Showing 9001 words to 12000 words out of 68203 words

Chapter 4 - JARABTA 1 TO END Book Complete Document hausa novels by Maman Abdul Shakur--.txt

M Shakur   

29 Dec 2024

8270

saisa duk idan Abba yay zakka yake bashi" shiru yayi yana sauraron shi hakan yasa Yusuf yace "gaskiya yau zakayi aski gashin nan naka yataru dayawa ga sajenka yay bususu, idan zamu koma saimuyi branching barbing saloon ko" shiru yayi baice komiba haka Yusuf yay ta janshi da hira sabida Ya Mustapha yace adena barinshi alone adinga yawan mai hira, Kuma Alhamdulillah ga so much improvement yanzu yau dakanshi yaje dakin Goggo at least yana amsa magana, jiyama shiya koyama Fa'iza assignment dinta, gashi yau ya yarda yabiyoshi sunfita. Lumshe ido yasake yi ya maida hankalin shi sosai Kan tukin dayake yi yana tunanin zuci yace "Ya Allah ka warkar da bawan nan naka gabaki daya, ya Allah kadawomai da farin ciki rayuwar shi, ya Allah kasanya mai danganar rashin Aisha kabashi wacce tafita, itakuma Allah ka jikan ta" haka yayta tunanin zuci harsukakai kai kofar gidan Malam Isya. Parking yayi yafito yadawo ta bangarenshi ya budemai kofan yace "zomu shiga ciki" yatsine fuska yayi "am not going" murmushin jin dadi Yusuf yakara yi ganin yanda yay dogon magana yau yace "okay I will be right back bazan dadeba". Barin wajen yayi shikuma yadan kwantar da kujeran yay relaxing bayan shi tareda lumshe ido.
Dadan sauri take tafiya wanda yay kama da ahankali, goyone abayan ta wanda yarinyar data goya ke kuka sosai kaman ansatota adaburce Yarinyar tace "yakuri Miemie gawani shago chan muje nasai miki ruwa" ahankali takara sauri harta wuce motarsu Yusuf, Dumm yaji kirjinshi yawani irin mugun bugawa, hannu ya daura akan kirjin tareda kara lumshe idanunshi.
Karasawa tayi shagon abirkice tacema mai shagon "Malam a bani ruwa guda daya" kwanto Miemie tayi daga bayanta tariketa a hannu sanan ta ciro naira hamsin daga jakanta tabama mai shagon takarbi pure water tasa abaki ta bude, sama yarinyar tayi abaki da sauri yarinyar tafara zukan ruwan hakan yasa budurwan tasaki wani murmushin kwanciyan hankalin tace "dats my gurl dama kishi kikeji shine kikemin ihu kaman nasa to kiko, ke wlh Miemie kin iya jarababben ihu" ganin yarinyar na neman shanye ruwan yasa ta fizge daga bakinta tace "cikin ki zai fashe, is okay Miemie" wani irin ihu yarinyar tayi da saida ya amsa ko ina a anguwan dan ihu tayi kaman an yankata, ahankali ya bude ido yana waige waige jin ihu dan kokadan yanzu bayason hayaniya, idanunshi ne suka kai kan yar karaman yarinya dake kan shoulder wata data bashi baya tana jijjiga yarinyar.. "Miemie I promise bazan kara fita dakeba, saidai nabarki agida, sai mutum zai fita kiyita binshi kina kuka kaman zaki mutu inmun fito kiyita min kuka" Mai shagon ne yay dariya yace "hajiya ai haka yara suke ungo chanjin ki" ahankali ta juyo sabida batason ta tada Miemie dataji tafara gyangyadi akafadanta chanjin takarba daga hanun mai shagon sanan ta juyo... Goge idanunshi yayi dan yakara tabbatar da abinda yagani lips din shine suka fara rawa "My.. My... My.. My Eee.. My Eesha".
[6/9, 3:34 PM] Maman Jedda: *JARABTA*




