Showing 36001 words to 39000 words out of 68203 words

Chapter 13 - JARABTA 1 TO END Book Complete Document hausa novels by Maman Abdul Shakur--.txt

M Shakur   

29 Dec 2024

8280

yake hakan yasa ta dawo ciki ahankali tahau gadon nesa dashi sosai ta kwanta tareda jan bargo ta rufe jikinta duka kanta kawai tabari awaje.
Yaci iya cinshi shima yaji ya koshi yatashi tsaye rike da plate din kallonta yayi yanda ta takure waje daya ta juyamai baya murmushi yayi ya bude kofa yafita kitchen ya wuce ya ijiye tray din yafito falo yay locking kofa sanan ya kashe TV ya kashe wuta sanan yay hanyar bedroom din, bude kofa yay ya shigo hakan yasa takara kudundunewa, kashe wutar dakin yay sanan yawuce bayi yay kusan 10min sanan ya bude kofa yafito duk tana jinshi, agaban wardrobe ya tsaya ya cire jallabiyar jikinshi yamaida a hanger sanan ya ijiye, zagayowa yay ta inda take kwance ta bakibakin gadon ya tsugunna batare dayace komiba, azabure ta tashi zaune tana kokkomawa baya tana sheshekan kuka, hayowa yay kan gadon ya zauna agabanta tareda kunna hasken wayarshi ya haskata, kare fuskar tayi da hannu tana kara matasawa baya tana kuka ahankali, kafafun ta yakama yaza yana murmushi hakan yasa tai zuit ta kwanto flat, hayowa kanta yay batare daya hade jikinsu ba kulle idanunta tayi gam tana kuka sosai, ahankali yace "shiiiii" gum tayi ko tari bata karaba, hanunshi yakai tabayan wuyarta yadan dagota kadan yasa hanun ya zare ribbon din data kama gashin ta dashi ya yar akan gadon hakan yasa gashin ya barbazu akan filo ya tsaya yana kallon yanda ta kamkame idonta kirjinta na bugawa fat fat, wayarshi ya dauka ya kashe flash light din sanan ya kwanta a gefenta, hanunshi yakai yadaura akan cikinta hakan yasa takara zabura zata mike ya riketa tareda janyota tafado kan jikinshi.
[6/23, 1:42 PM] Maman Jedda: *JARABTA*




Maman Abd Shakur


45 & 46


Yunkurawa tayi ta tashi yasa hannu ya kwato da kanta kan kirjinshi yana shafa bayanta ahankali yace "sleep" gabaki daya atakure take sabida yanda yawani riketa hakan yasa ta lumshe ido kirjinta na bugawa fat fat fat tafi hour daya takasa bacci sabida yanda yake shafa bayannata sai mutsu mutsu take daga bayane baccin dole yasace ta, hakan yasa tai relaxing gabaki daya ajikinshi tana ajiyar zuciya ahankali. Jinyanda jikinta yasaki yasa yagane tai bacci, ahankali gudun kada ta tashi yamika hanunshi ya kunna bedside lamp yana kallon fuskarta yaune rana ta farko daya tabamata kallon kurinla haka, gani yake kaman Eeshan shi yake kallo, dan lumshe ido yay ahankali yace "Allah ya gafarta miki my Eesha" ahankali ya bude ido tareda sa hannu asaman gashin ta yana shafawa jin gashin taushi gashi warawara, d'ayar hanunshi ya mika ya kashe bedside lamp din sanan ya mayar da hanun yanata shafa kanta ahaka wani bacci mai mugun dadi da natsuwa yay gaba dashi.


Wuraren 3 nadare ta farka sabida fitsarin datake ji, jinta datayi akan mutum yasa ta tuna inda take, kokarin cire hanunshi daga bayanta take takasa gashi dakin duhu batagani ko kadan ahankali taji yace "mekike so" bata ganin idonshi da kyar cikin muryan bacci tace "hanunka" hannu ya mika ya kunna bedside lamp din da sauri ta dauke kai ganin yanda idanunshi suka kara kyau sundan kankance sabida baccin dasukayi, ahankali yasaketa hakan yasa ta sauka daga jikinshi da sauri sanan ta zauna daga bakin gadon tana waige waige neman hijabin ta dan bataso ta tashi agabanshi ahaka ganin bataga hijabin ba gashi fitsari takeji sosai yasa tadan juyo ta kalli fuskarshi a lumshe taga idanunshi hakan yasa ta mike tsaye harda dan gudun ta tashiga bathroom din jin kaman fitsarin zai zubo, bata wani dade ba tafito tsayawa tayi tadan kallai ganin har lokacin idanunshi a lumshe yasa tafara tafiya ahankali tadan kwanta ta baki bakin gadon taja bargo ta rufa murmushi yay ahankali. Hartadan fara gyangyadi taji yamata peck a kumatu ya tashi ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito, jallabiya yasaka ya shimfida dadduma yafara salla tun tana kallonshi har bacci yay gaba da ita.


