Showing 27001 words to 30000 words out of 55242 words

Chapter 10 - BA DON MACE BA BY FATIMA FANTAH.doc

Advertisement

22 Feb 2025

3660

?arfi ya amsa yana kiran "LILBIRRAH!"




SH 11

Gaba Waya idanuwanta suka yo waje, "LILBIRRAH kuma?" Ta tambayi kanta cikin mamaki, "AbuDalib!" Ta kira shi da ?arfi. "Na am," Badiyya ya amsa cikin muryar galabaita, tashi ya yi zaune yana share hawayen da ke tarara daga idanuwansa, hannunshi ya kalla ya ga jini, "Ya Salam, Badiyya me ya same ni? Ina Lilbirrah? Kai ya Allahna, ina Ummanah? Badiyya su nake son gani, wani abu nake ji game da su, suna ina? Wurin su zan tafi..."
Yana fadar maganar ya mike tsaye yayin da Badiyyah ta daskare kamar wani gunki. BuWe ?ofar Wakin barcin ya yi ya fita, tozali da falon da ya yi ya dakatar da shi, ji ya yi ?wa?walwarshi ta ?ara hautsinewa, "Ina ne nan?" Runtse idanuwansa ya yi yana son tuno abinda ya faru. ?asa ya faWi daSas yana dafe kansa da ke juyawa. Da karfi ya kira sunan Badiyyah, a zabure ta iske shi tana raba idanuwa kamar an kai akuya mahauta. "Ke ina ne nan? Ina nake? Ina Lilbirrahta? Khouhar dina tana ina? Na ce tana ina?" Ya ?are maganar yana daka mata tsawa.
Bakinta kawai ke motsawa, amma sam ba ya jin me take furtawa, mi?ewa ya yi sam bai damu da tsamin da jikinsa ke yi, toilet ya shiga don ya yi wanka ya je gun Khouhar Winsa, tsaye ya yi yana kallon kansa jikin madubin ban Wakin, fuskarshi ya shafa da ya ga ta yi rama sosai, sannan ya yi wani haske kamar ba shi ba, ga jini a hancinsa ga hawaye sharkaf a fuskarsa. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una! Wai me ya same ni ne?" Wasu hawayen da ya rasa takamaiman dalilin zubowarsu suka sake yo ambaliya, du?awa ya yi wanke fuskar tass, "Babu wanda zai faWa mani gaskiyar abinda ya same ni sai Ummana da Khouhar Wina na san ba za su min ?arya ba, ba zan yi wankan ba ma, idan na je wurin Umma na yi, na san Lilbirrah ma tana can." Shi kaWai ke surutunsa, sai da ya gyara fuskarshi sosai sannan ya fice. Badiyyah na tsaye bakin kofa tana dakon fitowarshi, tsananin mamaki ya hana ta komai, so take ya fito ta tabbatar da gaskiyar lamarin da take tsammani. Wuce ta ya yi ya nufi wurin wardrobe, ba komai cikinta sai tarkacen kayan da ya sa ya cire, sai kuma akwatinsa daga gefe, "Ya salam." Ya faWa, "Ke wai ina ne nan? Na ce maki ina ne nan? Kaina juyawa yake na rasa gane inda nake."
Matsawa ta yi gab da shi cikin salon yaudara ta ce, "My Boo, ka manta wai muna Austria, ka mance mun zo Vienna..." labari ta soma ba shi, a tsawace ya ce, "Ke dakata! Dakata na ce!" FaWawa ya yi kan gadon ya runtse idanuwansa, jefi-jefin abubuwan da suka faru suke faWo mashi game da zuwan shi Vienna shi da Badiyyah, taron karrama shi da sauransu, "To me ya sa ban zo da Lilbirrah ba? Ya aka yi na zo da Badiyyah na baro Lilbirrahta? Ai da ita ya kamata na zo, duk wata nasarata Khouhar ce ?ashin bayanta... Ya aka yi to..." Ya ?are zancen zucinsa yana kallon Badiyyah.
