Showing 15001 words to 18000 words out of 55242 words

Chapter 6 - BA DON MACE BA BY FATIMA FANTAH.doc

Advertisement

22 Feb 2025

3634

me ye aniyarki ta biki na ayyana a raina na koma barcina. Domin tsarina sai sha Waya zan tashi, bayan na shirya na je gun Maman Nana na kai mata kuWi sannan in shaida mata ta aiko su Nana su Waukar mata abincin da na Wibar musu.


SH 7


ABU?ALIB
Kwana uku cif suka rage tafiyarsu zuwa Vienna, ba ?aramin dadi Badiyyah take ji ba da Abu?alib ya warware tass hakan ya sa za su samu damar tafiyar, sai dai abu Waya ya dame ta, wanda kuma ta mayar da shi ba abun damuwar ba, gaba Waya ya ?arasa sauyawa, yana wani bin ta kamar bawa da Ubangida. Watsar da tunanin abin ta yi gaba Waya, ta cigaba da shirya komai na tafiyarsu, wacce take buri da ?ulafucin a yi kawai don kuWaWen da za ta mallaka.
Yana zaune babban falon gidan ta fito cikin gayunta ya zuba ma matakalar benen da ke kallonsa ido. Mai da idanuwanta ta yi inda yake kallo, take ta kyabe fuska da baki, wannan jarabar duniya, wai ko Abu?alib zai manta da Lilbirrah har abada? Zai manta ta yadda nake so kuwa? Kallon me yake ma sashenta? Dan karamin tsaki ta ja ta ida ?arasawa inda yake, sake fuskarta ta yi kamar ba ita ce ta gama haWeta ba.
Zama ta yi kusa da shi turarenta ya bugi hancinshi, idanuwanta ta saka cikin nashi, "My Boo, me kake kallo ne na ga ka zuba ma kafar bene idanuwa?"
"Ba komai My shona. Me kika gani ne?"
"My ka san dai bana son abinda zai dame ka ko? Idan na ga kana damuwa kai kaWai sai hankalina ya tashi na ga kamar har yanzu ciwon ka bai warke ba." Ta kare maganar hawaye na ciko idanuwanta.
Hankalinshi tashe ya ce, "Am so sorry Shona, don Allah kar ki yi kuka ki bata kwalliyanki. Am sorry please ba abinda yake damuna na warke sosai."
Shararo hawayen ta yi a shagwaSe ta ce, "Ni dai ka fada mini gaskiya, ka fada mini gaskiya My Boo please." Rungumeta ya yi tsam jikinsa, "Na fada maki Shona ba komai ba abinda ya dame ni kuma, amma kin san akwai abubuwan da dole su saka ni tunani ko? Kin sani My Shona, wani lokacin ji nake kamar ina kwarar ki..." Dariya ta so kamata sai dai ta kara lafewa jikinsa, "Ni ba ka kwarata, ba ka min komai, and I luv you AbuDalib game da matsalarmu a zamanmu kar ka damu, kuma na sha faWa maka ka daina damuwa zan zauna da kai ko da za ka dawwama a haka." Ajiyar zuciya ya sauke, "Shi kenan to, na daina Shona, yanzu ki tashi ki tafi gun Mommy ki mata bankwana, kar ta ce na hana ki zuwa please, hankalinta zai tashi."
"Ni dai in har ba ka jin dadi ba inda za ni."
"A ah My shona ki tafi please."
Dagowa ta yi fuskarta duk ta hade da hawaye. "Ka tabbata ba abinda ke damunka My Boo."
"Ba komai wallahi, kin ji na rantse."
Share hawayen ta yi, "Shi ke nan na yarda My."
Mikewa ya yi da hanzari ya dauko tissue da ke kan table na tsakiyar falon ya goge mata fuskarta."Na san ba a rasa kayanku na mata ko, bara na shafa maki powder." Ya faWa yana buWe jikkarta.
Murmushi ta yi, "Bar shi My, na tabbata a haka na fi kyau saboda hannunkan nan mai albarka ya gyara mini fuskata." Ta kare zancen tana ba shi peck a kunci.
"Shi ke nan, Allah ya kiyaye ki gaida min da Mommy, sai kin dawo." Mikewa ta yi ta fita tana mishi bankwana.
Har ta bace ma idanuwansa yana bin ta da kallo. Tafiya za su yi gobe za su bar Katsina su isa birnin Kano inda jirginsu zai tashi. Badiyyah princess Shona dinsa ta tafi gun Ummanta. "To ni fa?" Ya fada a bayyane, shuru ya yi yana tunanin da ke kulle ?wa?walwar kansa.
Mikewa ya yi da sassarfa ya haye steps din bene, Wakinsa ya shige ya saka jallabiya ya fito da key din mota a hannunsa. Shi ma ficewa ya yi daga gidan, kai tsaye Yammawa ya nufa yana zuwa kan kwanar titin da za ta sada shi da Unguwar ya mi?e, sam ya kasa tinkarar gidan duk yadda ya so zuwa, da samun amsoshin da suka gagari ?wa?walwarshi ya kasa.
Cikin gari wuce don zuwa gun abokanshi, nan ma ji ya yi baya iya kusantarsu, tamkar wani abu na baya-baya da shi game da su, hakan ya sa ya kara ma motarshi gudu ya nufi wajen gari. Gidan zoo ya tafi, tamkar soko yake bin dabbobin daji yana kallonsu, ya jima a gidan Zoo Win yunwa da ta addabi cikinsa ta sa dole ya bar wurin ya nufi restaurant.
