Showing 51001 words to 54000 words out of 55242 words

Chapter 18 - BA DON MACE BA BY FATIMA FANTAH.doc

Advertisement

22 Feb 2025

3651

take na yanke hukuncin na ga matar aurena, ina fata mafarkin da nake ya zama gaskiya."
Murmushi na yi, "Lallai kam wannan shi ake kira daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi za?i,"
"Ni ba za?i kaWai miyar ta yi ba, tsokokin nama na ri?a gani cikinta."
Dariya ya ba ni sosai, "Kai na ji daWi sosai, ni Jameel yau sai na yi wa kaina kyauta domin na sa sarauniyata dariya."
"Uhmm, gaskiya kana da abun barkwanci Malam Jameel, amma abinda zan faWa maka ni matar aure ce."
"Kalar ki bata yi kama da ta masu ?arya ba, saboda haka a fitar kalamanki kaWai na gaza yarda, duk da dama kanwarmu Rumaisa ta faWa mani Lilbirrata ba matar aure ba ce."
"A surutunta har ta faWi haka? To shi ke nan, na ji ba ni da aure amma gaskiya ina da tsayayye."
"An sa muku rana?"
"A'a an kusa dai..."
"Alhamdulillah, na ji na kuma yarda, kenan a yanzu da ni da shi duk muna takara ne, saboda haka ina so a ba ni dama ni ma na shigo cikin fagen ya?in neman zaSe, a bar ni a fafata da ni ko a primary election na faWi, na dai gwada sa a ta."
"Shi ke nan toh, ban cika son jayayya ba, saboda haka Allah ya ba mai rabo sa'a."
Wani Wan ?aramin ihu ya buga, "Alhamdulillah, Allah ya ba mai rabo sa a."
"Amin," na faWa. Hira muka cigaba da yi sama-sama, a wayar da muka yi na lura da Jamil mutum ne mai saurin sabo, domin yadda yake magana da ni tamkar mun yi shekaru da sanin juna.
Kashe gari da safe Yaya ya shigo, kasantuwar muna hutun ?arshen mako ne ina gida. Bayan sun gama gaisawa da Baba sannan ya shigo Waki ya gaisar da Ummana. Mi?ewa ta yi ta fita daga Wakin jin Baba na kiranta daga can cikin Wakinsa, Ummana na Yaya ya ce, "Khouhar."
"Na'am Joonam, ya aka tashi, ya aka baro min ?awata."
"Ki yi shuru don Allah kar ki kuma Sata min rai."
"Me ya faru kuma Joonam?'
"Ba bu?ata sai kin sani, kawai rabu da ?awarkin can, sam ba ta da hali wallahi, a kanta yanzu ina jin tsoron mutane masu shuru-shuru."
"Yayana, me ya faru?"
"Na ce ki rabu da zancenta, mu yi magana mai amfani. Kin san wani abu bayan tafiyarki sai da Ankit ya sake kirana a kan harkar nan, Joonam gaba Waya hankalina ya karkata kan abun nan."
"Ka san ko Yaya, ina dawowa gidan nan sai da na faWawa Umma, ta ce haka ba zai yiyu ba ka siyar da kadarorinka ka faWa harkar 'trading'. Amma akwai abinda na yi tunani idan har Umma ta amince to haka za a yi."
"Me za ki yi Khouhar?"
"Ba zan faWa maka ba Joonam, sai na yi sannan."
"A'a fa Shalele, kar ki je ki Wauko min magana."
"Idan na Wauko ta ma Yayana ga shi a gabana zai biya."
Murmushi ya yi ya ce, "Haka yake Khouhar, rigima ko zan siyar da kaina ne domin tseratar da ke zan siyar."
"Kai Yaya, shi ya sa kullum kuke faWa da Badiyyah a kaina, dole ta nuna kishinta."
Dogon tsaki ya ja, "Don Allah idan muna tattaunarwarmu ki daina sako min Badiyyah, ki bar mu can mu cigaba da fafatawa, da ba don an ce aure Wan hakuri ba ne ta ya zan cigaba da zama da Badiyya ma." Ya ?are maganar ransa Sace.