"Ka tuna ko My Boo," wani kallo ya mata, "Dan Allah ki ?yale ni in huta, ki fita kawai ina son in huta." Tsaki ta ja ta mi?e ta fice daga Wakin. Runtse ido ya yi, yana jin wani irin abu, zuciyarsa ta yi nauyi ya rasa mene ne abin yi. Wayarshi ya jawo, duk ta canza, tun daga kan tsarinta, da dukkan yadda ya santa. ?o?arin fiddata daga key ya yi, sam ya mance shi, sai dai ya saka yatsanshi cikin sa a ta buWe. Lambar Ummansa ya fara kira, sai dai switch off matar ta tabbatar masa. Kan lambar Lilbirrah ya koma, ita ma shuru ya ji ta. Hankalinsa ya tashi, duk da yana jin jikinsa kamar da zazzaSi hakan bai hana shi tashi ya fita falon ba. Kai tsaye hanyar waje ya nufa, da sauri Badiyya ta tari gabanshi, "Kai AbuDalib, ina za ka? Zuba mata idanuwana ya yi yana kallonta kamar sabuwar halitta. Cikin Waga murya ta ce, "Tambayar ka nake wai ina za ka? Kodayake na lura kai ma ba ka sani ba, saboda na ga alamun haukar taka ta ida birkice ?wa?walwarka, ta watsa duka saitin tunaninka, shi ya sa kake wannan surutun, kake tambayar ina wata Ummanka da wata Lilbirrah? Ina Khouhar ko?" Wani irin kallo ya watsa mata, ya matsa gab da ita, "Badiyyah kin san me kike faWa kuwa? Ummana da Lilbirrah, Uwata da 'yaruwata kuma matata kike cewa wasu? Su kike cewa wasu?!" Ya faWa da ?arfin gaske. Baya ta yi tana Wan tsorata, "To Umman taka da Lilbirrah ba wasu ne Abu..." Kafin ta kai ?arshen zancenta ya watsa mata wani lafiyayyen mari.
Dafe kuncinta ta yi hawaye na biyo idanuwanta, "?arya kake wallahi, ?arya kake Abu?alib. Da kai da abinda ka mallaka nawa ne, kuma na kira su da ba wasu ba kuma ba kowa ba ne gunka ni kaWai ce..!"
Wani marin ya sake watsa mata Waya gefen fuskar, wanda ya tilasta mata haWiye kalamanta, "Ke kike ?arya Badiyyah..." Cikin ihu ta ce, "Na rantse da Allah kai ne ma?aryaci, ina Umman taka ina Lilbirrar suke a nan? Ba ka ga Vienna kake ba? Ka yarda da ni," ta faWa tana sakin wani malalacin murmushi hawaye na zarya kan fuskarta.
Kallon mahaukaciya yake mata, don abun nata ya fi kama da sabon hauka. "Lallai kin haukace Badiyyah."
"Uhmmm! Ka je ka neme su to mu gani, Umman da Khouhar Win naka da kake i?rari ka je ka neme su mu gani, in ka isa ka je inda suke." Wata mahaukaciyar dariya ta saki, "Umman da ta tsine maka da Lilbirrar da ka dan?ara ma saki uku ?warara da jar biro su kake batu ko?" Ta ?are maganar dariyarta na ?aruwa.
"Ke Badiyyah!" Ya faWa a kiWime, baya ya yi yana jin ?afafuwansa na neman kayar da gangar jikinshi, "Umman tawa ta tsine min. Kuma ni, ni, ni saki matata Lilbirrah? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Dariya take kamar mahaukaciya.
Mi?ewa ya yi ya koma Waki kanshi na wata irin juyawa. Waya ya Wauka ya soma kiraye-kirayen waya, sai dai ya gaza samun duk wani da yake tsammanin samu. Lallai akwai matsala gagaruma wacce ya kasa gane ainufinta da tushenta, fata Waya yake a ce zancen da Badiyyah ta yi mashi ?arya take.
BuWe akwaitinshi ya yi ya fiddo tarkacen passport Winshi, yellow card da sauran abubuwansa na tafiya domin shirin barin garin goben ranar ba sai wani lokaci ba. Wayarsa ya buWe ya Wauki lokaci mai tsawo ba ya a dandalin what's app. ?ayar wayarsa ta abokan kasuwancinsa ya duba, abubuwa ne ga su nan ya yi su ba yabo ba fallasa, sai dai shi yana aiki ba kamar na Wayar wayarsa ba, sannan ga tarin sa?onni da bai buWe ba.
Kanshi yake sarawa sosai, don ya rasa gane wane zaren tunani zai kama, duk abinda yake ji yake son sanin gaskiyarsa ya fi ?arfin Badiyyah. "Ummansa ta tsine masa ya kuma saki Lilbirrah saki uku da hannuwansa," Hasbunallahu wa ni'imal wakeel, yake maimaitawa.

