Showing 36001 words to 39000 words out of 55242 words

Chapter 13 - BA DON MACE BA BY FATIMA FANTAH.doc

Advertisement

22 Feb 2025

3638

nemo min Lilbirrah."
Wani abu ya haWe cikin ma?ogoransa wanda yake jin shi ya fi maWaci Waci a cikin makoshinsa kalamansa na katsewa ya ce, "Umma... Na... Don... Allah..." Sai dai duk yadda ya yi namijin ?o?arin ida zancensa abun ya ci, ji ya yi sam ba ya da jarumtar Waukar kalaman da Umman furza masa masu kama da feshin wuta cikin kunnensa, dgon salati ya ja kafin ya kai aya ya faWi ?asa wanwar.
Rumaisa ta zabga ihu, wanda ya sa Inna Uwale da ake komai kan idanuwanta ta baro dakin a hanzarce. A gaggauce suka fara ?o?arin ba shi taimako, sai dai masu kula da majinyata suka yi saurin kawo masu Wauki, inda suka Wauke shi suka nufi Wakin bayar da taimakon gaggawa. Ita ko Umma kan gadon ta koma ta kwanta, zuciyarta na raya mata rashin daidanta cikin kalaman da ta wanke shi da su.

&&&&

IKEJA
LAGOS NIGERIA

Zaune nike cikin kyakkyawan dakin da aka ba ni cikin tan?amemen gidansu Yunus, daki ne ciki da falo da toilet har biyu akwai Waya a bedroom sai Waya kafin shiga falo daga hanyar bedroom Win naw. Cikin sashen da aka ba ni har da kitchen da suke tare da dining area, da ka fito daga dining Win kuma kana haye matakala falona ne, wanda babu abinda Yunus bai zuba min ba, tun daga kan kujeru, kafet har zuwa kayan kallo.
kwanana biyu a asibiti jikina ya murmuje, saboda kulawa da nake samu ta musamman daga wajen Maman Yunus, AbunKaunata ma yana cikin koshin lafiya. Dattijuwar matar da Maman Yunus ta ajiye musamman don ta kula da ni da AbunKaunata mai suna Baba Abu na bawa Nadeer, domin amsa kiran Maman Yunus na wankan ruwan zafin safe.
Toilet muka je ta yi mani wankanta mai azaba wanda har na saba da shi, ina fitowa na tarar Baba Abu na yi wa Nadeer dina wanka. Zama na yi gefe na shafe jikina da wani lotion mai kyau mai kamshi, cikin 'yan kwanakin gaba daya na canza ina ji na wasai cikin kwanciyar hankali.
Mi?ewa na yi na tafi bedroom domin saka kaya, wanda kullum sabon kaya nake sakawa, idan na yi wankan safe sabon kaya zan saka, haka ma idan na yi na yamma, Maman Yunus komai sabo ta ba siya mana ni da Abun?aunata.
Bayan na gama shiryawa tsaf na koma falon, na tarar Baba Abu tana shirya Nadeer, raina ya yi sanyi zuciyata ta sake kallon Abun kaunata na faranta mini rai, jefi-jefi idan na ga yadda Maman Yunus da Baba Abu ke hidima da ni sai ya tuna mini Ummana, ina kewar Ummana sosai da Joonam dina, sai dai ko kadan bana jin kaunar komawa gidanmu, kamar yadda na ?udurta a raina sai da hujjah bayyanana, watakil wasu shekaru goma ko ashirin masu zuwa, wata?il kuma ya zama ?asa da haka ne.
Ina kallon yadda ake ta shirya Nadeer Maman Yunus ta shigo tare da mai aiki, kasantuwar yau ta kasance Asabar ce ba aiki, tana gida shi ma Yunus bai fita ba yana sashen shi.
Break fast ta ba mai aikin umarnin haWa min wanda shi kanshi wani tsari daban ta sa ake haWa min shi. Maman Yunus kenan, a lokacin da ban gani a aikace ba zan iya karyata samun mace mai kirkinta, wata zuciyar ta yi saurin ce mini Ummanki fa, tabbas Ummana mutuniyar kirki ce sosai na ba kaina amsa. Ji na yi hawaye na niyyar zubo mini, na yi saurin mayar da su. "Ama, ki mayar da hankali ki yi break mana, kin sa yaro a gaba kina ta kallonsa." Maman Yunus ta fada tana kallona.
