Showing 42001 words to 45000 words out of 68203 words

Chapter 15 - JARABTA 1 TO END Book Complete Document hausa novels by Maman Abdul Shakur--.txt

M Shakur   

29 Dec 2024

8279

akasa danji take kaman ana tsitsinke hanjin cikinta, kama fuskarta yayi yay tapping kumatun ta da karfi yace "wayabaki abincin chan" kara fashewa tai da kuka tana nunamai cikinta da kyar ta iya cewa "Fa.. Far" wani irin ihu tayi ta buga kanta akasa sabida yanda cikinta yay wani irin kara dahar shi saida yaji da gudu yay gaban tv danhar yana huge kafa da center table, key mota yadauka ya dauke ta yafita tsakar gida da gudu yana kwalama gateman kira "budemin gate" kwantar da ita yay abayan mota yarufe da gudu ya shiga gaba yatada suka fita agidan, yanda take juyejuye sabida azaba har saida tafado kasa daga kan kujeran juyowa yay da idanunshi dasukai jajir yakira sunan ta "Islam, Islam" kasa amsawa tayi saima bubbuga kai datake yi a jikin kujeran. Allah ne kawai ya kaisu asibitin lafiya dan yana tuki yana kallon bayane yanda take nukurkusu akasa.
Idan kaga Khaleel zaka zaci ya haukace ne sabida yanda yake ihu a asibitin, da gudu aka karbeta Dr yace "maiya sameta" da kyar ya iya cewa "I think sniper aka bata" ganin yanda tawani bankare zata Fado daga kan gadon da aka daurata yasa ya riketa yace "Islam Islam am here babu abinda zai sameki kinji" cikin wani daki akai da ita ya bisu amma akace yafita.


Har sunkai layinsu itada me napep din daya dauketa sai kuma taji jikinta yay wani irin mugun sanyi yanzu sabida namiji zata iya kashe Islam? Wata zuciyar tacemata amma ai idan ta mutu zai aureki, dafe kanta tayi tana girgizawa da sauri tace "no no, I can't do dis, Islam jini tace " da sauri ta kalli driver tace "malam komar dani GRA dan Allah kayi sauri" juyawa sukayi addu'a kawai take ido arufe Allah yasa bataciba jikinta har wani bari yake, har suka kai sauka tayi tacemai yajirata da gudun ta ta shiga gida mai gadi namata magana amma Kota kanshi batabi ba, a bakin kofa ta tsaya ganin plate din Indomie andan ci kadan sanan ga dan kwalin material dinta akasa maganan mai gadi taji tabayan ta yace "Hajiya basanan yanzun nan alaji yafita da ita kaman hajiyar ba lpy ne" wani irin bugawa kirjinta yayi tai wani irin suman tsaye, da kyar ta iya cemai to ganinan fitowa, wani luuu tayi zata fadi da kyar ta iya dafa bango tana kwalalo idanu tareda dafe kirjinta kaman wata mahaukaciya tafara lalubar jakarta watsar da komi tayi na jakan kasa ta ciro wayarta hanunta har wani barbar yake number Abba tai dailing ringing daya Abba ya daga kafin yay magana tace "Abba, Abba, Abba na kasheta, Abba nakashe yar uwata, wlh wlh bansan meyakai ni bata sniper ba, Abba na shiga uku shairin shaidan ne" maganganu kawai take zaroma Abba kaman zarrara hakan yasa Abba hankalin shi yatashi kodai Farida ta zarene ahankali yace "Farida mekike fadine haka wakika kashe?" "Islam, Abba kanwata, yar uwata jinina nakashe yau, Abba..." katse wayar Abba yay jin yanda take xazzaro maganganu kaman mara lpy number Khaleel dayaji kotaje gidan sune dan yasan batasan gidan bama, yay dailing number saida ya kusa katsewa yay picking ahankali yace "Abba" tashi tsaye Abba yay daga kan kujera dan yanda yaji muryan Khaleel yasa kirjinshi yawani irin mugun bugawa "Khaleel meke faruwa yanzun nan Farida takirani" da kyar Khaleel ya iya cewa "muna general hospital Abb..."wayarce tafadi kasa ta tarwatse sabida yanda jikinshi ke wani irin rawa, ganin ankara gunguro Islam daga dakin datake, wani irin abu kaman babban straw abakinta wata nurse kuma ta rike jakan ruwa da ake dura mata ta bakinta dan yay washing cikinta sunyi ICU da ita, da gudu yabisu amma har an shige da ita anrufe kofar bubbuga kofar yake kaman zai fasa yana kiranta, ahankali ya sulale ya cusa kanshi acikin kafafu tareda sanya hannu akan wuyarshi yafi 15mins ahaka a wurin, bayanshi yaji andafa hakan yasa ya dago jajayen idonshi Abba yagani da Anty Hindu dakuma Mum kana ganinsu kaga tashin hankali karara akan fuskokin su.


