Showing 24001 words to 27000 words out of 55242 words

Chapter 9 - BA DON MACE BA BY FATIMA FANTAH.doc

Advertisement

22 Feb 2025

3647

?ayyabu!" Ko kaWan ba ya motsi sam bai san abinda duniya ke ciki ba.
Wani irin sauti ya karaWe zagayen wurin, waige-waige Malam ke yi bai ga komai ba cikin wata irin tsawa aka ce, "Kai biladama! Me ya kawo ku nan? Saleh ka gaggauta bacewa daga wurin nan, kar ka shigo shirginmu kar ka taSa ajiyar da aka ba mu, hakan zai zame maka haWari!"
Wani irin dogon tsaki Malam ya ja ya yi saurin mikewa, cikin bacin rai ya nufi dutsin gadan-gadan, sam ba ya tsoro ko War, ayoyin Alkur'ani mai girma kawai yake karantawa. Kai tsaye wurin ?waryar da ke ci da wuta ya je, sai da ya karanta ayoyin samun aminci sannan ya sa hannu ya dauki kwaryar ya watsar da ruwan da ke cikinta a ?asa ba tare da wata fargaba ba. Wani irin ihu da wasu kalar sautika suka gauraye wurin kamar ana yaki, ihun da ya tashi lokaci daya kuma ya tsaya cik tamkar an kashe shi da wata na ura gefe inda wutar ke ci ita ma ta mutu murus, ?waryar ya buga ?asa da iya ?arfin da Allah ya hore masa yana karanta sunan Allah. Fashewa ta yi ta koma Salli-Salli, Malam Saleh ya zuba mata ido yana kallon yadda take narkewa tana shigewa cikin ?asa.
"Ya Ilahi, ya Ar-hamarrahimina!" Ya faWa cikin mamaki da al'ajabi. Matsawa ya yi inda wutar ta mutu ko kadan bakinsa bai bar ambaton ayoyi da addu o in duk da ya san suna kare mutum daga sharrin jinnu ba, lekawa ya yi inda wutar ta mutu yana kallon yadda ta bar wani tafkeken rami. ?agowa ya yi saboda bai ga komai a ciki ba, juyawa ya yi don Waukar ?ayyabu su koma inda suka baro, sai dai jin wani kuka-kuka yana fitowa daga saitin ramin ya sa shi ya ci birki. 'Bismillahir Rahmanir Rahim,' ya faWa sannan ya juya cikin sanyi, le?awa ya yi cikin ramin, wani Kwado ne ya yi lamo yana wani wahalallen kuka, duka jikinsa an tsire shi da wasu kananun ?ayoyi, sannan duk inda gaSarsa take ta ?afafunsa na gaba da na baya an yi musu dauri da wani abu kamar zaren saka mai tauri, KwaWon sai kukan wahala yake. Sai da Malam Saleh ya yi addu'o'i sannan ya sa hannu ya dauko shi, ?uri ya yi yana karanta rubutun da ya yi arba da shi jikinshi, cikin kidima ya sake karanta abinda ke jikin nashi, da manyan baki aka rubuta LILBIRRAH. "Innalillahi wa inna ilaihi raji una," ya fada a matu?ar ruWewa, sosai hankalinshi ya tashi. Kamar daidai lokacin ake tsira ma KwaWon ?ayoyin, da sauri ya ajiye shi ?asa, fakainiyar barin duniya ya cigaba da yi, cikin Wan lokaci ya mace. Dur?usawa ya yi kan gwiwowinsa domin fiddo duk abinda ya gani a cikin ramin, wanda ya?ini tabbatacce ya dirar mashi a kan duk abinda ke wurin ya ta'alla?a da gudan jininshi wato Abu?alib.