Maman Abd Shakur


11...
Bude marfin mota yayi yafita ko kulle kofan baiyiba yawuce wajen shagon da sauri kaman zai fadi yakarasa wajen daidai tagama goya Miemie abayanta, dan jakanta ta dauka daga kan table din wajen ta rataya akafada sanan ta juyo, mutum tagani agaban ta ya tsaya chak yay folding hannu akirji yanawani irin kallonta, wani irin mugun tsoro yabata daga juyawa tadau jaka saiga mutum abayanta kaman aljani ta ina yafito. Addu'a tafara azuciyar ta kafin tayi gefenshi sadaf sadaf zata wuce yace "My Eesha" ta gefenshi take kokarin rabawa ta wuce kai tsaye yakara tare ta yana sake kallon fuskar ta yace "My Eesha?" ahankali yarinyar ta kalli gefenta da bayanta dan kara tantance dawa yake magana "Eesha yimin magana, talk to me mesa kika gudu kikabarni eh" matsawa baya tafara yi dan yanzu tafara tabbatar da aljanine wanan dan jibi uban gashin kanshi wanda yafi na Miemie yawa, gabaki daya jikintane yafara bari takoma baya ganin kaman zai sata ajikin shine, hanunta ya kama ya rike gam adan rude, cike da murna, da murmushi yace "My Eesha am soo happy" yakara kamo dayan hanun nata ya rike arude yace "wlh is real, kece fa my Eesha maisa kika tafi kika barni for more than a year eh" da karfi ta fizge hannayenta bakinta har rawa yake tace "stop touching me, kai waye kaganni kawai kafara tabani" share kwallan daya gangaro mata tayi tace "niba Eesha bane" tajuya da sauri zata bar wajen dan idan takara minti biyu da mutumin nan wlh zata iyayin fitsari ajiki, hanunta ya kama ya fizgota saida ta bugu dashi yana mata wani irin kallo yace "is you, karya kike, kece, Aisha nane ke" ya nuna fuskar ta, kokarin fizge kanta take ganin yaki sakinta yana kallon ta kaman zai cinyeta yasa tafara waige waige, mai shagon nan takira da muryan kuka tace "Mallam dan Allah zoka rabani da bawon Allahn nan, wlh, wlh niban sanshi ba, dan Allah kataimake ni" takarashe maganan tana sheshekan kuka, fitowa mai shagon yayi ya kalli Khaleel da hankalinshi nakan yarinyar daya rike gam yace "Yallabai lpy dan Allah maike faruwa ne" kaman zai hadiye ta da kallo yasake rirrike shoulder dinta yana kallon fuskarta ko kyaftawa ba yayi batare dayama bi takan mai shagon ba yace "My Eesha plz come with me, zomuje gida, su Ammi sunyi kewanki sosai, please karki sake barina kinji" yakarashe maganan gwanin ban tausayi, ahankali taji fitsari na gangara yanabin cinyarta tunda take bata taba tsorata da firgita irin nayau ba sosai kuka keson ya subuce mata,, ahankali ta kalli fuskar mai shagon tace "wayyo Allah na, Mallam na shiga uku wlh ni bansan Shiba, dan Allah karabani dashi, na shiga uku... " "stop saying bakisanni ba it hurts" wani irin tsawa ya daka mata ya daura hanunshi daya akan kirjinshi jin wani irin zafi, hakan yasa ta fashe da kuka tsabagen firgita yasa ta mika hannu tana kokarin kamo rigar Mallam mai shago daya tsaya yana kallon ikon Allah, mutum daizai rirrikeka haka tabbas yasankane to ita ya akayi take cewa bata sanshi ba. Bayason ya shiga case din dan daga ganin motar Yaron yasan dan masu kudine shagon nan nashi dashi yake ciyar da Mata yen shi da yayan shi, ganin anzo siyan abu yasa yakoma cikin shago, sosai tafashe da kuka tace "Mallam dan Allah kadawo karka banni dashi" "My Eesha" yakira sunanta, ahankali yace "muje gida" hanunta yakama yanaja ihu tafarayi da karfi ta tace "Wayyo Allah na shiga uku, dan Allah ka sakeni, Wayyo Allah nabani" ganin yakai ta gaban wani mota yana shirin budewa yasa tai dabara ta take kafarshi hakan yasa yasaki da sauri sabida hill din yamai zafi akafa sosai, da gudu ta arce hakan yasa yabita da gudu shima yace "no my Eesha don't leave me again, dan Allah come back" sosai take gudu ga Miemie abayanta tana kuka, yana binta.
[6/9, 8:14 PM] Maman Jedda: *JARABTA*




