Showing 63001 words to 66000 words out of 68203 words

Chapter 22 - JARABTA 1 TO END Book Complete Document hausa novels by Maman Abdul Shakur--.txt

M Shakur   

29 Dec 2024

8277

sosai ko?" gyada kai tai ahankali dan bazata iya magana ba ayanda kirjinta ke bugawa Abba yay murmushi yace" masha Allah haka akeso akodayau she mace takasance mai yawan yima mijinta addu'a da fatan alheri, jeki huta idan ciwon kan baidena ba kizo kifadamin saina kira likita yadubaki" gyada musu kai tasake yi sanan takoma daki bakaramin kuka taciba ranan yanzu shikenan sakin nata zaiyi shine yakema su Abba kwana kwana, bahalin taje gidan Maman Sadiq dan sunriga sundawo.


Abangaren Khaleel ko kadan baiji dadiba dayazo hospital din baigantaba yana zaune ne kuma sako yazo daga wajen aiki ana neman su a headquarter dinsu na Lagos zasuyi wani assignment shine ya fadima Abba zaidan barta anan dan gobe zai tafi Lagos din idan yadawo saiyazo ya dauketa Abba yamai fatan alheri washe gari yabi jirgin safe zuwa lagos cike da kewanta.


Wasa wasa yau sati biyu kenan rabonta da Khaleel, duktabi tai wani irin ga Mummy tabi ta tsangwameta wani zubin ma idan su Abba ko Anty Hindu nanan ne take dan sarara mata, jiya aka sallamo Farida amma dakinta takaita, tsakanin Farida da ita kuwa yanzu bakaman da bane suna magana bawai basayi ba amma dai bakaman daba, Farida bata tsaneta ba kawai dai tanajan jiki da itane dan duk idan ta dade tare da ita tuna da takeyi saitaji tanajin haushi, tariga tama Mk alkawari zataji sauki and forget d past, sabida son datake mai abinda take kokarin yi kenan yadawo daga lagos yaga ta warke rass takoma Faridan da, Son datake ma Khaleel wani irin sone da tanajin har abada harta mutu bazata denaba, saisa takedan nisanta kanta da Islam sabida batason tana ganinta zuciyar ta tafara kulla mata wasu abubuwa dazaisa Mk ya tsaneta again, komawane zata aura nan gaba batajin zata daina son Mk ba superman dinta. Idan har Abba ko Anty Hindu basa gidan to tana daki dan batason tama hadu da Mummy, Abba yakan cemata Khaleel yakira shi, Farida ma takan cemata yakirata taita wani jin dadi hakan bakaramin ciwo yake mataba dan baitaba kiranta ba Koda ta wayar Abba bane dagaske kenan rabuwan da ita zaiyi, daki take shiga wani zubin taci kuka abinta ta godema Allah, dan Maman Sadiq sun riga sun koma Abuja amma tanada number ta takan kirata da wayar Maman Miemie idan tazo aiki suci hira, sanan kafin su koma tabata wasu magun guna da kullum take sha dan koyau ma tasha da yogurt adaki abinta, hakadai tacigaba da maneji wani irin mugun kewan Khaleel take da nadamar abubuwan data fadimai dan tariga ta gane duk duniyar nan banda Abban ta shine mutum nabiyu dake sonta so na gaskiya.