&

Kwance yake rub da ciki, tsananin tunani yana neman tarwatsa masa kai, yadda ya ga rana haka ya ga tsayin daren, sannan bai kuma bi takan Badiyyah ba, wacce yake ji da ganinta tamkar wata halitta ta daban ba mutum ba saboda munanan kalaman da ta faWi kan Ummansa da sanyin ransa Khouhar Winsa.
Ta janibin Badiyyah kiran Mom Winta take amma ta gaza samunta, hankalinta ya kai ?ololuwar tashi, duk da irin marirrikan da ta sha wurin Abu?alib wanda har ya kumbura mata fuska, amma sam bai dame ta ba, gagarumar matsalar da ta sako kai take son a yi gaggawar magancewa, sai dai duk yadda ta so samun wayar, ba ta samu ba Wib take.
Dubarar kiran yayanta Baba Alhaji ta yi, duk ta san ba sa ga maciji, amma bu?atarta ta dole ce kuma shi kaWai zai sada ta da Mom Win.
Kiran wayarshi ta yi, kamar yadda ta yi tsammani tana kira ta shiga. ?auka ya yi muryarsa a gimtse ya ce, "Lafiya?"
"Na kira wayar Mom ba ta shiga, ina so na yi magana da ita."
"Ni ma na kira ban samu ba." Ya faWa a gimtse.
"To kana ina ne?"
"Na yi balaguro, ki cigaba da trying har ki samu." Yana faWar haka ya datse kiran.
Sauke wayar ta yi tana sauke numfashi, jikinta a sanyaye ta kwanta kan kujerar da take kai.
Abu?alib ya fito ganinsa ya sa Badiyyah saurin mi?ewa zaune, "Idan kin ga dama ki shirya, gobe za mu koma Nigeria."
Gabanta ya yi wata irin faWuwa, tabbas suka koma haka ita da Abu?alib har abada, tarin kuWaWen fa? Zuciyarta ta tambaye ta. Wani huci ta fitar daga bakinta da ?yar ta ce, "Allah ya kai mu lafiya."