Zama ya yi cikin ?uncin rai da takurar zuciya da suka yi ma rayuwarsa dabaibaiyi, yana jin kanshi na juyi, jefi-jefi yana kallon mutane suna walwalarsu, to me ma ya sa suke dariya? Wani haushi ya taso daga ranshi, ya mi?e ba tare da ya ci abincin ba ya bar gurin.
Jigum ya yi cikin mota, tamkar ya fashe da kuka, cutar ?wa?walwar da ta same shi sam ba ta kyauta ba, ta raba shi da farin cikin rayuwarsa, ta salwantar da walwalarsa a haka kuma ya ji sau?inya warke, "To me ye ke damuna?!" Ya faWa da ?arfi tamkar zai tarwatsa motar. Sam ba shi da amsa, hakan ya sa ya yi lamo yana jin bigawar zuciyarsa ga wata azababbar yunwa tana jijjiga 'ya'yan cikinsa.
Gajiya ya yi da zaman, kai tsaye ya yi wa gidansu Badiyyah da ke unguwar Iyatanci tsinke. Kallon gidan yake kamar lokacin ya fara ganinshi, a da babban gida ne amma da likkafa ta cigaba an Webi wani sashi na gidan an gyara shi tsaf tamkar gidan wata sabuwar amarya. Sallama ya yi ya shiga falon Momin Badiyyah, kwance ya samu Gimbiyar tasa tana waya hankalinta kwance. Ganin shi wuri-wuri kamar an koro shi ya sa ta tashi zaune da sauri, "My lafiya na ganka kuma ko sanar da ni ba ka yi ba za ka zo."
Fuskarsa da tsananin damuwa ya ce, "Wallahi ko, tun Wazu na fito na rasa inda za ni kawai shi ne na taho nan, ban ma fito da waya ba ni Shona."
"Uhmm, to hakan ya yi. Ka ci abinci dai ko My."
"Na je restaurant na rasa me zan ci My, abincinki kawai nake so, girkinki."
"Eyyah My, ni bana son kana zama da yunwa fa. Yanzu bara na zuba maka abincin, Alala ce na tarar Mom ta yi."
"Ina ci Shona, a zuba mini," ya faWa a ?agare.
Mikewa ta yi ta shiga kitchen ba ta jima ba ta fito da Alala da miyar kifi, sai kuma Jug dauke da soSo mai sanyi. "Ga ya nan My ka ci don Allah," Ta ?are zancen tana ajiye abincin a gabansa.
Bismillah ya yi ya fara cin abincin, kallonsa yake yana son tuna wani abu game da shi amma ya kasa, sai dai ya yi Wan guntun murmushi ya ce Alala, yana zuba ma plate Win ido. Wani irin kallo ta watsa mashi tamkar ta yado idanuwanta. Alala tana cikin favorite din abincin Lilbirrah, tana yawan cin ta, tana yawan yin ta, ba ta wuce tayin ta idan an mata, takan saye ta ko a hanya ne saboda son da take mata, kenan tunanin Lilbirrah ne yake yi, wai tunanin nata ba zai taba barin ?wa?walwarsa ba, ko dai mugun bugu za ta yi masa a ?o?on kansa, idan ya yi karamin hauka sai ya mance komai daga baya ya warke. Dagowa da ya yi suka hada idanu ya katse tunaninta, duk yadda ta so kakaro murmushin ?arya da zai dishe Sacin ran da ke daddale cikiin zuciyarta ta kasa. Cikin kulawarsa a gare ta ya ce, "My Shona me aka yi miki? Me ya faru na ga kamar ranki ya baci?"
"Ba komai My Boo, gani na yi kana cin abincin nan daga gani yunwa ta kama min kai da yawa a wunin nan."
Uhmm kawai ya fada, ya cigaba da cin abincin cikin nutsuwarsa ta halitta.
Mommyn ta yi sallama cikin falon, ganin AbuDalib a falon ya matukar ba ta mamaki don ko a zuwan Badiyya ba ta sanar da ita zai zo ba. Bakinsa na rawa ya duka har kasa ya gaishe ta. "Mommy barka da dawowa, sannu da zuwa." "Yawwa," ta amsa mishi.
"Ina wuni Mommy," ya kuma gaishe ta.
"Lafiya lau, ai na je unguwa ne, ashe kana nan."
"Wallahi ko Mommy yanzu na shigo."
"Okay, to sannu ai yanzu ma sai tafiya ko?"
"Ehh."
"To Madallah ai marece ya yi."
"Eh Mom," ya furta.
"To bara ta shiga ta shirya sai ta zo ku tafi ko?"
"To Mom," ya fada tare da mikewa ya koma kan kujera ya zauna.
Tabe baki uwar ta yi, tabbas AbuDalib ya canza tamkar ba shi ba, sai yanzu ta gane abinda Badiyyah ke faman faWa mata. Uwar daka suka shige ita da Badiyya, suna shiga murya kasa ta ce, "To na zo maki da sako fa, ya za a yi ya zo ya yi kane-kane cikin falo."
"Hmm, Mom kin gani, haka fa ya koma haka nake fama da shi duk ya zama wani shashasha, yanzu idan ban ce ya tafi waje na haka zai yi zaune. Tsakani da Allah da yana yiyuwa na fi son in ga mijina dai tsaye cikakken namiji kamar yadda yake da, kin ga ay tsayayyan namiji ne amma yanzu duk ya wani susuce."