Kwanaki sunja lokaci nata tafiya yau kimanin wata daya da kwanaki biyar kenan rabonta da Khaleel, yaukam zazzabin data tashi dashi ne yasa Anty Hindu da kanta ta fadanma Abba nan aka kira Dr, bayan ya dubata yace "maleria ne" magani yarubuta mata Abba yasiyo Anty Hindu tasa tasha, Mum dai zamanta tai afalo tana marking script ko agefen kwalanta, Farida kuma ta debomata abinci dan sosai tabata tausayi takawo mata. (har yanzu fa wanan son dake tsakanin su nanan kawai dai Son Khaleel ne matsalan two sisters dinan)
Wuraren 6 ta tashi na yamma tadanji dadin jikinta, hakan yasa ta shiga bayi tai wanka da ruwan dumi tafito dan pink gown dinta na gida tasa dake tsayama ta a gwuiwa tasaka dogon hijabin ta dake sharan kasa tai sallan la'asar jin anfara kiran magrib yasa tayi sanan tayi azkar din yamma tacire hijabin ta linke ta ijiye ta kwanta akan gado tana maida numfashi, gabaki daya duk tayi wani irin laushi ga jikinta har yanzu da sauran dumi, lumshe ido tayi har bacci yadan soma tafiya da ita sama sama taji ihun Farida daga kasa "oyoyo MK, oyoyoo" da sauri ta tashi ta zauna, kasa hakura tayi tadan mike tsaye tareda saka silifas tabude kofa kadan maganganu taji kasa kasa kaman muryan su Abba, komawa tayi ta zauna abakin gado gabanta na faduwa sosai, bude kofa akayi hakan yasa ta daga kai Farida ne tashigo dakin da gudu jikinta har wani rawa yake tana murmushi tace "Mk yadawo Islam kinga yanda yay kyau kuwa, laa banma bashi ruwa ba" da sauri tajuya tafita daga dakin, harara Islam tabi bayanta dashi jin wani irin kishi ya turnike ta saikace mijinta ne yazo taja tsaki, tashi tayi afusace taje gaban wardrobe dinsu wani ubansu soft material taciro blue da akabishi da zanen flowers gold, zama tayi agaban madubi ta chanchara uban kwalliyan da ita kanta batasan ta iyaba tasaka red janbaki tadan shafa lip gloss akai hakan yasa lips din na wani irin maiko maiko yana kyalli kaman sabon candy da aka gamayi, tashi tayi tabuga uban dauri sanan ta dauko turaren khumar da Husna ta bata na matan aure ta shafe jikinta dashi dakin yadau kamshi sanan tadan kalli kanta amadubi dudda tarame amma baihana kayan karbanta ba tareda fito da kyanta da dirin ta dan sun dan kamata sosai, takalmi tazira sanan tabude kofan tafito tana wani irin kamshi akan bene ta tsaya hango Farida datayi ta zauna akan kujeran dake kusa danashi tanata mai hira, ta wutsiyar ido ya hangota har wani irin ajiyar zuciya ya sauke sabida yanda yay kewan ta yawani juya mata baya yabiye ma Farida suna hira harda dariya, wani irin abune taji ya tokare mata zuciya kasa daurewa tayi takarasa sakkowa daga benen da sauri ta tsaya tana kallonsu, ganin duk sunmaki lura da ita babu wanda yace mata Kala yasa taji zuciyar ta na tafarafasa ai wlh yau saita nunama Faree nan Khaleel mijinta ne ehe, da saurin ta harda wani dan gudu gudun ta taje kaman daga sama tawani fada jikinshi ta kankameshi tana kukan shagwaba ahankali tace "Ya Khaleel nai kewan ka sosai" wlh ya tabbatar da inda yay alwala babu abinda zai hana alwalan karyewa wanan irin runguma haka damafa adaddafe yay wanan wata dayan a Lagos, wani irin kara shigewa jikinshi takeyi tana hahhade kirjinsu tare, kasa daurewa yayi ya sanya hannayen shi duka biyu yay cuddling nata tareda sakin wani irin sassanyar ajiyar zuciya, tashi Farida tayi tabar falon tanajin wani iri iri hakan yasa Islam takara bin bayanta da harara tana tura baki taredayin lamo ajikinshi tana shakan kamshin turaren dayake yi.
[7/2, 2:19 PM] Maman Jedda: *JARABTA*




Maman Abd Shakur


79...