"Shi ke nan na daina Joonam, amma don Allah hakurin da ake a ?ara wani a kai, duka mata haka muke."
"To ke meyasa ba ki abinda take yi?' ya ?are zancen yana yi min kallon harara.
"Yayana, ni ma zan yi sai na yi aure ina kishin mijina sannan."
"Mtseww," ya ja wani tsakin. Mi?ewa ya yi a saluSe yana, "Ni kin ga tafiyata, idan kun yi magana da Umman kin neme ni."
"Sai an jima Joonam a gaida min ?awata." Sam bai bi takaina ba sai komawa da ya yi wurin su Umma ya yi musu bankwana.
Murmushi na yi a raina ina faWin, "Insha Allah na kusa aure, Yaya za su zauna da matarsa lafiya, domin rabin matsalolin zamansu a dalilina suke faruwa.
Mi?ewa na yi na shige bedroom Winmu, akwatina da ke kan wardrobe na sauko, buWe shi na yi na fara fito da kayan da ke ciki wanda ba kayan sawa ne a jiki ba kayane masu muhimmanci na adana ciki.
Wata leda wacce ke ?asa gaba Waya na Wauko, buWe ta na yi a nutse wanda ledar ita ma cikin wata ledar take, sai da na fiddo ta gaba Waya sannan na kwance wadda ke ?asa duka.
Wasu takardu ne a ciki wanda sai a yanzu na gane ma'anarsu.
"Wace ma'ana gare su Lilbirrah?" Yunus ya tambaye ni.
Nisawa na yi ina kallon shi, "Yaya Yunus, a cikin labarina babu abinda zan Soye maka, a hankali za mu kawo kan ma'anar tasu."
"Am sorry," ya faWa cikin lallausar murya.
Kallonsa kawai na yi sannan na kauda idona na cigaba da magana.
"Takardu ne a ciki kowace a jikinta akwai rubutaccen sunana, sai dai sam na kasa gane ma'anar rubutun da ke jikinsu, sai kuma wasu kyawawan 'yan hannu (awarwaro) na zinare guda sha shida, sai sar?a haWe da 'yan kunne manya masu masifar kyau, dukansu na manya ne ba size Win hannuna ba."
Shuru na yi ina tunani, "Lilbirrah waWannan 'yan hannu da sar?ar na mallake su tun kina 'yar ?an?anuwa, kuma tun a lokacin na mallaka maki su halak malak, dukiyarki ce ki yi yadda kike so da ita, ko Babanki ba zai ce don me ba, domin na mallaka maki ita, ke ko ni da kaina ba ni da iko a kanta taki ce. Sai dai abinda nake so da ke, ki bari sai kin kai kimanin shekara talatin ki siyar da su ki cigaba da kasuwanci..."
Motsin da na ji ya sa ni yin firgigi, Umma na gani tsaye wanda ban san lokacin da ta shigo cikin Wakin baccin ba.
Cike da mamaki ta ce, "Shalele, me za ki da wannan kayan da kika Wauko?"
Tsuru-tsuru na yi ina kallon Umma. Zama ta yi tana fuskantata, "Lilbirrah ko akwai wata shawara da kika yi a kan waWannan kayan ne?"
"Umma me ya sa ke ba za ki kasuwanci da kuWinsu ba?" Kamar daga sama na ji ina tambayarta.
Kallona ta yi a nutse, "Shalele, saboda na yi al?awari cewa na mallaka miki su har abada ba zan yi wani abu da su ba."
Nisawa na yi, "Ummanm to me ya sa kika ba ni ni kaWai? Ga Yaya Abu?alib ga Rumaisa."
"Kin san cewa Abu?alib Wan mariganyiya ne ko? Rumaisa kuma daga baya ta zo, a lokacin da har na fitar da ran zan ?ara haihuwa, ke ce tawa ke na fara samu, shiyasa na mallaka miki su." Ta ?are maganar tana murmushi.
Ni ma murmushin na yi sannan na ce, "Umma yanzu zan iya sayar da ko 'yan hannun ne na hannu guda na yi kasuwanci?"
