Showing 3001 words to 6000 words out of 55242 words

Chapter 2 - BA DON MACE BA BY FATIMA FANTAH.doc

Advertisement

22 Feb 2025

3653

biyun 'yan South Africa ne. A nutse suka fara abinda ya tara su a wurin. Bayan sun gama suka ?ara taya shi murnar zama babban trader na kasuwar Crypto a Nigeria. Bayan ma?udan kuWaWen da suka yi mashi albishir ya samu, wanda zai karSi shaidar girmamawa a babban taron da za a yi a Vienna da ke cikin ?asar Austria.
Sosai yake jin daWi yana farin ciki, tare da godiyarsa a gare su. Bayan sun ?ar?are wajen ?arfe takwas na dare ya koma masaukinsa. Wayarsa ya Wauka ya yi tsuru yana ta kallonta, ma'adanar ajiye lambobi ya shiga, ya daWe yana bin su Waya bayan Waya, sai dai ya rasa wa zai kira, wa zai sanarwa irin cigaban da ya samu a ranar yau, tabbas ya san yana cikin masu nasara a harkar sai dai, bai yi zaton shi ne zai zamo na Waya ba a kaff Najeriya, bayan tsabar kuWi dala dubu Wari biyar da ya samu, lambar girmamawa, sabuwar mota wacce ake ya yi, da Waukar nauyin yawon sha?atawa na tsawon kwana talatin shi da iyalansa, haWe da wasu kyautukan da bai san nawa zai samu ba, tabbas abin farin ciki ne. Wa ya kamata ya faWawa wannan babban abun albishir? Shuru ya yi, tamkar an shafe tunaninsa ya kasa tuna kowa, dogon tsaki ya ja tare da ajiye wayar gefensa.

"La, la, la, la. Phoolo ka taro ka..." Wayarsa ta Wauki ringing. Juyawa ya yi inda take kamar zai Salla wuyansa. Cigaba wa?ar ta yi cikin zazza?ar muryar Lata Mangeshkar. "Shona." Shi ne sunan da yake yawo a screen Win wayar. Zuciyarsa ta hau bugawa, wa?ar da ta daki dodon kunnensa ta wargaza ragowwar sukunin sa, sam ba shi da nutsuwa idan ba ya canza 'ringing' Win wayar ba. Tsaki ya ja har wayar ta tsinke bai Waga ba, hannunsa na rawa, ya yi saurin shiga sashen ringing Win wayarsa ya cire daddaWar wa?ar ya bar asalin kiWan wayar SAMSUNG Z-Fold latest version.
Wani kiran ya sake shigowa, cikin nuna ?auna ya Waga kiran. "My Shona. Kin manta da ni, bayan kin san ke kaWaice nutsuwata."
Daga gefe ta saki murmushi, "My boo... Ko ina manta kowa ba zan taSa mantawa da kai ba. Ka sani kai kaWai ne rayuwata farin cikina."
?an gajeran murmushi ya saki, "Shona, i'm in dilemma, baki Waya na kasa gane me ye ke damuna, sai in ri?a jin wasu maganganu har da motsi ma. I don know what's wrong with me..."
Shuru ta yi kamar tana nazarin wani abu, "Kin ji Shona." Ya faWa kamar ?aramin yaron da ke gaban Mamanshi.
"Sorry, Bubuna, ba gobe za ka dawo ba, idan ka dawo sai mu je hospital."
"Shi ke nan to. Kina lafiya."
"Lafiya nake."
"Ka ci abinci?"
"A'ah, ban ci ba."
"To ka sa a kawo maka yanzu."
"Okay Shona, ki kula min da kanki sai na dawo."
"Okay, Sweetheart, idan ka gama cin abincin sai ka kira ni."
"Okay." Ya faWa yana kashe wayar. Du?ar da kansa ya yi. A hankali ya mi?e ya kira wayar tarho. Mintuna kaWan a ka kawo masa abinci.
?an tsakura ya yi, sam ji ya yi ba ya da sha'awar abincin. Lemo ya Waga ya shanye gaba Waya. Jefar da kwalbar ya yi sannan ya Waga ruwa su ma ya shanye. Ba tare da ya wanke ko bakinsa ba ya zame kan kujerar.
"Yin sallah cikin lokaci yana kawo farin ciki, Joo..." DaWe kunnuwansa ya yi jin abinda ke hargitsa ?wa?walwarshi sun cika farantan kunnuwansa. Sai da ya ji guntuwar nutsuwa ta dirar mashi sannan ya sauke hannunwanshi.
Shuru ya yi, "Haka ne fa... Ban yi sallar azahar ba, ban yi ta la'asar ba, yanzu kuma ga Magrib da Isha." Tamkar ya mi?e ya yi sallarsa, sai kuma ya gyara kwanciya. "Na haWa in yi duka idan na tashi ?iyamul-lail." Ya faWa tare da juyawa ya yi kwanciyarsa, bai jima ba barci ya Wauke shi.

