Showing 39001 words to 42000 words out of 55242 words

Chapter 14 - BA DON MACE BA BY FATIMA FANTAH.doc

Advertisement

22 Feb 2025

3658

kira na da, "Rai," ko "Raina," ni kuma ina kiran ta da, "Aminci, ko "Amintacciyata." Sosai muka sha?u, muka ?ulla ?awance na gaske, duk wanda yake cikin ajinmu ya san ni Ran Badiyyah ce, ita kuma Amintacciyata ce. Badiyyah ta shiga jikina sosai, ko kaWan ba ta bari wata ?awar ta raSe ni, sauran ma da muke Wan ?awancen da su, abokan zamana Humaira da A'ishatu sun saka mana idanu, suna jinjina ?awancen da muke yi, amma kuma... Wani irin takaici ya taso mini wanda ya hana ni ?arasa maganar.
Yunus ya kalli fuskata da zallan Sacin rai ya bayyana a kanta, "Amma kuma me Ama? Wai Lilbirrah a yanzu. Amma kuma me? Me ya haWa ku?" Nisawa na yi, na mi?e na Wauko ruwa kan table na sha don rage zafin raWaWin da ya taso min, sai da na sha ruwan sannan na cigaba da magana. Ba abinda ya haWa mu a lokacin sai dai..

SH 16


Mun cigaba da ?awance ni da Badiyyah, sha?uwar da muka yi ya sa na fuskanci akwai matsalolin da ke damun rayuwarta, wasu lokutan ba ta zuwa da kuWin break, wasu lokutan kuma sai ta yi shuru duk da dama ba ma'abociyar yawan magana ba ce, tana da shuru-shuru she is so calm and innocent. Kamar yadda takan yi, zaune take ta yi jugum kallo daya za ka yi mata ka gane tana cikin damuwa. Zama na yi kusa da ita, amma ba ta ma san na zauna ba, ganin haka ya sa na sa hannu na Wan doke ta ina faWin,  Aminci, zabura ta yi. "Na am Rai.
 Aminci me ya same ki? Me ke damunki ne haka plsss.?" Na ?are maganar cikin bayyana kulawata gare ta. Hawaye suka ziraro mata, "Rai& Raina& ina cikin damuwa ina shan wahala sosai a rayuwar nan."
"Wace irin wahala Aminci?
"Rai& Ban taSa faWa maki ba, gidanmu, gidan da Mamana ke aure sam ba na jin daWin rayuwa cikinsa, wahalar da ni suke yi sosai, na soma gundura ji nake da ma ban kasance cikinsu ba."
"To Amintacciyata, ba nan ne gidanku ba?" Kada min kai ta yi, "A a ba gidanmu ba ne, ni Babana ya rasu shekara Waya kenan, to bayan Mamana ta gama takaba shi ne wannan ya aure ta abokinsa ne. Mu ba ma a garin nan muke ba, muna zaune a garin Shargalle ne, cikin ?aramar hukumar Dutsi, auren Mamana ne kawai ya kawo mu nan da zama, amma danginmu da dukkan 'yanuwanmu da kowa duka suna can. Da Mamana ta yi aure shi ne ta taho da ni nan, amma zaman gidan ba daWi Rai, kullum sai na yi kuka ina ma Babana yana nan..." Ji na yi zuciyata ta karaya, cikin tausayawa na ce, "Eyyah! Allah sarki, Allah ya jikansa da rahama."
"Ameen," ta fada cikin juyayi da kewar babanta.
"To nan din ba sa son ki ne? Ko wani abun suke maki?" Murmushin ya?e da ya fi kuka ciwo ta yi, "Raina, inda Mama ta yi auren nan matansa uku ita ce ta hudu, duka cikin gida guda muke ga tarin  ya ya manya da ?anana, amma duk yawan "ya'yan nan duk safiya sai ni na yi shara na yi wanke-wankensu, kar ki ga tarin kwanoni Lilbirrah, tamkar na gidan biki. Sannan kuma abinci ma ba kullum muke samu ba, idan kuma ya samo kadan sai dai ya ba 'ya'yansa kadai amma ni, ni Waya ?wallin ?wal na za su ba ni filet guda na ci ba Lilbirrah sau tari sai dai na kwana da yunwa, haka zan tashi da ita ranar da ya gama ya ba ni kuWin break idan bai ga dama ba haka zan taho da yunwa Lilbirrah kuma ba kuWin siyen abinci. Yanzu haka yau kwanan mu biyu ba mu saka wani abu a cikinmu ba ni da Mama, ga shi ba sana a muke ba kamar mu yi haka Raina..." Ta ?are maganar tana matsanancin kuka.
