Showing 60001 words to 63000 words out of 68203 words
Chapter 21 - JARABTA 1 TO END Book Complete Document hausa novels by Maman Abdul Shakur--.txt
mika mata ta karba ya dauko bottle water ya budemata shima ta karba tasha tanata kallonshi, ahankali ta tsulalle ta tsugunna wajen window tanajin wani irin kuka kuka, zafi zafi, fushi fushi, daci dacin dabatasan ko nameba taji tanaji, gawani irin abu daya tokare mata zuciya, kallon Farida yayi dakeci ahankali tanata kallonshi tana sauke ajiyar zuciya yace "bari naje gida zan dawo anjima" gyada mai kai tayi yafita daga dakin. Fitowan shi data gani yasa ta mike da sauri tabi bayanshi ko kallonta baiyi ba saida yakai wajen motar su sanan ya juyo ya kalleta, shi itama take kallo da idanunta dasuka dan chanza kala zatai magana ya tari numfashin ta yace "basai kinbani ba kiyi zaman ki agidan ku zan aiko miki da takardar ki sabida afara shirye shiryen aurena da Farida" yabude mota ya shiga batare daya jira mezatace ba suka bar hospital din, jingina tayi dawata motar dake wurin jin zata fadi kafin ta tsugunna tana wani irin numfarfashi kaman mai asma, wani irin kukane taji yazo mata wuya ba shiri tafara rera shi.
[7/2, 9:28 AM] Maman Jedda: *JARABTA*
Maman Abd Shakur
75 & 76
Tadade tsugunne a wurin tana raira kuka kafin ta mike tsaye da kyar ta share fuskarta da kyau tabar wajen tana tafiya kaman zata fadi sabida rashin karfi, ahankali ta tura kofar dakin da sallama ta shiga Mummy ce kadai zaune tana waya kaman ma da Abbane sai kuma Farida dake rungume da gwangwanin pringles din dayabata tana bacci, karasa shigowa dakin tayi ta maida kofar ta rufe, katse wayar Mumy tayi ta kalleta tace "me kuma kikeyi anan bakibi mijin naki bane?" girgiza kai tayi ta karaso gaban Mumy ta tsugunna ta daura hanunta akan cinyarta ahankali tace "Mummy dan Allah kidena fushi dani kiyakuri kinji" wani irin murmushi mai ciwo Mum tayi ta ture hanunta daga jikinta tace "Islam kenan inda kin kirani da sunana ai dayama fi dan kin dade da nunamin cewa nibani na haifeki ba, hakurin me kika bani iye? Mekika mini?" share kwallan daya zubomata tayi da bayan hanun muryar ta har rawa take tace "Mumy wlh bani bane kawai naga Abba yakaini gidanshi ne, ni bansan ya akayi ba dan Allah mumy am sorry" "are you?" Mum ta tambaye ta tana mata wani irin kallo, gyada mata kai tayi, dan shiru Mum tayi sanan tace "ai ga Faridan nan kinsa mata ciwon zuciya inta mutu ai duk a dadin ki saikiyita rayuwan ki da Khaleel tunda miji yafi miki yar uwa, Islam ni kikama abunan, ni Islam" ta nuna kanta da yatsa, "ni dana raineki uwarki nafama da sikila, oh duniya kenan, yata ke wahala haka sabida ke Islam" girgiza kai tayi tafashe da kuka sosai, tsawa mum ta daka mata tace "wuce, fita daga dakin nan, karki kara shigowa, nidai ba Mummy ki bace daga yanzu, ki nisanta kanki daga yata tariga ta hakura da mijin ki, kuyita shagalin ku, itama Allah zai bata wanda yafishi, yinan" ta nuna mata kofa, kasa fita tayi saima wani sabon kukan datake tana shashare fuska da hijabi, hakan yasa mum ta nunata da yatsa tace "wlh idan kika tadar min ya daga bacci bazan barki ba zan mugun sabamiki, ki wuce ki fita kafin na kaimiki hannu munafuka, nafada miki nidai ban tsaneki ba, bakimin komiba, kuma bazan taba cutar dakeba dan nima banason acutar min da ya, amma kawai dai bani