"Mama," na fada a dan kunyace. Murmushi ta yi mini ta ce, "Ama kenan, na ga wata kunya ta ma kike ko, kalli abinki ai Wanki ne, Wan abunka madubinka in ji hausawa."
Dariya ta ba ni sosai, bayan na gama na soma karyawa. Ina yi muna hira da Maman Yunus tana ba ni labarin ita asalin 'yar garin Bauci ce, harkar chanji ta kawo mijinta Lagos. Gyara zaman ta ta yi ta ce, "Lokacin da ya fara fa bai zama haka ba, amma yanzu kin ga yadda muka zama, bari ki gama wankan ruwan zafin nan za mu je gidanmu da ke Lekki za ki sha kallo."
?an zaro idanuwa na yi, "Mama yanzu wancen gidan har ya fi wannan?"
"Haba wannan Win me." Shuru na yi don gudun wuce gona da iri.
Nisawa ta yi ta ce, "Na dawo nan ne saboda ya fi min kwanciyar hankali, kin ga nan muna zamanmu a nutse ni da ?ana."
Sallamarsa cikin falon ta katse hirar, "Mom, gaskiya ni Wan halak ne na kirki. Kin ga ina zuwa kuna sako zancena."
Hararar wasa ta yi mashi, "Ah to, ni dai gaskiyata na faWa. Ko ba haka ba ne Amatullah, Maman Baby."
Murmushi na yj na sunkuyar da kaina, cikin girmamawa na ce, "Yaya Yunus ina kwana."
"Ni dai ban ganshi ba," ya faWa da sigar zolaya yana zama ?asa wajen ?afafun Mamanshi.
"To barka da kwana Yaya Yunus."
"Yawwah barka, ya My son,"
"Ga shi yana lafiya ranka ya daWe," Baba Abu ta faWa tana mi?a mashi Nadeer.
KarSar shi ya yi yana ta kallon shi yana fara'a. "Yaro yana ta ?ara kyau gwanin ban sha'awa, ni kam baya kama da ke Ama, ko Babansa ya biyo ne?"
Ji na yi kamar ya Wora min bulo, shuru na yi don tambayar ta zo mini ba shiri. Maman Yunus ta ce, "Ka ji ka ko? Rabu da shi Ama mu je hirar mu."
KaWa kai na yi, "Ba komai Mama don ya tambaye ni kuma sam bai yi laifi ba. Da gaske ne Nadeer baya kama da ni, da babansa yake kama, irin kamar da ake cewa kamar an tsaga kara."
"Ama, to mahaifinsa na da rai ko ya mutu? Me ye silar zuwanki Lagos?" Yunus ya tambaye ni, kallo Waya za ka yi mashi ka tabbatar ya za?u ya ji amsar tambayar, yayin da nake ji kamar ya mini tambayar ranar mutuwata, duk annurin da ke fuskata ya Sace.
Mama Yunus ta ce, "Kai ko me ya sa za ka tsare ta da tambayoyi haka."
Murmushi mai ciwo na yi, don ban yi tsammanin wannan ranar za ta zo mini kusa-kusa ba, na Wauka za ta Wauki wani lokaci kafin isowarta. Ajiyar zuciya na sauke, "A'a Mama ba laifi ay don ya nemi sanin abinda ke ?unshe a baWinin rayuwata. Kamar yadda ka tambaye ni mahaifinsa yana da rai, sanadin zuwana Lagos kuma wata rubutacciyar ?addara ce marar daWi a zahiri da baWini irin wacce zuciya ba ta da juriyar tunawa.
Ciwon 'ya mace, na 'ya mace ne. Shi ne zancen hikima da ya yi mini tasiri tun daga yarintata har zuwa lokacin da juyayyar ?addarata ta canza fasalin tunanina, ta karantar da ni sabon darasin da na fahimici cewa wata 'ya macen takan zamo silar zubar hawayen 'yar uwarta mace. Kamar yadda 'yaruwata mace ta zama silar zubar hawaye na, ta zama silar raba ni da farin cikina da maye gurbinsa da ba?in ciki da zullumi da tsoro, ita ce kuma silar zuwana Lagos. Ni sunana Lilbirrah.


