Showing 6001 words to 9000 words out of 55242 words

Chapter 3 - BA DON MACE BA BY FATIMA FANTAH.doc

Advertisement

22 Feb 2025

3657

tare da magunguna. Komawa ta yi cikin ofishin likitan. Iske shi ta yi?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ya kwantar da kansa bisa teburin da ke gaban likita. Wani kallo ya yi mata wanda ya sa cikinta juyawa, a Wan razane ta ce, "My Boo& lafiya dai." Rufe ido ya yi ya bude, "Lafiya lau."
Doctor ya karSi zancen, "Ba wani abu za ku samu lafiya. Yanzu sai ku mike na muku allura ko."
Tsaye ya tashi Doctor ya yi masa allura. Kafin ya zare tsinken alluran daga jikinsa barci mai kama da na tsafi ya dauke sh, a take ya faWa jikin Doctor din gijib. Gyara shi likita ya yi ya kwantar da shi kan kujera. "Amma Doctor ya zan yi da shi?" "Ba komai, ki kira wani yayansa ko kaninsa ya zo ya taimaka maki a tafi da shi gida."
Bata rai ta yi don sam ba ta son jin zancen da ya shafi 'yanuwan Abu?alib. "Okay, Doctor kamar na sani dama, yanzu za a zo sai mu tafi da shi Win."
"Ba damuwa to." Wasu magungunan ya ba su ya ce ga su nan ta tafi da su tare da lokacin da za ya rika shan su. Kudi ta zaro daga jakarta ta mi?a masa, tana maimaita mun gode sosai Doctor. Ba a fi tsayin mintuna sha biyar ba yayanta da suke kira da Baba Alhaji ya karaso. Har inda AbuDalib yake kwance suka isa, da taimakon Doctor suka Wauke shi suka kai shi har cikin mota. Fuskarsa a daure ya ce, "Me ya same shi ne?"
"Ba ya da lafiya Baba Alhaji."
Tabe baki ya yi ya zagaya mazaunin direba ya kunna motar suka tafi. Tuki yake fuskarsa a daure, "Badiyya." Ya kira sunanta. "Na'am," ta furta tana mayar da hankalinta kansa.
"Kin ga rayuwar nan duk abinda ka shuka shi za ka girba, idan alkhairi ka shuka to alkhairi za ka girba haka idan ka shuka sharri shi ma sharrin za ka girba. Wani lokaci mutane suna yin abu kamar su ne suka halitta kansu alhali kuma duka bayi ne da suke da ubangida, yana sane da komai yana kallon komai, kuma ya sanya sharuWa da dokoki."
"Uhmmm. Baba Alhaji to ni me ya sa kake mini duk wannan maganganun?"
"Kin san dalili mana." Shuru ya yi lokacin da suka isa get din tamfatsesen gidan. Ba kowa gidan sai jefi-jefin masu aiki, kama shi suka yi suka kai shi har zuwa bedroom dinsa, barci yake tamkar matacce. Jawo kofar dakin ta yi ta rufe, Wani kallo Baba Alhaji watsa mata sannan ya buga tsaki.
"Baba Alhaji wai duk me ya faru kake ta min wannan abun?"
"Badiyyah, kina bata min rai da wannan tambayar. Ni dai ina fada maki, abinda ka yi kamar jifar mashi ne, kai ka jefa amma ba ka san kan wa zai sauka ba duk iya ya?ininka, ko ya samu wanda ka sai ta, ko kuma ya samu wani wanda ba ka tsammani. Wannan ne abun tunanin ina zai fada. Na barki lafiya sai anjima." Bin shi ta yi da wata muguwar harara tamkar za ta yado idanuwanta. Dogon tsaki ta ja, a hankali ta ce, "Allah ya raka taki gona, wani jaye-jayen masifa. Ni kam na samu abun harina tunda har na kafa daula."
Wani tsakin ta ja ta baro sashen shi, ta yi sashenta na kasa.