&

A nutse yake tu?i, gefensa dattijuwar mace ce tana amsa waya. "Mama." Ya faWa lokacin da ya ga ta ajiye wayar.
"Na'am, Wan Mama ya aka yi ne?" Ta ba shi amsa tana mayar da dukkan hankalinta kansa.
"Yau na ga abinda ya dame ni ne."
"Me ka gani Yunus Wina?"
"?azu da safe na ga wata mata nan wajen Ipaja cikin masu barar nan, Mama matar fa she is pregnant and she is too young, it's not free Mama, ?aramar yarinya kamar wannan tana bara."
KaWa kai ta yi cikin damuwa ta ce, "Abin da ciwo kam, ?ananan yara da mata su ne cike da tituna da kasuwanni suna bara a yanzu. It's very unfortunately."
"Mama, ni ta tsaya min a rai, yarinya ce fa, wannan na tabbata ba ta fi 25years ba, ina mijinta? Ina iyayenta? Da 'yanuwa da danginta?"
"Allah kaWai ya sani Yunus. Allah ya sau?e ya sa kuma ba irin masu Wauko ma iyayensu magana ba ne, su kuma iyayen su kasa ha?uri su kore su."
"Masu Wauko ma iyayensu magana Mama? Kamar yaya kenan?" Ya tambaya cikin al'ajabi.
Murmushi ta sakar masa, "Yunus ina nufin masu Waukar ciki ba ta hanyar aure ba, masu haihuwar Wan gaba da fatiha, da yawa iyayensu ba sa jurewa sai su kore su."
KaWa kai ya yi cikin tsananin damuwa, "Amma ko haka ne sam bai kamata ba. Kuma..."
"Mene ne Yunus?"
"Na ga kamar tana cikin yanayin damuwa wannan, an ya lamarinta zai zama kamar haka kuwa?"
"Oho dai, ni ban sani ba." Ta faWa tana sakin zancen.
Tu?i ya ci gaba da yi zuciyarsa cike da tunani kala daban-daban a kan matashiyar matar da ya gani.

&

Zaune nake kan tabarmata. "Barka da yammaci abun ?auna." Na ayyana a raina ina shafa cikina. Murmushi na saki, tamkar ya maido min amsar gaisuwar da na masa. "Abun ?auna, ka yi mana addu'a ka san addu'ar ?ananun yara tana karSuwa, musamman ma jariri mai ?aunar Amminsa kamar ka. Abun ?auna wahala ba ta da daWi, rayuwa cikin aminci ta fi komai zama ma fi soyuwa a gun kowa."
Sauke hannun na yi na dafa shi ?asa, hawaye suka cika kwarmin idanuwana, zuciyata cike take da fargaba da tsoron ?arasa faWuwar rana, domin duhun dare yana zo min tattare da masifar da take barazanar katse igiyoyin rayuwata a duk ya yin da ta sakko mini. Fatan kowane mai rai mutuwa ta zama hutu a gare shi, haka shi ne fatana a kowane ta?i da tunaninta ya zo min cikin raina, sai dai soyayyar abun ?aunata, ya sa ina tsoron zuwanta gare ni a kowane lokaci. "Ya Allah, ka ba ni dama da ikon haifar abinda ke cikina." Na ambata cikin ?irjina. Addu'o'i na fara jerawa cikin raina, sosai nake cikin tsoron abinda ke zo mini, wanda yake saka mani yanke ?auna ga cigaba da rayuwa a kowane lokacin da ya zo mini.
Jin an fara kiraye-kirayen sallar Magrib ya sa na mi?e da ?yar na yo alwala. Sallar na gabatar saboda raunin da jikina ya yi na mi?e na gabatar da sallar Isha'.
"Ko na yi kwanciyata ma kawai, wata?il na kaucewa abinda ke kawo mani farmaki cikin daren nan." Zuciyata ta ayyana mani.
Jinjina kai na yi alamun na amince da shawarar zuciyata, Wan mayafi na sa na kakkaSe shimfiWar na kwanta.
Addu'o'in kwanciya barci na yi na shafe jikina da abun ?aunata.


