Showing 48001 words to 51000 words out of 55242 words

Chapter 17 - BA DON MACE BA BY FATIMA FANTAH.doc

Advertisement

22 Feb 2025

3655

Badiyyah, ranar murna a gare ni ba a magana, wata hudu aka sa bikin. Kuma tun a wannan lokacin ban sake fuskantar wata matsala mai kama da wannan ba a wajen Badiyya sai ma nuna min kauna da kulawa da take yi sosai wanda hakan ya faranta ran Yaya sosai, hakan ya sa ya kara kaunar Badiyyah.
Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah mai girma, lokacin bikin auren Yaya da Badiyyah ya zo, wannan lokacin yana daya daga cikin lokutan farin ciki a gare ni lokacin da auren Yaya ya yi zo.
A lokacin Wan madaidaicin gidan Yaya ya kammalu, wanda ya sha gyara tsaf daidai wa daida ga rayuwar talaka, sannan kuma ya hada ma Badiyyah lefe na ji da gani, wanda muka yo siyayyar kayan lefen ni da Ummana da Inna Uwale. Kamar yadda ta taSa faruwa haka lokacin kai lefen ma, yadda masu kai wa suka kai shi, haka suka dawo ko ruwa ba su samu ba daga gidansu Badiyyah, hakan ya sa dangi suka fara ?ananun surutai. Sma ba mu mai da kai ba muka cigaba da hidimar bikinmu, saura kwana biyar bikin muka fara shagulgula, murna guna tamkar ni ce ake wa auren, don ko Yaya bai fi ni farin ciki ba. Kullum cikin nishadi nake a wajen kowane event da aka yi kuwa ni ce gaba-gaba. Ranar asabar ta zo aka daura auren Yayana Abu?alib da ?awata kuma aminiyata Badiyyah. Ranar na yi murna marar misaltuwa, misalin ?arfe shida na yamma muka Wauko amarya daga gidansu zuwa gidan angonta Yayana.
A cikin kowane aure ba a rasa tsegunguma na dangi, wanda da yawa danginmu suke complain daga gidansu Badiyyah ba su kawo komai ba bayan gado da kujeru, babu kayan kicin da labulaye, babu gara da kayan dangin miji. Ummana ta yi ta kwabar bakunansu da hana su yin tsegumin, a cewar Umma da ma ba dole ba ne, sannan kuma babu laifin yarinya idan suka cigaba da tsegumin za ta ji ba daWi a ranta.
Karamci irin na Ummana bayan kwana uku da bikin ta sa Yaya AbuDalib ya ba da dubu dari biyar muka je muka siyo kayan kitchen 'yan daidai na bukata muka saka a kitchen din Badiyyah ni ce gaba wajen jerawa, sannan kuma muka siyo labulaye aka gyara Wakin tass.

Haka aka yi ta gungura rayuwar ana hakuri da yau da goben cikinta, na mayar da hankalina kwarai kan karatuna sannan na ki kula kowane saurayi kamar yadda na ci alwashi sai na kammala karatuna ko kuma idan ya zo saura shekara daya in gama sannan na fara kula saurayi don kar soyayya ta yi mini tasiri ta shafi karatuna.