Ganin Farida tabar falon tai sama yasa yaciro ta daga kirjinshi murya chan kasa yace "me haka nazo nabaki takardar ki kin wani shishigemini jiki, is over, today we are going our separate ways abinda kikeso kenan ai, bakiga nida Farida munyi making perfect coup.." daura hanunta tayi a bakinshi tareda kara matsowa cikin jikinshi tana girgiza mai kai tana turamai baki a shagwabance, "Hasbunallahu wa ni'imal wakil yarinyar nan naneman kasheshi ne wai" Ahankali ta zame hanun daga kan bakinshi ta kwantar da kanta a kirjinshi kaman wata baby tareda sakalo hannayenta ta bayanshi tana wani irin sheshekan kuka mai taba ran miji tace "dan Allah karke sakeni, wlh natuba bazan karaba, am really sorry, dan Allah karka rabu dani i cannot live without you, u are my endocrine" idan ba kana kusa dasu bane bazaka tabajin abinda suke cewaba, da kyar ya tattaro dan karfin daya rage mai dan tagama kashemai jiki ya ture ta yace "am wicked fa kin manta ne, tunda na shigo rayuwar ki matsaloli kawai naketa jamiki" hannunta takai takama kunnuwanta biyu, bilhakki take mai kuka tana girgiza mai kai tace "nai kuskure babba dana kalli fuskar mijina, mai gidana, mai sona abin alfahari na nagaya mishi wayan nan munanan kalaman, dan Allah ka gafarceni, inda inada karfin maida lokacin baya dana tariyo wanan lokacin na goge maganar danayi da eraser, Ya Khaleel i love you please karka rabu dani, ka hukuntani amman dont live me my endocrine" ahankali ya mika hannu yacire hanunta daga kunen nata data rike ya daga habarta yana kallon kwayar idonta dawata irin murya ya kashe mata ido daya yace "dole kam inhukun taki dawan nan bakin mai tsiwa, amma agado ake hukuncin" a kunyace ta fisge fuskarta ta fada kirjinshi tana murmushi kasa kasa, bakinshi yakai saitin kunenta yace "kinman ta ina gidan sirikai nane ko kike ta mammaneni haka, sokike na saki layi ko" girgiza kai tayi tareda sakinshi tana murmushi ahankali, hanunshi yasa ya shafo janbakin kan lips dinta yakai yatsar bakinshi yana lasa yana wani irin kallonta yace "jeki dauko abubuwan ki mutafi gidan mu"
[7/3, 10:24 PM] Maman Jedda: *JARABTA*






Maman Abd Shakur


80...


Tashi tayi ahankali ta mike tsaye tana kallonshi kaman yau tafara ganinshi, shima ita yake ma wani irin kallo da kyar ta iya janye nata idon tai stairs tana murmushi kasa kasa, haka yabita da kallo harya dena hangota, shi kadai yasan yanda yakeji akan matar nan nashi.
Kofar dakinsu ta tura ahankali ta bude babu kowa aciki, dan ajiyar zuciya ta sauke ta shigo yan tarkacen ta tahada a jakarta ta sanya hijabi tafito, dakin Mummy tai sallama ta shiga Farida ta gani tai filo da cinyar Mummy idanunta sunyi jajir dasu, maida kofar tayi tarufe takaraso ciki ta tsugunna agaban Mummy tana wasa da zip din jakarta ahankali tace "zamu tafi Mum" harara Mumy tabita dashi kafin ta tabe baki tace "Allah yayi, to agaida gida" ahankali ta mike tsaye ta juya zata fita tana satan kallon Farida dataga ta lumshe ido, harta daura hanunta akan handle zata mudra taji Farida tace "Islam wait" waigowa Islam tai ahankali, sakkowa Farida tayi daga kan gadon, zuwa gaban Islam tayi ta rungumeta tsamtsam hakan yasa Islam ma ta rungumeta back tareda sauke ajiyar zuciya, wani irin zazzafan hawaye Farida taji yazubo mata da sauri tasa hannu ta share tana daga idanunta sama kokarin hana kanta kukan datake ji, bakinta takai kunen Islam dawata irin murya chan kasa tace "please take care of Mk, dan Allah ki kula dashi Islam, Allah baku zaman lpy" sakin Islam tayi takoma kan gadon ta kifa kanta akan filo tana sheshekan kuka sosai, wani irin hararan bakin ciki Mum tabita dashi kafin taja dogon tsaki ta kalli Islam din dako kwakkwaran motsi takasa kaman wacce tai mutuwar tsaye tace "bazaki fita daga dakin nan ba ku tattara kubar gidan nan kosai kun dawo mata da ciwon datake" wasu irin zazzafan hawaye ne suka zubomata kafin ta juya da sauri tabar dakin, falon Abba tayi bayan ta tsaya ta goge fuskarta tass, suna tare da Anty Hindu kafin ma tai magana Abba yace "zaku wuce kenan?" gyadamai kai tayi, Anty Hindu ta riko hannunta tace "Alhaji ka sauka gamunan zuwa" fita yay daga dakin Anty Hindu kuma taja hannunta zuwa dakinta, wasu magani dake robobi daban daban tadauko mata tace "kin gansu nan yau dinan naje airport na karbo su kawata daga Cameroon nasa ta turamin sabida nabaki, wlh idan baki shaba sainazo har gidanki na bugi kudina dakika sa nai asara" tagama maganan tana kokarin bude wani gora wani magani tace "shanye wanan agabana" karba tayi tasha tana yatsine fuska sabida dadi dadi da ne dashi, murmushi Anty Hindu tayi ta karbi goran daga hanunta tace "gud girl kinga kafin kukai yafara aiki ajikinki, tashi muje ki kula da mijinki da kyau, kimai biyayya, karki sake kisa zancen Farida aranki duk wanan hauka datake dazaran tasami miji, tasami mai sonta zata mata dama waye Khaleel ne, kizama mai hakuri da juriya, mara korafi kuma, kindaiga abinda yawan korafi da masifa yajamin sakoni akayi" dan murmushi tayi batare data bari ta ganta ba, karban jakanta tayi ta sakamata magungunan aciki sanan ta riko hanunta suka sauko falo inda Khaleel da Abba keta magana anatse, har mota suka rakasu suna musu addu'a suka tafi sanan suka koma cikin gida, dakin Mum Abba yabude ganin Farida dayayi akan gado tana gunjin kuka batare datamaji shigowan shiba yasa yajuya kawai yafita yana girgiza kai lamarin Farida sai du'ai shifai yasan ba randa zaiyi salla dabazai rokan mata Allah yakawo sauki cikin lamarin nan nataba, tareda nemamata miji nagari, yasan Allah maji rokon bayinsane watarana sai labari.