Kamshin turaren dataji yacika mata hanci ne yatada ita daga baccin datake, ahankali take bude ido harta gama budesu Khaleel tazani zaune kusa da ita yaci uban shadda dark brown har kyalli take, ya gyara gashin kanshi da sajen shi sunata shining ya zauna yana kallon fuskar ta, tashi zaune tayi tadan dauke kai ahankali tace "ina kwana" murmushi yamata tareda kamo hanunta ya mikar da ita tsaye jitayi ya rungumeta hakan yasa ta tsorata batare daya saketa ba yace "morning Baby ya darenki" yay maganan tareda sakinta, kauda kai tayi, murmushi yasakeyi mata da sauri tabar wajen wajen akwatin daya bata jiya taje budewa tayi ta ciro wata atampa vilisco dataga an dinka yanama cikin leda da duk wani abu dazata bukata sanan tadan juyo kaman mara gaskiya ta kallai hada ido sukayi hakan yasa ta dauke kai ta tashi ta shiga bayi da sauri ta rufo kofar harda saka key dan bata yarda dashiba wanan kallo kaman wanda yaci maita.
Saida tagama wankan sanan ta shirya ta shafa mai tasaka kayan da aka mata dinkin riga da sket, ba karamin haushi rigan yabata ba dan V neck akama dinkin saidai kayan sun mugun amsanta, black da pink ne kalar atampar hakan yakara fito da hasken fatar ta, rashin comb yasa ta tattare gashin nata tai pakin dinshi ahaka sanan ta daura dan kwalin dan simple daurin tayi, gaban mirror bayin taje ta tsaya tana kallon kanta wani haushi ne yazomata ganin yanda gaban rigan yasa kana hango saman kirjinta dan rigan yakamata chas ajiki, tsaki tayi ta tuge daurin dan kwalin kanta ta warware sanan tadan yafa aka yarufe mata har wuya sanan tafito, ganin baya dakin yasa ta bude box din ta maida kayan data cire ta feshe jikinta da turaren data gani sanan tarufe akwatin tana kokarin daga akwatin taji yay sallama ya shigo, ciki ciki ta amsa batare data kallai ba ta daga akwatin ta juyo fadawa jikinshi tayi dan kwata kwata batasan yana bayanta ba, kokarin fita daga jikinshi tayi da sauri, yadaura hannayen shi a waist dinta yana kallon idonta mayar da kanta kasa tayi takai hanunta ta daura akan nashi tana kokarin cirewa daga waist dinta, kama hanunnata yay yarike hakan yasa ta fizge hanun da karfi ta tureshi ta juya zata tafi, fizgota yay ya zauna akan gado ya daurata akan cinyar shi kokarin mikewa take amma yariketa gam, dayan hanunshi yasa ya yaye lullubin datayi da dan kwalin ya ijiye agefe yana kallonta kawad dakai tayi gefe ta daure fuska, ahankali taji yakai hannu yana shafa wuyanta wani irin yarr taji tanaji ga heart dinta na racing, ture hanunshi tayi hakan yasa ya rike hanunta gam sanan ya mayar da danyan hanun nashi yana shafa wuyan nata wani iri taji tanaji hakan yasa tafara jujjuyar da kanta kaman wata kadangare, da kyar ta iya ta fizge hanunta ta tashi dagudu zatabar dakin ajikin kofa ya ritsata hakan yasa ya daura hannayen shi biyu a jikin kofar yasata a tsakiya yana mata wani irin kallo, hannu tasa tafara kakkare kirjinta tai crossing hannayen ta daurasu akafada ta yanda bazaiga komiba idanunta suka cicciko da hawaye, cire hanunshi daya yay daga jikin kofar ya daura akan hanunta yarike yacire hannun daga kafadan yana kallon fuskarta, ahankali ta shiga reramai kuka tana mutsitsike ido, hannu shi yasa ta bayanta jikinsu ya hadu tadan komar da kanta baya still tana mutsitsike idanun dake fitar da kwalla, hanun nata yakamo yacire daga ido yadan hura mata iska a ido sanan yace "meke damunki" kokarin cire hanunshi take daga bayanta ya girgizamata kai tareda hada forehead dinshi da nata, hancin shi ya goga akan nata yadan kalli kwayar idonta sanan yace "talk" kokarin kawad dakai take yaki bata daman yin hakan, da kyar tace "kama Farida alkawarin aure, jiya ta shirya she was so happy she invited all her friends shine ka aureni bayan I already told u bazan aureka ba, ashe wayau kamana, Allah kadai yasan wani hali Farida ke ciki yanzu, why did you do dis?" takarashe maganan tareda da fashemai da kuka, tunda take maganan yake kallonta baki ya bude zaiyi magana sukaji muryan wasu mata na buga kofa ta waje, handky yaciro daga aljihu ya share mata hawayen sanan ya kamo hanunta ya zaunar da ita akan gado yace "am coming". Falo yafita yabude kofa su Ihsan yagani da wasu manyan mata guda uku, Ihsan tai murmushi tace "Umma tace nakawo su, za'a mata lalle ne da gyaran kai, kuma wai kaje" cike da rashin jin dadi ya kalli matan yace "ku shigo" komawa yay ciki yasame ta azaune hanunta ya kama ta tada ita tsaye yace "wurinki akazo, zomuje" make kafada tayi hakan yasa yay folding hanunshi a kirji yana mata wani irin kallo da sauri tajuya zata fita daga dakin yakamo hanunta.
[6/23, 2:07 PM] Maman Jedda: *JARABTA*