SH 15


Ni 'yar garin masu kara ce, da aka san mu da kunya kuma mun yi hannun riga da tsoro, wato Katsina birnin Dikko a can na rayu tun daga yarinta har zuwa girmana. Babana shi ne Malam Abdulhadi sai Ummatah mai suna Sa'adiyyah muna kiranta da Umma. Babana da Ummatah suna matu?ar ?aunata, sun ba ni dukkan kulawa sun yi mini gata sun nuna mim so da ?auna musamman Ummatah, tana so na fiye da yadda take son duka 'ya'yanta.
Ni kaWai ce wurin Ummatah sai daga bisani aka haifa min 'yaruwa mai suna Rumaisa, mun kasance mu biyu kenan a wajenta, haka Allah ya ?addara ma Ummanmu ba ta da yawan 'ya'ya. Ko a lokacin da ta same ni ma kowa ya fitar da rai Ummana ba za ta taSa haihuwa ba, domin shekarunta goma da aure amma ba ta samu ?aruwa ba, sai daga baya ta same ni. A wajen Ummana muna da babban yaya mai suna Abu?alib, Yayana Abu?alib bayan Ummana babu wani mutum da ke ?aunata kamar shi. Shi ya kasance Wan ?anwar Umma ne, tana haihuwar shi ta rasu ko fuskarshi ba ta gani ba, Yaya Abu?alib bai san mahaifiyarsa ba sai dai a hoto, kuma tun daga ranar da aka haife shi mahaifiyarsa ta rasu Ummana ita ta Wauke shi, ta shayar da shi ta raine shi har ya girma, sai bayan ya girma ma sannan ya san cewa Umma ba ita ta haife shi ba. Rayuwa muke yi cikin jin daWi da farin ciki, duk da kasancewar mu ba mu su ?arfi ba ne, amma rayuwa muke wadata, saboda Baba bakaniken mota ne, yana da gareji babba na gyaran motoci. Baba yana da Wayar matarsa wacce muke kira Anty. Ita tana da yara biyar, cikin hukuncin Allah su duka maza ne, Yaya Abbas shi kaWai ne Yayana, sai sauran Ali, Yusuf, Kamal, Mustafa duka ?annena, kasancewarmu tsakiyarsu ya sa gatan mu ya ?aru ni da Rumaisa.

