Showing 42001 words to 45000 words out of 55242 words

Chapter 15 - BA DON MACE BA BY FATIMA FANTAH.doc

Advertisement

22 Feb 2025

3659

Shalele, Joonam shi ma farisanci ne yana nufin masoyi, ko na cancanci wannan sunan?" Tsirarun mutanen da ke wurin suka amsa da, "Ka cancanta Abu?alib."
"To Nagode," ya faWa sannan ya cigaba da magana.
"A kullum addu'a nake yi, Allah ya ba wa Khouhar miji nagari da zai kula min da ita wanda ba zai cutar da ita ba. A kullum addu'a nake yi Allah ya raya mana ita, ta rayu ta yi shekaru irin na dabino." Dariya mutanen wurin suka kwashe da ita.
"A kullum addu'a nake Allah ya ba ni ikon cigaba da kulawa da ita, fatana ko aure na yi ita ma matata ta ?aunaci Khouhar Wina..."
Hawaye suka zubo mani da wani kuka mai ciwo sa ya turni?e ?irjina, duk yadda na so jurewa na kasa hakan ya sa na fashe da kuka sosai. Yunus ya nisa ya ce, "Lilbirrah, ina jin irin abinda kike ji, tabbas dole ?arshen labarin nan ya yi ciwo, ya aka yi kika rabu da Ummanki da wannan yayan naki da ke ?aunarki, wanda na daWe ban ji wani Wan uwa da ke son 'yaruwarsa haka ba."
Ban iya cewa komai ba sai aikin kukan da nake yi. Maman Yunus ta ce, "Ni na rasa abun cewa ma, shin Lilbirrah shi wannan yayan naki shi ne Baban Nadeer, ko kuma saboda yayan naki kika saka ma Nadeer sunansa? I feel your pain Lilbirrah, ni ma ji nake kaman na yi kuka." Duka tambayoyin da suke mini ban samu fursar ba su amsa ba, sai da na sarara sosai, sannan na buWe baki na cigaba da magana.
"A cikin labarina duka akwai amsar tambayoyin ku, ku yi ha?uri wani zafi ne ya taso min, amma yanzu zan cigaba da labarin."


SH 17

Cikin yanayin da ke nuna zuciya ta motsa Yaya Abu?alib ya ci gaba da magana, "Khouhar Wina ita Waya ce a cikin dubu, mutane da aljanu sun shaida, da tsuntsaye da tsirrai suna faWa a cikin sautukansu, 'yaruwata Lilbirrah Waya ce a cikin dubu."
Juyowa ya yi ya kalle ni, "Duniya ba ta sanin dalilin fushinta, murna ko kuma damuwarta, amma ni a kallo Waya da na yi a cikin idanuwanta nake gane ha?i?anin yanayinta. Farin ciki ko akasin shi, walwala ko damuwarta, burina a kowane hali, na linka farin cikin zuciyarta, idan kuma tana ba?in ciki zan yi dukkan iyawata na kawar da shi daga cikin ranta. Khouhar... A kowane hali ki zo gare ni ki faWa mani matsalolinki na yi al?awari da ?arfin jikina da nauyin aljihuna zan yi maki maganinsu da taimakon Allahn da ya halicce mu ya yo mu daga itaciya Waya..."
TaSi aka hau yi, yayin da hawaye suka fara sintiri daga idanuwana, cikin kulawa ta musamman Yaya Abu?alib ya ce, "Khouhar ki daina kuka ba zan iya yafe ma kaina ba, matsawar na zama silar zubar hawayenki."
Hannuwa na sa ina share hawayen sai dai na kasa tsayar da su, "Ba za ki daina ba, to bara in cigaba da marin kaina na san za ki daina." Hannu ya sa ya Wan mari kansa, "Abu?alib baka jin magana ko ka sa ka Shalele kuka..." Dariya ta kama ni sosai, "Yawwa ko ke fa, sam kuka ba ya maki kyau Khouhar." Ya ?are zancen yana murmushi.
Mayar da abun magana ya yi wajen MC, ya dawo gefena ya zauna, du?awa na yi wajen shi, "Joonam Allah ya taimake ni ba ka da budurwa, da yau ta ta zuba mini mari kan wannan abun da ka yi."
