kici kawai dan ki yadda komi yawuce awurina" cike da murna Islam tace "to tashi muje mu dafa" ta mike tsaye harda jan hanun Farida tashi Farida tayi tace "ki zauna abinki, nizan dafa miki gawayata nan ki karanta Soyayyar mu yau Fati Teejay tai posting" da sauri ta karbi wayar sabida tana mugun son littatafan faty, Farida ta kalleta tace "inane kitchen din? " nunamata tayi da hannu tareda kwanciya dan ta karanta novel din, Farida tajuya ta shiga kitchen din, Indomie biyu ta ciro da Kwai tafara dafawa, komawa tayi ta kulle kofar kitchen din sanan tadawo gaban gas din ahankali ta bude jakarta ta ciro sniper tabare ledan tabude sanan ta zuba acikin ruwan Indomie, tai maza tai grating attarugu da yawa da albasa ta zuba aruwan sabida ya kashe warin sniper, saida tagama dafa Indomie dayay mugun kyau a indo ga egg agefe ta bare sanan taje gaban fridge ta dauko sabon exotic dayay sanyi sosai ta bude ragowan sniper ta zuba aciki ta jijjiga sosai sanan tahada komi a tray tadau fork da glass cup tasaka sanan wurgar da goran sniper a bin dake kitchen din, tadawo tadau tray tabude kofa tafito falon, table taja ta ijiye mata tace "tashi tashi kici" ta mika hannu ta karbi wayarta takoma ta zauna wurin ringing tone ta shiga ta danna hakan yasa wayar tai kara ta mike da sauri ta kalli Islam da ita take kallo tace "Abba nakirana bari natafi zaikaini airport ne saisa yake kirana nadawo" Islam tadan tabe fuska tace "to Indomie mufa bazaki tsaya muciba" hararan ta tayi tana murmushi tace "sabida nai missing flight dina ko" tashi Islam tayi tsaye da sauri Farida ta maida ita ta zauna tace "dalla kekuma sai Indomie yahuce, I cook it with luv so kici da kyau bye" murmushi Islam tayi tace "Allah kiyaye hanya, I love you Faree bye" fita Farida tai daga dakin tana daga mata hannu.
Komawa Islam tayi ta kwanta ta lumshe ido danji tayi hankalin ta ya kwanta yanda Farida tadena fushi da ita, jin kamshin indomie ya ishi hancin ta yasa ta tashi ta zauna fork ta dauka ta debo ahankali takai bakinta dan yatsine fuska tayi tana tunawa tace "kaman wari warin kalanzir" hadiye wa tayi dan ba karamin dadi Indomie yayi ba, ahankali ta sake debo na biyu takai bakinta hadiye wa tayi tana yatsine fuska tace "kodai akwai kalanzir agidan nanne" exotic din ta dauka ta jijjiga sanan tabude ta zuba a glass cup takai bakin ta tana sha, cire cup din tayi tana jujjuyawa tana shinshina jikin cup din, kodai hancin tane kejin warin kalanzir dinan tasake tambayan kanta, sanyin da exotic din yayi yasa takarashe kwankwadewa ta ijiye cup din, sanan ta tashi taje gaban TV tai plugging ta kunna, remote ta dauka tasaka zee world sanan tadawo ta zauna akan kujera takara daukan fork tadebo Indomie zatakai bakine taji cikinta yadanyi wani irin kara tareda tsukewa kadan, dan zabura tayi tareda yamutse fuska but tagama period mekuma cikinta ke haka, batare data kawo komi ba takara kai Indomie bakin ta ta hadiye da kyar, tashi tayi tana shahshafa cikinta sabida yanda taji kaman hanjinta na vibrating.
[6/23, 2:07 PM] Maman Jedda: *JARABTA*
Maman Abd Shakur
51 & 52
Da kyar ta iya ta zauna akasa ta daura kanta akan kujera tana wani irin numfarfashi da baki tana cije baki tana jujjuya kafa sabida yanda taji kaman ana jajjage acikin nata, wasa wasa abu sai gaba yakeyi wani irin barje dataji cikin nata nayi yasa tawani irin buga kai akasa tana mukurkusu ahankali tace "wayyo Allah na, cikina na shiga uku" kokarin kamo kujera take ta tashi tsaye hala cikin yadena, da kyar ta iya janyo filo daga kan kujeran ta tusa akarkashin cikin nata ta, ji tayi kaman takara azaban datake jine, nukurkushewa ta dinga yi a wurin tana jujjuya kai tana dukan kasa da awahale tace "Ya Khaleel" tafara kokarin jan jiki dantai wajen kofa amma takasa ta kife kanta anan kasa tana dukan tiles din wajen da hannu, kofa taji anbude an shigo tsabagen azaban datake ji tama kasa dago kai ahankali ya tsugunna yana shafa kitson kanta daya mugun mai kyau yace "mekike yi akasa haka" yakarashe maganan yana murmushi wani karfi ne taji yadan zomata da kyar ta tashi tsaye tahau kan jikinshi ta yaye rigarta sama tana wani irin lankwashewa tanuna mai cikin ta dan tamakasa magana, adan rude ya kalli cikin ganin yanda yake wani motsi up and down da kyar tace "cikina Ya..." kasa karasa maganan tayi tawani shige jikinshi tana bangarewa, fashewa tayi da kuka sosai ta kankameshi tana wani irin mika, adan rude ya wawwaigawa baiga kowaba da sauri yaciro fuskarta daga jikinshi yace "ina Farida?" kasa magana tayi saima wani kanannade shi data sakeyi tana wani irin lankwashewa kaman macijiya tana kuka, hanunshi ya daura akan cikin wani irin motsi da kara yaji ba karamin faduwa gabanshi yayiba ciro kanta yayi daga jikin nashi ya kwantar da ita anan kasa ahankali da idanunshi dasukai jajir yace "am coming" tashi yay yay bedroom yana kwallama Farida kira "Farida Farida" har bayi saida ya bude bata, hakan yasa yafito ya shiga kitchen da sauri nanma bata harzai fito saiya hango farin leda dakuma farin marfi akasa kusa da bin, hakanan yaji zuciyar shi bata kwantaba shiga kitchen din yayi yana kallon ko'ina dan wari warin magani yakeji, digon wani abu daya gani akan fridge kaman mai yasa yasaka yatsa ya dangwala yakai hanci ya shinshina warin magani yaji kaman kalanzir da sauri yakoma wurin bola inda yaga farin marfi akasa ya daga yakai hanci same wari yaji tashi yayi yana kalle kalle bolan ya leka ganin Goran sniper a kwance cikin bolan yasa yaciro yana kallon goran dan yasan babu irin goran nan agidan, harda dan gudunshi yakoma falon plate din Indomie daya gani yaje yadaga yanama abincin wani irin kallo, shinshina abincin yayi da sauri ya ijiye yadau juice din ya tsiyaya a cup abu kaman maimai dayagani a kwance kan saman juice din cikin cup din yasa ya dafa kirjinshi jin yanda ya buga da karfi yace "innalillahi wa innailaihi raji'un" harda dan gudunshi yazo inda take kwance tana wani irin numfarfashi tana kuka yace "waya baki abincin chan shikikaci?" kasa magana tayi saima wani irin kukkule ido datake yi tana bubbuga kanta