bake ne, kuma ki rabu dani da yata, dama baban kune yahada mu to acigaba a hakan, wuce kawai kifita" sum sum sum tawuce tafita daga dakin ta zauna anan kujerun da aka jera a gaban record inda patient ke jiran folder tana kuka tana shashare fuska. Haka ta zauna awurin o har azahar tawuce tafita taje massallaci tai alwala tai salla ta dawo takara zama a wajen saiduk taji tagaji gawani irin yunwa datake ji, bini bini mum na fitowa saidai ta watsa mata harara takoma ciki, gashi babu wani dan gidan su dayazo balle tadanji dadi, itane azaune awurin har la'asar, duwawun ta har zafi yake sabida zaman kujera, ta tashi ta wuce massallaci tai salla, kwanciya tayi awurin har dan gajeren bacci yay gaba da ita wuraren biyar ta tashi tafito ta wanko fuska tadawo cikin hospital din ta zauna a wurin tanata kallon dakin jin hanayina, ganin Mum tafito ta wuce ta kara zuba mata harara yasa ta mike tsaye tana waigen Mum ganin tai nisa yasa tayi dakin, Khaleel tagani wanan Karan ya chanza kaya zuwa Jean da riga ya zauna akan kujera yana kokarin bude takeaway daya yoma Farida da idonta biyu sai kallonshi yake, dan karasa shigowa dakin tayi tana satan kallanshi, Farida ne ta kalleta dayar muryar ta dabata fita da kyau tace "tun dazu natashi inata tambayan ki ina kikaje?" murmushi ta kakalo tazo kan gadon ta zauna ta wurin kafar Farida tace "ina mosque ne nai salla sai bacci ya kawasheni" tai maganan tana satan kallonshi, dan murmushi yayi ya kalli Farida yace "Mac and cheese ne nakawo zakici ko? Lemme feed u" gyadamai kai tayi tana soft murmushi, fork yasa aciki zai debo yabata da sauri ta tashi ta karbi take away daga hanunshi bakinta har rawa yake tace "un zan.. Zan.. Ni zan bata" ita kanta batasan yaushe tai hakan ba, dago kai yayi ya zuba mata ido itama shi take kallo da kyar ta janye idonta daga nashi jin kwalla yataru ta juya ta kalli Farida dake kallon su tace "is being long bari nizanyi feeding dinki" debo wa tayi takai bakin Faree ahankali ta bude ta karba tana murmushi, shima murmushi yay aranshi sanan yaciro wayarshi daga aljihu yana dannawa bini bini yana satan kallonta.
Saida ta cinye sanan ta ijiye take away a gefenshi tana kallon fuskarshi amma yaki kallonta komawa gefen Farida tayi ta zauna tana Satan kallonshi ganin wayarshi yake ta daddanawa abinshi, dan gyara kwanciya Farida tayi tace "what are u doing Mk" dago kai yay ya kalleta ya sakin mata murmushi yace "kinaso kigani?" gyadamai kai tayi, ya matso da kujeran dayake kai jikin gadon ya nuna mata wayar hakan yasa tadan matso da kanta tana kallon wayar game din ball yake bugawa hakan yasa tadanyi kara ashagwabe tace "nito ai ban iya wanan game dinba kamin bayani" dan gyara zama yay ya saci kallonta yanda take kallonsu kaman idanunta zasu fado kasa yace "kinga wanan shine goal keeper, ga defender, ga midfielders sune yan tsakiyan nan, ga referee shine mu hura wusur, sukuma linesman dinan suke assisting referee, ga strikers suke gaba" janye fuskarta tayi daga wayar ta kalli fuskarshi tace "haka kasan kan kwallo Mk" batare daya kalleta ba yay murmushi yace "best sport dina kenan" ahankali ta mike daga kan gadon zata fita hakan yasa Farida ta kalleta tace "ina zaki kizo mijin ki ya koyamana yanda ake kwallon tare" dan lumshe ido tayi dan sosai takeson danne hawayen dake zuwan mata sanan ta budesu