Showing 12001 words to 15000 words out of 55242 words

Chapter 5 - BA DON MACE BA BY FATIMA FANTAH.doc

Advertisement

22 Feb 2025

3649

office din Mamanshi, "Mama, kin san yarinyar nan ta karbi kayan kuma na ga ta ji dadi sosai."
"?an Mama, dole dai ka saka yarinyar nan a ranka." Maman ta faWa tana kallon shi.
"Mom, i have certainly yarinyar tana bukatar taimako and i believed ba irin yaran nan ne na Alaba ko Agege ba, duk da, da ka ganta ka san bahaushiya ce amma dai ko Mom..." Ya ?are maganar yana jinjina kai kamar Wan ?aramin yaro.
"Uhmm to ya yi Allah ya yi maka albarka."
"Amin Mamana. Yanzu Mama, so nake na kawo ta hospital a ga lafiyarta da ta babyn." Langabar da kai Mom din ta yi. "Yunus ka sani ko matar nan na da miji, kar ka wuce iyaka fa." Shuru ya yi yana nazarin maganar Maman. "KaWa kai ya yi, ni dai Mom ban ga alamun haka ba. Cause when i asked her about her Baby, i just saw tears pouring from her eyes, so Mom i didn't expect tana da aure. Kawai zan kawo ta nan, na san za ta amince don a duba lafiyarta, kin ga da zaran ta zo sai ki duba ta sosai Mom. Don Allah idan lokacin haihuwarta ya kusa mommy zan dawo da ita gun ki ta haihu, ko ba haka ba?" Kallon shi take yi, "Uhmm Yunus kenan, ga ka babba haka himmm a gabana, amma kuma lissafinka har yanzu na yara ne."
Kwabe fuska ya yi, "Mama, yanzu wannan lissafin yara ne? I swear kika ji yadda nake ji da tsammanin da nake da shi a kanta Mom za ki tausaya mata kuma ki irin abinda nake tunanin yi."
"Shi ke nan to na ji. Idan ta amince kuma na yarda da nutsuwarta ba abinda ba zan iya yi mata ba just for you."
"Yawwa Mamana Thank you, loads of love." Ya ?are maganar tare da ru?o hannunta ya sumbata.
&
Yau kam da na samu cigaba ban dafa komai ba, shayi na hada da ya sha madara da bournvita mai yawa. Hannuna dafe da abun kaunata kuma abokin hira da labarina, ina sha muna hirarmu jefi-jefi na ji sallama cikin gidanmu, tamkar na so in dauki muryar mai sallamar sai dai sam ban damu ba, domin a iya sanina bayan Maman Nana da nake kai mata abinda na samu sai ko Yunus da ya taimaka mini ba ni da wani abokin hulda a Lagos da kaddarata ta kawo ni rayuwa cikinta a lokacin da ban taSa zato ko tsammani ba.
Ji na yi an tunkaro dakina gadan-gadan. Kofar na zuba ma idanuwa domin ganin mai niyyar shigowa dakin, sosai na gane fuskarta. Matar da muka hadu ce wata rana na dawo da???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ga ipaja har ta yi mini kyautar kuWi naira dubu uku. To me ta zo yi wurina? Zuciyata ta jefe ni da tambaya. Fuskarta a washe tamkar gonar auduga ta ce, "Sannu, sannu baiwar Allah." Daga mata kai na yi alamun yawwa. "Na iya shigowa?" Ta tambaye ni.
Sake daga mata kan na yi. ?arasowa ta yi cikin Wakin ta nemi wurin zama tana, "Allah sarki sannu kin ji, wallahi kwana biyu na ga ban ganki ba, shi ne na ce bara na zo na san yanayin jikin naku sai a hankali ne, yau kwari gobe baka." Dan murmushi na yi, na zuba mata ido yadda na ga ta kasa dauke idonta daga kan cikin jikina. Hasbunallahu wa ni imal wakeel na ayyana a raina, sam na kasa yarda da matar da takunta tun farkon haWuwarmu.