____________________

&
Kwance take kan gado wanda ko shimfida babu, hannunta sakale da igiyar karin ruwa, numfashi take mayarwa tamkar yana neman ya gagareta.
"Umma, don Allah ki taimaka ki bari na je gidan Yaya ya taimaka mana da kudin magani, kar mu rasa ki Ummanmu, don Allah."
Kada kai ta yi, da kyar ta ambaci sunanta, "Rumaisa& watakil ke kina da Wanuwa amma ni ba ni da wani Wa, idan kuma kika je gidan AbuDalib ki sani kin je ba da yawuna ba, ba zan taSa yafe maki ba." Hawaye masu dumi da suka gangaro mata ta share, "Umma don Allah ki gafarce ni ki taimaka don Allah..." Ta ?are zancen muryarta na rawa.
"Idan kin gaji da zama inda nake, ki tashi ki tafi wurin ma ci amanar Babanki, ki cigaba da zama da shi. Ni dama gabar da nake ina kaunar mutuwa ne sama da rayuwa."
Dafe kanta ta yi ta hadiye yawun da ya yi mata tsaye a makoshi kamar dutse. Cikin muryar kuka ta ce, "Shi ke nan Umma, ni ina tare da ke, ba zan taba tafiya ko ina in bar ki ba, kuma ina nan ko mutuwa za ki yi mu mutu tare."
Rufe ido wacce ake kira da Umma ta yi, wasu 'yan kudi ta mika mata, "Ga shi ki hau abun hawa ki dauki wannan zoben nawa, ki je kasuwa ki sayar da shi."
"Shi ke nan Umma, idan na tafi kuma wa zai zauna nan?"
"Ki kira min Uwale ta zauna nan kafin ki dawo." Jinjina kai ta yi da sauri ta kira Uwale, cikin mintoci kadan ta kira Innarta Uwale ta iso. Fuskarta cike da hawaye ta durkusa gefenta, "Babbar yaya& Jikinki nisa yake yi, haka za ki zauna cikin wannan halin? Don Allah ki bari a shiga lamarin nan."
"Uwale& ba kiran ki na yi ki min wannan maganar ba. Ki kula da ni kafin ta je kasuwa ta dawo. Shi ma don kar na cika ba kowa a kusa da ni wanda zai maimaita mani kalmar shahada idan mutuwata ta zo."


SH 4


RUMAISA

Abaya kawai ta saka ta fita, Keke Napep ta hau zuwa kasuwar central market, tana isa ta ?arasa layin masu siyar da gold, ciro zoben ta yi daga aljihun rigarta, tsayawa ta yi bakin shagon tana kallon zoben, shi kaWai ya yi masu saura a abinda suka mallaka, idan suka siyar ba su da wani abun ?addara da za su cigaba da fuskantar rayuwarsu. Wani abu mai tauri ta hadiye cikin makoshinta, take hawaye masu Wumi suka tsiyayo daga idanuwanta. Da sauri ta juya ta bar ?ofar shagon, da sassarfa ta fita bakin hanya inda za ta samu Napep, 'yan kuWin da suka rage mata ta duba, "?ari uku," ta furta tana fitar da wani huci. Ba ta karaya ba ta tsayar da mai Napep ta ce ya kai ta Modoji, cikin sa a ya amince zai kai ta da kuWin da suka yi mata saura.
Bakin tamfatsetsen gidan Yayanta aka sauke ta, tsaye ta yi tana kallonsa, katon gida ne da ya ji gini na tsara, ko ba a fada ba kallo Waya za ka yi masa ka tabbatar mamallakinsa ya tara manyan kuWaWe.
"Idan kuma kika je gidan Abu?alib, ki sani kin je ba da yawuna ba, ba zan taSa yafe miki ba..." Wasu kalaman Ummanta suka soma yawo cikin ?wa?walwarta. Hawayen da suka zubo mata ta sharce, "Rayuwar Ummana na cikin haWari, sannan kuma ga rashin amincewarta a kan zuwana nan... Wannan shi ne gaba kura baya sayaki..." Hawaye suka sake wanke fuskarta. "Ya Allah ka sa ni ba da son raina na ?i bin umarnin mahaifiyata ba, ina son ceton rayuwarta ne, Allah ka yafe mini." Tafiya ta yi ta isa daidai ?ofar, kwankwasa wa ta yi sannan ta tsaya tana dakon jiran a buWe mata.
Mai gadi ya le?o, kallonta ya yi sama da ?asa sannan ya ce, "Hajiya barka da zuwa." Ba ta amsa mishi ba saboda ba ta cikin yanayin da za ta amsa mishi.
"Ammm Hajiya Rumaisa, Hajiya ta ce kar a bari ki shiga gidan nan..." Ya faWa cike da jin nauyin kalaman da furta mata. Wani kallo ta watsa mashi, "Salahu, ni kake faWawa wannan zancen? To, da ni da Hajiya wa ya fi matsayi a cikin gidan nan, ina iya dawwama a cikinsa ita kuma wata rana za ta iya yin waje ta bar shi, kuma wallahi sai na shiga cikin gidan nan." "Hajiya na sani, amma ki yi hakuri, cewa ta yi idan na bari kuka shigo bakin aikina..." Cikin bacin ran da ke nu?ur?usarta ta hankada shi har ya fadi ?asa, da gudu ta shige ciki, harabar gidan babba ce kafin ta isa wurin da zai sada ta da ?ofar shiga falon tafiyar da 'yar tazara. Hakan ya sa har Salahu mai gadi ya iya cimma ta. Muryarsa a rikice, yake maimaita, "Hajiya don Allah kar ki mini silar aikina..." Sam ba ta sauraren shi sai ma ?ara ?aimi da ta yi don isa bakin ?ofar.