"Wayyo Allah na! Badiyyah to me ya sa ba ki taba fada min ba, me ya sa ba ki gaya min ba sai yau?" Na faWa ina shirin kuka. Shuru ta yi hawaye na cigaba da sintiri daga idanuwanta. Jakata na jawo daga cikin locker din benci na fiddo kudi na ce, "Ki tashi mu je mu yi break, kin san kina cikin wannan halin amma ba ki taba fada min ba, to me ye amfanin taren mu?" Ba ta ce min komai ba muka fita wurin break. Sai da na siyo mana abinda na san zai ishe mu ni da ita sannan na muka koma class. Tun daga lokacin muka ci gaba da yin break tare da Badiyyah, wani lokaci idan zan tafi makaranta sai na tsare Yaya Abu?alib ya linka min kuWin break Wina saboda mu yi ni da ita, idan ya yi min kyauta ko ya ba ni wasu kuWi sai na raba su biyu na bawa Badiyyah rabi na yi amfani da rabi, da Umma da Abu?alib kunnuwansu sun cika da labarin Aminci wato Badiyyatah. Kwanci tashi rana na faWuwa dare na maye gurbinta da duhu, yanayi na canzawa daga rani zuwa damina daga damina zuwa sanyi aka wayi gari mun kammala makarantar Sakandare. Ranar da muka gama jarabawarmu ta ?arshe da ?yar muka rabu ni da Badiyyah, tana kuka ina kuka mun ?an?ame juna tamkar a ce wuri Waya za mu tafi. Sai dai muka rabu da al?awurran za mu ri?a ziyartar juna, za mu ri?a sada zumunci ta waya a kowane lokaci.
Ta janibin Yaya AbuDalib kuwa a cikin wannan lokacin ya samu cigaba a sana ar dinkinsa ?warai da gaske duk fadin garinmu an san shagon dinkin Yayanmu wanda ya sa mashi sunana, "LILBIRRAH FASHION DESIGN." Gata da kulawa da nake samu daga gare shi sai abinda ya yi gaba, duk wani jin dadi Yaya na yi mashi. Sati biyu ciff da gama jarabawarmu kenan, na shiga Wakin Umma na tarar da Yaya Abu?alib suna magana, ganin alamun maganar mai muhimmanci ce ya sa na ja gefe na zauna. "Shalele barka da shigowa."
"Yayana na kaina," kun gama magana da Umma?" Na ?are zancen tare da mi?ewa na dawo kusa da shi.
"Shalele," ya fada yana kallona. "Na'am Yayan Shalele," na faWa ina kallonshi. Wasu cards masu tsananin kyau ya mi?o mani, "Yaya wannan cards Win fa masu kyau haka kamar za a saka a wuya?"
"BuWa mana ki gani."
"To Yayana," na faWa ina zaro katin daga cikin ?ayataccen kwalin da aka adana shi.
"Please join us to the graduation and birthday party. To celebrate Lilbirrah Abdulhadi..."
"Yaya!" Na faWa murna na neman sumar da ni.
"Yaya Party za ka yi mun?"
"Ke washa, rufe bakin kar ?uda ya shiga." Sauri na yi na rufe bakina.
"Umma kin gani, katin nawa ne, na Party gama makaranta har da Birthday."
Umma ta ce, "Ni ma yanzu ake gwada min, yadda aka ba ki mamaki ni ma shi aka ba ni."
Wani irin daWi nake ji kamar na yi ta tsalle, kasa jurewa na yi na mi?e na ri?e hannuwan Rumaisa muna taka rawa. Yaya Abu?alib da ke mana dariya ya ce, "Shi ya sa ai na gwada maki da ranar partyn kawai zan zo na ce ki shirya mu tafi. Halinki na sani ya sa kar ki je ki suma."