SH 3

Kamar koyaushe tsira mai kama da ta allurai na fara ji tana ratsa cikin jikina, yun?urin tashi na yi daga kwancen da nake, sai dai ji na yi kamar an danne ni da tuli-tulin yashi na kasa motsawa ko in da can, hawaye suka fara taruwa a kwarmin idanuwana, domin halin da nake shiga yana jijjigani a duk lokacin da na kasance cikinsa, ba ni da abun yi sai sunayen Ubangiji nake ta ambato a ?asan raina.
Cikin wani sauti na ji tashin wata addu'a na ratsa kunnuwana, "Allahu ya Allahu, Rahmanu ya Rahmanu, Rahimu ya Rahimu, ya Rabbal Arbabi, wa ya Ilahal Ilahati, wa ya Malikul Malakuti Wa ya Sayyidis Sadati najjini min sharri ma ahammani." ?aga kaina na yi na kalli matar da ke rera addu'ar cikin muryarta da firgicin da nake ciki bai hana ni tantance daWinta ba. Jinjina mini kai ta yi tana cigaba da maimaita addu'ar, tsura ma bakinta idanuwa na yi alamun ina son in yi, da hannu ta yi mini nuni da na yi abinda na yi niyya, mu yi addu'ar tare. KaWa mata kai na yi alamun ba na magana. Sam ba ta damu da abinda na nusar da ita ba, ta ?ara yi mini nuni da na bi ta mu yi addu'ar tare. Hawaye suka gangaro mini saboda azabar da nake ji tana ?aruwa cikin jikina, Waga kai na yi na sake kallon matar da har a lokacin ba ta bar abinda take ba sai ma ?ara ?aimi da take yi. Kallon bakinta nake yi da umarnin da take ba ni, cikin azama da ?o?ari irin na mai neman mafita na yun?ura domin bin ta kamar yadda take yi mini nuni, bakina na fara motsawa cikin sa a na ji na fara kamo addu'ar, sake ?o?arin bin ta na yi, a hankali na ji ina maimaita abinda take faWa, cikin 'yan da?i?u bakina ya kama addu'ar raWam kamar na daWe da saninta. Sannu-sannu na ji tsirar da ke yawo cikin jikina ta soma raguwa, nauyin da nake ji ya danne ha?ar?arina ya kau tamkar cirar ?aya. Zufa ta fara karyo mini ta kowace hudar gashin jikina, lokaci bayan lokaci ina sauke nannauyar ajiyar zuciya.
Firgigi na farka daga barcin da nake yi, zuciyata na harbawa da Wan sauri tare da bitar addu'ar da na yi mafarkin ina yi cikin raina. Da sauri na mi?e zaune hannu na sa na fara karkaWa fitilata da haskenta ya dishe. Numfashi nake maida wa har a lokacin, kai na haWe da gwiwa ina bitar mafarkina. Hawaye suka gangaro mini domin a yau na tsira daga sharrin abinda ke cutar da ni a cikin dare a lokuta mabanbanta.
Maimakon na koma barci mi?ewa na yi ba Wauko jikkata mai Wauke da biro da littafi a cikinta, zama na yi na rubuta addu ar, zuciyata cike da fatan wannan addu ar ta zama silar yayewar kuncina, tare da maganin abinda ke damuna.
&
Kwana biyu tun da na lazimci karanta addu ar ban sake fuskantar matsalar da nake fama da ita a cikin dare ba. Yau ta kasance ba ni da ko sisi hakan ya sa na shirya tun da safe domin isa Ipaja na barato abinda zan sa ma cikina. A hankali nake tafiya cikin nutsuwata, wata mota na ga tana tunkaro babban layin da nake tafiya a kai, kokarin ba motar hanya na yi sai dai gani na yi tana tsayawa daidai inda nake, Wan dakatawa na yi ina bin motar da idanuwana.
