Showing 21001 words to 24000 words out of 55242 words

Chapter 8 - BA DON MACE BA BY FATIMA FANTAH.doc

Advertisement

22 Feb 2025

3648

suka zubo min, shin ba na ce gobe zan bar musu gidan ma gaba Waya ba, ta bar ni na ?arasa kwana Waya jal da ya rage mana. Juyawa na yi wurin Innarsu Kulu, "Ki ce ta taimaka min gobe zan tashi, Yunus mai Yunus Hospital zai mai da ni gidansu, ki ce ta bari sai da safe zan bar gidan..." Duk bayanin da na yi wa Innarsu Kulu shi ta yi wa Saratu, sai dai sam ba ta ji ba, sai ma gefe da ta yi ta buga tsalle ta dire ta ce sai na bar gidan babu fashi. Babansu da ke gefe duk da tsufansa ba ta sauraren shi balle ta ji me yake cewa.
Tuni fuskata ta ji?e da ruwan hawaye, sai bebenci nake na ?arin ro?onta, amma tamkar ina yi wa dutse. Innarsu Kulu ta ce, "Tun da dai wannan abu ya ?i ci, ya ?i cinyewa ke Sister (sunan da take kirana da shi) ki zo mu tafi gidana ki kwana gobe da safen sai na kai ki asibitin su Yunus Win shi ke nan. Ko haka bai yi ba?" Ba don raina ya so ba na ce hakan ya yi.
"Yawwah to shiga ki sanyo hijabinki mu tafi." Gaba na yi na shiga Wakin na saka Abaya na Waura kallabinta a kaina sannan na sa Hijab. Innarsu Kulu ta taimaka mini da Wauko kayana da suka yi saura, ni kuma na zaro jikkata mai Wauke da ?ananun tarkacena muka fito. Wurin Babansu Ayuba na je na sake mashi godiya. Jinjina kai ya yi tare da yi mini fatan alkhairi muka fita.
Maimakon mu yi cikin unguwar sai muka nufi bakin hanyah. "Na Wauka gidanki nan bayan mu yake?"
"Eh wallahi ko, nan yake Sister sai dai kuma tunani na yi ban faWa ma Babansu Kulu ba, kuma Wakin shi kaWai ne muke ciki gaba Waya. Shi ne zan kai ki gidan Sisterna nan gaba kaWan yake sai ki kwana a can Win."
Shuru na yi zuciyata ta kasa nutsuwa, cikin rashin sanin yadda zan yi na ce to shi ke nan mu je Win ba damuwa.
Kafin mu ?arasa titi wata mota ta yi fakin gefenmu, da wani suna na ji ya kirata, tafiya ta yi gurin mai kiran. Ban san me suka tattauna ba ta dawo tana, "Brotherna ne, gidana za shi kin gani mu je kawai ya sauke mu, mun ma samu sau?i." Jinjina kai na yi a sanyaye, tare muka isa muka shiga cikin Motar irin ?irar Sienna Win nan ta fi kama da motar jigila, mutum biyu ne a gaba sai baya ni da Innarsu Kulu, a hankali muka fice daga layin muka hau babban titi.
"Yawwah Boss, mu je Ikorodu aiki ya kammala." Ta faWa tana min kallon da na kasa fahimtarshi wanda ya sa gabana mummunar faWuwa da ya sabbaba ma abun ?aunata yin wani juyi tamkar zai diro duniyar a daidai wannan lokacin.

