Showing 18001 words to 21000 words out of 55242 words

Chapter 7 - BA DON MACE BA BY FATIMA FANTAH.doc

Advertisement

22 Feb 2025

3654

jirginsu ya sauka cikin International Airport na Vienna.
Vienna babban birinin Aistria gari ne matukar kyau da tsari da birgewa, wanda ya haWa manyan wuraren sha?atawa, gine-gine na tsara da manyan hotels da wuraren buWe ido. Tun da suka sauka hankalin Badiyyah ya kwanta, wani daWi da farin ciki na kaikawo cikin zuciyarta. Sai dai ta janibin AbuDalib sam zuciyarsa ba daWi, ba ya jin wani armashi kuma ba ya jin wani abun birgewa a lamarin tafiyar, jinsa yake kawai yana raye amma sauran lamarin rayuwarsa shi kanshi bai san takamaiman ina ya dosa ba, yana jinsa a wani yanayi marar misaltuwa. Kai tsaye masaukin da aka tanadar musu suka tafi, inda aka sauke su wani kasaitaccen hotel wanda za a iya cewa ya fi kowane kyau da tsada a Vienna. Murna gun Badiyya ba a magana domin ji take duk wasu burika da muradanta sun kusa cika, domin ko a haka ma za ta iya mallakar komai na AbuDalib domin susucewar da ya yi, sannan tun a yadda aka tarbe su tun a airpot ya nuna lallai Abu?alib ba ?aramin matsayi ya samu a harkar trading ba.
Tabbas daga zaran sun koma idan har wadannan kudaden suka shiga account dinta lallai wa'adin aurensu ya kare da AbuDalib.
Wanka suka yi baki daya, da kyar ya samu ya yi sallar Magrib da Isha, abinda yake ba shi mamaki sallah ta zamar masa wani kasurgumin aiki a rayuwarsa. Shuru ya yi ya kasa tuna yaushe rabon da ya yi sallah guda biyar cikakkiya, tabbas ba zai iya tuna tun yaushe ba, domin tuni ya manta sai dai idan ya yi asuba da kyar zai yi azahar da la asar, idan ya samu ya yi su kuma to a ranar duk dubararsa ba zai iya yin Magrib da Isha ba, abun ya dame shi kanshi kamar ya bare sai dai ya rasa ta yadda zai iya furta damuwarshi, ya rasa yadda zai yi ji yake wani abu mai nauyi tamkar dutsin Dala ne ke taushe shi ga wasu abubuwa da ya kasa tuna asalin hakikaninsu, amma zuciyarsa take son sani.
Haka suka yi ta lallaba rayuwar a Vienna, kwanansu uku aka gabatar da gagarumin taron traders na duniya, manyan masu gabatar da kasuwancin ne suka haWu, inda aka karrama AbuDalib da lambar girmamawa ta zinare a matsayin wanda ya fi kowa kasuwancin a fadin Nijeriya. Dala dubu dari biyar suka ba shi, sannan kuma suka kara mashi da wata dala dubu Wari biyar Win a take ya samu dala miliyan Waya, kyautukan wasu ababen suke ta yi mashi ban da kuWaWe da haWaWWaWiyar mota da suka siya mashi wanda suka Wora isarta.Najeriya cikin Wan lokaci kafin ma ya koma. Farin ciki fal zuciyar Badiyyah domin ana gabatar da taron tana lissafin kuWaWen. Shi ko Abu?alib yanayin da yake ciki shi ne cikakkiyar fassarar ya?e, fara'a da dariya kawai yake yi, amma ba ya jin ha?i?anin daWi da farin ciki wanda ya sani tuni ya yi bankwana da shi tunda ya samu lalurar da ta zame mashi karfen ?afa wacce ya rasa maganinta.
Bayan kwana biyu aka gama taron, inda aka ci kwanaki bakwai na kwanakin sha?atawar da suka ba su ya rage saura kwanaki 21 cikakken sati uku kenan su koma gida.