"Ya jikin naki da sauki ko?" Daga mata kai na yi alamun eh. "Ohh ka ga daki cike da kayan masarufi, wani bawan Allahn aka samu ya taimaka maki da su ko?" Nan ma daga mata kai na yi.
"Allah sarki, ay duk wani mai imani ya ga yanayin da kike ciki dole ya tausaya miki, Allah ya san zuciyata ni kaina ji nake da a ce ina da kudi ni wata mai tarin dukiya ce sai na miki abinda ya fi haka."
Nagode na yi mata nuni. "Sannu, sannu fa."
"Yawwah," na amsa mata da hannu.
"Na ce, amma dai kina zuwa awo ko?"
"A'ah," na bata amsa.
"Ayyah, ay ya kamata a ce ki je awo diyata, saboda kin san ba a son mai juna biyu ba ta zuwa awo. Kodayake na san ba ki san ko ina ba cikin garin nan."
"Haka ne."
"Allah sarki. Ni ai na kai shekara 30 garin nan ba inda ban sani ba, duk Jama'ar da ke zagayen gurin nan da kin ce Innarsu Kulu, za su gwada miki ni. Kawai abin da za a yi, bari nan da kwana biyu ko uku na shirya na zo na raka ki asibiti, a yi maki awo a san halin da Wan cikinki ke ciki."
"A ah, Allah ke tare da ni, ba sai na yi awo ba." Na faWa.
"A a ke kuwa 'yar nan, kamar ba ki yarda da ni ba. Ay duk Wa na kowa ne, ni jinki nake kamar Wiyata wacce na haifa. Ki bari dai a duba ki kar ki gardama 'yar nan kin ji, ki je ki awo a san lafiyarki a san ta Wan cikinki."
"Shi ke nan to, Allah ya kai mu."
"Yawwa ko ke fa, bara na tafi sai jibin na zo na kai ki kin ji."
"Allah ya kai mu lafiya." Tashi ta yi ta fice har ta fita ina bin bayanta da kallo.
Kashe gari tunda safe kafin ta wuce inda take sana arta ta siyar da abinci kamar yadda ta fada mini sai da ta biyo gidanmu muka kara gaisawa, bayan fitarta ina zaune na gama karyawa na ji karar tsayuwar mota, raina ya raya mini Yunus ne, haka nan na ji dadin zuwanshi. Kamar yadda na yi tsammani, Ayuba ya leko ya shaida mini wani Yunus yana nemana a waje. Mikewa na yi na saka yar yagwalgwal din abayata na fita.
Gaishe shi na yi, ya amsa da lafiya lau tare da jera mini sannun shi da ya saba.
"Amatullah, idan kin amince so nake yi na kai ki asibiti domin a duba lafiyarki da ta Babynki."
Kallon shi na yi, domin wani sanyin daWi da na ji ya dira cikin raina. "Kin amince?" Jinjina kai na yi alamun eh.
"To ki shirya anjima zan zo sai na wuce da ke asibitin."
"Allah ya kaimu." BuWe motar ya yi ya fiddo manyan ledoji ya aje gabana. Nagode da Wawainiya, Allah ya saka da alkhairi. Bai bi ta kan godiyata ba, ya yi min bankwana ya tafi.
Cikin gidan na koma, ina shiga Waki na buWe ledar, ga mamakina sai na wasu haWaWWun abayas da wasu dogayen riguna na leshi da atamfa da riguna masu sau?in nauyi, irin dai wanda za su yi wa mace mai juna biyu daWin sakawa, sai takalma irin marasa tudu Winnan masu shegen kyau, sai turare da sabulun wanka, har da Shower gel ko ba a faWa ba kasan kayan na kuWi ne sosai.
Jigum na yi na zuba tagumi da duka hannayena biyu. "Shin me wannan bawan Allahn ke nufi? Duk da ya yi kama da mutunen kirki amma fa an ce, hali ba shi ga kama. Wannan hidima tare da Wawainiya haka sun yi yawa." Zuciyata ta faWa.
"Kar ki fassara shi da mutumin banza ki yi amfani da zahirinsa da kika gani, wata?il Allah ya kawo shi ne don ya taimake ki."