SH 9

Cikin firgicin da ya dirar mani lokaci Waya na yi mata nuni, "Me kike nufi? Ina za ki kai ni?"
"Za ki ga inda zan kai ki Sister," ta ?are maganar tana sakar min wata shu'umar dariya. Hannunta ta mi?a wurin mutumin da ke gaban motar ta karSi wani farin ?yalle. Tabbas na san irin ?yallen nikan gani a talabijin, sannan na karanta a wasu litattafai, ana sa sinadarin hodar iblis ko wani sinadarin a sa wa mutum a hanci domin a fitar da shi hayyacinsa.
"Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!" A lokacin da na tabbatar cewa Innarsu Kulu da mutanen da take tare da su suna nufin cutar da ni ne. Tunkaro ni ta yi da ?yalle, sai dai duk da raunin da ke tare da ni hakan bai hana ni yin ?asa da fuskata da sauri, da duka hannayena biyu na sa na rufe fuskar. Hannunta guda tasa da ?arfin tsiya sai ta SanSare hannuwana sai dai ta kasa samun damar hakan, sosai kokowa ta kaure tsakaninmu, su ko wanda suke a gaban motar ko a jikinsu tamkar ba su san muna yi ba, wani irin karfi ya zo mini na bigi fuskarta da gwiwar hannuna, cikin azama na dunkule hannun Innarsu Kulu na ?wace ?yallen, kamar yadda ta yi niyyar saka mini shi a hanci hakan na samu nasarar dankara mata shi a nata hancin, baya ta yi suu ta faWa kan kujerar motar tamkar matacciya. Juyowa na yi na fuskanci gabana ina mayar da numfashi, idonuwana sun ?e?ashe babu alamun hawaye ko kaWan, sai zuciyata da ke tsananin suya tamkar kosan da ke cikin kwanon mai. "Ya za ni yi? Me ye abin yi? Ina za su kai ni?" Shi ne abinda ke kai kawo a cikin ?wa?walwata tare da tunanin samun mafita. Da sauri na sa hannu na fara kokarin bude murfin motar sai dai sam ba ta ko alamun motsi balle na saka ran za ta bude. Dayan ya juyo yana min kallon shashasha, cikin hausarshi mara daWi a kunnen mai sauraro ya ce, "Madam babu inda za ka je, saboda mun biya kuWinka da bebi naka, za ka ba mu bebi naka kafin mu kai ka inda za mu siyar da kai..." Wani irin gumi ya tsattsafo min, na daina fahimtarsa tun lokacin da ya ce, "Mun biya kuWinka kai da Baby naka..." Abun ?aunata, abun ?aunar nawa suke hari, abun ?aunar nawa ne suka karbi kudinsa da ni kaina da ke jigilarsa nake tsumayen zuwansa, da ma Innarsu Kulu bibiyar da take yi mini kenan. Dukkan illahirin jikina ya hau karkarwa, yayin da zufa ta ida wanke ni tamkar an yi mini yayyafin ruwa a kaina. Innalillahi wa inna ilaihi raji un na ?ara faWa a zuciyata, yayin da nake fitar da numfashi mai zafi kamar daga salansar babur. "Ya Ubangijin da yake ji na a halin da babu mai ji na sai shi kaWai, ya Allah ka kawo mini dauki ya Allah kar ka bari a cutar da ni da abun kaunata." Juyawa na yi gefe cikin tunani da neman hanyar nema wa kaina mafita, wayar Innarsu Kulu na yi arba da ita kan cinyarta, jikina na rawa na dauki wayar yayin da suke tu?insu hankali kwance babu abinda ya dame su da ni. Kallon wayar nake ya zan yi? Wane taimako za ta iya yi min? Wani abu ya faWo mini, "Wannan phone Win numebers ne na hospital da na business dinmu, wannan kuma na family ne, amma wannan ita ce official numberna duk wanda ya kira wanda yake da dalili ne da ni, duk mai kira a wannan numbern to VIP Wina ne..." Wata hira da muka taSa yi da Yunus wata rana za mu je asibiti. Tunani nake ta yadda zan haWa numbern a yadda ya zayyana ta, idan na samu to me zan faWa masa.