Zaune yake cikin ?aton falon hotel Win, wanda faWin yadda ya tsaru tamkar Sata lokaci ne. Zaune yake daga shi sai singlet da boxer, hannunsa yana karanta wani littafi, wanda yanayin da yake ciki ya sa ya zama mai shuru hakan ya saka mashi son yin kasance-karance don ya rage ?ullin damuwar da ya Waure zuciyarsa.
Kallonshi take yi, Abu?alib kyakkyawa ne sosai, duk da damuwar da yake ciki ta sa shi ya yi rama sai dai hutun da yake samu ya sa fatar jikinshi ta yi wani tsadadden kyau, ta ba da wata kala mai wuyar bayyanawa. Wani abu ta ji ya taso mata. A hankali ta ?araso inda yake, "My Man...," ta faWa tana zama kusa da shi.
"My Shona." Ya faWa yana ajiye littafin hannunshi.
Hannuwansa duka biyun ta kama tana juya da gangar jikinsa suka fuskanci juna. Cikin wani yanayi da ta tsinci kanta a ciki ta ce, "My Boo, ina kewarka, i miss you alot...," ta ?are zancen tana shafa fatar kafaWarsa da ke a bayyane. ?an baya ya yi, saboda yadda take shafa fatar jikinsa ta soma harmutsa tunaninsa. "My Shona... Stop it pl..." Kafin ya ?arasa ta yi gaggawar haWe bakinta da nashi. Gaba Waya reaction Win jikinsu ya canza, sun shiga wani irin yanayi marar misaltuwa wanda kewar juna da nisan da suka yi a mu'amalar ya sabbaba musu shi. Zaman ya gagare su suka faWa kan kujerar gaba Waya suna romancing junansu cikin fitar hayyaci. Sosai Badiyyah ta rikice take bu?ata da neman agajin kusanci na gaske, sai dai kamar yadda take faruwa a lokutan baya haka ta faru a wannan karan, ko kaWan babu alamun Abu?alib Win zai iya yi mata wani abu, jikinta na karkarwa ta mi?e daga kan jikinsa, shuru ya yi tare da faWawa cikin dogon tuna??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ni, jikinsa ya yi li?is tamkar an mishi duka, wani huci yake fitarwa ta hanci da bakinsa, tabbas yana cikin matsala, kuma abinda yake gudu kenan kar su ta?ulo abinda zai dame su gaba Waya. Da ?yar ya juyar da kanshi wurin Badiyyah, "Am sorry please..." Wani dogon tsaki ta ja ta gyara zaman rigar jikinta ta mi?e ta bar wurin da sassarfa. "Shona, My Shona," yake maimaita kiran sunanta, wanda hakan ya sa ta ?ara ?aimin gudunta. ?aki ta faWa ta banka ?ofar da ?arfi, kalaman Mom Winta suna yawo cikin ?wa?walwar kanta, "Yanzu haka Abu?alib zai dawwama?" Ta faWa a bayyana.
"Ta ya ya zan cigaba da zama da mutum tamkar 'yaruwata mace? Ina ba zan iya ba, ba zan iya ba dole ne na nema ma kaina mafita." Shuru ta yi tana mai da numfashi tana sakin nannauyar ajiyar zuciya, tana ?udira matakin da za ta Wauka da zaran sun koma Nijeriya.


&&&&&


BAYAN SATI UKU

Sosai nake samun kulawa daga wajen Yunus da mahaifiyarsa Mama, kamar yadda na ji yana kiranta, cikin satika ukun zuwanmu asibiti biyu, muna zuwa a kowane sati, sosai nake jin dadi zuciyata cike da amincewa Allah ne ya kawo min daukinsa da taimakonsa kamar yadda yake yi wa bayinsa ta inda suke zato da ta inda ba su zato ba su tsammani. Kamar yadda muke duk sati yau ta kama za mu koma asibiti karo na uku, shirye na fito na samu Yunus kofar gida, hannu nasa na bude kofar mota na shiga, juyawa na yi don rufe ?ofar, ganin Saratu na yi tsaye bakin kofar gidansutana kallon motar, tamkar ta karaso wurina bakinta da abin fada. Yunus ya ja motar ya tafi, har muka fice daga layin tana tsaye tana kallon motarmu. Kada kai na yi domin a cikin kwanakin gaba daya ta ida rikicewa, kullum kuma cikin son rigima da ni da yin sabon tsiri a cikin zamana na gidan wanda ya sa har na fara jin gundura a zaman. Sai dai Baban Ayuba da shi kansa Ayuban suna kyautata mini, da tausaya mini a game da hali da yanayin da nake ciki.