Agaban wani massallaci yay parking ganin antada sallan Isha'i ya kalleta yawani kashe mata ido yace "bari nai salla babyn Khaleel" dauke kai tayi da sauri hakan yasa ya zagayo ta wajen window ta yawani kanne mata ido rufe fuskarta tayi da hannu tana murmushi yajuya da sauri ya shiga matsalin yay wajan yin alwala.
Jingina da kujera tayi ta lumshe ido dan Ac daya barmata a kunne na ratsa jikinta sai taji tana wani irin jin bacci bacci, bude kofar motar bayan da akayi yasa ta bude ido tadan waigo, shine abu taga ya dauka dabata ga kome ba yamayarda kofar ya rufe ya dawo gaban ya bude ya zauna sanan ya jiye mata wani dan kwali da akai rapping dinshi da jan rapping shit anmaida shi kaman fulawa akan cinya, wani irin sassanyar murmushi tayi ta sanya hannu ta dauka tana kallon abin ahankali yace "open it tsaraban kine" gyada mai kai tayi ta ijiye akan cinyarta ta warware flower saman ta warware rapping shit din, kwalin sabuwar wayar Samsung tagani na latest model dinsu, wani irin ihu tayi ta matso ta rungume shi hakan bakaramin mai dadi yay ba, yay murmushi yana shafa bayanta, ahankali ta sakeshi tama wayar kiss ta kalleshi ganin ita yake kallo tace "thank you, Allah ya saka da alkairi ya kara bude ya karemin kai" sosai yaji dadin addu'an harsaida ya washe hakora ya kunna motar suka cigaba da tafiya, bude kwalin tayi taciro wayar ta kunna sai jujjuyata take, aranta tace "finally zan koma watsapp nama Maman Shakur magana tasani awanan hadadden group dinan nata" wani irin dadi taji hakan yasa ta kalli fuskarshi ganin tukinshi yake hankalin shi nakan hanya yasa tai murmushi tana kallon sajen shi yanda yake ta kyalli. Ahaka har sukazo GRA kofar gidan su Abba taga zasu wuce da sauri tace "baza muje mu gaida su Abba da Ya Yusuf ba?" dan juyowa yay yamata wani irin kallo dayasa ta dauke kai da sauri yace "gobe mazo" daidai nan yay horn mai gadi yabude gate shiga yayi yay parking ya bude motar yafito, ahankali itama tabude tafito hannunta yakama yanadan waigawa baya, ganin mai gadi harya rufe gate ya koma dakinshi yasa yawani dauketa afirgice ta kallai dan ba karamin tsorata tayiba, kanne mata ido yayi yasa hannu ya bude kofar dakinsu ya shiga da ita ciki, da jikinta yasa ya maida kofar yarufe tareda manne ta ajikin kofar yana mata wani irin mahaukacin kiss batasan lokacin data saki jakar dake hannuntaba yafadi kasa, jikinta har wani rawa yake dan har yanzu bata sababa, sake daukar ta yayi batare daya raba bakinsu ba yay hanyar bedroom da ita, akan table din dining ya daurata shiya tsaya a tsaye yana kissing dinta, sakin bakinta yayi ya cire hijabin jikinta tareda tumbuke daurin dan kwalin ya yar anan kan kujerun dining yana wani irin kallon idonta kasa kallonshi tayi ta kawad da kanta kirjinta na wani irin mugun bugawa ga lips dinta dake wani irin zagi dan tass ya shanye janbakin nan, hanunshi taji akan habarta ya juyo da fuskarta tareda sa