Vibration Win waya da ya gauraye motar ya sa na yi wata irin zabura, sai dai ba wayar hannuna ba ce, wayar mai tu?in motar ne. Dagawa ya yi ya soma magana cikin harshen turanci, ji na yi yana faWin, "Mun kusa zuwa oga, muna wurin Oshodi Markit, ta yi haka baby yana satinsa na hamsin da biyu so da mun zo cire shi kawai za a yi& " Wani yawu na haWiye mai kama da dun?ulen dutsi, kallon matattar wayar keypad Win Innarsu Kulu nake yi, ina sake tariyo numbern da Yunus ya faWa mini ta faWo tass 07080007007 tabbas haka take, ban kira shi ba, sai text na rubuta mashi, "Yunus ka taimake ni, ga ya nan wasu za su je su yanka ni ni da abun kaunata, muna wurin Oshodi market cikin mota Sienna ja, Ama ce." Tura message din na yi zuciyata cike da fatan ya shiga. Gudu suke yi sosai, ya yin da tsorona ya linku, da sauri na kashe wayar na yi kasa sannan na tilla ta ?ar?ashin kujerar da muke. "Ya huwa ya man la huwa illah huwa..." nake ta maimatawa a zuci. Dayan da ke gefe ya juyo, wata irin dariya ya saki, "Madam," hannuwana biyu na hada wuri Waya alamun ro?o, dariya ya saki yana kada kai, "Madam za mu sayar da kai sassan jiki naka zai yi kudi," kallon direban ya yi yana, I swear suna sake sakin dariya. Dukkan jikina ya saki, ya yin da jikina da na abun kaunata yana ta juyi tamkar ya san abun da ke faruwa da mu. Mun wuce Oshodi market sosai, mun yi nisa da ita mun tunkari Ikoroudo kamar yadda na ji suna fada, ganin mun shiga wata hanya marar mutane ya sa wani tashin hankalin ya sauko mini, "Shi ke nan, haka Allah ya hukunta ma rayuwata, zan bar duniya a kaskance jikina da bakin fenti mai muni, abun kaunata kuma sanyin idaniyata, shi Waya kwallin kwal a duniya zan rasa shi, gaskiyata mai girma za ta cigaba da wanzuwa a lulluSe ba tare da ta bayyana ba...," wani irin gunjejen kuka na yanke kauna da ke dugwigwiyar zuciyata na fashe da shi. Cikin fitar hayyaci na sa hannu na fara bubbuga kofar motar, domin neman taimako sai dai duhun dare da ya yi ma komai mayafi ya hana tsirarun masu gani shaida me nake yi, kuka nake yi sosai tamkar zan hado da makwagorona, wani haske ya dallo mu ta gabanmu wanda ya dishe ganin idanuwanmu. Ji na yi sun fara ?o?arin yin baya da motar da sauri, sai dai kafin mu yi nisa muka yi karo da wata motar ta bayanmu, wanda ya ida gigita mu ni da nake bayansu da su da suke sarrafa motar. Gefe suka yi da sauri, sai dai zancen da muka ji cikin mazu?ar sautikanmu ya ?arasa firgita su da wani irin karfi tsiya suka ja motar domin su gudu, motar da ke bayanmu ta bi motarmu yayin da kafin mu isa inda daga cikin layin muka yi kicibus da motar 'yansanda. Tsaye muka yi cikk, yayin da motocin 'yansanda suka yi mana kawanya, kuka nake na fiitar hayyaci domin ganin taimakon Ubangiji da ya zo mini a lokacin da na fidda tsammani. 'Yansandan suka ba su umarnin su fito hannuwansu a sama alamun sun zama kamammu, kasa motsawa na yi saboda yadda na ji jikina dukansa ya zama tamkar an Waure shi da igiyoyi. Cikin hasken da ya gauraye wurin na ga an tunkaro ni da sauri, Yunus ne cikin tashin hankali, "Ama are you fine, na ce kina lafiya?" Sabon kuka na fashe da shi, yunkurawa na yi da niyyar fitowa daga motar sai dai gani na yi wani duhu ya mamaye ilahirin ganina.