Maman Abd Shakur


47 & 48


Yakamo hanunta yarike gam yana yar dariya, turo baki tace "kasaken" make mata kafada yayi yaja hanunta har gaban wardrobe, wani madaidaicin black hijab yaciro ya warware yasaka mata sanan yarike mata hannu ya kalleta yace "banason ana kallon mu goody bag dina muje naraka ki" akunyace ta dauke kai, tare suka fita daga dakin suna zuwa dining tafara kokarin kwace hanunta sabida mutanen datagani su kusan five ga manyan kuloli kusan 5 dasuka ajiye a tsakar falon, kin sakinta yay ahaka suka shigo falon, kasa daina kallonta su Ihsan sukayi, tana tsaye agefenshi tadan kallesu tace "ina kwanan ku" manyan matan guda biyune suka amsa da lpy lau, harara ya watsama su Ihsan yace "ku baku iya gaisuwa bane" atare suka taso sukazo inda take tsaye Ihsan ta mika mata hannu tace "ni sunana Ihsan his sister, welcome to our family" ahankali tai murmushi ta bata hannu, Ilham ma tace "sunana Ilham welcome to the family" murmushi tamata tace "thank you" Fa'iza ma tace "nice Fa'iza welcome and u are very very cute wlh" murmushi tai tace "thank you" hanunta Ihsan tarike tace "ga masu lalle nan mum tace amiki idan angama za'a kaiki chan family house ne, muje afara yimiki sai muyi dishing abinci kiyi breakfast ko" gyada musu kai tayi sukaja hanunta hakan yasa yasaketa, dan juyowa tai ta kallai tai raurau da ido, girgiza mata kai yayi alamun no, ya kalli Ihsan yace "ku kullan min da ita kuma, ko kuda karku bari ya tabata, bari naje" hanun yadaga mata alamun bye kunya taji yakamata ta dauke kai da sauri su Ihsan sunata mata dariya. Harara ya balla musu sanan ya juya yafita daga dakin yana kallon fuskar ta.
Lalle aka fara zizara mata, daya nayin na hannuwa dayar kuma na kafafu, Ihsan ta debo abinci tana bata abaki, Ilham kuma da Fa'iza sun kwanta akasa suna bata labarin Khaleel suna tafawa suna ihu, bakaramin tunamata da Farida sukayi ba, sosai taji tana kewan yar uwan nata da kyar ta iya tahana kanta yin kukan. In less than awa daya lallen ya bushe da aka mata sabida sanyin ac dakuma fanka dasuka kunna, wankewa akayi ba karamin kyau lallen amaryan yamata ba, sanan aka wanke mata gashi akai using handryer aka busar dakan sanan aka fara yaryada mata kitso yan mini mini. Sai Wuraren azahar suka gama sanan suka tafi yarage daga ita saisu Ihsan sosai tasaki jiki dasu sabida yanda suketa janta jiki kaman sun santa, sata tai wanka sukayi suka shiryata cikin wani ubansu lapaya, Fancy glamour suka dauko ta chanchara mata makeup din amare idan kun ganta bazakuce itabane, sanan suka kira Umma cewa sun gama, Umma tace "to, yanzu za'a zo ataho da ita". Anty Hindu ne dawasu mata duk sunci gayu sukazo gidan, rungume Anty Hindu Islam tayi zatai kuka ta girgiza mata kai, sanan ta lullubeta mata fuska aka dauketa suna wakoki aka tafi da ita gida fuskarta a rufe, ta lapayan ta take hango yanda gidan ya cika da mutane sai taga gidan su kaman ba biki akeyi ba, wani babban falo taga an shiga