"Sosai kuwa Shalelen Umma da Yayanta, amma ki faWa min wace irin kasuwa ce za ki fara, a ina take wa ke yin ta?"
Fuskata da murmushin da ya yi mata mayafi na ce, "Umma babu wata kasuwar da zan fara, da ma game da maganar da na yi maki ne jiya na kasuwar Crypto da Yaya yake so ya fara, abun yana ransa ya zauna mashi sosai, sai tunani yake ya siyar da gidansa da motarsa da sauran 'yan abubuwan da ya mallaka, ni kuma bana so ya yi hakan, idan aka samu matsala asirinsa zai tonu, wannan ko ba wanda ya sani."
Shuru ta yi irin na mai nazari can kuma ta nisa ta ce, "Lilbirrah ke kin amince ki siyar da wannan 'yan hannun ki ba shi kuWin ya yi kasuwar Crypto?"
"Eh Umma, wallahi na amince Wari bisa Wari."
"Shi ke nan, ki fiddo 'yan hannun guda takwas Win kuma ki gaggauta mayar da sauran a ma'ajiyarsu, kamar yadda kika sani bana so Rumaisa ta san da labarinsu."
Jinjina kai na yi, "Umma ba za ta sani ba Insha Allah, ba zan taSa karya maki al?awari ba."
"Yawwa Shalele, sai kuma ki kira Abu?alib Win ki ce ina neman sa."
"To Ummana," na faWa zuciyata cike da farin ciki da jin daWi.
Mayar da kayan na yi kamar yadda suke sannan na Wauki awarwaron guda takwas na adana su cikin wardrobe.
Muna fita falo na dauki waya na kira Yaya na sanar da shi Umma na kiransa. Bai jima ba ya zo.
Umma ta ce na tafi Wakin Anty za su yi magana. Sam ban ji komai ba, domin kuwa na san za su yi magana mai muhimmanci da ba ta shafe ni ba.
Ina shiga Wakin Anty sabon saurayina Jamil ta kira ni muka cigaba da hira.
An kai kimanin mintuna talatin sannan Umma ta kira ni Yaya na zaune yana min wani kallo tamkar lokacin ya fara ganina. Umma ta ce, "Mun yi magana da Yayanki, ya amince zai karSi 'yan hannun amma na sa sharaWi Shalele, duk idan aka sayi haja aka siyar za a raba ribar gida uku a baki kashi Waya ya Wauki kashi uku."
"Ummana, Yaya Abu?alib ne fa, ni ba sai ya ba ni komai ba."
KaWa kai ta yi ta ce, "Na san haka Lilbirrah amma ha??inki ne, dole a fitar maki da ha??inki."
"Umma..."
Hannu ta Waga ta dakatar da ni, "A yi abinda na ce kawai."
Jinjina kai na yi, "To Ummana."
Mi?ewa ta yi zan je na faWawa Babanku sannan a zo a yi rubutu sannan a je kasuwa a siyar a ba shi kuWin.
Jinjina kai kawai na yi, domin yadda Umma ke yi tamkar ba ta san Yaya ba, ya ba ni mamaki, amma ni a nawa ganina abinda na mallaka zan iya mallakawa Yayana, shi mai iko da dukiyata ne da duk abinda na mallaka.
"Lilbirrah," Waga kai na yi na kalli Yaya yadda ya kira ni cikin wani kalar sauti.
"Ba kya jin komai ki mallaka min abinda yake mallakinki ne, wannan tanadi ne da Umma ta yi maki don rayuwarki ta gaba "
"Yaya to me ye ni ba zan mallaka maka ba, ka yi mun abinda ba wanda ya yi min a duniya, ko aure na yi mijina ba zai yi min kwatankwacin abinda ka yi min ba. Kuma na sani da a ce kai ne a matsayina tuni ka siyar ba tare da wata shawara ba."
"Haka ne, m" ya faWa yana fitar da wani nannauyan numfashi.
"Nagode sosai, Allah ya saka maki da alkhairi."
"Amin Yayana."

