Showing 45001 words to 48000 words out of 55242 words

Chapter 16 - BA DON MACE BA BY FATIMA FANTAH.doc

Advertisement

22 Feb 2025

3650

Inna Uwale za su tafi."
"Ba komai, kawai ki je za mu yi waya."
"Okay," na fada sannan na fice daga dakin. Yadda muka je gidansu Badiyyah haka muka koma gida, ko naira biyar ba su ba mu ba da sunan tukwici.
Ba mu mayar da hankali ba kan abun mun bar shi a gajiyawa da kasawa ta dan adam. Bayan azumin ya kama mun yi mun gama, ana cikin shagalin bukukuwan Sallah Yaya ya ce, les Win da ya yi mana kala Waya, za mu saka mu raka shi gidan abokansa ni da Badiyyah da wasu cikin danginmu su ganta.
Tsaff na shirya cikin kayan ba tare da wani tunani ba, ni da Yaya muka iske Badiyyah domin a motar abokinsa za mu tafi. Muna zaune a mota muna labari Badiyya ta fito, fuskarta sake take sai dai muna hada ido fuskar ta sauya tamkar na aika mata da sakon mutuwa. "Matar Yaya, wani ya mare ki ba ki rama ba?" Na fada da sigar tsokana.
Gefe ta kalla ba tare da ta samu fursar amsa min ba, Yaya AbuDalib ya fito yana faWin, "Gimbiyar... Wa ya taSa mani ke?" Bata amsa ba sai huci da take faman yi. "Shi ke nan tunda ba za a amsa min ba, ki shiga mota na san kya faWa min." Muryarta da alamun bacin rai ya gama cika ta ta ce, "To a ina zan zauna?" Fitowa na yi daga motar da sauri, "Badiyyah ga wurinki mana, ka gani Yaya shi ya sa tun a gida na ce zan zauna a baya ka ki ga shi nan an batawa Antyna rai."
Ba ta ce komai ba sai faman kallon gefe da take yi. Yaya ya ce, "To ki shiga mana tunda ta ba ki wuri."
Shiga ta yi tana kallona, da yadda kayan suka karSe ni, duk da ina baka kirin na fi Badiyya kyau nesa ba kusa ba, yayin da muka banbanta a dirin jiki saboda ita tana da tsayi ba sosai ba yayin da ni kuma nake da cikakken tsawo da madaidaicin jiki. Badiyya ta ce, "Ashe da muka yi ankon kayan har da dinki ma?" Yaya ya juya ya kalle ta, "To laifi ne Badiyyah, Winkin nan ni da kaina na zauna na yi shi, ban bawa kowa ya yi muku ba, ko bai yi ba?"
"Uhmm!" Kawai ta ce ta juya ta kalli gefen titi. Har muka isa kamar kurame ba wanda ya tanka ma wani, ni ko na mayar da hankalina kan waya ina bincike kan karatuna da ?ara na?altar na'ura mai ?wa?walwa. Gidan abokin Yaya AbdulJalal muka fara zuwa, a cikin abokansa shi ne shakikin amininsa tuni na dade da sanin matarsa wacce da mu aka yi hidimar aurenta, muna isa yadda Badiyyah ta ga mun san juna abin ya bata mata rai sosai. Sauran gidajen muka je, ma fi yawa sun san ni, cikin murna suke karSarmu, amma dalilin yanayin Sacin rai da Badiyya take nunawa ya sa suka fi mayar da hankali kaina.
Gidan wani abokin Yaya muka je karshe, muna fitowa Joonam ya ce, "Daga nan sai gida kuma." Jakata na buWe na fiddo kuWin da aka ba ta, "Ga shi Badiyyah," na ?are zancen ina mi?a mata. KarSa ta yi tana ta kumburi ta buWe jaka ta zuba su.
?an ?aramin tsaki ya ja, "Ki ?irga mana ki ga nawa ne, sai ki Wauki rabi ki bata rabi."
Tamkar ya watsa mata wuta haka ta yi, cikin zafin rai ta fiddo duka kuWin ta watso min, "Abu?alib da ma ka taho da ?anwarka ne don ka wula?anta ni ka nuna min iyakata, ka ce na shirya za ka kai ni gun family Winka da abokanka amma sai ka tane da tahowa da ita, abun takaici ga anko iri Waya, idan an je ma ita ka fi nunawa saboda ka nuna musu ta fi ni muhimmanci wurinka, a karshe ma kudin da aka bayar saboda ni su ma sai an raba to ta Wauka ni naira ba na bu?ata ciki."