Hawaye suka ziraro kan kumatuna, haka ?addara ta rubata mini, ya Allah ka sanya kamar yadda nake tsammani Yunus maceci ne ba macuci ba. Amin zuciyata ta amsa.
Cigaba da linke kayan na yi ina ?ara kallonsu. Sallamar da Saratu ta yi ya mai do ni hayyacina da tunane-tunanen da nake ta faman yi a raina. Fuskarta turSune kamar magribar Winya ta ce mini, "Ke, kamar kin mance da warning Win da na yi maki ko a kan zamanki gidan nan. KuWin haya za ki kawo yanzun nan..."
Mi?ewa na yi da ?yar na nufi wurin da na sa?e jikkata. "Dubu hamsin za ki ba da, na wata Waya." Ta faWa lokacin da ta ga na fiddo jikkar. Juyawa na yi na kalle ta, kaWa kai na yi sannan na ?irga adadin kuWin da ta faWa mini na ba ta.
KarSa ta yi ta lissafa, "Yawwah sun cika. Na ga kina mana 'yan kaye-kaye, idan iskancin za ki yi ai kya bari ki haihu amma don jaraba ba za ki hakura ba. Ga shege sai an ?ara loda wani kuma..."
Wani irin zafi maganganunta suke yi mini, ban furta mata komai ba don bana magana, amma tabbas watan wata rana sai na tabbatar mata da Wana ba shege ba ne yana da Uba.
Tafiya ta yi tana cigaba da yin maganganun. Zama na yi na ?arasa linke kayana sannan na fita na yi wanka, na saka Waya daga cikin rigunan da Yunus ya kawo mini. Kasa shafa kowane turaren da ya haWo mini da shi na yi, da ?yar hancina ya aminta da ?amshin sure Win Nivea da Body spray na wani turare Deal. Sallah na yi, bayan na idar na ?ara shan shayi kamar yadda na sha da safe.

&
Wurin ?arfe shida na yamma Yunus ya zo, a shirye na fita tsaf. Wani irin kallo yake yi mini, lallai sutura ita ce mutum baki Waya na canza tamkar ba ni ba. "Masha Allah Ama, sannu."
"Yawwah," yana yawan ce min sannu idan ya zo har ban san adadin da yake faWa mini ba.
BuWe ?ofar motar ya yi ya shiga sannan na zagaya ni ma na shiga bayan na zuba addu'ar neman tsari a raina. Tafiya yake yi a hankali har muka fita babban titi, ni ko na zama tamkar ba?auya duk inda muka wuce ina binsa da kallo ina ganin manyan gine-gine da ban saba ganin irinsu ba a al?aryar da na yi rayuwata ta baya. Kwana muka yi cikin wata natsattsar unguwa, sai na ga kamar na baro ?auye na shigo birni saboda kyawun wurin. Bakin wani ?ayataccen gini muka tsaya mai Wauke da wani rubutu da ke haske cikin duhun magriba da ya fara yi wa gari mamaya na ga an rubuta, YUNUS SPECIAL HOSPITAL. Sake karanta rubutun na yi da kyau, "YUNUS," Juyawa na yi na kalle shi yana ta ?o?arin kashe mota hankali kwance. Yunus Special Hospital, to wannan Yunus Win da nake tare da shi ko wani ne daban na tambayi kaina? Ba ni da amsar tambayata, sai aikin kallon asibitin nake.
Sai da muka tsaya tsaff sannan muka fita, gaba ya yi ina bin bayan shi, har muka isa cikin ainufin asibitin. Masha Allah, tabbas asibitin ta ginu kuma ta haWu, ta yi kyawu ba na iya wajen asibitin ba a cikinta ma haWaWWe ne. Daidai inda za mu hau bene ya tsaya, "Amatullah za ki iya hawa steps Winnan kuwa?" Ya tambaye ni.
Jinjina kai na yi alamun Eh. "Okay to bi a hankali Ama," ya faWa da tsantsar tausayinshi a kaina.
