Showing 45001 words to 48000 words out of 68203 words

Chapter 16 - JARABTA 1 TO END Book Complete Document hausa novels by Maman Abdul Shakur--.txt

M Shakur   

29 Dec 2024

8272

miji nan da sati biyu kokuma nahada ki daduk wanda naga dama namuku aure" sosai take kuka tana share ido, Anty Hindu sai wanke ta da harara take tace "tayaya ma Farida har kikasan da sniper kika bama yar uwarki, Farida bamu baki irin tarbiyan nanbafa, maisa kika bama yar uwarki guba?" shiru tayi tana matso kwalla Anty Hindu tace "badake nake magana ba" da sauri ta share hawaye da kyar tace "ranan da Bala ya kaini gidan tun kafin yay parking akofar gidan mukaga wata mata a tsaye baka tanada dan jiki, yana parking nafito zan bude gate na shiga sai kawai naga takira sunana Farida, nace mata Na'am, na tambayeta ya akayi kikasan sunana, murmushi tamin tace ai taganni randa nazo gidansu get-together, shine tacemin wai yanzu na yarda kanwata ta aure wanda nakeso bazan yi komiba niba mace bace, shiru nayi bance mata komiba, shine tacemin Ina sonshi? Ahankali nace eh, tace amma ai nasan idan kanwata ta mutu zai aureni nace mata eh, shine tabude jaka tabani sniper tace gashinan nasan yanda zanyi nabata idan tamutu ai shikenan zan auri wanda nakeso" shiru tadanyi tana goge hawaye kowa na falon na kallonta ahankali tace "wlh Abba banyi niyyan bata ba, nidai kawai na karba ne dan kaman tamin asiri tana bani na karba nasa ajaka na shiga cikin gidan, to Ina ganin fuskar Khaleel dinne shine shine wlh bansan meya shigeniba shine na a.. " takasa karashe maganan tana kuka sosai da kyar tai shiru Abban Yusuf ne yace "matar tafadi miki sunanta?" girgiza kai tayi tace "a'a tadaice taganni randa nazo get together, ni bansan taba" shiru kowa yay na falon Kafin Abban Khaleel yay dan murmushi yace "komi yawuce Allah ya yafemana gabaki dayan mu, tashi kitafi abinki" Ahankali ta tashi tafita daga dakin dakin Mum ta shiga ta rungume Mum tana kuka, tureta Mum tayi ta harare ta tace "Farida kinsan kai, haba Farida a ina kika koyo wanan mugun halin, tausayi kawai kikabani saisa na rokesu ayafe miki amma da wlh bazan yiba, haba wanan bakin hali har ina" shiru Mum tayi jin tasake rungume ta tana kuka kaman zata mutu hakan yasa tashiga bubbuga bayanta tana bata hakuri tace "bakomi zakaso ka sameshi ba Farida, Allah ya jarabce ki dason bawan Allah nan amma hakanan zaki dau dangana danba mijinki bane" tai maganan tana share mata hawayen dake zuba.