Hannu ya sa ya jawo wata kwalba hade da wani abu da ke du?un?une cikin leda. "Ya Ilahy," abun da ya fada kenan lokacin da ya yi ido huWu da Wan mitsitsin ABUDALIB yana birgima cikin kwalbar yana magowa. "Ya Allahu, ya Allahu," ya cigaba da maimaitawa. Ji ya yi durkushin ya gagari gwiwarsa hakan ya sa ya zauna dirshan kan ?asa yana ambaton, "Ya hayyu ya kayyum," hannu ya sa ya bude kwalbar take iskar guguwa ta turni?e wurin gaba daya, cikin mintuna kuma ta Sace Satt tamkar ba a taba yin ta ba. Bayan iskan ya lafa ya sake duba kwalbar, amma babu komai cikinta Wan mitsitsin Abu?alib ya yi samarya tamkar ba yanzu yake cikin kwalbar ba. Sosai Malam Saleh ya firgita da ganin lamarin da kuma irin rashin tsoron Allah da aka yi cikinsa, shi kaWai yake surutunsa, "Wannan abun mummunan sihiri ne da aka hada da aljanu munana aka yi tabbas an zuba rashin imani, zuciya ta Saci zuciya ta Saci wallahi na fuskanci haka tun farko, sai dai ban taba tunani abun ya kai haka ba, duniya ina za ki damu..." Shuru ya yi ya koma karatun addu'o'inshi, warware ledar ya soma yi, sai dai wani sauti cikin mummunan amo ya fara yawo cikin kunnuwansa, "Ni ba na yafiya Malam Saleh kuma ba na afuwa, ga abinda aka ba ni ajiyarsa ni mai tsayuwa ce, bibiya da binbinina mai dawwama ne, idan ka ga na dai na tabbas na kar ne, taSa ni taSa su, ka taSa ni zan taSa su& " Shuru Malam ya yi tare da 'yar karamar razana, "Insha Allah sai na warware ko me ye a nan ko me zai faru kuwa, wa la haula wa la kuwwata illah billah."
Fara kwanta ledar ya yi daga gefe zuciyarsa na ?ara azalzalar ya ceci Wansa da kuma 'yaruwarsa daga bakin ?ullin da ya dabaibaye su ya ruguza dukkan rayuwarsu, dole ne ko me zai faru ya warware shi ko ba gargaWi ba, ko da an yi mashi fiye da haka, budewa ya fara yi yana jin jikinsa ya hau karkarwa, wani huci na fita ta cikin kansa. Wata irin zabura ya yi lokacin da abinda ya bayyana cikinta ya watsu wanda ya fi karfin abinda idonsa ya gane masa linkin ba linkin, dariya mai muni kuma ta gauraye wurin. Komai ya kwance ma Malam saleh Bismillah kawai yake maimaitawa. Wasu irin ?anana-?anan kanu ya gani, a sifa kanum na tantabaru ne amma kuma ?arantarsu bai fi a ce sifar wani babban ?waro ne ba. Bismillar ya ci gaba da yi, sosai ya cika da mamaki tamkar zai wuce da rayuwarsa domin jikin kowane kai sunan AbuDalib ne da wani daga cikin makusantansa, sunan Lilbirrah ne farko Malam Saleh ya fara arba da shi, ajiyewa ya yi ya dauki wani shi kuma sunan Ummansa ne, na gaba ya Wauka cikin mamakin da ya jike ilahirin ruhi da gangar jikinsa ya ga sunan shi a rubuce, Malam Saleh. "Kai subhanallahi, ya Allah!" ya fada yana jijjiga kansa. Gaba Waya sunayen mutane ne da bai san adadinsa su ba,wasu ya san su a abokan Abu?alib din, wasu kuma danginsa ne abinda ya shafi ?anne da yayunsa, "Kenan a nufinsu sun raba Abu?alib da duk na tare da shi har abada?" Sanin waye Abu?alib ya sa ya ji wasu hawaye sun tsarga jijiyoyin ganin shi sun lulluSe ?wayar idonsa. Dukawa ya sake yi wani kullin ya gani, yana jawo shi kafin ya daidaita zamansa ya ga dutsin ya Sace daga wurin tamkar ba a taba yinsa ba, wani abu mai kama da yayewar duhu ya yi afku a wurin. ?ara addu'a Malam Saleh ya yi sannan ya sa hannu ya bude ledar wani kalar rubutu ne da bai san da irinsa ba a duniya jikin takardar da ya gani, sunan Abudalib da Lilbirrah da na Ummansa kawai ya iya ganewa sauran wani yare ne da bai san da shi a duniyarmu ba. Ya daWe zaune a wurin cikin zallar mamaki da al ajabi, haWe da tsoron Allah da ya ?ara mamaye zuciyarsa. Wani marayan tari da ya shiga kunnenshi ya sa shi juyawa da Wan sauri, Dayyabu ya gani ya farfaWo da sauri Malam ya tashi ya ce, 'Dayyabu sannu, sannu ?ayyabu."