&

"Ja?iri..."
"Sarkin Gombe..."
"Ya aiko ni..."
"A takarda..."
"A rubuce..."
"Bature..."
"Ya iya ?ira, ya ?ero jirgi ya ?ero mashin..."
"Wayyo Ummana..." Yaya Abu?alib ya faWa lokacin da ya ji saukar tasbaha bisa gadon bayanshi muna tsaka da wasan ja?iri. Harara Umma ta dallah mashi, "Kai dai kam an yi ?aton banza. Kana namiji, maimaikon a ce hula ta ja kallabi, a'a kallabi ne ya ja hula, ina amfani."
Dariya na kwashe da ita har da ?ya?yatawa, idanuwana kan Yaya Abu?alib yana sosa baya. "Ke ma za ki tashi ku tafi Islamiya ko sai na haWa da ke..."
"A'ah Umma bana son bulala." Na faWa ina mi?ewa tsaye. Kallona Yaya ya yi, "Sai na rama dariyar nan da kika yi min, tunda Umma ba ta dukanki ai ana dukan ki a Islamiya, can za a rama min."
"Yayah, kai da ba ka bari a dake ni ma, ta ya za ka rama dariyar to?"
"Za ki gani kuwa." Ya faWa fuskarshi da alamun Wan fushi. Harara Umma ta watsa mashi, "Kai ni yi mani shuru, me za a gani, ana dukan yarinya kana yi kamar za ka tashi sama. Hala ka Wauka ban sani ba, rannan har gida aka kawo min gulmar an ce ana dukan Lilbirrah Islamiya kana ?o?arin hanawa har tashi kake yi sama, kamar mai aljanu."
Dariya muka yi baki Waya har da Yaya Umma ta ce, "Ka gani ko? Har ka mance."
"Na ji a bar ni a mai aljanun, in dai a kan ?anwaliliya ne to ni mai aljanu ne."
Umma ta ce, "Na ji to Yaya mai ?anwa, sai ku mai da hankali ku tafi kar ku makara." Haka muke da Yaya Abu?alib sam baya son abinda zai taSa lafiyar jikina, ko a gida ko a makaranta duk wanda ya taSa ni to ya san Yaya Abu?alib zai tare mini, hatta Malaman Islamiyarmu idan za su dake ni sai ya ce a yi mishi bulalata, wanda suka ?i suka na???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ce sai sun doke ni sai Yaya ya yi kamar mai aljanu ya hana dukan.
Haka muke rayuwarmu ta makaranta, muna idar da Sallar asuba sai mu tafi makarantar allo ta Baban Abu?alib, da mun dawo kuma za mu shirya a gaggauce mu tafi makarantar boko inda nike firamare aji biyar, Yaya Abu?alib yana aji na uku. Makarantar kuWi ce ta masu ?aramin ?arfi, saboda daga aji uku ?aramar sakandare ta ?are da zaran mutum ya gama sai dai ya tafi wata makarantar ya ?arasa babbar sakandare Winsa. Da mun dawo daga makarantar boko kuma za mu tafi makarantar Islamiya da ?arfe huWu, idan mun dawo sai mu je Islamiyar dare, sosai Baba da Umma suka yi tsayuwa irinta daka kanmu a kan karatun sanin addininmu da na zamaninmu.
Lokacin da Abu?alib ya gama ?aramar sakandare, lokacin ni kuma na gama firamare Wina. Cikin kayan makarantar Pilot ya shigo a can zai ?arasa karatunsa, ni kuma ina makarantarmu inda zan yi ?aramar sakandare, Yaya ya zaSi 'Pilot ne saboda tana kusa da makarantarmu, idan ya ajiye ni makarantar sai ya wuce ta su makarantar haka ya tsara mana.
Cikin sababbin kayan makaranta na fito ina ya ?wambo na zama 'yar babbar makaranta, kallona ya yi sama da ?asa sai da ya gama ?are mani gani ya ce, "Lilbirrah."
"Na'am Yaya Abu?alib," na amsa mashi.
"Kayan sakandaren nan sam ba su karSe ki ba, kin ganki abunka da ba?ar fata sai kika yi kamar bokanya."
?uri na yi mashi da idanuwana, "Lilbirrah kika zuba min waWannan idanuwan naki."
"To cewa ka yi na yi muni." Na ?are maganar cikin shagwaSa.
"Ke wasa nake maki, ai ke ma kin san kyau kika yi." Murmushi na yi daidai lokacin Umma ta ?araso sai da ta dafa kaina sannan ta ce, "Lilbirrah tah, ki yi bismillah idan za ki shiga ajin nan kin ji, yanzu kin shiga babbar makaranta, ki mai da hankali sosai na san kina mai da hankali to ?i ?ara mai da hankali. Kuma na ji Yayanki na faWin wai ba ki yi kyau ba, kin yi kyau sosai ma, tamkar wata zaiba." DaWi na ji ya sauka cikin raina, saboda yabon da Ummana ta yi mini. Yaya Abu?alib ya ce, "Ba wani kyau, ina kyan yake. Kuma ni ma na faWa mata, ba ruwanta da kowa ta nutsu kafin ko irin ?awayen nan ta yi."
"To kin ji abinda Yaya ya faWa ko ?anwar Yayanta." Jinjina kai na yi, "Na ji Ummana."
"Yawwah, to ku tafi Allah ya kiyaye."
"Amin Umma."
Ficewa muka yi daga tsakar gida muka shiga farfajiyar gareji inda sabon Keken Yaya Abu?alib ke jiranmu. A nutse muka tafi makaranta, sai da ya ajiye ni sannan ya wuce tasu makarantar. Haka muka cigaba da rayuwarmu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, inda Yaya Abu?alib ya fara sana'ar Winki, a cewar shi yana matu?ar son sana'ar hannu, duk da jan hankalinsa da Baba ya yi ta yi na ya ri?a zama gareji amma sam ya ?i, ya cigaba da sana'ar Winkinsa. Lokacin da na yi jarabawar gama ?aramar sakandare lokacin Yaya Abu?alib ya gama babbar sakandare, farin ciki gare mu ba a magana, domin ji nake tamkar ni ce na gama. Yaya Abu?alib ya zama matashin saurayi mai kimanin shekaru ashirin da biyu.
A lokacin ni kuma ina da shekaru sha biyar, shekarun girma sun kama ni na yi tsayi sosai na ?ara kyau, ba?ar fatata ta ?ara kwanciya idan ka ganni za ka Wauka cewa, ni Win 'yar masu ?umbar susa ne saboda yadda Yaya Abu?alib ya tsare mini komai na bu?atar rayuwata da sana'ar da yake yi, sha?uwarmu kuma ta ?ara ?aruwa, duk wanda ya san Yaya to ya sanni haka wanda duk ya san ni to tabbas ya san Yaya Abu?alib.
Sana'ar Winki ta karSi Yaya, yana samun Winkuna sosai, duk abinda ya samu kuma sai ya kawo ma Umma, wani lokacin kuWinsa ma sai ta Wiba ta ba shi, idan ta yi mashi magana, zancensa Waya ne saboda mu yake neman kuWi. Hankalinku kwance yake, har muka shiga aji biyu na sakandare. Kowace safiya Yaya ke kai mu makaranta, idan ya ajiye Rumaisa sai ya wuce da ni, muna tafiya muna labarinmu, babu wani da zai same ni ban sanar da Yaya ba, haka duk abinda ya same shi zai sanar da ni. A dalilin yaya ko wata babbar ?awa ba ni da ita, domin Yaya shi ne abokin nawa, kuma babban aminina. A cikin wannan gaSar ne Allah ya haWa ni da ?awa wacce na Wauka aminiya a makarantarmu muna aji na biyu.