Tamkar ruwa ya ci ni na yi shuru a bayan motar, yadda ta watsa mini kuWin na kasa ko taSa su. Cikin tsananin Sacin rai Yaya ya ce, "An zo wurin, da ma ai tun da muka fito na ga walwalarki ta kau saboda kin ganta, na ji duk abinda kika faWi ba ni da bu?atar sharhi, kuWi kuma kan ki kika yi ma wa don na san kina da bu?atarsu fiye da ita."
"Uhmm, ka yi min gori sai me?"
Da sauri na ce, "Don Allah ku yi ha?uri, duk laifina ne, sam ban kyauta ba da na biyo ku. Badiyyah ki yi ha?uri wallahi Yaya shi ne ya ce na shirya na raka ku, din ya san ba za ki ji daWi ke kaWai ba." Dogon tsakin da ta ja ya tabbatar min da ba ta ma san ina yi ba. Shuru na yi, tuni zuciyata ta kariya, haka suka cigaba da musayar yawu ita da Yaya yana faWa tana faWa, a karshe dai baram-baram muka rabu. Sosai ran Yaya ya baci, a fusace ya ajiye ta a ?ofar gidansu. Yana yana ta ba ni ha?uri, ni kuwa zuciyata ta zo ma?oshi, kuka kawai nake son yi, muna isa na fita daga motar na shige cikin gida, tun daga bakin ?ofa na fashe da kuma Umma tana ta tambayar lafiya. Duk yadda muka yi da Badiyyah na fada mata cikin kuma, domin ko a tsammani ban taSa tunanin Badiyyah za ta yi min haka ba. Cikin jinjina lamarin ta ce, "Ikon Allah ita kuma haka take? To me ye damuwar don AbuDalib ya hada ku ya je da ku unguwa tare? A tunanina ai bayan auren ke ce za ki mata ido ciki family din." Umma na magana Yaya ya shigo a fusace, "Khouhar ki yi hakuri ki daina kukan nan, ki yi hakuri ki daina zubar da hawaye na ce. Ki kwantar da hankalinki wallahi daga yau na rabu da waccen yarinyar, ta je ta auri wani wanda ba shi da ?anwa ko wanda za ta juya shi yadda take so, amma ni ba za ta sa na yi abinda ban yi niyya ba, ta je Allah ya haWa kowa da rabonsa."
Da sauri na dago daga jikin Umma, "A'ah Yaya kar ka yi haka don Allah, na san bacin rai ne da zafin kishi kuma dama Badiyya tana da kishi tun muna makaranta in tana son abu ba ta son a rabe shi, ko ni ma sai da na rabu da dukkan ?awayena sai ita sannan ta samu natsuwa."
"Nagode ma Allah da ba ki iya ?arya ba, kin ga tun yanzu ta nuna za ta iya raba ni da 'yanuwana saboda kar na raSi kowa. Ba ta isa ba wallahi, ta je ta auri wani amma ni na gama da lamarinta babu ni babu ita."
"Yaya don Allah..."
A fusace ya buWe ?ofa ya fice faga gidan, faWawa na yi jikin Umma na saki sabon kuka domin sam bana so a ce abinda na haWa kuma na zama silar rabuwar shi.
Umma ta shafa kaina ta ce, "Ki bar kuka komai zai daidaita su duka Sacin rai ne ya jawo musu hakan, amma da sun sauko za ki ga komai ya koma yadda yake."
"Toh Ummana," na faWa ina goge hawaye na. ?aki muka shige ni da Umma, yayin da na rage kayan jikina na faWa toilet na yi wanka. Ina fitowa kasantuwar magrib ta kawo jiki, alwala na yi na zauna na fara karatun Alkur'ani mai girma, a hankali na ji zuciyata na sanyi, na yi kimanin wanda ya kai izif Waya aka fara sallar Magriba. Mi?ewa na yi na gabatar da sallar, ina gamawa na yi azkar, sannan na yi sallar Isha. Daga inda nake zaune barci ya yi nasarar sace ni, lokacin da na farka dare ya fara yi hakan ya sa na mi?e na cire kayan sallar na haye gado na kwanta. A ranar ko abinci ban iya ci ba saboda damuwar da ta lullube zuciyata yadda Badiyyah da Joonam Wina suka samu matsala a dalilina.