"Khouhar idan matata tana so mu zauna lafiya, kawai ta ?aunace ki, idan ta so ki to ni ta biya ni," ya ?are zancen yana murmushi.
"Joonam ina ?aunarka, ina godiya ga Allah da ya ba ni Wanuwa mai ji da ni mai ?aunata irin ka." Bai ce komai ba sai wani kallo da shi kaWai ya san fassarar shi.
MC ya ce, "Mun gama sauraren waWannan daWaWan kalamai masu kama da baitukan wa?a da Yaya ya shiryawa ?anwarsa, saboda haka muna kira ga duk wanda ya kawo ma Lilbirrah kyautar Birthday ya kawo mata, za a yi hotuna daga nan za a nannaWe tabarmar wannan taro sai Allah ya kai mu wani lokaci."
Kasantuwar duk wanda aka gayyato 'yanuwa da dangina ne haka suka ri?a kawo min kyautuka Waya bayan Waya, Badiyyah ta zo inda muke, cikin girmamawa ta gaishe da Yaya, ba yabo ba fallasa ya amsa mata. Muryarta ?asa ta ce, "Ni dai ban zo maki da komai ba Raina," Yaya Abu?alib ya juyo ya mata wata harara da ni kaWai na gan shi, "Ina maki fatan alkhairi, da addu'ar tsawon rayuwa raina."
"Nagode sosai Bady, Allah ya saka da alkhairi."
"Ameen," ta faWa sannan ta koma mazauninta. Sai da kowa ya gama bayar da kyautukanshi sannan MC ya ce, "To kowa ya kimtsa, za mu ga wace iriyar kyauta ce Yayan nan mai ji da ?anwarsa ya tanada mata, Babban Yaya muna jira mu gani daga gare ka." Mi?ewa Yaya Abu?alib ya yi, sannan ya yi wa babban abokinsa Abduljalal inkiya da ya mi?o masa ajiyar da ya ba shi.
Tashi ya yi ya fita bai jima ba ya zo da wata leda, ni kam na zuba idanuwana don ban san me Yaya ya tanada min ba a matsayin kyautar ?arin shekarata, ledar Yaya ya buWe, "Da farko dai na siya ma Shalele waya, domin ta jima tana son waya amma da na ce sai ta gama makaranta ko gardama ba ta yi mun ba, saboda haka Shalele ga wayarki."
TaSi na hau yi ina murna kamar yadda na ga saura na yi, "Sai kuma wannan turare ne domin na san Khouhar akwai tsabta ga son ?amshi, saboda haka na yi mata kyautar turare, wannan kuma kuWi ne dubu Wari ta je ta sha choculates duk da na san ita Win ba ma'abociyar shan su ba ce."
DaWi ne ya jagoranci ?afafuwana zuwa wurin Yaya, "Joonam nagode, nagode sosai Allah ya saka da alkhairi."
"Ameen Khouhar Wina." Ji na yi tamkar ba wanda ya yi min wata kyauta sai Yaya Abu?alib sosai ya faranta min rai, bayan na gama murna aka hau yin hotuna bayan an gama sannan aka sallami kowa. Haka muka koma gida zuciyata fess tamkar an biya mani hajji, wanda a raina ko shakku bana yi duk ranar da Yayana ya zama hamsha?in mai kuWi ina cikin wanda zai fara biya ma Hajji. Komai na kwashe na faWawa Ummana, ita ko koWan ba ta damu ba sai murna da farin ciki da take yi. KuWin na ba ta ta yi duk abinda za ta yi da su, ni Yayana ya sallame ni da waya da turaren da ya siya min.
Lambobin 'yan ajinmu da muka gama makaranta wanda na kwafa a littafi na cigaba da juyar su a waya, cikin Wan lokaci muka cigaba da zumunci da juna ciki ko har da aminiyata Badiyyah.