SH 20

ABU?ALIB

Mi?ewa ya yi domin tafiya gida, a sanyaye yake tu?i yana yi yana kallon hanya, zuciyarsa cike da tunanin Lilbirrah, wani irin matsayi da girma yake ji ta ?ara a zuciyarsa, irin matsayin da baya iya kwatanta shi a zuciyarsa. Karo na farko da ya ji wani abu mai ?arfi yana fizgar zuciyarsa a kanta, lumshe idanuwa ya yi ya karya motar kan kwanar gidansa yna cigaba da tunaninta.

&&&&&

Kashegari bayan an gama rubuce-rubucen da sa hannu muka tafi kasuwa aka siyar da 'yan hannun wanda suka bayar da kudi kimanin naira miliyan ashirin da hudu kasantuwar 'yan hannun manya ne sosai kowane dayansu an sayar da shi Naira miliyan uku. Cike da mamaki na ce ma Ummana, "Umma kenan tsakanin wancen da wannan 'yan hannun har da sarkar za su yi miliyan hamsin ko?"
"Za su fi haka ma Lilbirrah 'yar Ummanta."
"To Umma me zai hana a ce ba a siyar da su gaba daya ba sai mu yi kasuwanci watakil da yanzu ma mun zama masu kudi."
"Uhmm, hakkinki ne Lilbirrah lokacin da za a yi hakan idan ya zo za a yi."
"To amma Ummah dukiyar fa asalinta taki ce, to don me za a mallaka min ni, ni kaWai?"
Kallona ta yi da murmushi a fuskarta ta ce, "Ban san ki da yawan tambaya ba Lilbirrah, ki daina kin ji."
"Ummana na daina," na fada ina kwantar da kaina kan kafadarta. Shi ko Yaya yana gaba yana driving motarsa, ko kadan bai tanka mana ba, yana dai saurarenmu. Hira muke yi mai daWi ni da Umma har muka isa gida, da ma kuWin account Win Yaya aka tura su gaba Wayansu, yana aje mu ya juya domin tafiya gida, ita kuma Ummana ta yi masa fatan samun nasara.
A Sangarena cikin kwana biyu da haduwarmu da Jamil ya bukaci zuwa gidanmu, ban hana shi ba na fadawa Umma duk yadda muka yi da shi tun farkon haWuwarmu.
Jinjina kai ta yi ta ce, "Alhamdulillah, ina jin dai wannan za a yi da shi, tun da ga shi har an gabatar min da shi."
Du?ar da kaina na yi ina murmushi. "To bari na faWawa Babanki, idan ya ba da damar zuwan, sai ki faWa mashi."
"To Ummana," na faWa. Tashi ta yi don ta isar ma Baba sa sa?ona. Cikin sa a kuwa tana zuwa ta fada mashi ya amince, hakan ya ba ni damar ba wa Jamil izinin zuwa wurina. Ranar da ya zo mun sha hira sosai a yadda na fuskanci Jamil mutumin kirki ne sannan yana da nutsuwa sosai, hakan ya sa na ji ya kwanta min a rai.

&&&

ABU?ALIB

Kai tsaye wajen Yeaster ya je domin yin maganar kasuwar Crypto, cikin nutsuwarsa yake kallon Yeaster bayan ya faWa masa duk yadda aka yi ya samu kudin, "Ka yi nasarar sace hankali na Yeaster."
Murmushi ya yi yana kallonsa sai da ya kurSi ruwan kwakwa da ke hannunsa sannan ya ce, "Abu?alib ba za ka yi nadama ba, ina tabbatar maka za ka yi farin ciki, kuma ba za ka same ni na cuce ka ba, babu abinda zai samu dukiyarka domin a halin yanzu exchanger ta Binance, ko Vault ma fi tsaro a duniya wanda ke akwai WaiWaikunsu a shahararrun ?asashen duniya, bai kai wannna Exchanger Win tsaro ba, domin akwai tarin tiriliyoyin daloli a cikinta, ba manyan masu kuWin duniya, kai har ma sa wasu ?asashen suna saka hannun jari domin ?arin tattalin arzi?insu. Saboda haka ba abinda zai samu dukiyarka ka shiga harkar trading da nutsuwa za ka yi dariya da farin ciki za ka gane alkhairi nake nufinka da shi."
"Shi ke nan abokina Yeaster, Allah ya ba mu sa'a."
"Amin."
"Ka san Yeaster, ina jin kudin nan dukiya ma fi girman daraja a gare ni, bana jin akwai wani abu da ya fi ta ?ima a wurina."