Hawan benen na cigaba da yi da ?yar saboda jikina duk ya cunkushe saboda Wan kumburin da ya yi. A wahalce na ida hayewa, cikin tausayina Yunus ke ta faman yi mini sannu, tamkar ya sa hannu ya haye da ni. Ina hayewa ya ce, "Jira nan ki Wan huta, zauna a nan kin ji Ama." Ya nuna mini kujerun da aka tanada gun don hutawa. Zama na yi, gurin gwanin daWi domin sanyin A.C ya gauraye shi.
"Let me come back." Ya faWa yana tafiya da sauri. Gaba kaWan da inda nake zaune ya tura wata ?ofa ya shiga. Ina zaune a wurin ina sauke numfashi a hankali, suka fito shi da wata dattijuwar mata. Kallo Waya na yi mata na fahimci mahaifiyar Yunus ce, domin kamanninsa sak irin nata ne, sai dai hasken fata da ta fi shi da zubin kyawu irin na mace.
Fuskarta cike da fara'a ta ?araso inda nake, "Sannu, sannu kin ji." Dattijuwar mata ta ce mini.
Yunus ya ce, "Mama she can't talk fa, but she is hearing all what you said."
"Ohh, sorry ka faWa min fa, amma ka ga na manta shaf."
Gaishe ta na yi da bebenci, yanayinta ya nuna mini mace ce mai sau?in kai, da halin kirki kamar Yunus. Da hannunta ta mikar da ni tsaye, taku muka cigaba da yi zuwa Wakin da ta ce za a duba ni.
?akin jinya ne mai matu?ar kyau, toilet Win da ke cikin Wakin ta nuna min tare da ba ni wata 'yar ?aramar roba ta ce na yo fitsari a ciki. Kamar yadda ta ba ni umarni haka na yo, bayan na dawo ta kira wata nurse a waya ta zo ta karSa, a tare suka fita ita da nurse Win, na yi zaune cikin Wakin ina kallon TV da ke aiki ita kaWai. Ina zaune cikin Wakin ina ta sa?e-sa?e da zancen zuci iri-iri ta dawo. "Yawwah Ama, yanzu za ki tashi mu je wani Wakin, a yi miki scanning."
Murmushi na sakar mata, ina jin abun kamar almara, wai a yi mini scanning don ganin lafiyar Abun ?auna. Wani Wakin muka je, muna shiga ta mai da ta rufe. Gado ne a Wakin mai kyau tare da 'yan na'u'rori da wata talabijin da nake tunani ita ce ta scan Win. "Yawwah Amatullah sai a kwanta kan gadon nan don mu yi abun da ya kawo mu." Kwanciya na yi kan gadon, hannu ta sa ta kware rigar cikina sannan ta shafa mini wani abu a kan cikin. Bayan ta gama ta Wora wani abu mai haske kaman na'ura tana yawo da shi kan cikina.
"Masha Allah, Ama kin ga Babynki yana cikin ?oshin lafiya, kin ga yadda yake ta yawo abin sa ko?" Juya kaina na yi na Wora idanuwana kan 'yar TVn da ke gefena. Kamar yadda Umman Yunus ta faWa, haka na ga Abun ?aunata na ta yawo a makwancinshi, wani irin daWin da ban taSa kintacen kwatankwacinsa ba ya ratsa ni, hawaye suka fara biyo kumatuna, hawayen farin ciki da suke malala haWe da bayyananun fararen ha?orana da na kasa rufewa.
Umman Yunus ke ?ara taya ni fara'a da murnushi, ganin yanayin farin ciki da na shiga. Bayan an gama scanning Win na tashi na nemi wuri na zauna. Wata nurse ta shigo ta kawo ma Umman Yunus wasu takardu ta tafi. "Amatullah, a awon da aka yi miki ya nuna cikinki na cikin wata na takwas wato yana da wata bakwai da kwanaki yanzu za ki iya haihuwa nan da sati huWu masu zuwa, kin gani," ta ?are zancen tana nuna mani EDD na haihuwata a jikin takarda.
Numfashi na sauke, na farin ciki da ba?in ciki. Tsuru na yi ina kallon takardar, zan iya haihuwa nan da sati huWu?
