Showing 57001 words to 60000 words out of 68203 words
Chapter 20 - JARABTA 1 TO END Book Complete Document hausa novels by Maman Abdul Shakur--.txt
checking in suka zazzauna suna jiran afara boarding, goma dayan kai aka fara boarding suka shiga jirgin nan jirgin ya tashi jarida yake ta karanatawa abinshi chan yaji kanta akan kafadar shi Jaridar yarufe yadan kalli fuskarta bacci yaga tanayi hakan yasa yadan gyara mata kwanciya tareda sauke ajiyar zuciya shima ya lumshe ido.
Karfe tara da minti arba'in jirgin su ya sauka a airpot din Abuja, ahankali take bude ido harta bude su duka hada ido sukayi hakan yasa ya dauke kai da sauri, daga kanta tayi daga kafadar shi tana zare ido, fara fita akayi daga jirgin hakan yasa yatashi itama ta tashi sauka sukayi wata mota tazo ta dauke su ta ijiye su a gaban luggage claim nan suka jira akwatinan su suna zuwa ya kwasan musu ya gungura tana bishi abaya suka fita daga arrival din wani driver sune da Ammi ta turo musu yazo ya karbi akwatinan daga hanun shi yana gaidasu cikin fara'a, Khaleel ne ya amsa suka shiga motar sukabar airport din. A wuse gaban wani babban gida driver yay horn aka bude musu suka shiga ahankali tafito daga motar mai gadi yazo ya cicciro akwatinan daga bot shikuma driver yakoma cikin mota yamusu sallama yabar gidan, kofa ya bude ya shiga haka yasa tabi bayanshi duk agajiye wani hadadden duplex ne, falon anmai fentin brown da milk, furniture din cikima kalan su kenan, upstairs dataga yayi yasa tabi bayanshi dadan sauri wani falon tasake gani a upstairs din sanan ga dakuna uku, wani daki taga ya shiga kasa binshi tayi tabude dayar dakin akwatin ta da tagani adakin yasa ta gane nanne natama, karasa shiga dakin tayi tana karema dakin kallo anma dakin fentin baby pink ga akwatin ta da aka jera asaman wardrobe kaya tacire ta shiga bayi tai wanka Koda tafito abinci tagani lafiyayyen white rice da stew ga farfesu agefe duk anjera mata a tray, salla tafara yi sanan tazo ta zauna taci iya cinta ta ijiye sauran akan drawer gefen gado ta kwanta sabida ta mugun gaji within 2min bacci yay gaba da ita.
Koda tatashi da asuba tai salla tai karatun al Qur'ani sake komawa bacci tayi sai wuraren 7: 30 ta farka bayi ta shiga tadan kuskura bakinta tafito tasaka hijabi, ahankali tabude kofa tafito daidai shima yafito sanye da uniform dinshi na navy bakaramin kyau yayiba, dauke kai yayi da sauri daga kallonta, harda dan saurin ta takarasa gaban shi ahankali tace "good morning" batare daya kalleta ba yace "morning" juyawa yay zaibar wajen ta bishi da saurin ta ahankali tace "uhmm dan Allah kadan kiramin Abba inaso inyi magana da Farida ne" batare daya kalleta ba ya cigaba da sauka daga kan stairs din sanan yace "bazan kiraba" da kyar ahankali tace "to yaushe zamuje yolan?" baiko kalli fuskarta ba yace "babu inda zaki" wani irin kuka ne taji yazo mata, fita daga gidan yayi da sauri, ta dade tsaye a wurin tana hawaye sanan takoma dakint.