tajuyo tace "namanta da abu a massallaci ne am coming" da sauri ta juya tafita, dan murmushin gefen baki yayi ya kalli Farida yace "ya karfin jikin?" murmushi tayi tace "Alhamdulillah na warware" tashi yayi yace "zan tafi saikuma gobe" da sauri tace "to kajira Islam din tazo saiku tafi" murmushi yay yace "baki da lpy, ai nace ta zauna ta kula dake idan kin warke sainazo na dauketa mu koma gida" sosai abin yamata dadi tace "thank u so much Mk bye" bye yamata yafita daga dakin yana waige waige yana nemanta, fita yayi yanata Kalle Kalle kozai ganta hango ta yayi karkashin wata bishiya ta zauna tanata share kwalla, kasa daurewa yayi ya karasa wurin kamshin turaren shi kadai taji ta dago kai tana kallon fuskarshi daure fuska yayi yace "lpy kike kuka ko bakida lpy ne?" girgiza kai tayi hakan yasa ya tabe baki yace "dama nazo nabaki takardar kine, dan rikemin" yay maganar yana mikama ta byro ya kai dayar hannu aljihu kaman zai ciro wani abu ba karamin racing heart dinta yake ba da kyar har wani irin runtse ido take tace "ta.. Takardar mene?" tsayawa yay da tura hannu aljihu yace "bakince na sakeki ba na auri Farida, am coming jirani anan kaman nabarta takardar a mota" , mikamata byro yayi yace "rikemin wanan bari na dauko takardar saina rubuta miki" bai jira mezatace ba yajuya yay hanyar mota, batasan mesaba amma wani irin kunci da bakin ciki da tsoro taji ya diran mata arai, yar da byron tayi a wajen ta juya da sauri harda dan gudu tai hanyar massallaci ta shiga bangaren mata harda jan kofan tana rufewa ta zauna kirjinta na bugawa sai zazzaro ido take.
Koda yadawo bai ganta a wurin ba bakaramin dariya yayiba harda rike ciki komawa mota yayi ya shiga ya tada yabar hospital din.
Sai bayan magrib ta koma ward din dakin ta shiga lokacin Abba da Anty Hindu da Mummy duk suna wajen gaishe su tayi, Anty Hindu tace tabi Abba su tafi gida ta huta tunda mijinta yace anan zata kwana gobe da safe tazo, Abba tabi da Mumy dan Anty Hindu ke kwana da safe kuma mumy tazo ta wuni.
Wuraren 9 na safe ta sakko shirye cikin doguwar rigan atampan ta na gida tadauko hijabi ta rike da Mumy taci karo tafito daga kitchen rike da kula a shirye zata tafi, wani mugun kallo ta wurga mata tace "ina zaki, karna naji kince asibiti, ba nace ki nisan cemu, nida ita bama bukatar ki Islam kirabu damu, wlh inhar na ganki a asibitin nan kome namiki kekikasiya da kudin ki" wucewa Mum tayi tafita daga dakin ranta abace ahankali ta sulale ta zauna akasan wurin tafashe dawani irin mugun kuka batasan ma meke mata dadi ba tarasa inda zata sa kanta, takai kusan minti 30 tana kuka gashi ba kowa a gidan sai ita, tashi tayi ta zauna akan kujera tai tagumi daga baya kuma ta kwanta tana ijiyar zuciya, sake tashi tayi dan tarasa meke mata dadi hijabin tasaka tafita waje ta zauna kan bencin me gadi tana kallon mutane daidai dake wucewa alayin nasu idanun nan nata sunyi fayau sun kumbura, wani dan yaro da bazai wuce 2 years ba tagani yafito daga wani gida dake facing nasu ya shiga hanya yana wasa da bindigar ruwan hanunshi ga mota na zuwa da sauri ta mike tsaye da gudu taje ta dauke yaron daga kan titin tanamai murmushi har motar ta wuce, yaron mai kyau dashi gashi dan lukuti tace "mesa kafito kai kadai waje", daidai lokacin wata yar mata haka dabazata wuce 25 ba tafito sanye da dogon hijab.