&&&&

G.G.S.S

Zaune muke cikin aji an gama break Malami bai kai ga shigowa ba, kowa sabgar gabanshi yake ni kuma kamar koyaushe ina zaune tare da abokan zamana ina ba su labarin Yayana ya ce zai siya min waya idan muka shiga aji uku. Sallamar Malam Bashir cikin ajin ita ta sa muka yi tsit kamar ba wani mahalu?i cikin ajin. Bayansa wata yarinya ce da ba za ta wuce sa'armu ba, zubinta yarinya ce mai matsakaicin tsawo ba ka kiranta doguwa haka sam ba gajera ba ce, fara ce sosai a halittar fuskarta kuma tana da komai tsaka-tsakiya, tun daga kan hanci da baki da idanuwana. Gyaran muryar da Malam Bashir ya yi ya dawo da ni hayyacina daga kallon da nake yi mata. "Ga abokiyar karatu an kawo muku, ya ma sunanki kika ce?" Ya ?are zancen yana juyawa wajenta.
"Badiyyah Salisu," ta faWa cikin sanyin muryarta mai laushi. Du?awa na yi wajen Humaira Shamsu ?asa-?asa na ce, "Da gani saliha ce, mu uku ne sit Win mu mu yi mata wuri." Du?awa ta yi wajen Aishatu Kallah ta raWa mata abinda na faWa mata, take su duka suka yarda. Malam Bashir ya ce, "Ga ta nan ita ma abokiyar karatunku ce, ku zauna lafiya da ita." Duka Waliban suka Wauka, "To Malam." "Yawwah, je ki zauna." Malam ya faWa.
Tahowa ta yi sumumu irin na ba?o a sabon wuri, tana zuwa kan sit Winmu wanda shi ne na biyu na yi karaf na ce, "Zo ki zauna nan, kin ga sauran duk su huWu ne nan kuma mu uku ne." Murmushi ta yi fuskarta na bayyana daWin da zuciyarta ta ji. Matsa mata muka yi ra zauna, duk da ta kasa sakin jikinta da mu jefi-jefi muna sako ta cikin hirarmu.
Kwana biyu muka yi tare da Badiyyah ta fara sakewa da mu, inda da ni da abokan zamana muka dage kwafar mata dukkan rubutun da aka yi na zangon karatun da muke ciki. Sannan bayan mun gama aikin kwafar mata muka fara aikin koya mata karatun da ya wuce ta, a cewar mu kar a zo jarabawa ta kasa ba da amsa. Sosai Badiyyah ta ji daWin zama tare da mu ta kuma ji daWin yadda muke mata hidima. Muna haka na ji ta fara kirana da wani suna, "Aminci," ko kuma ta kira ni da, "Rai." Duk yadda ta kira ni haka ni ma nake kiranta sai muka zaSi suna WaiWaya, tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login