SH 18

Ta janibin Badiyyah kuwa, tana komawa gida ta kwashe duk abinda ya faru tsakanin ta da Lilbirran da Abu?alib ta faWawa Mamanta. Shuru Maman ta yi, "Ke ko Badiyyah ina ganinki da wayo ashe sakarya ce."
Cikin fushi da ?unad zuciya ta ce, "Haba Mama, haba Mama, ba ki ji yadda zuciyata ke zafi a kan ?anwar nan tasa ba, Mama har ji nake na tsani Lilbirrah, na tsane ta, saboda ta yi Ka-ka-gida cikin zuciyar mutumin da nake mafarkin zai zama mijina, Mama ko rabin son da yake mata baya min, ta ya ba zan ji haushinta ba, na tabbata a yadda yake kaunarta da ba kanwarsa ba ce har aurenta sai ya yi haba Mama," ta ?are maganar tana shirin kuka.
"Haba mana Wiyata, duk abinda kike fadi na san shi kuma ina ganinsa ina tsammaninsa, kuma duk abinda kike ji nima ina jin kwatankwacinsa. Amma kuma wannan hanyar da kika bi ai ba mai Sullewa ba ce, fushin da kika yi sai ya sa ki biyu babu. Shi ko wannan AbuDalib din tamkar lu'ulu'u ne a cikin ruwa sai kin tona kin tona kin sannan ki samu. Ina nufin sai kin yi tuna, tuna mai tsanani sannan ki samu kamar shi a cikin maza, saboda haka ko da wasa ka da ki kuskura ki asarar shi."
"To Mama, wannan abun zai iya sa wa na yi asarar shi?"
"Ka ji ki, shiyasa na ce sam ba ki da wayo. Ba ke kika ba ni labari a taron ?arin shekararta da kike je yana faWar ko matarsa idan ba ta sonta zai iya rabuwa da ita?"
"Haka ne Mama, amma ni na Wauka sha-ci-faWin zance ne ya yi a gun."
"Kayyasa! To da gaske yake, ke ce dai sam ba ki da tunani. Zai iya rabuwa da ke saboda ita, yanzu haka ma kar ki Webe tsammanin ya yanke hukuncin haka."
"Don Allah ki bar wannan maganar Mama."
"Ba zan bar ta ba saboda bana son ki rasa shi, don kika rasa shi ba ke kaWai ba har ni kin yi wa asara. Abinda nake so ki sani, ba haka za ki yi ba."
Shuru ta yi irin na mai nazari, "To Mama ya zan yi?"
Nisawa uwar ta yi, "Abinda za ki yi shi ne ki bi shi ta ruwan sanyi yadda za ki mallaki zuciyarsa ki bi shi a hankali har ki mamaye ?o?on ransa, wani faWan ba gaba da gaba ake yin shi ba, sai an bi ta ya?in sun?uru."