"Aiko ba wuya," Umma ta faWa tana dariya.
"Na ji Yaya ba komai, yanzu ma ji nake kamar na suma Win don daWi cikin raina, dubi fa inda za a yi Partyn, wallahi ranar duniya za ta shaida Yayana yana so na."
"Ehh, wannan kam a faWa da kiWi a ?ara da busa." Yaya ya faWa.
"Yawwah Yaya, wannan ?awayena zan gayyato."
"Ehh amma na mutum biyar kacal zan ba ki, saboda so nake a yi partyn nan a nutse, duka friends and family mutum hamsin ne."
"Ba komai Yaya, da ma ?awayena ba su da yawa, daga Aminci sai Humaira sai A'ishatu."
Hararar wasa ya yi mun, "Ni wannan sunan haushi yake ba ni, wai ita amincin ba ta suna ne?"
"A'a Yaya sunanta Badiyyah."
"To ki ri?a kiranta da Badiyyarta kawai, ba ki da wani amintacce idan ba ni ba, sai kuma Rumaisa idan ta girma."
"To Yaya daga yau na daina, duk abinda kake so dole haka za a yi."
"Yawwa 'yar albarka Shalelena."
"To Yaya yanzu sai na kama shiri kawai nan da kwana uku ne fa."
"Eh mana, me kike jira. Ki je a yi maki wankin kai, har dilki a yi maki, sai a yi maki wankin ?afa da lalle. Na san inda zan kai ki duka a yi maki."
"Kai Yaya, har da dilka kaman wata amarya." Na ?are maganar cikin sigar zolaya.
Murmushi ya yi, "Shalele, ai ni a wurina kin fi amaryar ma, don ina ga a bikina sai kin fi amaryata kyau, don zan iya kashe maki kuWi ko nawa ne ba tare da na ji komai ba fiye da amaryata ma."
Umma ta ce, "Uhmmm. Da yake dai ko budurwa ba ka da ita, balle a je ga batun amarya. Don haka ba zan ce komai ba, amma amarya ai daban ce." Dariya muka yi mu duka.
"To Yaya ka kai ni gidansu ?awayena na gayyato su, sai ka kai ni gidansu Aminci na kai mata gayya ta musamman."
Tsaki ya ja,  Ni Shalele kin dame ni da batun wannan kawar taki ni sunan da kike kiranta da shi ke kona min rai na ce ki ri?a kiranta da sunanta."
"Kash, Yaya wallahi na mance." Na faWa ina daWe bakina.
"To kar ki ?ara mancewa Shalele."
"To Yaya."
"Gobe da safe ki shirya na kai ki duka gidajen, ba zuwa za ki ki zauna ba. Kin san ban san wannan 'yan zaune-zaunen na gidan ?awaye, ki shiga ki fito."
"To Yayana."
Umma ta ce, "Allah ya yi muku albarka ya ?ara muku haWin kai "
"Amin Umma." Yaya ya faWa. Bankwana ya yi mana ya mi?e ya fita. A ranar daWi da ?yar ya sarara mani na yi barci. Kashegari da sassafe na shirya, Yaya yana zuwa gida ya shirya ya Wauke ni muka tafi. Gidansu Humaira muka fara zuwa, sai muka wuce gidansu A'ishatu, sannan muka wuce gidansu Badiyyah.
Ban taSa zuwa gidansu ba, wannan shi ne karo na farko da na ziyarce ta. Sallama na yi cikin zaure, tun daga bakin ?ofa na tantance gidan na iyalai ne da yawa, domin kuwa sai ka Wauka ya?in basasa aka yi a cikinsa, gidan rikice yake kowa na hidimar gabanshi. Sake sallama na yi cikin tsakar gidan ina rarraba idanuwa, saboda ban ga Badiyyah ba.
Wata daga cikin 'yanmatan gidan ta ce, "Wurin wa kika zo?"
"Badiyyah," na faWa a Warare.
"Okay, wuce ga Wakinsu can." Ta faWa tana nuna mini Wakin da ke ?arshen gidan. Tafiya na yi inda ta nuna mani, ina shiga cikin Wakin Badiyyah ta rugonda gudu ta rungume ni. Sai da ta gama murnar ganina ta sake ni, "Rai... Raina." Dariya kawai nake, na kasa furta komai.