"Malam, kaina ciwo yake yi," ya fada a wahalce.
"Sannu, sannu, Insha Allah zai daina..." kama shi ya yi ya mikar da shi tsaye, a sanyaye ya ce," Malam ina iya tafiya."
"???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?To shi ke nan ?ayyabu." Juyawa Malam ya yi ya koma wajen tarkacen da ya gama gani, tattara su ya yi tas ya zuba a hularshi domin ya nunawa Umma da ta dauki zafi kamar ?arfen da ke cikin wutar ma?era, sai kuma Uwale tare da sauran zuri'arsu. Tare da Malam da Dayyabu suka koma cikin ainufin gonar, Malam har a lokacin sunayen Allah na bakinsa, bai daina ambata ba. Su ko yaran Malam sai bin su da idanuwa suke, Malam ya tattara su gaba Waya suka haye mota domin komawa gida, addu a kawai Malam yake har a lokacin ya gaza komawa ciki cikakkiyar nutsuwarshi haka mamaki ya ?i barin zuciyarsa.
Kai tsaye suna komawa gida shagon magani aka yi da Dayyabu, Wan gyaggyara mashi fuskarshi aka yi da ta ji rauni a dalilin buguwar da ya yi. Daga nan gida suka wuce, Malam yana shiga wanka ya yi da sallar la'asar da ta riske su suna gona. Jikinsa ya yi sanyi duk ya mutu, matarsa Sa'adatu sai tambayarsa take amma ya kasa ce mata komai, abincin da ta kawo masa ma ido ya zuba masa. Nisawa ya yi, a sanyaye ya kira wayar Rumaisa, cikin sa a ya same ta, bai ce mata komai ba sai yana neman Uwale ta zo akwai maganar da za su yi, idan da hali ta zo kafin gobe idan babu ta zo gobe da safe inda rai. Yana gama faWar sa?on ya kashe wayar, yana cigaba da tunani da mamaki da ya ?i barin ransa.

&&&

BADIYYAH

Zaune take cikin wani wurin shakatawa mai masifar kyau, duk kyawun wurin da kayatuwar shi amma ya kasa birge ta saboda damuwar da take daddale cikin ranta. Babu abinda ke mata ciwo a ?warya kamar yadda AbuDalib din ya ida koma mata cikin 'yan kwanakin da suke rayuwa a Vienna, wasu lokutan ta kasa gane kansa ta kasa fahimtarsa, ga tsabar shashashanci kamar ya rasa rabin hankalinsa ga kuma wani shuru da yake mata bayan maganar da suke jefi-jefi da ta ce ya zama kurma. Dogon tsaki ta ja wanda har ya ja hankalin wani saurayi da ke gefenta. Kallonta ya yi suka hada ido, daga mata gira ya yi, ba tare da neman izininta ba ya taso ya karaso inda take.
"Sannu beautiful Queen."
Ba ta amsa mashi ba sai wani kallo da ta watsa mashi, "Tun da kika zauna nan na ga alamun kina cikin damuwa, sannan ga alamu kina bukatar mai dauke maki kadaici, i'm sorry."
"Uhmm," kawai ta furta tana cigaba da kallonsa. "Babe ita duka duniyar nan babu abun takaici cikin ta da, duk wanda kika ga ranshi ya Saci to shi ya so, kuskure ne ka ta'alla?a farin cikinka a kan wani, ke ke da kanki saboda haka ki ji daWin rayuwarki Babe... Kina ji ko?" Jinjina masa kai ta yi, domin kuwa maganganunsa sun shige ta har sun mata tasiri.
"Ki taso kawai mu je ki huta," Plssss ya faWa tare da sa hannu ya sa ya jawo hannunta. Cikin ingizawar shaidan ta mike ta bi bayanshi. Wani ?ayataccen wuri suka isa cikin dandamalin shakatawar wanda ba ta ma san da shi ba, lemu ya sa aka ba su su duka biyun, "Ki sha wannan zai kauda maki ?uncin ranki, da damuwar da ke zuciyarki ina mai tabbatar maki Baby."