da ita an zaunar da ita akan kujera Anty Hindu ta zauna a gefenta tana gaggaisawa da mutane anata guda, wata matace dataga suna kama da Khaleel taci gayu sosai tazo gaban su, Anty Hindu tace "ga maman mijinki nan" yaye lullubin fuskarta Ammi tayi, ahankali tasa hannu ta daga habarta kasa dago ido tayi sabida kunya hawaye taji ya gangaro, murmushi Ammi tayi tace "masha Allah daughter" sababbin kudi taciro ajaka yan 500 tadinga mata manni ana guda har saida kudin yakare sanan takoma ta zauna, haka ma Umma tazo ta wanketa da liki, duk wanda yazo Anty Hindu tana fadamata waye, sosai aka dinga ihu ana guda sanan aka tafi da ita bangaren Goggo, Goggo Kam harda rawa sabida murna tai manni tai manni har saida duka kudinta ya kare, wata malama tagani ta tashi tai musu wa'azi da addu'a sanan Goggo tace "to kowa yatafi abarmata amaryan ta tahuta" haka duk aka watse ya rage Anty Hindu da Ammi da Umma, tashi sukayi suka shiga uwar daka Goggo sunata magana, muryan Goggo taji tana cewa gaskiya anan zata zauna. Fitowa sukayi Ammi tazo ta dafata tace "kinajin yunwa insa akawo miki abinci daughter?" akunyace ta girgiza kai, murmushi Ammi tai ta kalli Anty Hindu tace "daughter na badai kunya ba" dariya Anty Hindu tayi daga nan duk suka fita suka basu wuri, sosai Anty Hindu tamata wa'azi da fada akan tabi mijinta, sanan tacemata Khaleel yamata sabon akwati set daban daban har 6, Abban ta duk yahada an wuce mata dasu gidanta na Abuja. Sai bayan sallan Isha Anty Hindu ta tafi ba karamin kuka tasha ba hakanan ta hakura tai shiru gyangyadi tafara yi akan kujeran Goggo sabida yanda tagaji gakuma kukan datayi hakan yasa Goggo tace "tashi ki shiga ciki ki kwanta abinki ki huta kinji, sannu yarnan yan iskan yaran nan duk sun wahalar dake" murmushi tai dan hakanan taji Goggo ta shiga ranta gatadai tsohuwa amma akwaita da tsafta, "au bazaki tasoba" Goggo tai maganar tana kokarin tashi daga kan tabarmar data shimfida a tsakar dakin, kamo hanunta tayi tace "muje ki kwanta bakisan bacci nada amfani ga lafiyar dan Adam ba" kofar uwar dakanta ta bude da gadon ke agyare tsaf tace "jeki kwanta abinki zanga dan kan uban dazaizo yafita dake, jekiyi baccin ki saida safe kinji yar albarka" gyada kai tayi sanan tace "saida safe Goggo" kwanciya tayi akan gadon da aka gyara tsaf dakin sai kamshin turaren wuta yake within 2 min bacci yay gaba da ita, Goggo dake kishingide akan tabarma taji ana kokarin bude kofar ta tashi tayi ta zauna da kyau tana wawware ido, Khaleel ne ya shigo sanye da doguwar jallabiya sai kamshi yake yawani daure fuska yace "ina matata? Daga barinta tazo gidan naku shikenan kuma bakusan ku komar da ita inda kuka daukotaba?" ko kallonshi Goggo bataiba taja filo abinta takara kwanciya sanan tace "jeka tambayi uwarka, bata fadama daga yanzu anan gida zata zama ba, to saikun koma Abuja ne zata tare a gidanka" karaso wa ciki yay yace "nida matar tawa lallai nema" yazo zai wuce yay bedroom Goggo ta