Farida tafi minti 10 tsaye a wurin sanan ta daddafe bango tafito tana ganin jiri ta shiga napep din tareda cemai muje, tafiya kawai suke dan gabaki dayanta bata hankalin ta da kyar tace "kaini asibiti" "wani asibiti hajiya" Ahankali tace "kowanne" tafiya suka dingayi yay parking agaban general hospital yace "kije wanan sunfi kwararrun likitoci Allah sawake" duka kudin purse dinta taciro tabashi kaman wata tababba take tafiya har taje reception tana waige waige Allah sa nan suke, hijabin Anty Hindu ta hango ta cikin emergency ward hakan yasa ta daga kafa da kyar ta shiga ward din, tsayawa tayi daga ta wurin kofa tafashe da kuka sosai tana kallon su yanda suka tsattsaya gaban ICU.
Dago kai Khaleel yayi karap suka hada ido da ita, mikewa tsaye yayi kaman namijin zaki yana kallonta hakan yasa Abba suka jujjuya suna kallon inda yake kallo, hannu ya daura akan belt dinshi na jikin wando yana kwancewa batare daya dena kallonta ba, wani irin Fizgo belt din yayi azuciye koni bantaba ganin Khaleel ahakaba wanan zuciya hmmm! Ko kallon fuskar su Abba da mutanen dake ward din baiyiba yay inda take tsaye yana tafiya kaman wani mayunwacin zaki jikake fui fui fui dukan Farida yake da belt Kota ina...


Ahankali Islam ta rike hanun Dr yake daddane cikinta tana amayar da ruwan dasuka duramata ta baki, wani irin hawaye ne ya gangaro daga gefen idanunta da kyar ta iya magana tace "please stop abinan dakekemin yamafi min azaba kan komi, please I want to see my husband" yanda tai maganan yasa jikin Dr yay sanyi sosai, wani irin tari tayi hakan yasa ruwa yakara fitowa daga bakinta tace "please I want to see him" ahankali Dr yajuya yafita daga dakin hango Khaleel dayayi yana chasa Farida ga mutane duk antaru ana kallo su Abba dai na tsaye danko yunkurin kwatota basuyiba Mum ce ke kuka sosai, da gudu Dr yay wurin yana "subhanallahi" rike belt din yayi yana kallon yanda Farida ke kuka kaman zata mutu, dawani irin ido Khaleel da kallai, girgiza mai kai Dr yayi tareda janshi yace "kayakuri, Matar ka nason ganinka" bin bayan Dr yayi aka budemai dakin ya shiga kadan tabude idonta tana kallonshi da sauri yay kanta yana shafa kanta hawayen daya gangaromai ya share yama forehead dinta kiss yama kasa magana hanunshi yaji tarike gam hakan yasa ya dago kai yana kallon fuskarta, twisting jikinta tayi tareda fito da ruwa sosai daga bakinta tashi yayi zaije yakira Dr yaji takara kamkame hanunshi da sauri ya kalleta, dan murmushi tamai sanan ta bude bakinta da hakoran ta dasuka dan hade tafara magana, da sauri yakai kunen shi saitin bakinta yaji tace "Yaya Khaleel inaso Kamin alkawari" tadanyi shiru tana numfashi sama sama tace "inasonka sosai, I love you so much Muhammad Khaleel" daura fuskarshi yay akanta ahankali ya lumshe ido wani irin zazzafan hawaye ne suka zubo daga idonshi suka sauka agoshin n
ta da kyar yace "and I love you more than anything Islam, please stop talking, kidena magana kinji u will be fine lemme go and call d Dr" yajuya zai tafi hanunshi takara kankamewa tana kallonshi da idanunta dasuka kankance tafara magana, kai kunenshi yayi saitin bakinta ahankali yaji tace "Kamin alkawari, promise me zaka auri Farida idan namutu, Farida na sonka so na gaskiya, promise me" Ahankali ya dago kanshi dudda bata da lafiya bai hana ya mata wani irin mugun kalloba ya fizge hanunshi daga nata yana goge wasu hawayen bakin ciki dasuka zubo, da kyar ta iya daga hannu ta mikamai idanunta na fitar da hawaye ta gefe, ahankali ya tako zuwa gabanta yarike hanun gam zatai magana yadaura yatsan shi akan lips dinta ya girgiza mata kai idanunshi sunyi jajir, idanunta yaga sunsoma jujjuyawa wani irin nishi tayi tafara wani irin nannade kanta tana bankarewa sabida yanda cikin nata yafara wani iri kaman ana kakkatse duk wani hanji naciki, ihu Khaleel yay yace "Doctor".
[6/23, 11:35 PM] Maman Jedda: *JARABTA*