Daga Abban Yusuf harna Khaleel jiki asanyaye suka dawo gida kowanne su na zargin mutum dayane amma kasancewa babu proof yasa kawai suka share suka dawo gida.
Da sallama ya shiga part dinta, dakinshi direct yay niyyar wucewa ganin bai ganta a palour ba, daidai ta kofar dakin ta dake rufe yazo wucewa dariyar dayaji tanayi yasa ya mika hannu zai bude handle din tsayawa yay chak batare daya bude kofan ba jin tai dariya tace "ai ingaya miki shinai niyyan kashewa amma na rasa ta yanda zan shiga gidan, kinsan ba shiri nake dashiba idanma na shiga nace mene, saiko ga kanwar matan, kinsan ko lokacin datazo gidanmu nazaci itace yakeso ashe ba itabane kanwartane yakeso, dan naji lokacin dasu Ihsan suke labarin yanda yar ke sonshi kazakaza kaza, shine Ina ganin yar nai instigating dinta sosai, na bata abin nace tabama kanwar tasha kinga ai idan tamutu zai aureta" dariya tasake yi sosai sanan tace "wawiyar ta yarda not knowing fully dat kaina nake taimaka nasan dai yanda yakeson mai kama da Eeeshan nan tunda bansami daman kashe shi ba idan na kasheta kinga ai za'a koma gidan jiya" wani dogon uban tsaki taja tace "ke bata mutu bafa, amma dai rai a hannun Allah dan mutum mutumin ce yanzu, batada amfani" Ahankali yaji tace "hmmmm bazaki gane bane takano, wlh Allah ya jarabce ni dason kaninshi ne tun randa yazo dashi tadi wajena, na fadinma kanin amma shi yama tsaneni haka na auri wanshi Ina dawainiyar sonshi kirikiri sabida ni yadena zuwa yola yanzu ma badadan bikin danshi ba da bazai zoba Kuma wlh bakigani ba ko kallo ban isheshiba saisa nace zan dandanamai azabar rayuwa, zanso yasan yakake ji idan karasa abinda kake mugun so, Kuma Kinga yanda yakeson yaronne shikadai ne namijin shi, ai kinga idan na kashe Yaron koya karashe rayuwan nashi a haukace sabida mutuwar mai kama da Eeshan ainaci riban abinda mahifin shi yamin, yanzu ma idan bata mutuba zansan abinyi" dan dariya tayi tace "to shikenan ki gaidamin dashi idan yafita ki kirani, takano tawa kenan" tai wani uban shewa. Shirun dayaji yasa ya bude kofa ya shiga dakin adan firgice ta kallai tanadan murmushi tace "harkun dawone Alaji?" yafi minti biyu yana kallonta sanan yace "na sakeki saki biyu, ba wanan kadai ba zanje nai filling complain akanki a police station ba Khaleel kadai ba koma waye awanan family wani abu yasake sama keza'azo akama, kije keda Allah" yana fadin haka ya rufomata kofar bam yabuga yawuce, da gudu tabiyoshi har tsakar gida tana bashi hakuri amma ko sauraronta baiyiba saima sake juyowa dayayi yace "kifara tattara yinaki yinaka kibar min gida, karki sake kitafin min da ya" yana gama fadin haka ya shiga mota yabar gidan, ahanya ya kira Abban Khaleel yace "maisa baka taba fadamin halin Mujiba ba, abinda tama" dariya yadanyi sanan yace "Yaya nazaci yarinta ne" murmushi Abba yayi yace "kazo kasaman a office muyi magana".
[6/25, 2:17 PM] Maman Jedda: *JARABTA*




Maman Abd Shakur


59 & 60


🇬🇧
Taxi yatare ya shiga motar suka fara tafiya wani shago ya hango da ake saida teddies masu kyau cema mai taxi din yayi ya tsaya ya shiga shagon wani jan teddy yasai mata mai kyau da taushi yabiya kudin yadawo mota ya shiga ya zauna yana kallon teddy din yanda yarike flower.


Ahankali yatura kofar ya shiga dakin bata kangadon ma hakan yasa ya ijiye teddy akan gado, maganar nurse dayaji tana cewa gently raise your head yasa yaja kujera ya zauna yana kallon kofar bayin, wajen 3 min da zaman shi sanan nurse din tabude kofa ta gunguro ta akeke an chanza mata rigar asibiti zuwa pink amma desame design ne fuskar ta dadan ruwa ga nurse din rike da karamin farin towel a hanunta saida takawo ta bakin gadon sanan nurse din ta gaida Khaleel daya kasa cire idonshi akan Islam dan gani yay bakin yadan sabe jan dayayi ya ragu sosai, tsugunnawa nurse din tayi zata share mata ruwan fuska da towel din hanunta ya tashi tsaye yana tattare hanun doguwar rigar dayasa yace "may i" yay maganar tareda mika ma nurse din hannu murmushi tai tace "sure" tabashi towel din tsugunnawa yayi yana kallon fuskar ta yakai towel din kan fuskar yana share mata ruwan ahankali, lumshe ido tayi tadan saukar da ajiyar zuciya wuyarta ya share sanan ya dauketa ahankali daga kan kujeran sabida karya fama mata ciwo ya mike tsaye yana kallon fuskarta, ahankali tadan bude ido takallai kara gyara kanta tayi akan kirjinshi tasake sauke ajiyar zuciya, kwantar da ita yay akan gado ya rankwafo yamata runfa batare daya dagoba yace "good morning wife" hanunshi dayaji ta rike yasa yadan dago ya kalli hanun, murmushi yamata sanan ya zauna yakai hanunshi kan filon ya budemata yana kallonta, ahankali tasake matso da fuskarta tadaura kan hanun sanan ta lumshe ido tareda sakin ajiyan zuciya takara kankame dayan hanunshi data rike within 1min bacci yay gaba da ita, batare datamaga teddy ba.
Murmushi Nurse din dake tsaye tana kallonsu tayi cikin turenci tace "her mind is at ease anytime u are around, inhar tana ganinka haka kullum zaiyi helping recovery nata" murmushi yamata batare daya dena kallon fuskarta ba hakan yasa nurse taje ta bude wardrobe din dakin ta ciro wani ruwa dake cikin farin gora ta ijiye akan table din gefen gadon tace "wanan ruwan zata sha dazaran ta tashi, bari naje inta tashi ka danna mana alerm" tana fadin haka tajuya tafita daga dakin, yadade yana kallonta kafin ya daura kanshi agefen gadon shima bacci yay gaba dashi dan jiya kasa bacci yayi sabida tunanin ta.