Zaunar da ni ta yi kan kujera, "Rai sannunki da zuwa, kin cika al?awari tun kafin ni na cika."
"Aiko dai Badiyyah."
Mamansu ta fito daga Waki, "Ahhh, yau mun yi babbar ba?uwa, ina ta jin labarin Lilbirrah yau dai ga shi na saka ta a idanuwana, yarinyar kirki."
Saukowa na yi daga kan kujerar cikin ladabi da girmamawa na ce, "Mama ina wuni."
"Lafiya lau, ya Mamanku?"
"Lafiya lau suke."
"To madallah. Sannu, Badiyyah a kawo mata ruwa."
Badiyyah ta ce, "Mama ba ruwa fa."
"To, je ki ki sawo mata."
Laluba jakarta take ga alamu dai ba komai ciki. Cikin basarwa na ce, "Umma ni na gode ba sai an sawo min ba, yanzun nan zan tafi. Yayana yana waje yana jira na, kuma ya ce kar in daWe."
Badiyyah ta yi karaf ta ce, "Kai jama'a rai, da ma ba yini za ki min ba."
Murmushi na sakar mata na ce, "Kai! Ay Yaya bai bari, sam ba ya yarda."
"Shi wannan Yayan wallahi," ta ?are maganar kamar mai shirin kuka.
Katin gayyata na fiddo mata daga cikin jakata, "Ga shi Badiyyah. Jibi idan Allah ya kai mu, ina bikin ?arin shekara da murnar gama makaranta."
Zaro idanuwa ta yi tana kallon katin, "Don Allah da gaske Rai. Kai! Gaskiya ina murna, Allah ya kai mu lafiya."
"Amin ya Allah, bara na tashi na tafi kar Yaya ya fara gajiya."
"To Lilbirrah Allah ya kiyaye."
"Amin," na faWa ina mi?ewa tsaye. Tare muka fito da Badiyyah har bakin zaure. ?an tsayawa muka yi kafin mu ?arasa fita waje, "Badiyyah ya lamurran gidan nan ina fata an Wan samu sauyi."
"Uhmmm, Lilbirrah har abada abubuwan gidan nan ba za su sauya ba, yadda suke haka za su cigaba da wanzuwa. Ban sani ba ko ni nan gaba ranar da na yi aure, ko ba bar gidan a gare ni su sauya. Yanzu haka yau Win nan, haka na sha shara da wannan tulin wanke-wanken nan, kuma wallahi Lilbirrah ko yau tun safiya har yanzu ruwa ban sha ba, kin gani sai dai su karya da 'ya'yansu mu kuma ni da Umma ko oho."
"Kai! Badiyyah ina tausaya maki sosai a kan wannan rayuwar, cire wahalar aikin nan, yunwa sam ba ta daWi, shi ya sa gashi nan duk kin rame."
Tuni hawaye sun ciko idanuwanta, "Ki bari kawai Rai."
"Ki yi ha?uri kin ji, wata rana sai labari," na faWa ina share mata hawaye.
KuWi na fiddo daga jakata dubu biyar na ba ta, "Ga shi Badiyyah ku ci wani abu, sauran jibi idan za ki taho ki hau abun hawa."
"Kai Lilbirrah, wannan kuWin har haka."
"Ba komai Badiyyah, sam kar ki damu don na maki wani abu. Ke fa aminiyata ce wallahi da ina da dama, sai fitar da ke daga wannan halin."
"Nagode ?awata," ta ?are zancen tana rungume ni. Bankwana muka yi saboda kukan da take yi, na ce ta tsaya a nan ba sai mun fita waje ba.
Ina zuwa na tarar Yaya Abu?alib har ya koma cikin inuwa saboda na jima a cikin gidan. "Shalele kin daWe sosai." Ya faWa yana tasowa daga wurin da yake zaune.
"Yayana nan gidansu Badiyyatah ne, shi ya sa na daWe." Guntun tsaki ya je ya ce, "Haye mu tafi."
"Toh," na faWa na haye kan mashin.