Tunda na mallaki waya, kusan kullum Badiyyah tana kan faWa mini halin da suke ciki a gidansu, ni kan taimaka musu da abinda nake da shi wani lokacin har abinci sai in aika mata da shi, sosai nake jin tausayinsu da tunanin ta wace hanya zan sama musu mafita. Tun da ta gane gidanmu kuma tana yawan zuwa, amma ba su taba hadewa da Yaya AbuDalib ba, saboda idan ya fita da safe sai dare yake dawowa daga shagonsa.
Ina zaune ina aikin da na saba na latse-latsen waya Yaya AbuDalib ya shigo, "Khouhar," ya fada yana zama kan kujerar da ke kallona. "Joonam," na amsa cikin yanayin damuwa.
"Me ya faru ne Khouhar?" Ya tambaye ni cikin kulawa.
"Yaya wallahi ko, kawar nan tawa ce Badiyyah, Allah Yaya tana cikin wani hali wallahi kuwa, tana shan wahala sosai a gidansu ga yunwa, ga wuya tana shan gun kishiyoyin mamanta, Yaya tausayinta nake ji sosai."
Kada kai ya yi, "To Allah ya ba ta mafita." Tashi na yi tsagwayam daga inda yake na koma kusa da shi, ?asa- ?asa na ce, "Joonam, wani tunani ne na yi, ka gani da ma Umma tana so ka yi aure ba, Baba ma yana maganar ya ce har ka kusa zama tuzuru, amma kullum sai ka ce ba ka ma da lokacin neman budurwa."
"Uhmmm, ina jin ki," ya fada yana ba ni dukkan hankalinsa.
"To Yaya na zaSa maka budurwa, kawai ka auri kawata Badiyyah, yarinyar kirki ce ga ta kyakkyawa, sannan tana da ilimin addini da na boko, kuma tana da kokari a school ka ga 'ya'yan da za ta haifa mana za su yi kokari. Sannan Yaya ba ruwanta shuru-shuru ma gare ta, tana da tarbiyya sosai& "
Tun da na fara maganar bai ce komai ba har na kai karshe. "Khouhar, kin sani duk abinda kika fada min zan yarda da shi, kuma idan har ke da kanki kin yaba da hankali da nutsuwar kawar taki ni ma zan iya amincewa, saboda tunaninmu daya da ni da ke, kuma na san in har kin amince tabbas kin ga inganci."
"Yaya wallahi ni na yaba da ita dari bisa dari."
"Shi ke nan to, amma fa ni ko kare mata gani ban yi ba."
"Ahhh, Yaya ba ka lura ba ne ranan Birthday dina, bara ka ganta," na kare zancen ina kokarin nuna masa hotunan mu na taron birthday da ke a wayata. Kallonta yake yi a nutse, yanayin yadda yake kallonta na tabbatar da da shi ma ya yaba. "Shi ke nan, yanzu sai ki kokari ki gabatar mata da ni, ki ce za mu ri?a gaisawa daga nan zan jarabata in gani idan ta dace da tsarina."
"Da gaske Yaya, kai amma na ji dadi sasai." Murna na yi ta tamkar ni ce aka ce za a aura, sosai na ji dadin yadda Yaya ya amince da ita farat daya. Kasantuwar Umma ba ta nan yana fita na daga waya na kira Badiyyah, daga tsaginta ta amsa min da lafiya lau Rai. "Kina ji ko Bady kin san wani abu, Yaya ne ya ce tun ranar da ya gan ki nutsuwarki da kamun kanki ya birge shi sosai. Shi ne na ce masa ai ke ce Amincina da nake ba shi labari, shi ne ya ce na ba shi lambar wayarki za ku rika gaisawa."
Murmushin da ke bayyana jin daWinta ta yi sannan ta ce, "Ba damuwa Rai, Yayanki ai Yayana ne, Insha Allah ba damuwa zan amsa masoyiya."
"To shi ke nan Badiyyatah." Godiya na yi mata sannan na kashe waya.