"Amatullah," sabon sunana da Yunus ya kira ya katse mini tunanina. Juyawa na yi na zuba mishi idanuwa, kamar yadda na saba yi ga duk wanda ya kira ni ko ya yi mini magana. Muryarsa a tausashe ya ce, "Ya karfin jikin naki?"
"Da sauki, Alhamdulillahi." Na fada mashi.
"Masha Allah, ya Baby yana lafiya ko?" Jinjina kai na yi alamun, Eh. Murmushi ya sakar mini yana sannu Ama.
Nisawa ya yi a hankali cikin nutsuwarsa ya ce, "Amatullah ina son yin wata magana da ke, sai dai ina Shakkun shin za ki amince ko zan samu akasin haka, duk da dai na san yanzu kin fahimce ni kin gane ko ni waye, ga shi har ma kina mu amala da mahaifiyata, kin ga asibitinmu, kuma na san duk da ba ki mu amala da mutane da yawa ba za ki rasa jin feedback a game da mu ba."
Jinjina kai na yi alamun eh, sannan na dora da, "Kuma ban ji wata magana marar kyau a game da ku ba, ni ma kaina zan iya shaida wannan."
"Haka ne. Ama, a halin yanzu kina cikin hadari, ina nufin a yanzu kina bukatar kulawa fiye da ta kowane lokaci, saboda a yanzu haihuwa za ta iya zo miki a kowane lokaci. Don haka na yi ma Mama magana a kan ina son ki koma gidanmu ko na ?an?anin lokaci ne. Duk da ba ki sanar da ni ko ke wacece ba, i agreed 100% ke bahaushiya ce."
?an murmushi ya yi, "Ni ma da kike gani na, da Mama da Babana dukansu Hausawa ne, Babana yana zaune a Lekki amma ni da Mamana muna zaune a G.R.A Ikeja, daga ni sai Mamana da ma aikatanmu muke zaune a gidan, Amatullah a can ko kaWan ba za ki samu takura ba, kuma ina mai tabbatar maki za ki samu cikakkiyar kulawa. Idan kin amince sai a gyara inda za ki zauna gobe weekend sai na zo na dauke ki ki koma a can, amma fa sai kin amince."
Magana yake yana kallon hanya, ni kuma na yi kasake ina saurarenshi, zuciyata na matsanancin gudu tsakanin amincewa da rashinta. Saratu koyaushe cikin laluben hanyar da za ta wulakanta ni take haka zalika tana aibata ni da aibata abinda ke cikina, za a iya samun matsala gagaruma bayan haihuwarsa, sannan bugu da kari koyaushe ina tsoron tsohuwar bayarabiyar nan Innarsu Kulu, wadda haka nan zuciyata ta kasa amincewa da ita duk da tana kawo min ziyara da duba yanayin lafiyata a kowace safiya. "Kin yi shuru Amatullah? Da ma na yi tunanin ?in amincewarki, hakan ya da?ile ni ga yi miki magana tuntuni, sai dai kuma tsorona a kan hali da yanayin mutanen unguwar da kike zaune ya ingiza ni har na amayar maki da zancen, don Allah Ama ki amince kin ji."
Saddar da kaina na yi ?asa saboda irin kallon da yake mini mai cike ma'anoni daban-daban da kuma nuna ?agara na son ya ga na amince mashi. "Kin amince?" Ya faWa a tausashe.
A hankali na daga kaina, tare da yi masa nuni da hannuna na amince. "Alhamdulillah, Alhamdulillah," ya maimaita har sau uku, alamun jin dadi na amincewa ta.
"Na ji dadi Ama, kuma insha Allahu rabbi na yi maki alkawarin ba za ki samu damuwa da mu ba tsawon zaman da za ki yi Insha Allah."