BADIYYAH
Ta tagar bene ta hango su, Wan guntun murmushi ta saki sannan ta mike ta bude kofa ta le?o, cikin isa da kasaita ta ce, "Kai Salahu bar ta ta shigo." Tsayawa ya yi, ita ma cikk ta tsaya daga kai ta yi ta kalle ta, ta Wora hannuwanta kan bagalar benen ta yi kyau sosai ta ?ara kiba da haske tamkar wata matar Gwamna. Wasu kwalla suka zubo mata, Wan adam kenan ka yi ma shi rana ya yi maka dare, har abada ba za ta taba mance Badiyyah ba a cikin kundin tarihin rayuwarta. "Lafiya kika zuba min ido?" ?an firgigi ta yi, a hanzarce ta sa ?afa ta cigaba da tafiya. Badiyya juyawa ta yi ta koma cikin dakin, ita ma cigaba da tafiya ta yi ta shiga cikin falon gidan.
?arema falon kallo take ya zame mata sabo kamar yau ta fara ganinsa, cike da yake da kayan alatu tamkar falon wani basarake. Kallon sashen "Yaruwarta ta yi, wasu sabbin hawayen suka zubo mata ta yi saurin gogewa. Badiyya ta ?araso ta zauna kan kujerar da ke kallon ta Rumaisa.
Cikin sigar rainin wayo ta ce, "Rumaisa u sannu fa, ya gida ya su Iya?"
"Uhmmm,' kawai Rumaisa ta furta, cikin ?yama da tsanarta ta ce, "Da ma ba wurinki na zo ba, wajen Yaya na zo, yana nan?"
"Na ce ba, na sha fada muku ku daina neman sa, saboda baya da lokacinku abubuwa ma sun masa yawa, lokacinsa nawa ne ni kaWai. A gare ku kuma ni wakiliyarsa ce, so me ye damuwar? Rashin abinci ko? Nasan ma fi yawan matsalar talakawa ta yunwa ce." Rumaisa ba ta iya furta komai ba sai na mujiya da ta zuba mata. A wula?ance ta ce, "Laure, Laure, Laure..." Da sauri ta ?araso, "A kawo mata abinci..." ta ?arashe maganar tana kallon Rumaisa.
Muryarta na rawa ta ce, "Badiyya ke ma kin sani tun da kika san mu ba mu da yunwa, kuma har kika shiga cikin rigar arzi?inmu kina wula?anci ba ma nema wurin ki. Ke, ke ce dai matsiyaciya, mayunwaciya, butulu. Kuma ki sani wata rana sai kin kwashi kashinki a hannu sai kin girbi abinda kika shuka, indai rana na fitowa dare na maye gurbin haskenta da duhu."