Maman Abd Shakur


12...
Da kyar ta tseremai ta labe awani lungu tana haki sosai da tari, tunda take batajin ta tabayin irin gudun nan datayi yauba, dafe kirjinta tayi dan jitayi kaman zai fito sabida yanda yake bugawa, jin kaman motsi yasa tafice daga lungun da sauri ta bullo wani anguwa dat is very quiet mai kyau, da dan gudu gudu takara sa gaban wani katoton gida dakeda brown gate, bude gate din tayi ta shiga ciki da sauri, katoton gidane dakeda flowers a tsakar gidan sai motoci kusan biyar a compound din, ahankali take tafiya dan ta bala'in gaji kaman zata fadi sai zufa take kofa ta bude ta shiga babban sitting room din da aka rabashi bangare biyu bangare daya ansanya kujera Kiran royal brown sai dayan Kuma asha ga wani makeken tv bango daketa aiki shi kadai danba kowa adakin, maida kofar tayi tarufe sanan tadaura kanta akan kofar tareda da lumshe ido ta dafe kirjinta tana sauke ajiyar zuciya, wata matace mai aikin su da akalla zatai 30 tafito daga kitchen dauke da katon food flask tazo dining ta ajiye zata juyane ta hango ta tsaye a jikin kofa, dan murmushi tayi ta karaso cikin falon cike da fara'a tace "a'a su Anty Islam har an dawo ne" ahankali ta bude ido murmushi ta kakalo ware ido Matar tayi tana kallonta ganin yanda idanuwan ta sukai ja tace "Islam badai ahaka zaki koyi rainon bako yanzu Miemie ne tasa kika galabaita haka harda kuka" hannu takai dan ta kwanto kyakyawar baby da tunda ta ganta take tsalle a baya dan ta dauketa, kwanto ta Islam tayi ta mika mata murmushi matar tayi tace "oyoyo an babyn mamanta, iyye andawo daga anguwa ne da Anty Islam" dariya yarinyar takeyi sosai kaman ba ita ke shegen kukan nan ba, zanin goyon Islam ta mika mata sanan tawuce wajen stairs hawa tayi ta tafi sama, dogon corridor ne da dakuna kusan shida a wurin, wani kofa ta bude ta shiga dakine dake dauke da gadon yan boarding house saidai shi wanan na katako ne da akamai fenti pink, bunk biyu ne kadai adakin sai center carpet shima pink, da study inda uban littatafai kekai, gaban wardrobe taje ta tsaya tana kallon mirron dake jikin kofan wardrobe din ahankali takai hannu ta warware rolling din gyalen dake kanta dogon gashinta ne ya warware ya zubo har kirjinta dan tsaki tayi ta ciro ribon din daya hade da gyalen ta kama gashin, doguwar rigan jikinta tacire tabar shimi da sket ajikinta kan gado taje ta kwanta tareda sauke ajiyar zuciya dan har yanzu kirjinta bugawa yake.


Harwajen motansu Mallam isya ya rako Yusuf yana karamai godiya ganin marfin mota abude yasa Yusuf ya bude bangaren shi da sauri ganin ba Khaleel aciki yasa ya fara waige waige adan arude, Malam Isya ne yace "lpy Yusuf" arude yace "nabar Khaleel a mota bangan shibane" ganin yanda ya rude yasa yace "karka damu bari mudan tambaya" samarin dake gaban shagon Adamu yatambaya dan Allah kunga wani matashi bako nane" da sauri Yusuf yace "yanada gashi sosai akai" da sauri mai shago yace "to kodai wanan wanda ya rike yar mutanen ne yace yasanta? Dan naga gashi rututu akanshi" da sauri Yusuf yace "shine a ina ka ganshi?" "anan gaban shago na ya rike wata yarinya datasai ma wata yar baby ruwa yanace mata Eesha wai sutafi gida" ahankali Yusuf yace "Eesha kace?" "eh haka naji yanata kiranta nidai" "to yanzu ina suke" "Naga tagudu yabita chan sukayi" Ya nunamai hanyar dasuka bi da gudu Yusuf yabi hanyar da aka nunamai hankalinshi atashe.
Akarshen layin Yusuf yaganshi ya zauna akan wani dakali ya rike kanshi, karasawa wajen Yusuf yayi ya daura hanunshi akan kafadar shi, dago kai yay ya kalli Yusuf da idanunshi dasukai jajir, zama Yusuf yay kusa dashi ahankali yace "Khaleel wat is d matter?" murmushi yay mai ciwo yace "yau naga wata da ta tunamin da Eesha, for a second I tot she was my Eesha, yanda Eesha ke tafiya haka yarinyar ke tafiya" shiru yadanyi kafin yafuzar da iska yace "I think am loosing my mind" hanunshi Yusuf yarike gam ya girgizamai kai Yace "Khaleel Eesha tariga ta rasu bazata taba dawowa ba, and inhar son dakake mata is real kamata yayi kadawo normal kai kaman yanda kake da, kazaci inda Aisha na nan she will be happy da yanda kadawo ne? Bakama mutane magana, bakacin abinci kullum kana daki Ammin ka kullum saita kira Umma kusan 5 times tana tambayan jikin ka, duk ka rikita gabaki dayan family mu is that fair do you think Aisha zatai murna dajin labarin nan?" shiru yayi kawai yana kallon Yusuf, tashi Yusuf yayi daga dakalin yace" mutafi "ahankali ya sauko daga dakalin waigawa yasake yi kafin yajuya sutafi.