"Mama ai ina bin sa a hankali, kuma ina nuna masa ?auna da kulawa."
"Ba haka nake nufi ba, za ki mallaki zuciyarsa ta hanyar ?anwar tasa, ki nuna kina sonta kina ?aunarta, kar ki yarda ki ?ara nuna mata abu mai kama da wanda kika nuna mata yau Winnan, idan kika yi haka har ya yarda da ke, sai mu nemi hanyar da za mu yi maganin ta, don ba zan zauna kina auren miji wata ba?ar ?anwarsa ita ce a zuciyarsa, ba laifi ya so ta, amma kar son ya wuce na yau da kullum na al'ada."
"Mama to ya zan yi maganinta, kina gani akwai wata ziga ko zancen iska da zai sa AbuDalib ya juya ma Lilbirrah baya?"
"A a ta ya zai juya mata baya, da kamar wuya wannan, ke dai ki abinda na ce za ki ga yadda za a yi maganin nata."
"Shi ke nan Mama." Badiyyah ta faWa.
"Yawwa, wannan matakin da kika dauka kar ki zato ko tsammanin biyo ki za ya yi, wallahi zai iya kyale ki har abada duk da ba zan lamunci hakan ba."
"To Mama yanzu ya zan yi don Allah? Kar fa a ce ya kyale ni din, don na kira wayarsa kin gani bai dauka ba bai kuma biyo kiran ba."
"Kara kira mu gani, da ya Wauka sai ki ba shi ha?iri."
"To Mama, bara na sake kira mu gani." Hannunta har rawa yake wajen kiran AbuDalib, sai dai kiransa take amma ko kadan bai dauka ba, kuma babu alamar zai Wauka. Hankalinta ba ?aramin tashi ya yi ba, a Wan firgice ta ce, "Mama kin gani bai Wauka ba fa."
"Ba shi rata daga yau zuwa gobe mu gani," Maman ta faWa tana sha?ar iska. Har aka kwana aka yini aka sake kwana Abu?alib bai dauki wayar Badiyyah ba, sannan duk irin tarin messages na ban hakuri da take yi masa bai amsa ba.
Wani murmushi Maman Badiyyar ta yi, dafa Badiyyah ta yi wacce ta zuba tagumi hawaye na bin fuskarta, 'Ki kwantar da hankalinki dole ne sai kin auri Abu?alib tunda har Allah ya kawo shi to fa ya zo hannu. Yanzu kafin na fara Waukar mataki, kira wayar Lilbirrar, kin san shashasha ce, kina yin kalar tausayi za ta karSe ki."
"Shi ke nan bara na tura mata sa?on ban ha?uri, na san da ta gani za ta kira."