Karba ta yi ta ci gaba da sha, sai dai ta gama ta ji ta soma fita hayyacinta, dan dakewa ta yi can ta ce, "Ina cikin matsala Babe," ta fada tana fuskantarshi.
Kallon lebunanta da suke furta maganar yake, cikin muryarsa da ta fara canzawa ya ce, "Me ye matsalar?" Hannu ta sa ta rungume shi, dariya ya saki ya mikar da ita tsaye suka shige cikin wani daki, da ma abinda yake so kenan, don ya ga alamun sosai a kan wuta take, tana bu?atar agaji.
&
Kimanin awanninsu uku a dakin, a hankali ta bude idanuwanta, jinta jikin wani sankamemen ?ato ya sa ta yi saurin tashi zaune, juyawa ta yi gefe barci yake abinsa cikin kwanciyar hankali, ba?i ne sosai irin wanda ake ce ma ba?i wuluk, wuf Waya baka ce mashi mummuna amma kuma ba a saka shi layin masu kyau, kanshi ya sha wani aski mai kyau, fatar jikinsa kuma da gani ta ji hutu.
Haduwarsu ta yi saurin dawo mata cikin kawakwalwar kanta, "Kai!" Ta furta tana tafka mashi wani bugu a jiki. Bude idanuwansa ya yi da suke cike da barci, "My beautiful," ya faWa yana shafa gefen fuskarta, bige hannun ta yi cikin ?yan?yami ta yi niyyar tashi tsaye sai dai ganinta haihuwar uwarta ya sa ta komawa inda ta baro da sauri. Hawaye suka gangaro daga idanuwanta, "Me na yi maka da za kai min haka?"
"Haba ke kuwa kamar ba 'yar zamani ba..." ya ?are zancen yaja tashi zaune. "Kar ki wani damu, kin san wannan is common sam ba wani abu ba ne? Kuma me ye matsalar? Kin san ba abinda ba ki faWa min ba, game da damuwarki?"
"Kana nufin ka ji komai game da sirrina?"
Jinjina kai ya yi yana faWin tabbas. "Kuma ni ban ji komai ba, ma Wauki wannan haWuwar tamu a matsayin wata ?addara da za mu faranta ran junanmu, ke ba ki yi tunanin haka ba?" Shuru ta yi saboda wani tunani da ya shigo mata. "Yess, ki yi tunani, na ganki& ," du?awa ya yi ya furta mata wata magana cikin kunne. Gyara zamanta ta yi a hankali ta ce, "Ni matar aure ce, kuma kamar yadda na faWa maka Win Wazun Win, mijina ya samu matsala yanzu..." Rufe bakinta ya yi da tausasan hannuwansa, "Na ji komai fa, kuma bana son na sake jin komai." Jawota ya yi ya hada da jikinsa, cikin kunnenta yake fada mata wasu irin maganganu masu natsar da zuciyar mace, dago ta ya yi ya ce, "Kin amince da tarayyarmu?" Jinjina kai ta yi, "Na amince," fuskarta har da Wan murmumushi. Shafa kanta ya yi,"Na ji daWin yadda kika amince da wuri haka, ni sunana Nawwaz, haifaffen Kano ne ni, na zo nan jinyar Unlce dina but next week za mu koma Nigeria, saboda har na gama jinyar."
"Okay, ba damuwa, mu ma next week Win za mu tafi, kuma mun zo karSar award ne..." sai da ta labarta mashi abinda ya kawo su gaba Waya. Musanyar waya suka yi, cikin jin daWi Nawwaz ya sake fara romancing dinta, take ta biye mashi shi ko ko kadan bai sahirta mata ba wurin nuna mata wata kalar soyayya irin wacce ta yi kewa kuma take ?ulafuci. Sai da suka gama suka yi wanka a tare, sannan ta shirya ta koma masaukinsu sosai take jin ta cikin farin ciki da jin dadi.