&&&&&

YUNUS SPECIAL HOSPITAL

Zaune nike gaban Maman Yunus jikina duk ya yi sanyi, cikin tausayawarta gare ni ta ce, "Amatallah, Insha Allah kina gab da haihuwa kin ji." Haka nan na ji hawaye sun zubo mini, jikina ya yi nauyi sosai ga wani abu da ya dan?are mani ?asan zuciya, na kasa walwala tun ranar da Innarsu Kulu ta yi nufin sayar da ni da Abun ?aunata.
"Sorry Ama, Insha Allah lafiya lau za ki haihu ba tare da wata matsala ba."
Ban ce komai ba, sai aikin share hawaye da nake yi, "Za ki sha tea?" ?aga mata kai na yi alamun eh. Tashi ta yi ta jawo flask Win ruwan zafi, kallonta nake tana ta ?o?arin haWa shayin, ji na yi Ummana ta faWo mani a zuciyata, tabbas na yi rashinta, wani irin kewarta ta ratsa dukkan jikina, na kasa kintacen wani irin gata da kulawa zan samu daga gare ta, a lokacin da zan haifar mata jika, halittar da take son gani tun kafin zuwansa a duniya.
Hawayena suka ?ara bulbowa, sorry Maman Yunus take ta ce min. Mi?o mini shayin ta yi, hannu na sa na karSa kaWan na sha na ji ya ginshe ni. Komawa na yi na kwanta kan gadon asibitin tare da fatan Allah ya kawo min barci mai nauyi ya yi awon gaba da ni. "Salamu Alaikum." Yunus ya yi sallama bakin ?ofar Wakin, Mamanshi ta ba shi umarnin ya jira domin na kimtsa, tashi na yi zaune na saka hijabi saboda jikina daga ni sai wata doguwar rigar bubu irin marar nauyin nan. Sai da ta ba shi damar shigowa sannan ya shigo, fuskarsa sake take ko kaWan Yunus ba shi da Wacin rai. Kallon Maman ya yi, "Mama, shi ne na tafi ko ki kira ni ki ji yadda aka ?are da case Winnan ko?"
"?an Mama, ka yi ha?uri mana ka san ina fama da patient ko, kuma Ama ba ta jin daWi sosai."
Murmushi ya sakar mata, "Ba komai Mom, zolaya ce kawai, ni ki kula da Ama ya fi mun komai yanzu."
KaWa kai ta yi tana kallon shi cikin so da ?aunarshi. Ni ko ina gefe na yi dukum, a tausashe ya ce, "Mutanen nan sun jijjiga mana Ama, ga shi har yau ba ta cikin walwala. Sannu ya jikin naki?" Du?ar da kai na yi, 'yar gaisuwar da hannu ma ta gagare ni, sai hawaye nake kamar wacce aka yi wa duka.
Mama ta ce, "Yau kam jikin ba daWi a bar ta ta huta."
"Okay, Allah ya sau?e ya kawo Babyn nan ki samu sau?i ki huta Ama."
Mom ta ce, "Amin. To yanzu faWa min ya aka yi da case Win?"
"My Lovely Mom, bara na faWa maki, kin san case Win nan ma yanzu gwamnati ta nemi na fitar da hannuna kuma bar musu. Saboda kin ga waWannan da aka kama, dama ana neman su Mama, saboda ashe manyan masu safarar mata da yara ne a garin nan, sannan kuma har siyar da naman sassan jikin Wan adam suke, ita kuma wannan Inna take ko me ye sunanta ma, tana kai musu mutanen ne, nan take silfarsu a wajen sana'arta. To tunda ta ga Ama a gidan nan ta saka ran ita ma za ta kaita, riba biyu saboda ga ta ga Baby, shi ne suka haWa baki da 'yar gidan ko me ye sunanta ita ma." ya ?are zancen irin na mai nazari.
"Yawwa na tuna, sunanta Saratu ita ma jami'an tsaro sun kamo ta. Saboda da ita aka haWa baki aka yi plan aka kori Ama a gidan yadda za su je su siyar da ita Win." Kasa?e na yi ina sauraren labarin da ya girmi hasashena.
"Allah Mama, na ji daWi nagode wa Allah da ya kai ni rayuwar Ama, kuma ya ba ni damar ceton rayuwarta da ta bebinta kin ga na samu lada." Murmushi ta sakar masa, "Haka ne ?an Mamansa, Allah ya saka maka da alkhairi ka ji."
"Amin, Mamana."
"Yaushe za mu tafi gida to?"
"Yau zan kwana gun Ama, ka je kawai."
"Wayyo Mom, zan yi kewarki fa."
"Kar ka damu, Ama ba lafiya dole na tsaya."
"Ni ma na fi son haka ai, da kanki kina kula da ita Mom."
"Zan tafi sai an jima My Mommy, Gud Night nake son cewa." Mi?ewa ya yi tsaye, wanda kusan a tare suka mi?e, ni dai ina kwance daga gefe ina kallo da saurarensu, wayayyun mutane ne sosai, sam ba su da matsala.
Rungume Maman ya yi bayan sake ta sannan suka fice waje, ba a jima ba ta dawo cikin Wakin. Sannun ta da ba ta gajiya da ita ta hau yi mini, rufe idanuwana na yi ban san lokacin da barci ya sace ni ba.

&

3:00am

Kamar ana buguna na ji hakan ya sa na buWe ?wayar idanuwana, kallon agogo na yi ?arfe uku daidai na dare. Gabana ya Wan faWi ganin ukun dare ne. Tashi na yi zaune dangal-gal, hular kaina da ta cire na Wauko na saka, gefe kuma kan Wayan gadon Maman Yunus ce ke barcinta a nutse. Ji na yi fitsari ya taso mini kamar na daWe ina jinshi, mi?ewa na yi na taka da ?yar na buWe toilet Win. Sai da na gama abinda nake na fito, ji na yi jikina ya fara sauyawa, kamar tsira-tsira na tasowa daga ?ar?ashin tafin ?afata.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un," na ambata ?asan raina. Tun bayan da na samu addu'ar a mafarki ban sake fuskantar zafi da tsirar da ke galabaitar da ruhi da gangar jikina ba. ?o?arin tuno addu'ar nake yi, sai dai tamkar ban taSa saninta ba, bayan ina karantata a kowace rana, safe, rana da kuma dare. Tsirar na ji ta fara yawa a cikin ?warukan ?afafuna, "La haula wala ?uwwata illah billah," na ayyana a raina cikin yanke ?auna da fuskantar wani sabon bala'i da na ji ya diro mini daidai lokacin.