Dan gajeran murmushi na yi, har muka isa asibitin yana yi mini surutu da ba ni labarai kala-kala. Muna isa ina tafiya da ?yar, duk da abubuwan ?arin jini da Yunus yake kawo mini bai sace kumburin jikina gaba daya ba, wanda Maman Yunus ta ce min ba komai, kuma da yardar Allah ba zai ba ni matsala wurin haihuwata ba. A wahale na haye matakalar bene, muna isa Yunus yana min sannu, sannun da ya kamata na samu daga Uban Abunkaunata, sai dai ya yi fatali da ni ya watsar da ni bayan ya goga mini bakin fenti da mummunan tabo a rayuwata. "Mace ce ta yi komai," wata zuciyar ta ayyana mini lokacin da muke isa ofishin Maman Yunus.
Muna shiga ita ma ta dora nata sannun. Dakin da take yi mini gwaje-gwaje muka isa. A wannan karon ma ta tabbatar da komai lafiya kuma haihuwa tana gab da yardar Allah kamar yadda ta ga alamu. Bayan an gama Yunus ya dauko ni domin komawa gida.
"Ama bara na siya miki dan tsire da nama mai taushi a wurin nan na san zai miki dadin ci." Ya faWa yana yin fakin daidai wurin.
Fita ya yi daga motar, bai jima ba ya dawo mini da naman wanda kamshinsa ya sa na ji yawuna na tsinkewa, karbar ledar na yi na bude nama ne ya yi jajir, Wan Salla na yi na saka baki, daWinsa ya gauraye mini bakina ga taushi da laushi kamar auduga. "Ya yi daWi ko? Ai ina son naman gurin yana da laushi sosai." Yunus ya faWa.
Jinjina kai na yi alamun ya yi daWi kam sosai. BuWe wani Wan sif da ke gefensa ya yi, a mamakina sai na ga ya fiddo waya ?irar kamfanin apple. Tsuru na yi ina kallon wayar,  Khouhar, ga iPhonazation nan na siyo miki ki ri?a fa-fa, na san ku 'yam matan nan, sai kun rike iPhone kawai kuke ganin kun cika 'yan gayun 'yammata, a yi ta nunawa ana fa-fa... Kin ga tawa, Andoroid touching-touching kuma ta ishe ni& 
Muryar da na yi kewarta na ji ta dawo mini sabuwa fil cikin ?wa?walwar kaina a lokacin da ya siyo mini iPhone don ya faranta raina kuma ni ma na shiga ya yi.
"Ki karba mana Ama, ni duk abinda na yi maki na yi fisabilillah kuma na san ko nan gaba ba zan yi da na sani ba." Zancen Yunus ya dawo da ni hayyacina, jinjina mashi kai kawai na yi, na karbi wayar ina jujjuya ta, sabuwar waya kirar iPhone latest version. Kafin na fara jera mashi godiya na ya ce, "Kin san wani abu, na manta da siyen SIM Card, ga yamma ta yi sosai bari sai gobe kawai idan kin koma can gida, sai na siya maki SIM din, kuma ka ki yi chargy, kodayake na ga nan gidan ma kaman ba wearing ko?"
Jinjina kai na yi, "Koma ka tafi da ita duka gobe na karba wayar na da tsada kar a kwace min." Yar dariya ya yi, "Duk wanda ya kwace ko ay sai ya ji a jikinsa Ama, don nasan zai iya taSa lafiyarki ni ko ba zan lamunta ba." Murmushi na sakar masa. Na ce, "Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi."
Har muka isa gida muna yin yar hira irin wacce muka saba, wanda da yawa Yunus yana ba ni labarai ne wasu na barkwanci wasu kuma na shi ne wanda ke cike da abubuwan ban dariya da irin gata da kulawar da yake samu gun Mamanshi, wacce takan tunatar da ni tawa rayuwar mai yanci kafin na fada halin garari. Kamar yadda ya saba har kofar gida ya ajiye ni, bankwana muka yi sannan ya juya a kan zai je ya dauki Mama su koma gida, saboda Juma'a ne lokacin tashinsu ya yi.