"Kar ki damu, Inshallah za ki haihu lafiya." Umman Yunus ta faWa ganin kogin tunanin da na afka. Wasu magunguna kuma wata nurse ta kawo, tana ba ta ta mi?o mini su, "Amatullah, jikinki ya nuna akwai ?arancin jini a tare da ke, saboda haka ki dage da cin kifi, nama, da ganyayyaki musamman alayyahu." Jinjina kai na yi. Wasu shawarwari ta ?ara ba ni, sannan daga ?arshe ta ce, nan da sati Waya Yunus zai dawo da ni a ?ara duba ni.
Waje muka fita, kiciSus muka yi da Yunus, kallon Maman ya yi, "Mom, you keep me waiting, kin shiga kuma kin daWe, ina fata komai dai lafiya ko."
"Lafiya lau Wan Mama. Ba wata matsala a tare da Amatullah, sai Wan ?arancin jini shi ma ba sosai ba."
"Yawwah, to Alhmdlillah."
"Tare za mu wuce ko ?an Mama? Da ma ka tsaida ni dai na biya na duba Amatullah."
Murmushi ya saki yana faWin, "Haka ne Mamana. Thank you."
Tare muka fita suna ta hira gwanin ban sha'awa irin ta Uwa da ?a. Tunanin Ummana ya faWo mini, da yadda muka yi rayuwarmu mai cike da sha?uwa da ?aunar juna, da kuma ?arshen tarihin rayuwarmu da muke ciki yanzu. Ko Yaya Ummana take? Numfashi na sauke, domin tun idaniyata na zubar da hawaye a kan irin wannan tunanin, har ta bushe ta ?e?ashe. Kuma ba zan taSa komawa cikin zuri'ar da muka yi hannun riga da su ba a yanzu, har sai na samu tudun dafawa, ranar da zan koma ri?e da hannun Abun ?aunata, ranar da zan shelantawa duniya halascin Wana tare da hujjojina bayyanannu.
Umman Yunus ta ce, "Bi a hankali ki shiga mota." Motar na shiga wacce na zauna baya, Umman Yunus kuma suka shiga gaba suna cigaba da hirarsu.
Har ?ofar gidanmu suka kai ni, lokacin da muka isa ?arfe takwas na dare ta Wan gota. Bankwana suka yi mini sosai, tamkar ni Win 'yaruwarsu ce, ga alamu dai Umman Yunus tana ?aunar Wan nata sosai.
Shigewa na yi cikin gida, ?ofar Waki na samu Saratu wani kallo take mini, ban kulata ba na yi shigewa ta Waki.
Kashe gari tun da safe zuwan Innarsu Kulu ya tayar da ni daga barci. Yadda ta saba rakaWi da surutu haka ta shigo, "Wallahi kina raina, na ce bara na biyo na ga ya kika tashi."
Tsuru na yi mata, kai matar ta faye alamun mutane marasa gaskiya. "Ya ?arfin jiki ya kika tashi?"
"Lafiya, ina kwana an tashi lafiya?"
"Lafiya lau."
"Cewa na yi, kawai ki shirya mu je awon."
Mi?ewa na yi na Wauko takardun awon da aka yi mini asibitin su Yunus, karantawa take tana yi har da tishi, gana Waya sai na ga launin fuskarta ya canza.
Sakin fuska ta yi, "Tooo, ai ko na gani. Kenan bawan Allahn nan da yake taimaka maki ya kai ki Yunus Hospital? Lallai kam. Ai asibiti ce mai kyau da tsada a garin nan, sun san aikinsu sosai. Shi ke nan, ai kin ga sun hutar da ni, illah iyaka na ri?a le?owa ina duba ki, tun da na ga haihuwar ta kusa, na shigo na karSi ?an Baba ko 'Yar Baba. Allah dai ya raba lafiya."
"Amin." Kawai na yi mata nuni a ta?aice. Surutu take ta yi kala-kala, daga ?arshe ta tashi ta tafi. TaSe baki na yi, koma dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login