Yaya suna fara mu'amala da Badiyyah ya shigar da zancen soyayyarsa gare ta, ita ma ba ta ja ba ta amince, domin Yayana yana da halayen ?warai, mutumin kirki ne, kuma kyakkyawa ne, sannan dogo ne cikakken dogo, yana da hasken fata amma ba fari ne irin tass-tass din nan ba, mutum ne mai gargasa domin gashin Nadeer da kuke ta yabawa ya same shi ne a gun Babansa Abu?alib, haka yake yana da kwantacciyar suma, saboda shi ma babansa Malam Saleh cikakken bafulatani ne karatun allo ne ya shigo da shi birnin Katsina har Allah ya kaddara masa rayuwa a nan. Yayana yana da gira baka sidik, saboda duhunta da yawan gashin da ke kwance cikinta sai ka dauka jagira aka yi mashi haka ma girar idanuwansa mai duhu ce sannan dan-dandandan take, hakan ya sa idan ka kalle shi sai ka dauka kwalli ne ya shafa a idanuwansa yana da hanci dogo da madaidaicin baki, shi ya sa mata ma ?aunarsa suke yi suna bin sa, amma bai taba son wata daga cikinsu ba har sai lokacin da na ?ulla alakar soyaya tsakaninsa da Badiyyah. Ta Sangaren Ummana, ita ma ta yaba da hankalin Badiyyah hakan ya sa ta amince da zancen soyayyar wadda ta mike shantal zuwa ga aure. Tunda Yaya AbuDalib suka fara soyayya da Badiyya ta rabu da fama da irin matsalolin da suka addabi rayuwarta, saboda yadda yake hidima gare ta da yi mata dawainiya, abinci ma haka yake siyen buhun shinkafa da mai da taliya yana kai wa gidansu duk karshen wata, Yaya bai zama mai kudi ba, amma yana da zuciyar yi tsayayyen namiji ne na gaske. A janibin sana'arsa, shagonsa yana daWa yin gaba wanda ya zama katafaren shagon da ake dinki, kaya har da zo da wanka, na kowane irin kaya mai sau?i ko mai tsada.
Irin hidimar da Yaya ya ke yi ma Badiyyah ya sa Babansu ma kanshi ya daina yi musu irin wulakancin da yake musu, ya koma mutunta su da ba su filin wuri.
Shekara daya ciff suna soyayya wanda Yaya ginin gidansa da ya fara ya yi nisa sosai, yayin da mu kuma muke ta shirye-shiryen biki. Ta janibi na kuma bayan fitowar sakamakon jarabawarmu Yaya ya nema mini 'Yaradua University inda nake karantar Computer science domin shi ne burina tun tasowa ta.
Wata rana ina zaune kan cinyar Ummana tana min tsifa Yay??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a ya shigo da manyan ledoji a hannunsa. Jibge su ya yi cikin Waki, sannan kuma wani almajiri ya shigo da wata ledar, su ma karSar su ya yi ya aje inda ya ajiye na hannunsa.
"Khouhar," ya faWa yana zama kan kujera.
"Na am Joonam barka da shigowa," na fada ina mayar da hankalina kanshi.
"Yawwa, Ummana ina wuni barkanku da gida," ya gaisar da Umma.
"Yawwa, Wan albarka, ya aiki ya kasuwa ya jama'a?"
"Duka lafiya lau Ummana."
Hira suka fara shi da Umma can ya ce, "Yau saura kwana nawa a fara azumi ne?
Karaf na yi na ce, "Yau saura kwana kusan goma fa."
"Yawwah, lissafina na tafiya daidai kenan."
"Eh Yaya, ai ni kullum sai na duba calendar."
"Ni yi mun shuru, ke da na ga hankalinki sam ba ya ma wurin azumin, kullum hankalinki na kan makaranta da wayar nan taki."
"Joonam yana kai fa," na fada a shagwabe.
"To na ji," ya ?are maganar yana buWe manyan ledojin da ya shigo da su. Umma ta ce, "Me muka samu?" Daga inda nake kwance na ce, "Wani abun ne Ummana?"
"To ki tashi mana ki gani, don kin ga ina ji da ke shi ne kike wani sha min kamshi." Tashi na yi zaune na gyara zama, "Yaya da ma fa tashi zan yi da an ?arasa Wayan nan."