"Islam, Islam" ahankali ta bude ido, wata yar budurwa ce wacce suke kai daya da Islam tana sanye da doguwar rigar atampa ja take tashin ta, yatsine fuska tayi cikin muryan bacci tace "uhnnn wat Farida" yaye bargon data lulube dashi Farida tayi tace "kitashi" juyawa tayi ta kife cikin muryan bacci tace "leave me aloneeee" tsaki Farida tayi tahau up bonk dinta ta kwanta abinta, tsaki tasakeyi tace "Islam" shiru tamata bata amsaba, hakan yasa tai kwafa tace "okay o dama Anty Hindu ne tazo kinsan ta very well" zabura tayi ta tashi ta zauna ware manyan idanunta tayi, leko dakai Farida tayi daga sama ganin ta tashi ta zauna yasa tai dariya, juyo dakai tayi ta kalli Farida hannu tasa ta dafe goshinta tace "Faree please da gaske tazo?" gyada mata kai Farida tayi, da sauri ta tashi gaban wardrobe taje zaro wani abayan ta baki tadaura akan dan singlet din dake jikinta ta wuce tafita daga dakin.
[6/11, 9:19 AM] Maman Jedda: *JARABTA*




Maman Abd Shakur


13...


Juyowa kakkyawar matar tayi tace "Islam yaushe kika tashi Farida tacemin kanki na ciwo sannu ko, kinsha magani?" Gyada mata kai tayi sanan takara matsowa kusa da Mum tai wani kini kini da fuska kaman zatai kuka da murya chan kasa dan tasan Allah yama Anty Hindu baiwar kunne tace "Mum wai mesa tazone, yanzu dukzata damu mutane da masifa" murmushi kawai Mum tayi ta girgiza kai tana arranging abincin a babban tray mai kyau tace "yayar mahaifin nakine kike cewa haka akanta ko yaran zamani, matsamin kiga na wuce jekiyi salla" fita Mum tayi ta barta a kitchen din, fitowa tayi takoma sama tana shiga daki Farida ta fashe da dariya tace "our Baba sister don land again" tsaki Islam tayi tana balle boturan abayan datasa Farida tace "wlh ko yau datazo jinayi kaman inyi kuka shikenan yanzu mun shiga uku" abayan Islam ta wurga akan gado tai hanyar bathroom Farida tace "Islam wai dan Allah mesa Anty Hindu batason muna kiranta dawani suna kaman irin su Mama, Inna ko Goggo tunda dai yayar daddyn muce amma saidai muce Anty Hindu" hararan ta Islam tayi tace "go and ask her" tabude bathroom tashiga batare data karabin takan taba, daga murya Farida tayi tace "okay nikikema iskanci ko next time bazan rufamiki asiri ba wlh" daga bayi tadaga murya tace "eh karkiyi din" dariya Farida tayi dan tasan abinda zatayi. wanka tayi tareda dauro alwala tazo tai sallan magrib sanan ta kalli Farida dake daddana waya tace "Daddy is back zomuje muyi dinner" sakkowa Farida tayi suka sauka kasa, afalo aka zazzauna yara mazane manya guda uku biyu manya sai karami da bazai wuce 5 years ba akan cinyar Daddy duk ana zaune anacin abinci, gaishe da Daddy sukayi ya amsa musu sanan suka zauna kusa da Mumy, rice ta zuba a plate da pepper soup na goat meat, spoon tasa a abincin tanata wasa dashi takasaci tunanin abinda yafaru yau kawai take, tunda ta sakko Daddy ke lura da ita, dan gyara murya yayi yace "Islam" da sauri ta dago kai ta kalli Dad ahankali tace "Na'am Daddy" "meke damunki?" murmushi tayi da sauri ta girgiza kai tace "bakomi Daddy kaina ke ciwo har yanzu" Yayan ta Abdallah dake gefenta mai kimanin 25 years ne ya kalleta yace "kinsha magani?" gyadamai kai tayi, murmushi yamata yace "eat to ko kadanne" rice din tadebo takai baki tafaraci.