"To ba haka ake so ba?" Mom ta faWa.
"Ba haka ba Mom, ni na fi son shi yadda yake da, yanzu fa ko abu na yi sai dai ki ji yana ta yi hakuri, yi hakuri Shona, yi ha?uri. Haka zai ta faWi. Ni bu?atata ya mance da waWancan mutanen, na cigaba da tsara mishi rayuwa da mutanen da zai yi mu'amala da su, amma ya tsaya yadda yake a da," Badiyya ta ?are zancen cikin damuwa.
"Ni ki kwantar da hankalinki duk wani abu za a gyara shi Waya bayan Waya, yanzu ki je ki lallaba shi ya fita na miki bayanin maganin nan."
Fita ta yi falo ya yi zaune cikin jangwam Win da ya saba. "My mu tafi gidan ko?" Mikewa ya yi, "To My Shona. Mu tafi." Gaba ya yi har sun kusa ficewa daga falo ta ce ba ka yi wa Mom bankwana.
"Wai na manta wallahi," hararar shi ta yi ta baya.
"To mu je ka yi mata bankwana, sai mu tafi." Komawa ya yi ya ce, "Mun tafi sai anjima Mom," yana fadar haka ya yi kwana ya koma ya ce mu tafi.
Kada kai kawai ta yi, sunan wata waka wai ita halittah, Abu?alib ya zama wata halitta cikin 'yan kwanakin nan. Tafiya suka cigaba da yi sai da suka yi nisa da kofar gidan ta ce, "Kash!"
Bakinsa na rawa ya ce, "Me ya faru Shona?"
"Na baro hand bag dina ne My."
"Ko na koma na dauko miki?'
"A'ah My, karasa mota dai sai na dauko."
"To," ya fada ya yi gaba ita kuma ta yi baya.
Da sauri ta isa falo ta iske Mom, "Yaya dai na ga kawai kin kama kin tafi."
"Uhmm. Mom, ai in ba haka na yi mashi ba, ba tafiya zai yi ba."
Hannu ta sa ta bude jakarta ta fiddo wani kullin magani, "karbi wannan..."
"Na me ye kuma? Game da wannan aikin da aka yi masa baya wannan ne makarinsa, hade yake da muguwar mallaka, kin ga maganin nan shi kadai ne, idan ya bace AbuDalib zai dawwama a cikin wannan matsalar, haka Boka ya tabbatar mini."
Yamutsa fuska Badiyyah ta yi, "Zai dawwama fa Mom? Yanzu idan wani abu ya samu maganin nan shi ke nan AbuDalib zai dawwama a haka?"
"Haka ya fada mini, kin san lamarin nasu yadda yake, su ma wani bin gardamammu ne."
"Yanzu kuma ban da wannan mallakar da wata wacce ta fi ta?"
"Sosai ma, ai wannan sai yadda kika yi da shi ce."
"Ai ko yanzu Winma."
"Ke dai ki amfani da shi, tunda na ce."
"To Mom ya zan yi da shi?"
"Yawwah. Ki tabbata daren yau kun samu kusanci ke da shi."
"Tunda ya samu wannan matsalar ko kadan ba ya fuskantata da nufin wannan sai ya ce baya son ya kware ni."
"Ka ji Shashashar yarinya, to ke a matsayinki na mace ba za ki iya ki jawo shi jikinki ba har ki san yadda aka yi kuka samu kusancin? Ke dai an yi sakarya wallahi."
Turo baki Badiyya ta yi alamun ranta ya baci, "Kina ji na ki ji abinda zan gaya maki, wannan maganin da kun koma ki zuba mashi shi cikin ruwa ya yi wanka da rabi, rabin ke kuma ki jika ki sha sannan ki samu zummuwa ki gauraya ta da shi ki yi matsi da shi, na farko zai warke na biyu mummunar mallaka ce sai yadda kika yi da shi, duk abinda zai samu a tafiyar nan idan kika ga dama ma, za ki iya mallake kudin gaba daya, ko ya aka yi ba zai ce miki ba balle ya bi bahasi."
Sakin fuska Badiyyah ta yi, "Wai da gaske Mom, kai amma na ji dadi, Boo zai samu lafiya wallahi dama ina kewar kayana, sannan kuma na samu waWannan kuWin kuma ai shi ke nan."
"Uhmmm Badiyya ba ko kunya?" Ficewa ta yi tana dariya, har bakin get din gidan ta bi ta tana kiran ki kula fa Badiyya, ki kula sosai, kin ji abunda aka ce game da maganin. Bankwana ta sake yi da uwar sai bayan sun dawo daga Austria kuma.
Da dan sauri take tafiya zuwa mota, hannu ta sa a handbag dinta ta dauko wayarta da ke ta faman tsuwwa. Ganin sunan me kiran ya sa ta buga tsaki ta mayar da wayar a jakar ta cigaba da tafiya.
Zaune ta same shi a mota, ya yi zuru yana kallon hanya, kwankwasa kofar ta yi ya bude zama ta yi gefe tana na dade ko?
"Eh wallahi ina ta jiranki, amma na san Mom ce ta tsaida ki."
"Haka ne," ta faWa. Bai ce komai ba ya ja mota suka fara tafiya. Ta hanyar unguwarsu suka wuce, zuciyarsa ta hau bugawa da sauri kamar yadda take yi duk idan ya zo wurin, sai dai ko iya tada zancen nan unguwarsu ne be yi ba, a dame ya juya ya kalli Badiyyah wani kallo ta yi masa hakan ya sa ya juya cigaba da tuki.