[7/2, 2:18 PM] Maman Jedda: *JARABTA*
Maman Abd Shakur
77 & 78
Ta karaso inda suke tsaye tace "laaa nan kayo Sadiq daga shigana wanka fa" murmushi Islam tayi ta mika mata yaron, karban shi tayi tace "nagode, nanne gidanku bansan kowa a anguwan ba, jiya jiyan nan mukazo daga Abuja biki gidan baban shi, gidan yacika ne saisa mukazo nan gidanmu, Ya sunan ki?" gyada mata kai Islam tayi ta nunama ta gidansu tace "ga gidan mu nan" matar tace "ba shakka" juyawa Islam tayi ahankali tace "bye" komawa kan bencin tayi ta zauna hakan yasa Matar tabita da kallo kasa tafiya tayi saikuma tadawo inda Islam take, hakan yasa tadaga kai ta kalleta murmushi Matar tamata tace "Sunana Husna Maman Sadiq mekike yi ke kadai awaje?" jitayi kaman ta fama mata ciwo hakan yasa kwalla yataru a idonta, kawad dakai tayi da sauri tace "bakowa ne agidan mu saisa" "ayya to zomuje gidana muyi hira nima ai sai anjima bayan sallan la'asar baban shi zaizo ya daukeni muje dinner, zomuje" maida Sadiq tayi hanun haggun ta, tasa hannun dama takamo hannun Islam kaman tasanta, tashi Islam tayi ta bita badan tasoba suka shiga gidan gidane dan daidau mai kyau dashi ko ina sai kamshi yakeyi zaunar da ita kan kujera tayi sanan tacire hijabi ta ijiye nan kan kujera ta wuce kitchen ta kawo mata drink mai sanyi da snacks ta ijiye mata a gabanta sanan ta zauna kusa da ita ganin tanata kallon Sadiq dake wasa da kayan wasanshi anan tsakiyar falon tace "baki fadamin sunan kiba kawas" juyoda kai tayi ta kalleta ahankali tace "Islam" baki tarike tace "waiwaiwai Islam no wonder kike da shagwaba ai duk masu sunanku haka suke inada kanwa ma haka sunanta Islam" murmushi kawai tayi tace "ni bana shagwaba" "shine dan amfita an bakki ke kadai kike ta kuka ga idanun kinan sunyi jajir" da sauri Islam ta kalleta, dan murmushi tayi tace "bahaka bane kawai" shiru tayi tasa bayan hannu ta goge idanunta, ita kadai tasan yanda takeji bakaramin zafi kirjinta yake mataba, da hijabin ta lullube fuska jin wani irin kuka yazo mata sosai take kukan mara sauti tana wani irin sauke ajiyar zuciya, hanun Husna taji akan hijabin ta janye daga fuskarta hakan yasa tadago rinannun idanun ta kalleta da sauri ta tashi zatabar dakin Husna ta rikota "ina zaki?" Ahankali tace "gida zani" girgiza kai Husna tayi tace "zoki zauna babu inda zaki saikin fadamin meke damunki, zonan mai sunan kanwata" zaunar da ita Husna tai akan kujera sanan taja center table ta zauna agabanta tareda mikamata ruwa ta karba tasha kadan ta ijiye, dafata Husna tayi tace "mecece matsalar Islam? Wanan kuka haka bana lafiya bane? Bansan kiba amma wlh daga ganinki jinai kaman naga yar kanwata, kifadi mini matsalar kona taimaka miki da shawarwari dakuma addu'a" hartagama maganan bata dena kallon Husna ba girgiza kai tayi tace "bakomi kawai kawai" takasa magana "zurfin ciki na halaka mutane fa, yana sakaka cikin matsaloli dabaka taba zatan zaka shigaba, idan bazaki fadimini ba bazan takura kiba dan nasan yau kawai mukasan juna baki saba daniba, amma dai kidena saka damuwa aranki karya jamiki wata matsalar kinji mai sunan kanwata" gyada mata kai tayi tana tunanin maganganunta zurfin ciki da rashin fadama Farida labarin Khaleel tun lokacin data hadu dashi shi yajawo musu wanan matsalar fa, da sauri ta kalli Husna ahankali tace "zan fadamiki please bayan nagama fada miki ki gayamin me kuskurena" murmushi Husna tamata tace "ok inajinki to" shiru tadanyi kafin tace "Ya Khaleel ne matsala ta" saikuma tai shiru kaman tana tunanin wani abu Husna tace "waye Ya Khaleel" dan ijiyar zuciya ta sauke sanan tace "mijina" shiru