Shuru ta yi tana mata kallon rainin wayo. "Ga abinci nan an kawo miki ki ci na san matsalarki dai duk ta yunwa ce, ita ta sa kike wannan Wumumuwan."
Hawaye suka kara wanke fuskarta, a hankali ta ce, "Ina son in ga Wanuwana." Harararta ta yi, "Ai fa sai ki ci gaba da yi."
Mikewa ta yi ta haye matakalar bene inda part Winsa yake, da sauri ta bi bayanta, "Ba inda za ki je na gaya maki."
"Wallahi sai na je tunda na tabbata Wanuwana yana nan." Fizgo ta ta yi baya hakan ya sa ta gangaro daga kan benen, tim ta faWa ?asa. Dagowa ta yi jin yadda kanta da kirjinta suka bugu da ?asa, Mikewa ta yi, daga inda Badiyya take ba ta motsa ba sai kallonta da take yadda ta dafe kanta. Juyawa ta yi ta haye benen, ba ta jima ba ta dawo, Rumaisa na tsaye inda take ta fito. "Na ga kamar kanki ya Wan bugu, ga wannan ki sha paracetamol." Kudi ta tilla mata bandir daya na kilon Najeriya. Hannu ta sa ta dauki kudin. "Ba zan ?i Wauka ba saboda ha??inmu ne, amma Insha Allah kudin nan da kike jeho wata rana sai kin nemi daya daga cikin darinsu kin rasa, ?arya fure take ba ta 'ya'ya."
"Yar dariya ta yi sannan ta shige part dinta har da bugo kofar da karfi don ta ji. Jinjina kai Rumaisa ta yi sannan ta juya ta nufi kofar fita. Tafiya ta cigaba da yi tana yi tana zubar da hawayen ba?in ciki, ba za ta fada ma Ummanta cewa ta karbo kudin wajen Badiyya ba, za ta yi shuru tare da fada mata wani ya taimaka mata da su.
Kai tsaye gida ta wuce, samu ta yi Umman na barci, sai Inna Uwale zaune gefe ta zuba tagumi. Ganin ta ya sa ta sauke hannun, "Nawa aka sayi zoben?"
Juyawa ta yi ta kalli Umman, tabbas bacci take yi. Dur?usawa ta yi wajen Inna Uwale, muryarta ?asa-?asa ta ce, "Inna na je gidan Yaya ne, sai dai ?udirina na ganinsa bai yiyu ba... Inna Uwale anya ko za mu sake ganin Yaya Abu?alib? Anya zai sake dawowa cikin rayuwarmu?" Ta ?are zancen hawayenta na ?ara yawa.
"Za mu sake ganin shi, kuma zai dawo gare mu, saboda ?arya fure take ba ta 'ya'ya, ki bar ta ta sha sharafinta, wannan na Wan lokaci ne kamar ?iftawar ido da bismillah za ki ga komai ya warware gaskiya ta Wauki kambunta." Numfashi mai Wumi Rumaisata furzar. KuWin ta fiddo daga cikin abaya ta mi?a ma Inna Uwalen, "Dubu Wari ne Inna, abun ba?in ciki da takaici jifa ta ta yi da su." KaWa kai kawai Inna Uwale kawai ta yi. "Yanzu tunda an samu waWannan 'yan kuWin asibiti za mu koma, a yi mata awon nan da suka ba da."
"To Inna, ni ma shi nake ta so a yi, saboda jikin Ummana ?ara nisa yake yi, kullum jinina kan akaifa yake Inna..."
"Insha Allahu ba abinda zai same ta, ai cuta ba mutuwa ba ce za ta ji sau?i Insha Allah. Kuma zan yi duk yadda zan yi a shiga lamarin nan."
"To Inna Allah ya ba da sa a."
"Ameen." Ta faWa.