Suna isa gida sun tarar Laure ta gama girki da komai, dakinsa ya nufa don yin wanka, "My Boo na zo na hada maka ruwan wanka ko?" Jinjina kai ya yi, hannu ta sa jikkarta da niyyar dauko maganin da za ta antaya masa a ruwan, sai dai wayam ita ta yi mata sallama gabanta ya fadi, "Yana ina to? Ina maganin yake?" Shi ne abinda take ta faman maimaitawa.
Runtse ido ta yi ta bude tabbas maganin ya fadi, kalaman da Mom ta yi mata su suka kara tayar mata da hankali, babu wanda lalurar AbuDalib za ta fi bawa matsala kamarta, ya za ta yi kuma ina za ta sa kanta yaushe ta tara abinda take buri balle ta gudu ma ta bar shi? Ay tafiyarsu ta Vienna somin taSi ne, yanzu aka fara da ya samu wannan matsayin...
Wata zufa ta karyo mata, ba tare da shawarar komai ba ta Wauki key din motar da ya ajiye ta fice.
Kai tsaye inda ta tsaya don amsa waya ta koma, tana karyawa kan kwanar ta yi tozali da wani yaro dauke kullin maganin yana ?o?arin kwancewa, a guje ta nufe shi tamkar za ta tashi da shi, ba karamin tsorata ya yi ba cikin zafin nama da kokarin kauce ma motar ya yi baya, cikin rashin sa a maganin da ya riga ya kwance ya watse gaba Waya cikin iskar Subhana. "Innalillahi wa inna ilaihi raji un!" Kawai ta iya fada. Gaba ta yi don yin fakin ganin mutane sun yo mata caa ya sa ta ja motar cikin fushi ta bar gurin domin abinda take gudun ya riga ya faru.