Gani na yi mamallakin motar ya soma sauke gilashinta, zuba masa ido na yi zuciyata cike da tsammanin ko yana tambayar wani wuri ne duk da na kasance ba mai dogon zama ba a unguwar, wata?il ko da taimakon da zan iya masa da yarena wanda kowa ke ji.
Kallon fuskarsa na yi, ban manta ta ba, ban mance tsayayyun idanuwansa da suka kafe ni da tuhuma kwanaki biyu rak da suka shuWe.
Zuciyata ta buga da ?arfi, hakan ya sa ni yin taku da sauri domin guje ma tuhumarsa irin ta waccen ranar wadda nake tsammanin ita ta kawo shi. "Hey!" Ya faWa. Ban tsaya sauraren shi ba cikin azama na ?ara saurin tafiyata.
"Baiwar Allah...!" Na ji ya ?ara faWa.
?arar rufe ?ofar motarsa na ji alamun ya baro cikinta kenan.
"Baiwar Allah na san dai ke musulma ce , don girman Allahn da ya halicce ki ki tsaya."
Cikk, na yi ina sauraren mai zai faWa kuma. Da sauri ya sha gabana, "Baiwar Allah, don Allah ki tsaya ina son magana da ke." Kada masa kai na yi alamun ba na iya magana.
Fuskarsa da bayyanannen tausayi ya furta, "Ya salam! Ba kya magana?" Daga kai na yi alamun eh.
"Okay. Alamu na nuna ke ba 'yar nan ba ce, domin kalarki da tsarinki bai yi kama da na wanda suke rayuwa a nan ba. Na tabbata akwai boyayyen labari a tattare da rayuwarki, kina bu?atar..."
Juyawa na yi na cigaba da tafiya, "Baiwar Allah don Allah kar ki tafi ki tsaya mu yi magana, ki tsaya don Allah na ce." Sake tsayawa na yi, da saurinsa ya dawo gabana, "Ni sunana Yunus, tun da na gan ki zuciyata ta yi amanna akwai wani abu tattare da ke, na tabbata kina bukatar taimako. Ba taimaka miki zan yi ba, na za ki taimaka ki nuna mini gidan da kike domin na yi abinda ya hau kaina." Kada kai na yi alamun ba na bukata. Wani murmushi ya saki mai nuna taurin kaina ya gundire shi. Baya ya yi ya shiga wani kutumbutsattsen shago, "Don Allah ina ne gidan wannan matar?"
Kunnuwana suka zu?o mini tambayar da yake yi ma mai shagon. "Nan kawai nake ganinta tana wucewa..."
Iya abinda na ji mai shagon ya ba shi amsa, yayin da na fara nisa da inda suke.
Jim kaWan har na kusa ficewa daga layin na ji ?arar motarsa bayana. Fakin ya yi ya fito ya zo inda nake, kudi ya dauko ya miko mani masu yawa. Tabbas na ji dadin kyautar kuWin har tsakiyar raina. Sai dai ban nuna masa a zahiri ba, na yi saurin girgiza kaina alamun ya bar shi.
Ajiye su ya yi a gabana, "Gasu nan Malam, ko ki ri?e su ko ki bar su, a nan duk Waya. Ni ba zan fasa abinda na yi niyyah ba." Yana faWar haka ya juya ya tafi alamun ya fusata. Tsaye na yi sororo ina kallon kuWin, a kowace rana ina neman taimakon Ubangiji, safe, rana, dare da kowane marece. "Fiii!" ?arar iskar wucewar motarshi ya katse min tunanina.
Bin motar na yi da ido, na du?a a sanyaye na Wauki kuWin. Maimakon na tafi bara, baya na yi na koma gida, domin Allah ya hutar da ni.