&&&&&


KuWin da Yunus ya ba ni kamar yadda ya faWa mini sunanshi suna da dama, a dun?ule naira dubu Wari uku ne domin daurin Kilon Najeriya ne uku a haWe. Na Wauki kwanaki masu tsayi ban fita don bara ba, sai dai kamar yadda nake zuwa barar ina fita ina bayar da sadaka a cikin kuWin da Yunus ya ba ni. Tun daga ranar ban sake saka shi a idona ba, domin bai sake zuwa inda nake ba, duk da na ta'alla?a rashin ganinsa da nake yi a kan rashin zuwana Ipaja bara da safe lokutan da ya fi zuwa yana bayar da taimako. Na fi zuwa da rana bayan na gama 'yan abubuwan da nake, gami kuma da cikin jikina da ya ?ara mini nauyi.
Juyin da abun ?aunata ya yi ya dawo hayyacina, hannu na Wora kan cikina, zancen da muka saba daga zuciya zuwa zuciya muka fara, "Abun ?auna... Yau ba mu gaisa ba ko? Amminka tana gaishe ka, ya ka wayi gari?" Shuru na yi ina sauraren shi, ina ji kamar yana amsa mini. "Yawwah kana lafiya ko abun ?auna. Ni ma ina lafiya, kuma na daina shan wahala sosai, ai ka gani ko abun ?auna."
Na daWe zaune ina hira da halittar da na fi ?auna a cikin duniyata, wacce ba ni da masaniya game da jinsinta, ina dai tsananin ?aunarta sama da son da nake yi wa ruhin da ke manne da gangar jikina. Sai da na yi mai isata sannan na mi?e. Bokiti na Wauka da kwandon wankana, wanda na samu damar siyen su bayan na samu kuWin da Yunus ya ba ni. Ruwan da Ayuba ya tara mani na Wiba na fita domin yin wanka.
Zaune na iske Saratu bakin toilet Win tana ta busar da haya?in taba, Wago jajayen idanuwanta ta yi ta kalle ni, gabana ya faWi rass na ja baya domin ban san me ta shirya ba, domin ina jinta, shi kan shi Ayuba da Mahaifinta fama suke da ita, amma sam ba ta shiga shirgina, ko gaisuwa ba ta haWa mu. Kallona ta yi sama da ?asa, "Wai ke a Alaba kika kwaso wannan cikin kika zo nan ki haife mana shi? Ubansa ya gudu ya bar miki shege, shi ne kika zo nan ki haife ki gudu ki bar mana ko..."
Har tsakiyar raina na ji saukar kalamanta tamkar ta watsa mini ruwan zafi, karo na farko da na ji ba?in cikin rashin yin maganata tabbas da na sauke mata kalamai daidai da wawan zancen da ta yi mini. KaWa mata kai kawai na yi, alamun ba haka ba ne.
TaSe baki ta yi, "To bara ki ji, na farko daga ?arshen watan nan za ki fara biyan kuWin haya domin zaman cin banzar ya isa haka. Na biyu kuma... Ki tabbata ba ki haife mana shege a gidan nan ba, na ga alamu nan da Wan lokaci kin haihu ba wani da nisa ba, so ki koma inda kika baro ki haifi abinki, domin mu nan namu sun ishe mu."
Kallonta nake yi, ba?a ce wuluk kamar an mata fenti da kwalta, gefen kumatunta na hagu an yi mata ?aton hetali 'bille'. Juyawa na yi na kalli gidan, bayan ?azni da warin naman da Ayuba yake siyarwa da yake damunmu wasu lokutan, ga rashin gyara a haka take so na ri?a biyan ta kudin haya, shi ko Ayuba Wan uwanta cikin tausayawa ya ce, "Na zauna iya lokacin da na ga dama, me ya sa ita 'yar uwata mace ba za ta tausayawa matantakata ba? Me ya sa ita ba za ta rufa min asirina ba ko da kuwa cikin jikina shege ne kamar yadda take i?rari?"
"Kin zuba mini idanuwa kaman na mage. Ay kin ji abinda na ce ko? Idan kika ?i yin abinda na ce za ki sha mamakina..." Mi?ewa ta yi ta bar ni tsaye kamar dasasshen icce.
"Wata?il ta ga sauyin da kika samu, domin kwana biyu ay ba ta fita tana nan tana masifa. Shi ne take son sai ta samu a jikinki," Wata zuciyar ta faWa mini. Kada kai kawai na yi, domin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login