Maman Abd Shakur


53...


Ihu yake yana kiran Dr tareda danna alarm din gefen bed nakiran Doctors, hakan yasa Abba yana ganin Doctors din sunzo zasu wuce dawayan su nurses suna gudu yabisu hankali atashe suka shiga dakin...
Wani irin mugun rawa da jijjiga jikinta keyi tana kallon sama idanunta na kakkafewa tawani irin bankarewa dan kumfa kumfa na fitowa daga gefen bakinta ta rike zanin gadon gam, riketa gam Khaleel yayi yana wani irin ihu "Islam-Islam stay with me" yanda yaga jikinta ko ina narawa tana wani irin mimmikewa yasa yafara "innalillahi wa innalillahi raji'un, innalillahi wa innalillahi raji'un, Allahumma ajirni fi musibati" harda gudu Doctors da nurses din suka karaso wajen gadon da sauri wani babban Dr dan tsoho nema ya kalli wata Nurse yace "kunna Defibrillator, her heart is over racing" handglove ya dauka daga gefen gadon yasa da sauri yadau paddles din defibrillator ya rike yay robbing dinsu together sanan yadaura akan kirjin Islam dake kakkarwa yay ihu yace "clear" kaman electric shock wani irin bangarewa Islam tayi sanan takara komawa kan gadon bam, cirewa yay yana kallon machine din yana reading abunda yake nunawa sanan yakara putting dinsu together ya daura akan chest dinta yay shouting "clear" kara bangakarewa tayi tayo sama sanan takoma kan gadon idanunta na kukkulewa wani irin kara machine din yafara "diiiiiii
, din, din, din, din" ahankali Khaleel yafara komawa da baya da baya yana kallon fuskarta yana dafa bango, sama sama yakejin Dr yana "cewa one more time we can't loose her" dumm yaji kunenshi yayi sanan ya dauke, ganinshi yay duhu, yay baki, chan sama sama kaman daga nesa yaji machine din yay kara sosai sanan kuma shiru, sama sama yaji likitocin suna "we are loosing her.. Time of de... " dip yaji kunenshi ya dauke yadena jin komai idanunshi suka rufe ruf.


Good morning lovelies 😍
[6/23, 11:35 PM] Maman Jedda: *JARABTA*




Maman Abd Shakur


54...