&&&

Ina zaune da safe ina shirin tafiya makaranta na ji ?arar shigowar sa?on karta kwana cikin wayata, a ta shigo wayata.
"Lilbirrah, na sani har abada ba zan samu mutum mai ?aunata kamar ki ba, wacce babu ala?a ko ta jini amma ya nuna min soyayya irinki. Shekaran jiya na tafka miki babban kuskure ki taimaka ki yafe mini tabbas ban kyauta ba, amma na gane kuskurena ki yafe min Lilbirrata, ki yafe ma amincinki."
Na karanta sa?on ya kai sau uku, kafin na yi reply kiran wayar Badiyyah ya shigo. ?agawa na yi cikin damuwa kafin na ce wani abu na ji ta ce, "Lilbirrahta!" Kafin ta yi wata magana ta fashe da kuka, wani irin tausayinta ya kama ni, cikin muryar kuka ta fara magana, "Lilbirrah don Allah ki yi hakuri, kan abinda ya faru wallahi sharrin shaidan ne, na yi nadama kuma ba zan sake aikata hakan ba, don Allah ki yi ha?uri..."
Hakan da ta fada ya sa na ji zuciyata ta karaya har ni ma ina shirin yin kuka, "Badiyyah wallahi babu komai ya wuce, ni dama ban ri?e ki a zuciyata ba, na san ba halinki ba ne kawai zafin soyayyah ne da kishi irin namu na mata."
"Da ma na san za ki fahimce ni, ki yafe min ina ?ara ro?onki."
"Wallahi na yafe miki, Allah ya yafe mana gaba Waya."
"Nagode Lilbirrah, don Allah ki ba wa Joonam Winki ha?uri, tunda wannan abun ya faru ko wayata ba ya Wauka."
"Insha Allah Badiyyah da ya zo zan faWa masa duk yadda muka yi." Bankwana muka yi da Badiyyah tana ta ?ara ba ni ha?uri. Sati daya da faruwar lamarin amma sam bai canza ba. badiyyah da kanta ta kira ni da kanta ta ba ni hakuri, na fadawa Yaya amma sam bai yarda ba.
Ina sauke wayar daga kunnena Yaya ya shigo Wakin, da saurina na gaishe shi, "Yaya AbuDalib barka da safiya."
Sai da ya zo gab da ni ya ce, "Khouhar barkanmu juna, ya kika tashi?"
"Lafiya klau Joonam Alhamdulillahi." "Masha Allah," ya faWa a gimtse.
"Amm, don Allah Yaya, ka janye kalaman da ka fada na ka fasa auren Badiyyah, kar ka Wauki abinda ya faru wani abu, wallahi bacin rai ne kuma yadda muke mu mata kowace mace ma za ta iya yin haka, daidaiku ne a cikinmu za su amince da abinda ka yi din Yaya, ni ma daga baya na gano kuskurena, bai kamata gata da kulawar da kake ba ni ta shafi rayuwar soyayyarka ba Yaya."
Dagowa ya yi ya kalli cikin idanuwana, "Lilbirrah, cikin kadan da kike ce ana samu a cikin matan wanda ba su da wannan mugun halin cikinsu samu, yanzu na riga na gama yanke hukunci ba zan fasa ba." Shuru na yi tuni hawaye sun ciko idanuwana, "Yaya kana gani fa har an kai kudin neman aure, ana lissafin nan da kwanaki goma za a sa rana, yanzu idan ka yi haka daidai ne?"
"Bara ma ka gani, yanzun nan Badiyyah ta kira ni ta ba ni ha?uri, har da kukanta Yaya, ta yi nadama na tabbata ba za ta sake ba."
Dan karamin tsaki ya ja, wanda ke nuna maganar da na yi tamkar na yi a iska ne. "Yaya don Allah ka yi hakuri," mikewa ya yi ya fice har Ummanmu ma ya fasa gaisarwa, makarantar ma da zai kai ni duka ya fasa, goge 'yar ?wallar da ta zubo mani na yi na mi?e na tafi makaranta.
Wasa-wasa ?aramar magana ta zama babba, saboda Yaya ya tsaya kai da fata ba zai auri Badiyya ba, duk da ta yi nadama sosai a kan abinda ta yi mini amma ya kafe ya ki ya sauko. Babana da Baban Abu?alib ba su san me ake ba, sai da aka ce ya kawo goro saura kwana uku a sa rana.
A nan ake sanar ma Baba Wanyen hukuncin da ya yanke, Baba ya ce sam bai sam wannan maganar ba, kuma ma kayan shirme kan Wan abinda bai taka kara ya karya ba. Duka Babbaninmi caa suka yi ma Yaya, wata ranar Laraba suka hadu suka yi mishi magana, a ranar aka samu ya sauko daga kan bakanshi, shi ma sai da ya ga rayuka sun Saci sannan. Sai a lokacin ya amince da cigaba da soyayyarsu bayan ya yi ma Badiyyah kashedi sosai.
Na ji dadi kwarai da gaske kan sasancin da aka yi, bayan nan da sati daya a ka sa ranar auren Yayana Abu?alib da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login