BAYAN SHEKARA BIYU

Daidai gwargwado muna Wan mutunci da Badiyyah duk da bai kai na lokacin farkon bikinsu ba, a lokacin abinda na lura da shi sam ba ta son ina zuwa gidansu, da na fahimci haka sai na yi nesa da zuwa gidan. Joonam Wina zai kai ni, shi kuma babu ranar da rana za ta fito ta faWi ba tare da ya zo gidanmu ba. Mu'amala tsakanina da shi babu abinda ya sauya, sai ma ?ara ?aunata da yake yi da kulawa da ni da yi min duk abinda nake so, daidai gwargwado kuma ita ma Badiyyah yana sauke dukkan nauyi da hakkinta da ya rataya a kansa, ba ya taue ta da komai, amma kuma hakan bai hana ta jin ?ai?ayi a duk wani abu da zai yi min ba, sai dai in ya yi ba ta sani ba.
A Sangaren karatuna ya rage saura shekara daya na hada degree, hakan ya sa min tunanin fara kula samari da suke ta naci a kaina. Ina zaune ina amsa wayar wani abokin Yaya Mustafa Yaya ya shigo, bankwana na yi ma shi na kashe wayar.
Hararar wasa ya yi mini, murmushi ja yi ina gyara zamana, "Yaya yau kuma da fushi aka zo mana."
"Dole in yi fushi mana, a ce shekara Waya ciff wai ba ki kai mana ziyara ba, haba Khouhar ban taSa tsammanin za ki wata ma ba ki ziyarci gidana ba."
"Kai jama'a Joonam, kamar ka sani Wazun nan muke zance da Rumaisa za mu kawo muku ziyara ran asabar weekend kenan. Na san a ranar ba ka zuwa shago da wuri."
"Shi ke nan Allah ya kaimu."
"Amin Joonam Wina, da ma iya wannan ne laifin?"
"Ehh mana, kina zuwa kuma kin wanke kanki."
Dariya na yi ina faWin, "Za mu wanke shi ko tass."
"Ina Ummana?" Ya tambaye ni.
"Ummanmu tana kitchen."
"Ke kuma kina nan?"
"Yanzu ban jima da shigowa ba, na je kuma ta ce na je na huta."
"Yar Umma kenan, to shi ke nan, bara na iske ta can."
"Okay," na faWa, yayin da shi kuma Yaya ya fice zuwa wurin Umma.
Ranar Asabar muka shirya muka tafi gidan Yaya ni da Rumaisa kamar yadda na yi al?awari.
Ina yin sallama tun a zaure ya taso da hanzarinsa ya tare mu. Dariya nake yi sosai, "Haba, Yaya so kake tun kafin na shiga ka ja min laifi?"
TaSe baki ya yi yana, "Ku dai mu shiga ba wani laifi, ku da ba ku zuwa daga shekara sai shekara."
"Wayyo Joonam, makaranta ce fa ta boye ni kasan aski idan ya zo gaban goshi ya fi zafi."
"Uhmm," kawai ya fada. Tare muka shiga cikin falon, Badiyyah na zaune kan kujera hakimce tana latsa waya, "Aminci bari a tuna da," na fada ina dariyar tsokana. "Uhmm ai da ?eya ce in ji masu hikimar zance," Badiyya ta fada a dan gimtse. Zubewa muka yi kan kujera mai zaman mutum uku ni da Yaya, ita kuma Rumaisa ta yi zamanta ?asa kan kafet da ke shimfiWe a tsakiyar falon.
"Haba Lilbirrah haba Khouhar shekara guda daya ciff kafarki ba ta tako gidan Joonam ba."
"Yaya wai ni kam Bady ta koya maka tsegumi ne, Allah har maganar ta soma tu?a ta, kuma fa abun nazo din ne bai taso ba, ka ga da ?awata ma ta kira mu da na rika zuwa ganin da na ko diyata."
Kallonta na yi ina dariyar wasa, sosai ta haWe girar sama da ?asa, "Haihuwa ai sai Allah ya kawo Lilbirrah, tunda ba mu za mu ba kanmu ba."
"Haka ne don Allah ki yi hakuri wasa nake miki wallahi kin san ba zan faWi haka don in muzanta ki ba."
"Okay, to ya gida ya kike ya su Umma?"
"Suna lafiya wallahi, ta ce ma a gaishe ki."
"Aiko ina amsawa."
"Ya wajen su Mama mun dade ba mu gaisa ba?" Na tambaye ta.
" Suna lafiya kalau Lilbirrah," yawwa na fada. Mikewa ta yi tana, "Bara na kawo maku ruwa to."
Mai da kallona na yi wajen Yaya. "Joonam ya gida ya aiki, na yi maka tambaya ta musamman tunda gidanka na zo."
"Ke dai kika sani."
"To Yayana har yanzu ban goge laifina ba ne?"
"Kin goge mana. Mu ba mu jima da yin break ba, amma tunda kun zo me zan girka muku?"