Ahankali yake bude idanunshi dasuka mai mugun nauyi ga kanshi dake mugun sarawa, da kyar ya iya bude idanun duka ya sauke su akan wani Dr dayaga ya rikemai hannu yana shafa tafin hanunshi yana bubbugawa, sama sama yakejin doctor nacemai "can u here me, I need you to tell me your name" kadan kadan idanunshi ke kukkulewa ganin gabaki dayan dakin na juyamai in a circle, kara bubbuga tafin hanun nashi Dr yayi yana rubbing tsakiyar yana kallon fuskar shi da kyar yasake bude idon yadan kallai kadan yace "can you hear me? Me sunanka?" da kyar ya iya bude bakinshi sabida wani irin nauyi dayamai sosai yace "Islaaam, I want to see her" yana maganan yana kukkule ido har suka rufu tass, murmushi Dr yayi ya juyo ya kalli su Ammi harda Goggo dasuka tsattsaya kowannen su hankali tashe yay murmushi yace "Alhamdulillah ya farka, anytime from now zai farfado full.. " "Islam" da Khaleel yakira yasa dukansu harda Dr sukai kanshi wanan karan yabude idon duka saidai kanshi dayaji yana mugun ciwo, Ammi ne tai maza ta rike hanunshi tana share hawayen dataji yazo mata, ahankali ya kalleta yace "Ammi ina Islam?" shafa goshin shi Ammi tayi tana girgiza mai kai tace "kafara hutawa tukunna Son, kasan yau kwanan ka Uku unconscious ko" ta kalli Dr dake checking pulse dinshi tace "Dr yayake yanzu?" murmushi Dr yay yace "Alhamdulillah he's pulse is stable, blood pressure din kuma yadawo normal, ku taimaka mai yay wanka da lukewarm water it will really help him" kokarin tashi yake amma yakasa sabida yanda kanshi yaji kaman zai fadi ahankali ya kalli Abban shi da Umma da Yusuf da Goggo dake wajen dakuma Anty Hindu da idanunta sukai jajir sabida tausayi hanunshi ya daga da kyar yay pointing Anty Hindu ahankali yace "ina Islam dina?" bude kofar dakin akayi hakan yasa dukansu sukabi kofar da aka bude da kallo wheelchair din asibiti yafara gani, dan dago kanshi kadan yayi da taimakon Mum yana kara kallon kofar, Abban Islam yagani ya gunguro Islam dake zaune akan wheelchair ta duke kai sosai dan bata iya dagowa complete sabida cikinta, lips dinta sun kumbura sosai sunyi jajajir bakinta nata dilallar da miyau, kasa dauke kanshi yay daga kanta har Abba yakawota jikin gadon dayake ya tsaya, kokarin tashi yake Yusuf yayo kanshi zai taimakamai ya tashi dagamai hannu, alamun yabari, rike kanshi yay ya sakko daga kan gadon da kyar kaman zai fadi, da kyar ya iya ya tsugunna agabanta ya mika hannayen shi ya daura akan fuskarta ya dago kanta yana wani irin kallonta idanunta alumshe, ahankali dawata irin murya mai taba zuciya yace "Islam" shiru tayi batare data bude idonta ba batare datace mai komiba, ahankali Abba yace "Muhammad Khaleel Ummi tasamu nakasu guda biyu, na farko dai tana fama da wanan uncontrollable zuban miyau wato drooling, nabiyu kuma tunda ta farfado ko uppan batace ba, Dr yace yana tsammani Sniper yamata dameji a wuya ne amma basuyi concluding ba, sanan bata iya mikewa tsaye sabida intestine dinta wai basu warkeba tukun, and kaga bakinta yanda yakoma" Abba yadanyi shiru sanan ahankali yace "banason na daurama dawainiya aka, after all yar uwarta ce ta maida ita haka, to Khaleel idan baka sonta, idan bazaka iya zama da itaba wlh bazan taba ganin munin kaba, bazan ji haushi ba, zaka iya sauwake mata" tunda Abba yake maganan yakasa dauke ido daga kanshi gawasu jijiyo yi dasuka fiffito a forehead dinshi, da kyar ya iya janye idanunshi daga kan Abba sanan ya kalli Islam dahar lokacin taki bude idonta, ahankali yasake matasawa kusa da ita yadade yana kallon fuskarta da bakinta dake dulalar da miyau ya daura kanshi akan cinyar ta ya fashe da kuka sosai, Yusuf ne yafara fita daga dakin jin idanunshi sun kawo ruwa, hakama sauran iyayen da Dr suka fita daga dakin yarage daga shi sai ita, yafi 5min yana kuka sanan ya dago kanshi ya share idanunshi da kyar dan muryanshi ma ta dishe yace "Wife" ahankali ta bude ido ta sauke su akan nashi, ganin yanda yake kallonta yasa ta daga hanunta ta rufe fuskar ta tana wani irin kuka mara sauti dan kunyan fuskarta take sosai, hannu yasa yakamo hanun ya saukar dasu yana girgiza mata kai, hanunta ya daura akan kirjinshi daidai wajen zuciyar shi ya goge kwallar data zubomai yace "kinga wanan zuciyar, only beat for u" ahankali yace "koma yakike, koma yakika koma, koma menene you will always be my Islam, my one and only wife, wacce nakeso wholeheartedly" sosai yaga take kuka ahankali ya kai hannu ya share mata hawayen dake zubowa yace "am sorry, am sorry Islam is all my fault" hannu tasa ta kara kare lebenta tana kawad dakai dan ba karamin kunya takeji ba idan yana kallonta, wani hawayen yasake gogewa ya juyo da fuskar nata tareda saukar da hanun nata yana girgiza mata kai ganin yanda take kuka mai cin rai, ahankali yakai bakinshi ya daura akan katon lips dinta dake fitar da miyau.