A massallaci suka fara tsayawa sukai magrib sanan suka wuto gida. Part dinsu suka wuce, direct bayi ya shiga yay wanka yafito sanye da bathrobe white ajikinshi ganin Yusuf baya dakin hakan yasa ya zauna akan kujera lumshe ido yay nayan sakkanni da sauri ya bude tareda fuzar da iska tashi yayi yaje gaban wardope ya canza zuwa milk color jallabiya, tsayawa yayi agaban madubi yadau turare a fesa, wayar shi yagani dake jikin madubi hakanan yaji yanaso yakira Ammin shi, daukar wayar yayi yakoma kan kujera ya zauna yay dailing number Ammi ba karamin mamaki Ammi tayiba dataga kiranshi na shigowa ba, ringing biyu ta dauka cike da murna tace "Son" har cikin ranshi yaji wani irin natsuwa, ahankali yace "Ammina I missed you" share hawayen daya zuboma Ammi tayi da sauri azuciyar tako godiya takema Allah, Allah na godema daka amsa addu'a ta, ya Allah kadawo mai da farin ciki da walwalan shi back, ka bashi mace tagari wacce zata maye gurbin Aisha. "Ammina are you there" da sauri yace "yes Son, ya kake hope kanacin abinci sosai ko" Ahankali yace "eh" murmushi sosai tayi tace "are you okay" shiru yayi baice komiba cikin wani irin muryan lallashin yaro tace "how about tomorrow kayi your two fevorite thing, read your Quran, and kaje ka buga kwallo ko kaje stadium ka kalli kallo anyone dakayi is okay" murmushi mai kara yay tunawa da dafa Ammin ce ke masifa duk idan yaje kwallo, murmushi yasake yi yace "okay Ammi bari naje nai salla" katse wayar yayi yatashi yafita dan zuwa massallaci.
Washegari da safe yadade yana karatun AL qur'ani da muryar shi mai dadi, sai wajen 9 yarufe ya ijiye haka nan yaji kaman ancire mai wani nauyi dake damunshi arai, yajuya ya kalli Yusuf dake bacci abinshi, bathroom ya shiga yay wanka yafito ya shirya cikin brown shirt, short sleeve ne hanun rigar ya kama muscle dinshi hakan yakara bayana girman muscles din, dogon black jeans yasa dayamai kyau sosai ya dauko turaren shi ya fesa, ya zira takalmin shi Prada, agogon da Eesha ta bashi ya dauka daga gaban mirror, shafa agogon yayi yay shiru yana kallonshi, ahankali ya daura ahannun shi sanan yadau car key dinshi da waya yay hanyar fita daga dakin, da Goggo yacikaro tana dauke da tray hakan yasa ya karba tace "ina zaka haka?" komawa dakin yay da tray din tana biye dashi abaya yace "inaso nai aski ne" washe hakora tayi danba karamin dadi tajiba tace "toai saikayi break ko, kaga dakaina fa a hadama, ina Yusufa" muryan Yusuf sukaji daga bedroom cikin bacci yace "tsohuwar nan kidena batama mutum suna, niba Yusufa aka yanka rago aka samin ba" hanyar bedroom din Goggo tayi tace "uwar kace tsohuwa, katambayi Sama'ilan koni saida na yanka maka rago da aka haifeka" da sauri Yusuf yaja bargo ya rufe kanshi jin ta shigo bedroom din, duddu Goggo ta zubamai Abaya tace "dan kan uba" ihu sosai Yusuf yayi abin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login