mike tsaye da sauri tasha gabanshi ta rike kugu hakan yasa yaci birki yana kallonta cike da bacin rai, dariya tayi tarike haba tace "mara kunyar banza, fitarmin daga daki tunda bakai ka ginamin ba wlh kona hadaka da ubanka" ganin Goggo ta daure babu alamun wasa tawani rike kugu yasa yajuya yafita daga dakin rai abace, Goggo tarakashi da dariya sanan ta maida kofa ta rufe harda saka Sakata tace "fitinannun yara" kwanciya tayi abinta rai fes tace "dan kanuba to yarinya sai tasha gyara sanan za'abaka, idanma nabari ka kara sata a ido ba sunana Lami ba" lumshe ido tayi tana sauke ajiyar zuciya. Direct part din Ammi yawuce duk ranshi a dagule Yusuf yagani zaune afalo yana jiran Ihsan tagama dafamai Indomie dayace tadafamai, yana ganinshi ya gimtse dariyar datazomai, ko kallonshi baiyi ba ya shiga bedroom din Ammi wata kawarta ya tarar tana magana da ita hakan yasa yaje kusa da ita ya zauna, sallamar matan tayi sanan ta juyo ta kalleshi tace "Ya akayi Son?" da kyar ya iya cewa "Ammi wai kekika cema Goggo karta bari Islam tabini anan zata dinga kwana" Ammi taso tai dariya da kyar ta saita kanta sanan ta kallai tace "eh nafiso kawai ran Sunday idan duk mun tafi Abujan basai ta tare wajenkaba, yanzu ga duka family anan mezataje tai ita kadai achan gidan kadaici zai isheta mana" zaiyi magana tace "ka bacemin daga nan I have alot of things to do" tashi yay yafita daga dakin duk ranshi acinkushe ta gefen ido yaga Yusuf ya ijiye Indomie hanunshi yanamai dariya ciki ciki haka yay kaman bai ganshi ba yana zuwa dai dai inda yake yadau plate din Indomie yace "wlh bazaka ci shiba" Yusuf ya kwalama Ammi kira yace "Ammi kinga wai akaina zai huce takaicin shi" da sauri Khaleel yafita yay part dinsu ya kulle kofa ya ijiye Indomie anan kan kujera yawuce bedroom yafada kan gado kasa bacci yayi sai juye juye yake daga baya yatashi ya shiga bayi kawai ya dauro alwala yazo ya kabbarta salla.


Bari muleka Faridan mu.
Idan kunga Farida saikun tausayamata ta rame sosai, da kyar Mum kesata taci abinci, bata da aiki sai daukar waya taita dailing number superman da baya shiga ko kadan, Abba kullum wa'azi yake mata da fada, Mum dai duniya yay mata zafi hakan yasa wani zubin idan Farida tafara kuka itama jonata takeyi suyi tayi tare, ba irin Allah ya isan da basuma Islam ba sabida bakin ciki.


Hakanan yau Wednesday taji tanajin fita kotadan ga rana, doguwar riga baka tasaka ta yana gyalen ko hoda bata shafaba tafito daga gidan danko Mum bata fadimawa ba, keke napep ta tare tace "yakaita Infinity gym" ta shiga ciki yaja har wajen yana ijiyeta ta ciro kudi ta bashi, sucurity ya bude mata ta shiga ciki, wani kukane yazo mata ganin treadmill din data taba ganin superman dinta akai, da kyar ta hadiye hawayen ta karasa wajen eatry din, order strawberry smoothie tayi ana kawomata ta karba tareda bada kudin tanata kallon smoothie din tana tuna ranan da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login