Guys yau weekend am a little busy ne so manage this I love you all.
[6/25, 2:17 PM] Maman Jedda: *JARABTA*




Maman Abd Shakur


57 & 58


Batare daya dago kaiba yace "Islaaam" kadan ta kallai dan wahalan bude idanunta duka takeji sosai, murmushi yay ya matso da kujeran saitin fuskarta yasa hannu yana shafa kitson kanta ahankali ya sumbaci forehead dinta sanan ya shafa wurin yana kallon fuskarta murya chan ciki yace "I have to go yanzu 7 ake koran mutane but da sassafe zanzo gobe" shiru yay yana kallon fuskar ta ganin kaman tai bacci danta lumshe ido, addu'an bacci ya tofa mata sanan ya matsar da kujeran baya yatashi, yadade a tsaye kafin ya juya da zumin tafiya hanunshi yaji takama da sauri ya juyo ya kalleta, girgiza mai kai yaga tanayi da dan idanunta data bude kadan ga wasu hawaye dasuke gangarowa ta gefen idon, da sauri ya kwanto da kanshi daidai saitin fuskar ta yasa hannu ya share hawayen ahankali yace "u don't want me to go" daga kai tayi wanan karan tana kuka sosai, "okay nafasa tafiya" yafada tareda zama ya riko hanun nata data rike shi dashi yana shafawa kadan kadan, dayan hanun Kuma yana share mata hawayen datakeyi sanan ya ijiye hanun agefen filon yana shafa gaban goshin ta, ahankali tasanya fuskarta cikin hanun tareda sauke ijiyan zuciya sanan ta lumshe ido within 3min bacci yay gaba da ita, numfashin ta dayaji yana sauka ahankali ahanunshi yasa yagane tai bacci, ahaka wata nurse ta shigo dakin cikin harshen turenci tacemai lokacin tafiya yayi yatashi yatafi itace mai kula da ita, kallon fuskarta yayi kafin ahankali ya zare hanunshi ya mike tsaye tareda sanya hannayen acikin aljihu ya tsaya yana kallonta kara komawa yayi ya tofeta da addu'a sanan ya juya yafita daga dakin yana leken fuskarta. A reception yasami Ihsan sanan suka fito daga asibitin taxi yatare musu suka shiga, tafiyan kusan 20min sukayi sanan sukai parking agaban wani dan madaidaicin gida, kofar ya bude ya shiga Ihsan na biye dashi Yaron dazu suka tarar yanata mopping kasan dakin murmushi yamai yace "weldone Raymond" zama akan daya daga cikin kujerun yay yana kara karema gidan kallo, babban falone da akamai penti off white irin dakunan turawan nan saita bangare daya kuma kitchen ne wanda komi yake a gyare, sai dan corridor da dakuna biyu ne awajen kowanensu da bayi aciki, saida Raymond yagama yamusu sallama yatafi shikuma yatashi ya shiga daya daga cikin dakunan hakan yasa Ihsan ta tashi itama ta shiga dayan dakin dan yin wanka tai salla saita fito tadan sama musu abinci.


Zaune yake shida Anty Hindu suna magana akai sallama jin muryan su Abban Khaleel yasa yatashi tsaye yana murmushi tareda basu izinin shigowa ganinsu tareda Farida idanunta sunyi zuru zuru yasa ya daure fuska ya nuna mata kofa "fitan min daga gida, fita nace" fashewa tai da kuka ta tsugunna jikinta har wani barbar yake tace "Abba dan Allah kayakuri kayafe min" Su Abban Khaleel ne suka saka baki suna tausasa shi da kyar ya sauke ajiyar zuciya ya kalli Anty Hindu gyadamai kai tayi hakan yasa ya kalleta ya gyara murya yace "shikenan na hakura amma inada sharadi daya kifito da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login