Saida taji yunwa na neman mata illa sanan ta sauko kasa tana neman kitchen sallama dataji yasa ta amsa wata ma tace da zatai 29 haka tanadan murmushin ta tashigo tace "sunana kande nice mai tayaki aiki mai gidan ne ya turo ni, ai tunda akazo akai jere nike zuwa kullum Ina gyara gidan, yau da safe ya kirani yacemini kun dawo nazo natayaki aiki" dan murmushi tai ta gaishe da Matar, tare suka shiga kitchen suka dafa abinci mai rai da lafiya sai kallon yar torch light phone din matar take ahankali tace "indan ari wayar ki?" da sauri Kande tace "eh gatanan" ta dauka ta mika mata karban wayar tayi tafita daga dakin taje parlor ta zauna number Abba tasaka tai dailing ringing biyu Abba ya daga da sallama da sauri tace "Abba Ummi ce" murmushi Abba yayi yace "Ummi dazuko nake tambayan mijin ki ke yake sanar dani yana wajen aiki toya kuke ya karfin jikin naki" ahankali tace "Alhamdulillah Abba ya Farida" ajiyar zuciya ya sauke yace "ga Farida nan sai addu'a batama San wanda ke kanta ba" wani kuka ne taji yazo mata hakan yasa ta taushe bakinta "amma muna ta addu'a in sha Allah zata sami lpy so karki damu kanki ki kula da kanki kinji kinsan kema baki dade da samin lpy ba, Allah muku albarka duka" kasa amsawa tayi ta katse wayar tafashe da kuka sosai, kande tafito daga kitchen din da gudu tana lpy, kasa amsawa Islam tayi saima kukan datake yi da kyar tai shiru ganin yanda Kande dukta damu ta mika mata wayarta dadan murmushi tace "Ya tace batada lpy" Kande tace "to ai addu'a zaki mata ba kukaba Allah bata lpy" ahankali tace "Ameen nagode" share idonta tayi tace "dan Allah tayani diban abinci kibama su mai gadin, kema ki diba" murmushin dadi kande tayi sanan tace "to" diba tayi ta kaima su mai gadi Sanna itama tazo tadiba a yar kula tamata sallama ta tafi.
Har dare haka ta wuni tana kuka, bayan tai sallan Isha tashiga bayi tai wanka tafito daure da towel, yunwar dataji tana addabar cikin ta yasa tafito daga dakin ta sauko kasa, kitchen ta shiga ta bude warmer ta dibi dan rice a bowl karami tadau spoon tafito daga kitchen din tareda kulle kofar, karan anbude kofar sitting room yasa ta daga kai hada ido sukayi yana sanye da uniform da sauri ya dauke kai yazo yafara hawa stairs da sauri ta ijiye abincin akan dining tabishi sama harya bude dakinshi ya shiga itama tabude dakin ta shiga wani kamshi ya bugi hancinta, dakin tsaf tsaf komi fari, ko kallonta baiyiba saima kokarin bude boturan rigar shi dayake yi, ahankali tace "Ya Khaleel dan Allah yaushe zamuje duba Faridan?" ko kallonta baiyiba saima karasa cire rigarshi yayi ya ijiye agefe ya tsugunna yana kokarin kwance igiyar takalmin kafarshi, duka ya kwance ya ijiye agefe yatashi tsaye yana kokarin cire dogon wandon uniform din jikinshi, tadan matso kusa dashi jikinta nadan rawa tana gyara towel din jikinta adan tsorace tace "eh yaushe zamuje" bai kalleta ba saima zame wandon dayayi yace "babu inda zaki" sosai tafashe mai da kuka hakan yasa yabude bayi ya shiga abinshi kuka take sosai tasa hannu tanata murza idanu tace "dazu dana kira Abba yacemin batasan wake kanta ba, Farida is suffering, tun ina yarinya mu biyu Mummy ta raine mu tare, Farida ita ke tare min fada a school, ita ke bani snacks din break, itake rikemin hannu, she is my best friend, so kake karaba mu yanzu?" tacigaba da kuka sosai kaman yanda yara suke suna kuka suna magana, da kyar tai shiru tana sauke ajiyar zuciya tace "tun ranan da ka karbo mata jakanta Farida take sonka, Farida loved u so much, Allah ne ya jarabce ta da wanan son and ni take fadama komi, yanzu she is seriously sick bazaka sakeni ka aure ta ba, wlh idan wani abu yasa meta bazan taba iya yafema kaina ba" takara fashewa da kuka harda shesheka, cikin kukan tace "kaki kiramin su nai magana da ita, sanan kuma bazaka barni naje naduba taba rabamu kake so kayiko hmmm" tacigaba da rera kukan sabida yanda abun ke mata ciwo, ya dade tsaye abakin kofar bayin daure da towel yana kallonta sabida ta juyama kofar baya, wani irin cije lips dinshi yayi sanan ya fuzar da iska sabida yanda ranshi ya mugun baci, rufo kofar bayin yayi da karfi har saida tai kara hakan yasa ta juyo a firgice ta kallai, ganin idonshi yasa ta tuna marin da tasha ranan da sauri tai hanyar kofa zata bar dakin ya fizgo hanunta ihu mara kara tayi, jijjigata yay rai abace yace "bazaki yolan ba, and saki kikeso ko baza'a sakekin ba, barima kiga" towel din jikinta ya fizgo ya yar arude tafara kokarin tsugunnawa tace "na shiga uku dan Allah ka yakuri Ya Khaleel, wlh bazan karaba" jefata yayi kan gado.