*

?alibai ne daya bayan daya suna biya allunansu gaban Malam Saleh, sai da suka kare tass suka koma wurin karatu sannan Malam ya gyara zaman shi. "Dayyabu, Dayyabu," ya fada murya sama.
Da sauri almajirin da aka kira da ?ayyabu ya zo.
"Tun jiya nake so na tambaye ka gama saukar nan?"
"Ehh Malam tun da asubar yau na kammala."
"To ba ka min magana a yi sadaka." Kudi ya mi?a mashi, "Ka je maza ka ba yaro ya siyo waina ta dubu uku a yi sadaka. Zan shiga cikin gida idan an tashi a yi Tabbat yada ta tunkuWe sihiri, idan an gama a yi salatil fatihi sha Waya, Dayyabu a yi na zihiri cikin satin nan nake so a hada salati miliyan daya."
Cikin girmamawa irin ta Dalibi ga MalaminsaDayyabu ya ce, "To Malam," Mikewa Malam Saleh ya yi ya koma cikin gida ya bar ?ayyabu domin ya gabatar da abinda ya ce. Shi ma Malam na shi addu a da rokon Allah yake yi daban ban da wanda suke yi na jam'in dalibansa, da kuma na manyan dalibansa gardawa, duka suna yi a kan lamarin AbuDalib da ya zarce tunanin mai tunani.
Dayyabu ya ba da aka siyo waina kamar yadda Malam ya umarce shi, sai da lokacin tashi ya yi sannan ya sa yara suka karanta, Tabbat yada kafa bakwai-bakwai kowane ya tofa a allonsa, bayan sun gama kowa ya dira kafar allonsa guda Waya a kasa. Kamar yadda ya umarta kuma, sai dai suka yi salatil fatihi kafa goma sha daidaya, almajiran Malam Saleh suna da yawa sun fi karfin dubu daya domin babbar makarantar Allo ce da ta hada da yara da manya maza da mata almajirai da suka yi balaguro daga garuruwansu da kuma 'yan cikin gari masu zuwa gun Malam neman Ilimi. Sai da suka gama a kintace sun yi sama da dubu dari, bayan sun idar aka yi sadaka aka yi addu a aka sallami kowa.


SH 8


AUSTRIA

Wajen ?arfe bakwai agogon Austria

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login