Ina shiga gidan ba kowa sai Babansu Ayuba da ke cikin gidan, sannu ya yi min ni ma ita na mayar mashi na wuce dakina. Bude ledar naman na yi wanda a irin yadda nake cin abinci zan iya wuni biyu ban cinye shi ba, duk na san sana ar Nama suke yi a gidan hakan bai hanani na dauko naman na kawo ma Baban Ayuba ba. "Nagode sosai, nagode kin ji." Komawa na yi Waki na zauna irin zaman nan na cin tuwo na fara cin naman domin na ji dadin shi sosai. Sallamar Ayuba na ji bakin ?ofa, ta?ar?arawa na isa bakin ?ofar, "Kai mun ga abun alheri mun gode sosai."
"Ba komai," na yi mashi nuni. Ba tare da shawara ba na kwaso 'yan kayayyakin da na tara na amfani, kayan abinci da sauran tarkacena na ba shi. "Na me ye?" Ya tambaye ni?
"Da ma gobe zan tashi, shi ya sa na ba ka kayan ina godiya da irin taimakon da ka yi mini a lokacin da nake cikin bu?atarsa, Allah ya saka da alkhairi Nagode sosai," na zayyana mashi da bebencina.
Sosai Ayuba ke murna don yana sane da cigaban da na samu, ya ji daWin samun kayan amfanin da na ba shi. Tafiya ya yi yana ta mani godiya da Allah san barka.
Komawa na yi Waki na ?arasa cin namana, bayan na kammala na fita waje na wanke hannuna na yi alwala na koma cikin daki. Sallolin magrib da Isha na yi a tare domin tashi na mini wahala sai na yi sallolin gaba Waya. Hannuna rike da wata hadaddiyar tasbih counter da Yunus ya ba ni, dayan hannuna na dago na sumbace shi sannan na dora a kan cikina. Hirarmu ta zuci da zuci na fara. "Abun Kaunata..." Wani murmushi na saki mai bayyana zallan farin cikina. "Abun kaunata, ka gani ko, duk da an tozarta mu an wulakanta mu, Allah ya yi nufin ba za ka zo duniyarmu ba a wulakance, abun kauna cikin 'yanci za ka zo kafin 'yancinka cikakke kuma na ha?i?a ya bayyana. Ina sonka Abun kaunata. Kai ma kana son Ummanka ko?" Murmushi na yi, zuyciyata cike da amincewa Abunkaunata ya amsa mini na sauke hannuna. Kishingidawa na yi inda nake na cigaba da tasbihina, gefe ina jin Abun ?aunata yana ta juyi cikin duniyarsa mai cike da duhu.
Gani na yi Saratu ta Wage labulen ?ofata da ?arfi, wanda har ya tsorata ni ya sa ni tashi zaune da Wan razana. "Fito, fito..." Take ta maimaitawa cikin faWa da hayaniya. Da hannu na ce mata lafiya? Me ya faru?"
Tsaki ta ja ta ce, "Fito na ce, so nake ki bar gidan nan yanzu-yanzun nan, don har na samu wacce za ta zauna ma Wakin," ta ?are zancen tana nuna mani wata mace ti?e?iya da ke bayanta.
Rasa me zance mata na yi, cikin kiWima na yi mata alamun ro?o, hannu biyu ta sa tana niyyar jawo ni. Hannu na Waga mata alamun kar ta taSa ni, domin bana muradin irin azabar da na sha a lokacin da abun ?aunata yake a gudan jini na kuma maimaitawa a lokacin da nake sa ran zuwansa a kowane lokaci. Sosai gidan ya kacame da hayaniya, ko kaWan Saratu ba ta jin ban baki balle hakuri, mutanen da suka shigo sai dai su kalle mu su wuce. Cikin hayaniyar da ake Innarsu Kulu ta shigo, hankalina tashe na yi inda take.
Tambayar Saratu take, "Me ya faru?" Harara ta watsa mata, sannna ta ce, "Gidan za ta bar mana, yanzu-yanzun nan, don na gaji da zamanta haka nan." Wasu irin ?wallah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login