hannu ya ware kafafunta ya shiga tsakakaninsu ya matso dab da ita sosai hartana jin saukar numfashin shi da yanda kirjinshi ke bugawa fast fast, kara matsota yayi hakan yasa akunyace ta boye fuskarta a kirjinshi sanan tasa duka hannayen ta ta tattaro rigar soft yadin jikinshi ta kakkare fuskar ta dashi ta nannade kafafunta a bayanshi gam hakan yakarasa ya mannu da ita kaman zasu koma one, wani arin ijiyar zuciya mai kara yasaki da saida yasa ta dago kai ta kalleshi dan ita kunya ce tasa ta nannade kafar tata a bayanshi, da wata irin murya kasa kasa yace "zaki kasheni Islam, ahhh" kankameta yayi tareda saka hannu ya cire ribbon din dake kan gashin ta ya barbazar da gashin yana wani irin kallon fuskarta, bakinshi yakai saitin idanunta hakan yasa ta lumshe su da sauri kirjinta na fat fat, wani irin kiss mai kara yama saman idonta nata hakan yasa taji wani irin yirrr dahar saidai taji kanta nawani irin motsi, daukar ta taji yakara yi yay bedroom d ita yawani wurgata agado tai kara wash Allahna, murmushi yayi yayo kanta yahade bakinsu ganin yana kokarin zuge zip din rigarta yasa ta fizge bakinta da kyar ahankali tace "banyi salla ba" sakinta yay ahankali jiki asake hakan yasa ta tashi da sauri tafada bayi kafin yakara kamata, wanka tayo tafito daure da towel tana wani mammatse baki tana kallonshi tana dauke kai kaman yarinya, lamo yayi akan gado tareda janyo filo ya rungume yakasa dauke idonshi daga kanta, batada kaya agidan hakan yasa yar rigar singlet din maza tashi fara datagani ta dauko ta wuce bathroom ganin yanda yake kallonta, saka wa tayi amma takasa fitowa ganin rigar ko cinyarta bata kaiba, ga hammatar duk abude ana hango abubuwa, dan tsaki tayi ta daura towel akirji tafito taki yarda su hadda ido tabude kofa tai falo jakarta ta dauka taciro zani tadau hijab a dining ta dawo dakin bata sameshi akan gado ba hakan yasa ta kabbarta salla. Yana fitowa shima wankan yayo da alwala yasaka jallabiya ya zauna abakin gado yana jiranta tana idarwa yajasu nafila raka'a biyu tare.


Sosai yamusu addu'a bayan ya idar ya kalleta tareda daukan car key yace "mexaki ci babu abinshi agidan nan" jingina tayi da jikin gado tace "banajin yunwa naci abinci agida" tai maganan tana wani lumlumshe ido, ajiye car key yayi dan shima akoshe yake ya cire jallabiyar yadawo inda take zaune akasan dagashi saidan boxer na Louis Vuitton ya zauna agefenta, kin kallonshi tayi, ahankali ya jawota jikinshi hakan yasa tai lamo tana shakan kamshin da fatarshi keyi, ya sanya ta kan kafafun shi kanta akan hanunshi kaman yanda ake daukar yara ya kalli fuskar murya chan kasa yace "meke damunki ur body is warm?" bude ido tayi kadan tareda turomai baki tace "bakaine ba kasa naketa ciwo ba" dan murmushi yayi ya lashi bakin data turamai yace "ai mun shirya ko hukuncin kine kawai yarage wanda yanzu zaki karbeshi" shigewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login