Rumaisa ta yi saurin cewa, "Yaya Irishi potato da soup Win egg and fish."
"Ke Rumaisa ki rufa mina baki, sai wani lissafi kike,".mai da kallona na yi wurin Yaya, "Ni dai Joonam bana son ka mana wani girki, idan lokaci ya yi mun yi da kanmu."
"A'a, ni zan yi muku girki da kaina, a gida ba na yi ba?"
"A nan Yaya ai gidanka ne kai za a yi wa, ko kana taya kawata ne?"
"Ina fa? Ayyuka sun mini yawa."
"To ka gani, koyaushe ba ka gajiya da goga mani bakin fenti gun matarka shi ya sa ma bana zuwa."
"Abinda za ki ce kuma kenan, ni dai zan yi abinda auta take so Irish Potato da miyar kwai da kifi."
"Allah ya ba da sa a, wannan ai ba ni na ce ba."
Murmushi ya yi yana jawo wayarsa, "Ban ba ki labari ba Khouhar, kin san harkar mining dinnan da ake yi?"
Dan daga gira na yi, "To na ji dai ana fadarsa kuma na ga irin abroad dinnan suna yinsa sosai, amma na ga bai yi yawa ba a nan."
"Ke Khouhar ba ki sani ba dai ne, amma ana yi, kuma harka ce da za a yi nan Win ma sosai."
"Allah ko Joonam?"
"Na ce maki zancen kike so ya yi tsayi, kin san wani Yeaster da ke zuwa shagona ina masa Winki?"
Shuru na yi irin na mai nazari, "Gaskiya na kasa tuna shi Yaya."
"Ina wani Wan ?asar Sin wanda ya zo a bikinmu har yana kula ki, kina cewa ba kya son farar fata."
Dariya na yi ina faWin, "Joonam ka ce mini Yass abokinka kawai zan fi ganewa."
"To shi, in faWa maki shi babban Wan Crypto Currency ne, shi yake koya min harkar trading Winnan, tun bana ganewa yanzu na fahimta, wallahi Khouhar da zan samu jari na zuba a harkar nan, to nan da shekara biyu zuwa uku za ki ga na zama hamsha?in mai kudi, kawai sai dai ki ji sunana a manyan masu kudin kasar nan ba ma garin nan ba."
Dariya na kwashe da ita, "Yaya kenan 'yan shafe-shafen za ka rika yi ko me? Kuma na ga masu yi fa ba su sa komai."
"A ah ba ki gane ba ne, masu shafe-shafen dai idan sun tara wannan coins din za su sayar sai na rika saye, nima idan na siya ni ma sai in siyar a market din crypto."
"Okay na gane Joonam, za ka siya sai ka siyar, to da ka ce jari kenan kudi ake bukata."
"KuWi da yawa ma Khouhar akalla a ce kadan ina da dala dubu ashirin kasuwar."
"Ahhh, lallai kudin da yawa, ai za su kai a?alla miliyan ashirin ko Joonam."
"Ehh mana, sun kai haka, ko a ce ba su ida ?arasawa ba."
"Joonam ya za a yi kenan? Na ji ni ma kasuwar ta zauna min a raina."
"Gaskiya kudi kawai nake so idan na samu wannan kudin sai kasuwa, yarinya kar ki ce me ye muna Makkah? Ke har China zan kai ki mafarkinki na zama software engineer na mayar da shi gaskiya."
"Kai!" Na fada baki bude.
"Tunani nake yi na siyar da gidan nan, da 'yan abubuwan da na mallaka na ga nawa zan samu sauran Allah ko bashi ne zan ci na cigaba."
Shuru na yi saboda wani tunani da ya zo mini. "A ah Yaya ba za a yi haka ba, harkar da ba ka san ya take ba sai ka rabu da kadarorinka saboda ita, ba za a yi haka ba Yaya, Umma ma ba za ta bari ba."
"Shi ke nan da ma ke ce abokiyar shawarar, tunda ba ki yarda ba shi kenan."
Duk labarin da muke zubawa Badiyyah ba ta dawo daga kichin ba, na sha?i iska zan cigaba da magana ta shigo. Gaba Waya Wan sauran annurin da ke fuskarta ya ?arasa dishewa, "Uhmm na ji ana ta zuba hira tsakanin Yaya da kanwarsa, na ji har da su zancen China."
"Ke dai Bady rabu da Yaya kawai." Zama ta yi tana mana hararar kasan ido, duk da shi Yaya bai ganta ba amma ni na lura da ita.
"To ita Lilbirrah haka za ta yi ta zama ba aure, ko bayan auren mijin kamar sakarai zai bari kawai ta tafi China karatu shi ya nan zaune kamar sakarai."