Kwance ta iske AbuDalib yana ta aikin barci, kallon shi ta yi ta saki Wan siririn tsaki, domin kallonshi ma takaici yake ba ta, wayarshi da ke kan bedside lokcker ta dauka, kokarin bude key ta yi sai dai kuma ya sha banban da wanda ta sani kafin ta fita. Kamar ta fasa ihu, tsayin kwanaki sha hudu tana bi?in tura kudin daga asusun AbuDalib zuwa nata asusun abun ya gagara, sai ma wani kara son kudin masifa da ya yi bayan ya ida susucewa, ga taurin kai kamar ba shi ba, a da irin ra?umi da akalar da ya zamar mata da tuni ta tura kudaWen, sai dai duk ya sauya ya zama kamar wani tababbe, kowane dare ya yi gari ya waye da kalar da zai tashi da ita. Wayarta ta dauka ta kira Mom saboda ya ki taunuwa ya ki haduwa gareta, ya kuma ki tura mata kudadenta, dole a gaggauta Waukar mataki, sai dai daga gefe matar ta sanar mata wayar ba ta tafiya. Wani tsakin ta kuma ja ta jefar da wayar gefe, yadda ta samu wannan Man din ya mata daidai a soyayya, haWuwarsu a sa'o'i ?alilan ya gama mata komai, dole ta same shi ya zame mata mallaki, da ta watsar da Abu?alib sai ta rungume shi ta yi aure cikin kwanciyar hankali. Ajiye wayar ta yi ta koma ta zauna, "Abun dai gashi nan," ta fada a bayyane, "Shi ya zama wawa gaya nan ba aikin fari ba na baki ba hira ba labari, yo me zan ma da mutum haka? Tunda an ce ya koma haka kuma zai dawwama a hakan wallahi ba zan zauna da kai ba." Wayar ta dauka ta sa yatsansa ta fara kokarin saka thumb print sai dai kamar ta sa dutse wayar ko motsi ba ta yi ba. "Don Ubanka bara na fito maka a mutum, tashi ka tura mini kudi miliyan dari AbuDalib." Sam ko motsi bai yi ba, kara girgiza filon da kansa yake kai ta yi, "AbuDalib. AbuDalib."
Wata dun?ulewa da ya yi ya sa ta yin baya tana kalloshi, dunkulewa yake kamar wanda ciwon ciki ya turnike, zuba mai ido ta yi idan mutuwa ma za ka yi, "Allahumma sauki, abinda ka bari ni kadai zan ci in cinye." Kofa ta nufa tana "Bara na fice kada na yi mugun ji da mugun gani ma..." ihun da ya yi ya sa ta tsayawa cik, juyawa ta yi a dan tsorace tana kallonshi, zaro ido ta yi ganin ya mike ya sandare kamar icce, da sari kuma ya sake dunkulewa cigaba ya yi da magowa yana kiran hasbunallahu wa niimal wakilu, maimatawa yake ba adadi yana dunkulewa yana mikewa, wata juyawa ya yi ya fado daga kan gadon, ?asa ya faWa tim. Zabura ya koma yi kamar ana tsittsira mashi allurai, magowar da yake ta ?aru, yi yake tamkar wanda ciwon cikin ya yi ma mummunar kamu sai dai abun ya fi karfin haka, gaba daya Badiyyah abun ya girmi kwakwalwarta kallonshi take a tsorace, "AbuDalib," ta fada dan karfi ganin jini ya biyo ta hancinshi, "Wace irin mutuwa ce wannan?" Shuru ya yi kamar ba shi ke bige-bigen ba.
"Abu ?alib," ta ?ara faWa ?asa-?asa wani irin tashi ya yi zaune, sai dai ko idanuwansa bai buWe ba, "Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un," yake maimaitawa da ?arfin masifa.
"Kai Abu?alib!" Shuru ya yi jikinsa ya hau wata irin jijjiga, a slow yake faWin, "La haula wa la ?uwwata illah billah." ?ura mashi idanuwana ta yi, don ta ga wani abun ne daban da wanda take tsammani. BuWe idanuwansa ya yi yana kallonta, hawaye suke kwararowa daga cikinsu, kamar an mishi duka. Rufe idanun ya yi ya koma ya kwanta ?asa kan shimfiWaWWen kafet Win Wakin.
"Abu?alib..." Ta sake kiran shi, zuciyarta na WaWarniyar kar mugun ganin ne da ta guda ta yi. "Abu ?alib," ta sake faWa. Da wani irin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login