SH 12

Ji na yi azabar na cigaba da ratsa sassan jikina, yun?urin motsa ?afata na yi sai dai ita ma ta yi cik tamkar an kafe ta da kusa, "Tabbas babu makawa yau mutuwa zan yi." Na ayyana a raina, hawaye na silalowa daga idanuwana, jikina tamkar an zuba mini ruwa zufa ta wanke ni ko'ina, wani irin gurnani da na fara ya tayar da Maman Yunus, ganin yanayin da nake ciki ya sa ta mi?ewa tsaye a rikice, "Ama me ya same ki haihuwar ce ta zo?" Ta ?are zancen tana ?arasowa gare ni. Yadda ta ganni ne ya sa ta ida shiga cikin tashin hankali, jikina ya sandare wuri daya sai rawa yake yi tamkar an hada mashi wutar lantarki. "Amatullah, Ama& " take ta kiran sunana tana ?o?arin jijjiga ni, sam ta kasa motsa ni, ni ma kuma na kasa motsawa ko kaWan. Yun?urawa na yi da ?arfin tsiya jin wani abu da ya tokare mini cikin ma?oshi kamar zai tsirga ma?wagowarana, Ya Allahu, na kasa yin komai ko da a ?asan raina ne, sai wani irin numfashi da nake fitarwa tamkar zan shiWe. Maman Yunus ta rike ni tana kiran sunayen Allah, gaba Waya ta rude ta rikice ?o?arin tankwara jikina take yi amma ta kasa agaza mashi da komai kamar yadda ni ma na kasa sarrafa shi ko yaya, abinda ya tokare makoshina ya ?aru take jini ya fara Wiga daga hancina idanuwana suka yo waje kamar mai shirin barin duniya, a guje Maman Yunus ta fita don samo Wauki, wani irin juyi cikin jikina ya yi wanda ya zo daidai da sarawar wani abu cikin ?uguna kamar an buga mini guduma. Innalillahi wa inna ilaihi raji un ta zo mini cikin zuciyata, cikin neman rayuwa irin na mai rai na sake kokarin yunkurawa a wannan karon na yi nasarar motsa ?afata, jan ta na yi da kyar na isa jikin gadon. Maman Yunus ta shigo tare da wasu nurse guda uku, kama ni suka yi su duka hudun suna ?o?arin hau da ni kan gadon, sai dai abun ya gagare su azabar da ta ishe ni ta sa ni dur?ushewa ?asa kan gwiwoyina, gaba daya na fice daga hayyacina sai wani numfashi da nake yi da kyar wanda ya bawa su Maman Yunus tsammanin mutuwa na gab da tafiya da ni.
?aya daga cikin nurses Win ta ce, "Ma, wannan ya yi kama da har da wani abun daban, amma ba iya haihuwa ba ce."
"Okay," Maman Yunus ta faWa tana ida rikicewa. Ruwan roba ta Wauko ta kwarara cikin cup, addu a ta fara tofawa cikin tana gamawa ta tsiyaya su cikin bakina, ji na yi azabar ta karu kuguna ya ci gaba da sarawa wanda nake ji har cikin gadon bayana da dukkan ilahirin jikina, yanayin yadda nake yi ya sa Maman Yunus fadin, "Haihuwa ce ta zo yanzu, haihuwa ce Ummi," ta ?are maganar tana neman Waukin nurse Ummi.
Sosai lamarin ya koma mini nakuda gadan-gadan, Maman Yunus tare da nurse din suka cigaba da shirin tarbar haihuwa, tabbas nau ikan azaba kala-kala ne amma ban taba jin kwatankwacin wanda nake ji ba daidai wannan lokacin. Na kai kimanin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login