Yau kwana su sha bakwai a asibitin, sosai condition din Islam ke improving dan bakin tass ya warke babu kumburin babu zubar yawu tana iya hadeye magani yanzu, cikin ne yanzu ake kai, kullum Khaleel na tareda ita abinda ke dagashi daga dakin salla ne kokuma idan zaije siyo magani a pharmacy hospital, shima idan zaije to Ihsan na wurin, Ihsan taita karanta mata novel tana murmushi kadan kadan, idan kaga yaci abinci to coffee ne yadan sha, baya iyacin wani abinci ko Ihsan ta girka saidai yay wasa da abincin kawai yatashi yabarshi, jiyake kaman ciwon yadawo jikinshi.


Zaune suke adakin itada Ihsan dake karanta mata wani novel tana kwance kan gado suka bude kofa suka shigo hakan yasa ta dago kai ta kallai shida Dr Om ne suna dan magana, murmushi Dr yay ya kalleta suna karasowa jikin gadon yace "how's my patient doing" dan murmushi tamai tana kokarin gyara kanta akan filo, ya makala mata wani abu kaman camera karama a hannu sanan yace "Gud, I need you to do something for me, inaso kitashi ki tsaya naga" karamin tablet din hanunshi ya daddana sanan ya kalli Khaleel yace "dago min kanta" ahankali Khaleel ya dago kanta ya zaunar da ita, kafarta Om yanunamai hakan yasa ya sauko da kafarta kasa yana kallon fuskar ta, kallonta Dr yayi yace "now try and stand on your feet" dan dafa bango tayi Khaleel ya tsaya kusa da ita dan karta fadi ya sakin mata murmushi tare da nunama ta thumb dinshi alamun good, ahankali take daddafa bango harta dan tsaya amma aduke tana dan ciccije lebe sabida zafin datake ji, dadi Dr Om yaji yace "gud now try and raise ur head, stand straight, inaso naga inda yarage dabai warke bane acikin" fuzar da iska tayi tareda karasa mikewa ahankali ahankali Khaleel yace "sorry wife" Dr Kuma na duba tab din hanunshi, kasa daurewa tayi jin zafin yay yawa tacire hanunta daga bango tai luuu zata fadi Khaleel yatare ta da sauri hakan yasa ta fado kanshi wani irin shocking yaji tunda ga yatsar shi har brain dinshi sabida yanda hanunshi yakama kirjinta mistakenly, itama wani iri yarr taji duka karfin ta tasa tadan juyar da jikinta ta yanda abin ya sauka daga hanunshi ta lumshe ido tana sauke numfashi, yafi 3minute ahaka sanan ya kwantar da ita ahankali yaja bargo ya lullubamata yana kallon idonta dasuke alumshe, maganar Om ce yadawo dashi daidai yace "Khaleel zokaga" zuwa yay ya kalli tab din yace "kaga wanan mucus dinne keda inflammation dazaran ya sabe shikenan zata iya tana mikewa tana komi saimuyi focusing kuma a dawo da maganarta" rungume shi Khaleel yayi cikeda murna yace "Alhamdulillah, Dr am grateful" fita Om yay daga dakin yanata dariya.
Cikin sati daya cikin ya warke fess, takan tashi tai tafiya ahankali ta shiga bayi da kanta tai alwala tai salla, kuma takanci abincin dan har tuwo ranan nan Ihsan tamata Kuma taci sosai danyamata dadi, Khaleel ko babu wanda ya kaishi murna harda yima nurses kyauta.