tasake yi sanan tadago kai tasake kallon fuskar Husna hakanan taji zuciyar ta ta natsu da ita ahankali ta shiga bata labarin tun ranan farko tada fara haduwa da Khaleel filla filla har zuwa yau da safe abinda yafaru tagama labarin duka tana matsar kwalla kafin ta kalli Husna datai tagumi tana kallonta, tagumi Husna tacire tareda sauke ajiyar zuciya tace "wlh Islam kin tafka uban rashin hankali, ai gwara ya sakekin tunda ke banza ce mara wayau" da sauri ta daga kai ta kalleta kirjinta na bugawa, hararan ta Husna tayi tace "eh mana bake mai yar uwa ba kinacema mijinki mai sonki ya sakeki akanta ai shikenan ya sakekin, wai inama yan uwan mummyki sukene da suka barki babu abinda kika iya na zamantakewa da daraja miji" kwalla ta share tace "Abbana humanitarian ne, yana zuwa gari gari yana bada taimako yana taimakon mutane, to lokacin dayaje Sudan wani gidan marayu anan yaga Umma na tana fama da sikla shine fa yaji yana sonta dayake shi AA ne saiya auro ta yataho da ita nigeria, Ummana batada yan uwa, Mummy kawai na san yan uwanta" sosai Husna taji tabata tausayi hakan yasa ta sassauta murya tace "Islam abinda kikama Khaleel wlh bai daceba ki rokeshi ya yafemiki tun kafin lokaci ya kure miki ke yanzu dayake nuna ya damu da Farida yakike ji?" Ahankali ta shiga rera kuka tunawa da yanda ya dinga koyama Farida kwallo jiya datayi da kyar ta tsayar da kukan ta kalli Husna da rinannun idanun nan tace "abun cizona yake sosai azuciya" dan dariya Husna tayi tace "bari namiki ta hausanki idan kika gansu tare abin na cizan miki zuciya shine kuma zakice baki sonshi, nan gabama zuciyar taki yagewa ma zatayi gabaki daya in kika cigaba da ganinsu tare, ko kinfiso kiyita ganinsu tare ne yana bata kulawa?" girgiza kai tayi "yariga ya aureki babu aure tskaninshi da Farida, kinriga kin tafka babbar kukure, kin kira mijin ki wicked sanan ki cemai shine yasaki aduk matsalolin nan dakike ciki Islam, mutumin daya zauna dake lokacin dakike ba mutum ba yasoki ahaka yabar aikinshi yana jinyanki, zamanin nan a ina ake samin namiji haka, keme yar uwa ko, to wlh tun wuri ki bashi hakuri kafin ki rasashi gabaki daya ko so kike ya sakeki kikoma ma Fahad ne?" Girgiza kai tayi tace "ni banmasan inda Fahad yake yanzu ba shiya koranmin shi, kuma Mum ta karbi wayana hala yanata kirana baya samuna" saikuma tafashe da kuka da kyar tai shiru ta kalleta tace "Maman Sadiq wlh zuciyata zafi takemin" "aike kikaja ma kanki zaki bata auran ki akan wayanda basu damu dakeba, keme yan uwa gashin kin dameshi ya kawoki yabarki dasu kinata shan wulakanci anma hanaki zuwa asibitin" ahankali tace "Yaya zan bashi hakuri yariga yace nai zamana agidan mu zai aiko min da takardar" murmushi Husna tayi tace "Khaleel na sonki bazai taba sakin kiba, kece dai yanzu zaki lallabo shi ki shawo mana kanshi, akwai hanyoyi daban daban da ake lallaba miji abashi hakuri yanzu dai tunda kina gidan kune kuma anhanaki zuwa asibitin balle ku hadu duk randa yazo zakici gayu sosai kije ki dane jikinshi ki rungumo kayanki kina mammatse shi da kukan kissa ki cemai kin tuba ya yakuri" nan Husna ta shiga bata shawarwari da dabaru na gidan aure da yanda zata shawo kanshi sai wuraren 1 takoma gida salla tayi tafito jin Abba ya dawo tareda Anty Hindu gaishe su tayi Abba yace "maisa baki biyo Mummy kinje asibitin ba?" "kaina ke ciwo Abba" Anty Hindu tace "kindai sha maganin ko?" gyadamai kai tayi, Abba yay murmushi yace "ai muna ma tareda mijin naki a asibiti yakecemana zaidan barki anan anturashi wani assignment a Lagos zaidan yi kwana biyu dafatan dai kinamai addu'a