"Kai, abokina kaunarka da sister Win nan taka tana birge ni, da a ce wannan ba sisrer dinka ba ce uwa daya uba daya ba da na ce ka aureta, tabbas za ku yi zaman farin ciki saboda kuna kaunar juna kuna son ganin farin cikin junanku."
Shuru ya yi yana kallon Yeaster da ke ta zuba zance. Murmushi kawai ya yi ya ce, "Yeaster yanzu me zan yi na gaba?"
"Za ka yi register da makarantarmu da ke Kano wacce za ka ?ara gogewa a harkar, kuma na maka al?awarin da duk iyakar iyawata zan taimaka maka abokina."
"Nagode Yeaster." Abu?alib ya fada yan ba shi hannu suka tafa.
?ara tatttauanawa suka yi sosai a kan harkar sannan AbuDalib ya yi bankwana ya bar wurin. Tafiya yake yana driving amma zuciyarsa cike take da fal da tunanin Lilbirrah wanda abun har ya soma yi masa yawa ya fara tsikarar walwalarsa ta yau da kullum.
Kwana ya yi ya nufi wajen abokinsa AbdulJalal, yana isa Abdul ya gan shi very week. Cikin kulawa ya ce, "Ya ne abokina me ke faruwa ne na ganka sai a slow."
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke sai da ya nisa sannan ya Wora idanuwansa kansa suka yi kallon ido cikin ido, a sanyaye ya buWe baki ya ce, "AbdulJalal, ina cikin matsala."
"Matsala kuma Abu?alib ta me?" Abdul ya tambaye shi cikin tsantsar damuwa.
"Abdul zuciyata ce ke neman saka ni a wata koma wacce nake da tabbacin za ta ba ni wahala, na sani da wahalar gaske na wanye da ita lafiya."
"Komar me kenan Abu?alib? FaWa min da sauri."
"Ji nake zuciyata na bugawa da so da kaunar Lilbirrah, so irin na aure wanda za mu kasance mata da miji ni da ita Abdul."
Kallonsa ya yi baki sake, "AbuDalib kana sane da abinda kake fadi kuwa?"
"Ina sane mana Abdul shi ya sa ma na faWa ma, domin damuwar ita ke diddigar zuciyata a cikin yini biyu tana neman fitar da ni hayyacina. Kuma na bayyana maka ita a lokacin da ba wanda ya san da ita idan ba ni ba, na bayyana maka a matsayinka na namiji Wan uwana wanda zai iya kintata zafi da raWaWin da ke raina, abokina na fada ma don ka ba ni mafita."
Numfasawa Abdul ya yi, "AbuDalib ta wace fuska za ka tunkari Lilbirrah da zancen soyayyah, soyayyah irin ta aure? Bayan kai tana daukarka a matsayin Yayanta Wanuwanta na jini, ina jin hakan zai zo mata banbarakwai Abu?alib."
"Abduljalal, Lilbirrah tamkar Waya ce a cikin dubu, ta ya zan yi sake matar da ake kira daya a cikin dubu ta kuSuce daga hannuna, bayan ina da damar mallakarta, Abduljalal ka san Lilbirrah fa, ta cika kamalar da ake so kowace mace ta kasance da ita."
"Abu?alib, ni ko na san Lilbirrah, yarinyar da ta tashi a gabana tun daga yarinta har zuwa girmanta, na sani tun tasowarta yarinya ce nutsattsa, mai burin aikata alkhairi da kyautatawa, bana manta lokacin da take debo ruwan Umma da soSonta a fridge ta kawo mana idan na je wurinka, sannan kuma abincin kowa ta samu a kitchen sai ta kawo min, tabbas ina tuna wannan halin nata na karamci. Sannan ga ta da tausayi, na sani saboda ita aka rika ba wa Aminu wannan almajirin naku abinci har zuwa yanzu da ya girma ya zama saurayi ita ta yi dalilin girmansa a hannunku. Na sani halayen kwarai irin nata kam abin so ne kuma duk wanda ya aure ta ya yi dace mai yawa, ilimi, hankali, nutsuwa, tarbiyyah sanin ya kamata kyawawan halaye duk ta haWa Abokina, sai dai ina jin ka yi sake Abu?alib samunta wurinka zai yi wuya."
"Abdul ina sonta, ina son in aure ta, kuma Lilbirrah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login