Zaune suke adakin yana bata tea abaki kiran Om daya gani yasa ya dauka ahankali yace "okay" sanan ya katse wayar Ihsan yamika mug din tea yace "zoki bata am coming Om nason ganina" fuskar Islam ya kalla dake kallonshi da idanunta masu kama danamai jin bacci yace "am coming wife" fita yay yawuce office din Om shiga yay ya zauna, Om ya bashi wayansu hotuna yace "kaga wanan hoton damukama wuyan tane, babu any damage a vocal dinta so Ina suspecting infection ne awuyan dake hanata magana, yanzu abinda zanyi shine zan bata magunguna sanan zan sallameku inyaso every every week zaka dinga kawota chech up tunda for now ai babu wata matsala saita maganan ko" kasa boye murnanshi Khaleel yayi hakan yasa Dr yafara rubutu akan paper asibiti yace "ko aje ai amarce hmm" yagama rubuce rubucen ya mikamai yace "your discharge letter, I will be expecting you guys next week Thursday" ahankali ya karba yana murmushi sanan ya mikamai hannu sukai musabaha tareda kara godemai sanan yafita daga dakin, dakinsu ya shiga Ihsan dake zaune agefen gado tana nunama Islam wani hoto yazo ya daga yana jujjuya ta yana murmushi dariya tayi tace "Ya Khaleel menene wai?" murmushi yamata yace "an sallamemu" yay maganar yana kallon fuskar Islam ahankali yaga taja bargo ta rufe fuskarta tana murmushi dan wlh tagaji da asibitin sosai itama. Ihsan ya kalla yace "tashi kitayata shiryawa bari naje nakira taxi" fita yay daga dakin yana Satan kallonta, shiryawa tayi cikin dogon black skirt din kanti na jean tasa shimi fari tadaura sweater akai pink dan garin da sanyi sanan Ihsan tamata rolling black gyale sanan tasamata flat slippers, tahade yan littatafai da kayansu dasu tea dake dakin ajakan trolley ta kulle ta daga, shigowa dakin yay yana kallonta tana zaune akan gado kanta akasa hanunta rike da teddy daya saimata kallon Ihsan yayi yace "fita da jakan taxi din na waje" jan jakan tayi tafita shikuma ya karasa cikin dakin har gaban gadon ahankali ya daura hannayen shi akan nata ya dagata tsaye ya karbi teddy ya ijiye akan gado kasa daga kai tayi ta kalleshi, jinta tayi kawai ajikinshi ya rungumeta tsamtsam tareda kissing gefen wuyanta.
[6/25, 2:22 PM] Maman Jedda: *JARABTA*




Maman Abd Shakur


55 & 56


Ya sakin mata light kiss gudun karya ji mata ciwo sanan ya dago kai ya kalleta murmushi kwance akan fuskarshi, jiyay duk wani ciwon kan da yakeji yabace, sake kai hannu yayi ya share hawayen daya gangaro mata tareda girgiza mata kai yace "am here for you now, koma inane I don't care saina kaiki koda bangon duniya ne inhar zaki sami lpy, zakiji sauki in sha Allah, stop crying..." dan kwankwasa kofa akayi Anty Hindu ta shigo takaraso inda suke ta kalli Khaleel sanan tace "Dr nason ganin ta, za'a wanke mata bakinne, kaga yanzu ma yadan warke tadan iya hadiye tea mai sanyi yau, amma tunjiya babu abinda take iyaci da bakin danyay jajir kaman kuna, bari nakaita" da sauri yatashi yakoma bayan keken yace "zankai ta Hajiya" dan hararan shi Anty Hindu tayi tace "banason gardama Muhammad, ba gamunan ba duka, salla yakamata kayi tukun yanzu sai asan abinyi, oya shiga bayi ka dauro alwala saika wuce massallaci, idan ka Ida aisai kazo kasamemu a dakin nata" tana fadin haka ta gungurata suka fita daga dakin, zama yay akan gado ya dafe kanshi tareda fuzar da iska shikadai yasan yanda yakeji, wayarshi ya dauko dake gefen gado yay dailing wani number yafi minti biyar yana magana aharshen turenci sanan ya katse wayar ya shafa kanshi yana fuzar da iska, ahankali yatashi ya shiga bayin dakin ya dauro alwala sanan yafito yafita daga dakin baiga su Abba awajen ba hakan yasa yawuce massallacin dake cikin asibitin.