"To aure dai zuwa yake idan lokacinsa ya yi, sannan kuma idan na samu halin ko bayan auren ne sai ta tafi mijin ba zai hana ba, ai ba mai tsawo za ta yi ba tunda masters ne."
"Ni tunda nake ban taba ganin wa da kanwa irin kai da ita ba, da a ce ana aure wa da kanwarsa shakikai ai da na ce me zai hana kawai ka aure ta sai in ga ta karshen soyayyah."
"Ai ko yanzu ma zan iya aurenta ko ba ki sani ba ne?"
Kallon Yaya na yi sam ban taba zaton zai mayar mata da amsar haka ba. Kallon shi ta yi a fusace, "Lallai so ya kai karshen rufe maka ido, da har kake tunanin take iyakokin Ubangiji?"
"Take iyakokin Ubangiji kamar ya?"
"Na auren ?anwarka mana da kuka fito ciki Waya."
Mayar da abun na yi wasa, "Kai ku kenan muka hadu wuri daya dole sai kun yi fada a kaina."
"Rabu da ita na ga tana min wata fassara ne, ki bari na fada mata ta ji kuma ta sani ni ke ba ciki daya muka fito ba iyayenmu ne suka fito ciki daya, akwai halastaccen aure tsakaninmu." Mai da kallonsa ya yi wurin ta, "Idan gatsen da kika yi ya zo da bakin mala iku ke ce za ki fi kowa tashin hankali na sani."
Kallon Yaya take yi kamar za ta hadiye shi, "Wai da gaske Lilbirrah ba Umma ce Babarsa ba?"
Jinjina mata kai na yi, "Haka ne amma wallahi ba soyayyar aure tsakaninmu, kin ji ma na rantse miki da Allah, ni ina matsayin kanwarsa ne haka shi kuma yana matsayin Yayana ne, kuma ko mutane a haka suke daukarmu ba mu fadar cewa ba Uwa daya uba daya muke ba, don a hakan muke jin kanmu."
Hararata ya yi, "Ni ki min shuru kina ta mata wata rantsuwa, idan aurenkin na yi ai ban aikata haram ba, babu laifi a shari'ar kowane littafi."
"Yaya a bar wannan maganar mu je zancen mu na Crypto, idan ba ya yiyuwa kuma mu mike mu koma gida."
"Lilbirrah kenan, ki kyale shi ya fada mani duk abinda yake so...," kafin ta kai aya na yi hanzarin mikewa, "Sai ku cigaba da musayar yawunku ni kun ga tafiyata, Rumaisa taso mu tafi gida, yaya sai wani lokacin kuma." Na ?are zancen muna tunkarar ?ofa ni da Rumaisa.
"Khouhar ki dawo mana," Yaya ya faWa.
"Allah ni mun tafi, mun karasa maganar a gida, yini kuma na fasa ziyara dai ga ta na kawo sai wani lokacin kuma."
Hannu ya sa cikin aljihu ya fiddo kuWi ya miko min, "Gashi tunda ba za ku tsaya ba na shirya mu tafi tare, kun hau keke napep."
"To mun gode Yaya sai ka zo," na fada sannan muka fice daga gidan.
Muna fita muka tsaya jiran Napep, wata dan?areriyar mota ?irar Marcedes ta yi fakin gabanmu kaWan, juyawa na yi na kalli Rumaisa, ita ma ni take kallo domin ga alamu mai motar domin mu ya tsaya.
Le?owa ya yi ta windown motar yana magana, ganin haka ya sa muka Webi hanya ni da Rumaisa muka cigaba da tafiya har mu yi gam da katar da Napep. Horn Win da muka ji bayanmu ya dakatar da mu, mai motar ne ya sake cin taren mu. A wannan karon fitowa ya yi tsagwayam daga motar bayan ya yi fakin, "Haba baiwar Allah, tun can nake maki sallama amma kamar ba 'yaruwata musulma ba kin ?i amsawa."
?aga kai na yi na kalle sa, "Masha Allah, barakallah," ya faWa yana kallona, irin kallon da ke bayyana soyayyah a zahiri.
"Assalamu Alaiki,"
"Wa alaika salam," na faWa can cikin ma?oshi.
"Daga ganin yanayinki ba za ki shiga mota na rage maki hanya ba, amma don Allah ba don halina ba a taimaka a faWa min suna, numbern waya, da kuma unguwar da ake zaune, ba zan Soye maki ba ni dai na gani kuma ina so."
"Rumaisa ke taho mu tafi," na faWa ina jan hannunta domin mu bar wajen.
"Rumaisa ?anwata tsaya mana," ya faWa har yana jan abayarta. Sakinta na yi na cigaba da tafiya, sai da na yi Wan nisa da inda suke tsaye sannan na tsaya. Gani na yi suna magana da Rumaisa, ni ko sai aika mata nake da sa?on harara. Ina tsaye ina dakon jiranta ta ?araso.