[7/2, 9:28 AM] Maman Jedda: *JARABTA*
Maman Abd Shakur
73 & 74
Bakaramin wahala Khaleel yabata ba dan wlh ta gurzu, tun tana iya rokonshi daya ya hakuri har takasa magana sai ajiyar zuciyar wahala take tana kuka, wuraren 3 ya saketa tafashe da kuka kasa kasa tana saukar da numfashi juyowa yay ya kalleta fuskar nan adaure yace "get out" da sauri ta dira daga gadon dan wani irin mugun tsoron shi taji tanaji anan kasa ta tsugunna tadau towel dinta ta daura tana goge hawayen dake zuba, sanan tafita daga dakin tanadan dingishi ta shiga dakinta bayi ta wuce direct.
Runtse idonshi yayi da karfi sabida yanda kukan ta ke taba rashin shiya rasa wanan wace irin jarabta ce, da kyar yatashi ya shiga bayi yadan dade sanan yafito ya tsane ruwan jikinshi da towel yasaka jallabiya yahau kan dadduma yafara salla. Da aka tada salla asuba ne yafito yawuce massallaci saida gari yay haske yadawo yawuce dakinshi ya shirya cikin shirin zuwa aiki yafito kofar dakinta yabude da sauri ta tashi zaune kan gado jikinta har wani bari yake sabida yanda taji wani irin tsoron shi daya shigeta bakinta har rawa yake tace "in ina kwana" bai amsa taba saima harara daya jefeta dashi yace "ki tashi ki shirya ina jiranki amota" barin wurin yayi so yake ya kaita gidan su ko tadan walwala, yasan idan ya barta a gida haka zata wuni tana kukane. Yakai kusan 15 minute amota ta glass ya hango ta tafito sanye da riga da zani na brown and yellow atampa tasaka brown hijab da takalmi da brown jaka fuskarta dadan hoda da kwalli sosai tamai kyau tana tafiya ahankali, bude kofar gaban tayi ta shiga ta zauna hakan yasa yaja motar batare daya cemata kala ba har gidan su, parking yayi ababban compound dinsu yafito hakan yasa tafito tana biye dashi har suka shiga gidan da sallama su, Ihsan dake falo dan dama yariga yakira Ammi yace suna zuwa suka taso da gudu suka wuce shi suka rungumeta suna ihu Ammi da Abba dake sakkowa dan rakoshi tayi zai tafi aiki tace "karku karyamin daughter bafa hankali cikakke gareku ba Ilham" sakin ta sukayi suna dan turo baki, murmushi tayi tazo gaban su Ammi kanta akasa dan bakaramin kunyan su takejiba tace "ina kwana Abba, Mummy ina kwana" dagota Ammi tayi tace "daughter ya jiki" Abba yace "kun iso lpy" murmushi tayi tace "Alhamdulillah" Ilham ne tazo tace "muje dakin mu Amaryan Bros" dan murmushi tayi suka riketa Ammi tace "kujata ahankali mana" shidai yana zaune a dining yadau apple yanaci yabisu da kallo dan ajiyar zuciya ya sauke ganin murmushi akan fuskarta, tareda Abba suka fita yacema Ammi zai biyo ya dauketa idan yataso daga aiki. Abinci Ammi tahada mata sanan takira Ilham ta sakko ta dauka ta kai mata sai nannan suke da ita sai wajen karfe sha daya sanan suka shirya badan sunso ba suka tafi school shima sabida test din dasuke dashi ne. Ita kadai suka bari adakin hakan yasa tai shiru tana tuna jiya wani zazzafan hawaye ne taji sun fara zubo mata, kofar dataji anbude da sallama yasa ta share hawayen da sauri amma Ammi tariga tagani tashi tayi ta zauna akan gadon Ammi kuma ta shigo ta zauna a gefenta tana kallon idonta tace "lpy daughter kike kuka menene?" girgiza kai tayi tareda kakalo murmushi tace "bakomi Ammi" hanunta Ammi ta rike tace "menene karki boyemin komi, ni mahaifiyar kuce un menene daughter fadamin wani abin yamiki?" girgiza kai tayi da sauri tana kokarin tsayar da wasu hawayen dake shirin zubowa ahankali tace "Farida ne batada lpy Mummy" da sauri Ammi tace "subhanallah tun yaushe?" "tun muna chan" cike da tausayi Ammi tace "oh Allah meke damunta?" fashewa tayi da kuka hakan yasa Mum ta shafa bayanta tace "bansani ba amma tanata tarin jini Abba yace bama tasan wanda ke kanta ba" "shine baisan ya kaiki tun jiya kuje dubiya ba, zaizo ya sameni ne, in sha Allah gobe goben nan zansa shi ya kaiki kuje ku dubo ta, dena kuka kinji tashi muje dakina kin zauna ke kadai awanan dattin dakin nasu" dan murmushi tayi dan ba tawani ga dattin da Ammi ke fadaba banda kayan sawan su dasuka tara akan gadon, tashi tayi suka fita daga dakin tareda Ammi sosai tasaki jiki da Ammi ganin yanda taketa janta jiki tabata wasu magunguna tasha sanan tahada mata wasu aleda dazata tafi dasu ta dinga sha da yogurt, Ammi ta kunna mata kallo wai dukdan tasaki jiki.
Bayan sallan magrib ya shigo gidan afalo yasameta dasu Ihsan suna bata wani labarin novel sai dariya take dan bama ta lura dashi ba, hada ido sukayi da sauri ta hadiye dariyar ta janye idonta daga nashi ganin yanda yake kallonta, daure fuska yayi dukan su suka gadaishi bai amsa suba yawuce dining dan yunwa yakeji sosai, warmer yabude yadebo potato porridge dayaji nama ya zuba a plate yasa spoon, Ihsan tace "Ya Khaleel Ammi na kiranka" daukan plate din yayi yawuce sama dashi, da sallama ya shiga dakinta ya zauna akan gadonta yanacin abincin, kallonshi tayi ta daure fuska tace "mesa bakakai Islam ta gaishe da yar uwarta ba" plate din abinci ya ijiye agefe baice komiba hakan yasa Ammi ta sassauta murya tace "haba son koma me Farida tayi yariga yawuce ai, so kake karaba su danka auri wanan, karka manta fa tare suka taso koma me yar uwarta tamata bazata taba dena sonta ba eh son, kai yanzu idan aka cema Ihsan ko ilham basu da lpy basuma san inda kansu yakeba yazaka ji eh?" shiru yayi hakan yasa Ammi tai murmushi tace "don't be selfish, inaso gobe kubi jirgin safe kutafi yola" ahankali yace "Ammi aikina fa" "nadai goben, gobe ai Friday basai kudawo ran sunday ba, haba Son" dan murmushi yayi yace "shikenan naji" abincin shi ya dauka ya cigaba daci ya cinye, fridge dinta dake nan daki ta bude ta daukomai ruwa agora tabashi ya karba yasha sanan ya sauka kasa wanan karan basa falon massallaci yawuce yaje yayo Isha sanan yadawo tareda Abba suka shigo, afalo suka sami Ammi suka zauna sunata hira sai wuraren goma sanan Abba yacemai oya yatashi yadau matarshi sutafi, Ammi ta tashi tawuce sama, dakinta takira Islam din tabata abubuwa dayawa aleda sanan tamata addu'a suka fito har wajen mota suka rakata, Abba dakanshi yabude mata gaban motar ta zauna yarufe duk suka daga musu hannu jitayi kaman karta tafi sukabar gidan, amota shiru dukansu sukayi har suka kai gida tabude mota zata fita batare daya kalleta ba yace "ki shirya gobe da safe zamu yola" yafita daga motar batare dayajira cewarta ba bayanshi tabi ta shiga dakinta wanka kawai tayi ta kwanta.