"To in ma ba ki tashi ba, kallo zai bar ki." Wasu irin manyan lesuka da atamfofi ya fito da su, wanda suka dauki hankalina, saukowa na yi daga kan kujerar na zauna gaban kayan, "Kai! Joonam kayan nan sun yi kyau sosai na fara sakawa a lefe ne?"
KaWa min kai ya yi yana rarraba su, "Kin ga wadannan," ya fada yana nuna mani laces Win, "Kin ga daya na ki ne dayan kuma na Badiyya ne."
"Kai Yaya, amma na ji dadi sosai kenan anko za mu yi?"
"Sosai kuwa Khouhar, tunda ni da ke ba za mu iya anko ba, ai dole matata ta yi anko da ke."
"Joonam ko kunyar Umma," Dariya ya yi ya ce, "Ke, kar ki mini sharri," ya ?are zancen yana dukar da kanshi.
Umma ta ce, "AbuDalib to ita matar taka ta yarda ta yi anko da Lilbirrah ne?"
"Ni ko ta yarda ko kar ta yarda Umma ra ayi na ne, kuma kin ga kala daya ne kaWai za su yi anko din, sauran kala hudun da ya rage kowane da kalar nashi."
"Haka ne, amma duk da haka Allah ya sa kar abun ya yi mata zafi." Umma ta faWa.
Bai ce komai ba ya cigaba da buWe Wayar ledar, hadaddun less ne masu kyau su ma kala uku, "Wannan na Rumaisa ne idan ta dawo daga makaranta, wannan na Anty, wannan kuma zan kai wa Inna Sa'adatu."
Sai kuma ya jawo dayar ledar, nan ma kala biyar ne su har an dinke su tass, "Wannan kuma naki ne Ummana." Duba kayan muke yi babu wanda za ka kalla ka ce bai yi kyau ba sai dai ka ce wannan ya dara wannan kyau, sosai nake murna, "Umma ta ce, "Allah ya yi maka albarka Abu?alib."
"Amin Umma, gobe idan Allah ya kai mu ki shirya mu je mu siyo sauran kayan da kuke bu?ata, na gida da na Badiyyah." Ya faWa yana kallona.
"To Joonam, Allah ya kai mu lafiya," na fada cikin farin ciki. Cigaba suka yi da magana da Umma tana faWa mashi kayan da zai siyo na azumi wanda Baba ya riga da ya siya wasu zai ?arasa ne.
&
Kashe gari muka je kasuwa muka siyo dukkan kayan da muke bukata, tun daga kan kayan abinci, takalma jikka, da sauransu. Bayan kwana biyu da yo siyayyar muka shirya zuwa gidansu Badiyyah ni da Rumaisa da Inna Uwale kanwar Ummanmu muka kai kayan azumi da Yaya ya siya mata masu tarin yawa. Dakinsu Badiyyah muka yi zaune, yayin da suke bude kayan ana ta yabo ana sa alkhairi, sai dai fuskar Badiyyah ta yi gijim-gijim, a dan dame na tabo ta na ce, "Lafiya Bady?"
"Zo mu je kuryar Mama," ta fada tana jawo hannuna. Shigewa muka yi kuryar dakinsu kafin su gama.
Cikin kulawa na ce, "Bady, me ya faru? Me aka yi maki ba daidai ba?"
"Ba komai wallahi, amma me ya sa AbuDalib bai kawo min kayan da kanshi ba? Haka kin san duk sai makwarmata sun gani, karshe sai an ba su wani abun daga ciki."
Ban damu ba na ce, "To me ye Bady, ai a ci abun ka ma arziki ne."
?an karamin tsaki ta ja, "Ke ba za ki gane ba ne Lilbirrah." Nisawa na yi na ce "To shi kenan."
"Kina ji na ko?"
"Ina jin ki Bady, wai ke ko Anty ba za ki rika ce min ba, ni fa yanzu matar yayanki ce ba wai kawarki ba."
Dagowa na yi domin abun nata ya soma ba ni mamaki, "Yanzu kenan mun daina kawance saboda za ki auri Yayana?" Na tambaye ta.
"Eh mana, yanzu na zama Antynki, kuma kawarki," ta kare zancen tana mayar da abun wasa.
"Na ji, yanzu fada min abinda za ki fada min ga shi can su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login