"Yaya Lilbirrah mutumin yana da kirki," ta faWa lokacin da ta zo gab da ni. Kamar in kwaWa mata mari, "Yanzu a cikin abinda bai fi five minutes ba har kin gano yana da kirki." ?aga min kai ta yi, "Kin ga ma na ba shi lambar wayarki, na faWa mashi sunanki, ya ce in faWa maki sunan shi Jameel..."
Dogon tsaki haWe da kyakkyawar harara da na yi mata ya sa ta tsuke bakinta. Daidai lokacin Napep ta zo ina ganinta ba kowa ciki na shige, a fusace na ce, "Idan kin ga dama sai ki shigo mu tafi idan kuma kina da sauran abin cewa sai ki zauna a nan." Shigowa ta yi tana kallona, faWa mashi inda za mu je na yi, har muka isa gida tamkar kurame ba wanda ya ce ma Wanuwansa wani abu.

SH 19

Ina zaune da dare na ji wayata na kuwwar neman agaji, Wago kai na yi na kalli wayar, ganin lambar da ke yawo kan madu???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?bin wayar ba suna hakan ya sa na bar ta ta cigaba da kuwwarta har ta gama. Sake kira aka yi a karo ba biyu, shi ma har ta yi ta ?are ban dauka ba. Jin ?arar shigowar sa?on kar-ta-kwana da na ji ya sa na ja Wan gajeran tsaki sannan na sa hannu na Wauki wayar, "Please pick My call Dear." Karanta sa?on na yi har da maimaici, kafin na ?arasa yanke hukunci wani kiran ya sake shigowa, har ta kusa yankewa wata zuciyar ta ba ni shawarar in Wauka.
A sanyaye na kanga wayar a kunne, wata doguwar ajiyar zuciya na ji ya sauke cikin kunnuwana, "Da ba ki Wauki wayar nan ba na tabbata da yau na kwana a asibiti." ?an gajeran murmushi na yi, "Kwana a asibiti kuma?"
"Ehh mana, saboda ruhin da ke Wauke da gangar jikin yana cikin matsala kin san dole mamallakiyarsa ta fi shi shiga matsala don tafi shi rauni."
"Haka ne," na faWa a gajarce.
"To ya kike ya kika je gida?"
"Lafiya lau."
"Ya su Mamana da Babana?"
"Duka lafiya suke."
"Na ji daWin haka My Queen." Shuru na yi daga haka ina sauraren shi.
"Lilbirrah." Ya kira ni cikin wani sauti mai nauyi.
"Na'am," na amsa ina sauraren abinda zai faWa min, "Zan faWa maki gaskiyar abinda ke raina, tun lokacin da kika tunkaro ni a kallo Waya da na yi maki na rasa tunani da dukkan nutsuwata, kuma a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login