Wuraren 8 suka tafi airport din bata wani dau kayaba banda hadadden lace din dake jikinta orange da black shikuma shadda ce ajikinshi fara gizna sai uban kamshi yake, karfe goma da arba'in jirginsu ya sauka a yola driver su daya kira yazo ya dauke su dayake Abba yafadi mai a general hospital suke nan direct yasa driver ya kaisu, parking yayi suka fiffito gabanta sai faduwa yake yanda taga ko kallonta bayayi wani super market ya shiga yayo sayayya dabatasan nameba sanan yadawo yana gaba tana biye dashi abaya har cikin asibitin cardio ward taga sun nufa daki na uku taga yay salama ya shiga tabi bayanshi, Mummy ce kadai adakin da Farida take kwance oxygen manne a hancin ta tana bacci, Mum tabisu da kallo Khaleel yace "ina kwana Mum yamai jiki" daidai nan Islam ta karaso gabanta ahankali tace "ina kwana Mummy yamai jiki" ko kallonta Mum batayi ba saima kallon Khaleel tayi tace "sannu da zuwa Muhammad, Alhamdulillah gatanan dai jiki da sauki" dudda abin ya daki ranshi yanda bata amsa gaisuwan Islam ba sai bai nuna komiba yawuce inda Farida take yaja kujera ya zauna a saitin fuskarta yana kallon fuskar ta tareda ijiye ledar hanunshi agefen ta yay shiru, kasa karasowa wurin gadon tayi sabida yanda Mum ke hararan ta, tashi Mum tayi ta kalli Khaleel tace "ina zuwa Khaleel zanje naduba ko testes dinta are ready nakaima likitan ta" ahankali yace "to mumy saikin dawo" fita daga dakin tayi tareda wanke Islam dawani irin mugun harara, daidai lokacin Farida tafara mutsu mutsu da ido zata tashi da kyar ta iya bude baki tace "Mk, Mummy ku kiramin Mk" kara jan kujeran yayi ya matso kusa da gadon sosai ya rankwafo da kanshi saitin fuskar ta ahankali yace "Farida na" wani irin dukan zuciyar ta sunan yayi hakan yasa ta dago kai ta kalleshi da sauri, ta wutsiyar ido yake kallon fuskarta hakan yasa yasake cewa "Farida na bude idonki gani nan nazo" ganin tana kokarin bude ido yasa yajuyo fuskar nan kaman bai taba murmushi ba yace "dan bamu wuri" kaman wacce kwai yafashe mawa aciki ta juya tafita daga dakin, bude ido Farida tayi dasukai jajir, dishi dishi take gani amma bai hanata ganshi ba kokarin cire oxygen din take daga hancin ta yataya ta cire wa, ahankali tace "Kaine ko idonane kemin gizo" dan murmushi yayi dan ta mugun bashi tausayi yace "nine" wani irin fashewa tai da kuka tana tari da kyar ta iya cewa "kayafe min dan Allah kadaina fushi dani, nariga na hakura nabar ma Islam kai, banason na mutu kana fushi dani please" takarashe maganan tana tari, hanunshi yay folding a kirji tareda daure fuska yana kallonta yace "fine naji zan hakura zan yafe miki only idan kin yarda zaki warke, forget everything and move on, and I promise zan kula dake like a sister, deal?" gyada mai kai tayi da sauri tana murmushi tace "deal" dan murmushi yamata shima yace "gud" ta wutsiyar ido ya hango Islam na leko su ta window kaman wata munafuka dan kasa hakura tayi ga zuciyar ta sai wani iri take mata, dan murmushin gefen baki yayi ganin ta ya kalli Farida yace "zakici abinci?" da sauri ta gyada mai kai, tashi yayi ya koma ta bayan gado ya dago da gadon ta yanda kanta zaiyi sama kaman ta zauna sanan ya koma, ledan daya shigo dashi ya bude ya dauko pringles ya budemata ya