Tun da muka tafi kan mashin labarin Badiyyah nake ba wa Yaya, ina faWa mashi irin halin da take ciki na wahalar rayuwa da Allah ya jarabce ta. Daga eh sai a'a kawai yake ce min. Da na lura sam ba ya muradin labarin sai na muka shiga wani zancen.
Kashe gari Yaya da kansa ya kai ni wani shago da ake gyaran jiki haWe da lalle da har da kwalliya. Tsakanin gyaran jiki da lalle da kwalliya da za a yi min dubu tis'in da biyu Yaya ya biya. Kamar na yi kuka na ce, "Yaya kuWin sun yi yawa."
"In ji waye, a shagonki fa aka samu, shi ne za ki ce sun yi yawa." Ya faWa sam babu abinda ya dame shi. Tafiya ya yi shago, sai da ya kintaci lokacin da suka bayar za a gama ma ni ya zo ya Wauke ni muka koma gida.
Kashe garin ranar za a gabatar da shagalin ?arin shekarata da gama makarantana. Tun da safe Yaya ke kai kawo tsakanin event hall da ya kama zuwa gidanmu, da misalin ?arfe biyu bayan na gama salloli muka tafi wurin kwalliya. Tabbas ni kaina na godewa Ubangiji kuma na yabe sa lokacin da na ga kaina cikin madubi. Duk da ni ba?a ce wuluk, amma kallo Waya za ka yi min ka ga tsuran kyawun da Allah ya yi min. Yaya yana ganina, ba abinda yake kira sai Masha Allah. Haka muka tafi ni da shi tamkar amarya da ango saboda ankon kaya da muka yi.
Muna isa hall Win taron, ma fi yawancin jama'ar da muka gayyata sun zo amma Badiyyah ba ta kai ga ?arasowa. A nan aka fara abinda ya tara mu a wurin, Party muke yi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ba hayaniya ko kaWan. MC da aka gayyato ya ce, "Shin a labari kun taSa jin inda Yaya ke ji da ?anwarsa kamar wannan? A saboda haka wannan Yaya ya bu?aci mu saka mashi wata wa?ar India ta Yaya da ?anwa don ya sake jaddada ma ?anwarsa irin ?aunar da yake yi mata." Murmushi kawai nake yi, shi ko Yaya faWar farin cikin da yake ciki Sata lokaci ne.
Mi?ewa ya yi ya fara bin wa?ar da aka kunna mashi mai taken Pholo ka taaroka... Wa?a ce mai nutsuwa da kwanciyar hankali, saboda son da Yaya yake ma wa?ar tuni na hardace ta na san abinda ake faWa cikinta. Bin wa?ar yake yana taku cikin nutsuwa yayin da ni kuma nake tsaye ina Wan juyawa sashe-sashen da ya juya shi ma. Muna cikin bin wa?ar na hango Badiyyah ta zo, hannu na Waga mata kafin mu gama abinda muke yi.
Sai da aka gama tsaf wasu na taSi wasu na ihu, bayan mun koma mazauninmu MC ya ?ara kiran Yaya domin taya ni murna. Mice Yaya ya karSa ya fara magana, "Godiya ta tabbata ga Allah mai kowa da komai da ya nuna mana wannan lokaci, lokacin da 'yaruwata ta cika shekaru goma sha takwas a duniya kuma ta kammala karatunta na Secondry, ina taya ta murna kuma ina farin ciki sosai, farin ciki marar misali ko kwatance. Lilbirrah, kowa ya sani ita Win ?anwata ce, jinina, a cikin jinin nawa Allah ya fifita sonta a cikin zuciyata fiye da sauran 'yanuwana, ina sonta ina ?aunarta Allah ne shaida ta, ina farin ciki da farin cikinta ina ba?in ciki da ba?in cikinta, idan kana son ka ga fara'ata ka kyautata ma Lilbirrah, kuma zan iya Satawa da ko waye a kan Shalele.
"Yaruwata da yarena na Hausa, Ukhteey da yaren Larabci, Sister da yaren turanci, Didi da yaren Indiyanci, Khouhar da yaren Farisanci. Na zaSi na kira ta Khouhar don ba kowa ya sani ba, don ya zamana sunan da ni kaWai ne ke kiranta da shi. Khouhar ke wane suna za ki ba ni?"
"Joonam," na faWa daga inda nake zaune.
"Ina godiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login