& &
&
Kwana uku curr da dawowarsa daga Kano, amma sam ba ya jin dadin rayuwarsa, haka nan yake jinsa cikin yanayi na ?unci da ba?in ciki, ga maganganun da kunnuwansa ke jiyo masa suna neman su zarar da shi.
Cikin sanyi ya fito daga Wakin baccinsa a shirye, kicibus suka yi da ita a bakin ?ofa.
"My boo," ta fada tana kamo hannunsa. Sororo ya yi yana kallonta, "Ni bana son ina ganinka cikin damuwar nan, za ka samu lafiya fa, mun yi magana da Doctor Win, yanzu haka yana can yana jiran mu."
Kallonta yake yi kamar sabuwar halittah, ba tare da ya furta komai ba. "Mu je asibitin ka ji My Bubuna."
Shiga gaba ta yi ya bi bayanta, a nutse suke tafiya har suka isa inda ma'ajiyar motoci take. Ba don ya so ba ya shiga motar don yi tu?i zuwa asibitin, har suka isa asibitin ta masu saukin hankali bai tanka mata ba. Wuri ya samu ya yi fakin, kai tsaye wurin likitan mai suna, Doctor Bashar suka isa.
Masauki likitan ya ba su suka zauna, cikin mutuntawa da girmama juna suka gaisa. Kallon Abu?alib ya yi, sai da ya gama ?are masa kallo tsaf, sannan ya fara masa wasu tambayoyi. Cikin muryarsa da ba ta cika kaifi ba ya ce, "Doctor, ni dai ba abinda ya same ni, amma wasu lokutan sai in rika jin wasu maganganu, idan na ji su kuma sai in ji suna ta min yawo a cikin kwakwalwa kamar na taba saninsu, sannan kuma wasu lokutan ina jin kaman na san wasu mutane amma kuma na gaza sanin su waye. Sai kuma ina ji kamar na aikata wani laifi, zuciyata ta yi ta ayyana mini idan na mutu daidai wannan lokacin wuta za a sanya ni. Doctor na ruWe na rikice, cikin kwanakin da ba su na mako ba, ina nema na haukace..."
Jinjina kai Doctor ya yi. "Okay, amma ba abinda ya faru da rayuwarka?" Badiyyah da ke gefensa ta yi karaf ta ce, "Ba abinda ya faru da rayuwarsa Doctor, lafiya lau yake, a kwanakin nan abun ya same shi."
Jinjina kai Likita Bashar ya yi, sannan ya yi wasu 'yan rubuce-rubuce ya mika ma Badiyya takardar.
"Ki je nan clinic dinmu ki siyo wadannan magungunan."
"Okay Doctor," ta fada. Jikinta na rawa ta fita waje. Tsayawa ta yi tana kallon takardar, sam ba ta fahimci komai ba game da magungunan da aka rubuta. ?an gajeran tsaki ta ja sannan ta jawo wayarta. Juyawa ta yi gefe-gefenta ta tabbar ba kowa a wurin sannan ta danna kira. Cikin 'yan sakanni aka Wauki wayar, "Mom, akwai matsala fa. Kamar yadda na fada maki, AbuDalib ya zama wani soko-soko haka, kansa kamar yana nema ya kwance, sai kokarin tuno wadannan mutanen yake yi. A tsorace nake, kar ya koma hayyacinsa mu shiga uku, domin duka damarmakin da muka samu za su ruguje."
Numfashi uwar ta ja, "Ai kin san hada abu dama da 'ya'yan malaman zaure akwai wahala, amma ki rabu da shi, kar ki damu ko kadan, komai zai daidaita."
"To Mom, amma fa dole sai an yi gaggawa."
"Na ce kar ki damu. Kina ji na, yanzu ki siyo maganin in sha zai yi ki ba shi ya sha, in ci zai yi ma dai haka, ke ko ma dai me zai yi ki masa. Zan warware matsalar nan da kwana biyu."
"Okay Mom. Amma na ce, Baba Alhaji na nan?"
"Yana nan."
"To ya same mu nan asibitin, don kin san magungunan sakatiri (Psychiatry) barci suke sa wa, kar ya yi barci kuma kin san ban kware a tuki ba na rasa yadda zan da shi.
"Bari gaya nan zuwa, yanzu nan zai taho," kashe wayar ta yi gaggauce ta isa clinic din.
Takardar ta mika, take suka ba ta wasu allurai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login