Saida ya gama salolin dasuka hau kanshi sanan yafito daga masallacin yana tafiya ahankali dan yay nisa acikin tunani, mutum yagani yasha gabanshi ya tsugunna hakan yasa yadan tsaya yana kallonta ba karamin ramewa tayiba tai duhu sosai idanunta duksun fada ciki, fashewa tai da kuka sosai ta hade hannayen ta tace "dan girman Allah kayafe min, wlh shirin shaidan ne saida nayi sanan hankali na yadawo, am very sorry Mk, dan Allah na tuba kayafemin" tunda take maganan yake kallonta harta gama kara daure fuska yayi kaman baitaba murmushi ba ya matsa zai wuce takara tasowa tasha gaban shi tace "dan Allah, kaga Abba yakoreni daga gida idan kaima baka yafemin ba dame zanji, am very sorry, dan Allah inaso naga Islam na roketa gafarta please" hannu takai zata kama kafanshi hakan yasa yace "wlh if your hand should touch my leg, wlh saina ballasu tass, just stay away from me, kinason ki ganta sabida kibata another poison dinne?" cizon leben shi yayi cikin fushi ya nunata yace "stay away from me dan zan iya.." shiru yay yawuce dan koda minti daya yakara awajen zai iya mata abinda shikanshi bazaisoba, fashewa tayi sosai da kuka ta tsugunna awajen har wani irin ajiyar zuciya take saukewa sabida wahala, gashi ba halin ta shiga sabida Abba yamata mugun warning akan yin hakan.


Dakinta yay daidai lokacin Dr na fitowa hakan yasa yabi Dr office dinshi, zama yay ya nunamai waje ya zauna, kafin ma Dr yafara magana yace "Dr Inaso a sallamemu sabida gobe nakeson nafita da ita, UK 🇬🇧 zan kaita" murmushi Dr yayi yace "dama advice din danake so nabaku kenan, nan Nigeria 🇳🇬 bamuda kayan aiki inda bahakaba aida zamu iya komi, bari nabaka sallaman amma kadan bari anjima kadan saika tafi da ita dan ansamata ruwa sa karfi da kuzari dawasu allurai, kasan she is very weak sabida rashin abinci aciki" rubuce rubuce yay yabashi yace "ga Bill dinku nan kaje account kabiya" karba yay yatashi yafita daga dakin, account yawuce direct da POS yabiya, yaciro ATM card dinshi yabasu nan yabiya kudin komi sanan ya karbi ATM card dinshi ya maida wallet yabar wajen. Ahankali ya bude dakin ya shiga kowa na dakin Ammi na kan gado ta daura kanta akan cinyarta ta mikar mata da hannun da akasa ruwan tana shafamata kai ahankali dan bacci take, ajiyar zuciya yadan sauke ganin tana bacci sanan ya kalli iyayen nasu anatse yace "Abba zan fita da ita waje, gobe nakeso mutafi, and inaso Ihsan tarakamu, nariga nai magana da Omprakash babban Dr ne tun ina school achan na sanshi yace nazo da ita" Ya kalli Ihsan dake zaune tai zuru zuru yace "ke taso muje gida muhada kaya dagangan am going to the airport nai booking first flight to UK gobe" Ahankali Abban Islam yace "inada contacts din ambulance flight, medical transport gwara su, sabida incase of zazzabi ko wani abu suna tareda nurses da doctors dat will attend to the patient acikin jirgin, abokina ne pilot dinsu to inaga shizai fi koya kuka gani" Abban Yusuf yace "hakan yamafi kyau Alaji kamusu magana saimuyi handling komi" Ya kalli Khaleel yace "ku kutafi gida to kuhada kaya da duk wani abu dazaku bukata inyaso matan saisu zauna da ita" shida Yusuf ne suka fita Ihsan tabisu abaya.
Fita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login