&&&&&


Farfadowwa na yi na gan ni a kan gadon asibiti, da sauri na dora hannuna a kan cikina. Abun Kaunata yana nan, mu duka muna nan a raye, na ayyana a raina. Runtse idanuwa na yi abunda ya faru yana dawo min tarr cikin kwanyar kaina, wasu sabbin hawaye suka ziraro mini, na gode ma Allah da ya tseratar da ni ya kiyaye ni ya kiyaye mini abun kaunata. Har abada ba zan manta Lagos ba ba zan manta Innarsu Kulu ba, kuma ba zan gushe ba ina yi musu addu ar Allah ya yi min sakayya da ita da sauran wanda suke da hannu a alhakin cutar da ni. "Sannu Amatullah," Juyawa na yi da ?yar hawaye na cigaba da bin gefen fuskata, "Sannu kin ji, lallai Allah ya auna miki arziki, Allah ya dada kare ki kin ji." Jinjina kai kawai na yi, "Ya jikin naki? Ina fata babu inda yake miki ciwo."
"Babu Mama, jikina da sauki sosai," na yi mata nuni. Tashi na yi zaune, saboda fitsari da na ji ya kulle marata, a hankali na taka na shiga bayin cikin dakin. A daddafe na fito yayin da na ji jikina ya kara nauyi, ?asan cikina ya ?ara ?ullewa, har na gama abinda nake a bayin na fito na kasa tsaida hawayena. Maman Yunus ta kara yi mani sannu. Shayi ta hada mai kauri ta miko mini, tana ta yi mani maganganu na lallashi masu taushi da sanyaya zuciya, tare da sake jaddada mani ba abinda ya same ni kuma ya samu abun?aunata. Sam na kasa tsaida hawayen, abubuwa marasa adadi da tunane-tunane sun cika kwanyata, kadan na sha tea din na koma na kwanta. Yunus ya shigo, na yi gaggawar rufe idona na yi lamo kamar ina barci.
Daga gefena na ji yana, "Mama ya jikin Ama, ta tashi da karfi ko?"
"Da sau?i sai dai akwai tarin damuwa tare da ita." Tattaunawa suka cigaba da yi ina kwance ina saurarensu barci ya yi awon gaba da ni.

&

Gaba daya daliban Malam Saleh sun hadu a kofar gida, Dayyabu da suke kira da Babban Yaya ya karaso da mota J5, kafin ya ce wani abu daliban sun fara ruguguwar hawa kan motar. Malam Saleh da ke gefe ya ce, "A bi a hankali yaran Malam kuma kar a yi abinda bai kamata ba idan an je gona, kun ji ko?" Bara ma in fada muku ina nan zuwa yanzu zan biyo bayanku. Cikin jin dadi yaran suka tafi, domin ransu sake yake a duk lokacin da za a gona ranar ba a karatu. Kai tsaye suka nufi gonar da ke yammacin garin Katsina, suna isa suka hau aikin gona na barbaje taki kafin saukar ruwan shufka.
Lokacin da Malam Saleh ya zo har sun ci karfin aikin, bayan sun gama suka ci abinci da hura da Malam ya je da su. Dayyabu ya karaso wurinshi cikin girmamawa ya ce, "Malam gida za a tafi?" Shuru ya yi yana nazari. Dan nisawa ya yi ya ce, "Mu je a cirema Gonar can ta gabas sabra an dade ba a yi mata shufka ba ita ma sai a kawo taki, yanayin da ake ciki bana dole duka gonaki zan yi noma." Cike da mamaki Dayyabu ya ce, "To Malam."
Zuwa ya yi ya ja motar suka haye suka yi gonar wadda ke da nisa da wadda suke. Suna isa yaran suka hau aiki, Waya daga cikinsu ya Wan yi nesa da su dan yin fitsari wani abu ya gani kamar hayaki na tashi a gaba kaWan da inda yake, kura ma wurin ido ya yi sai kuma ya ga wuta ta taso ta nufo shi gadan-gadan, a guje ya bar wurin yana ihun wuta, yaran malam wuta. Duka yaran gudu suke yi, yayin da Dayyabu ya hango su sun nufo shi a guje, cikin faWa ya ce, "Kai, lafiya? Me ya faru?" A rikice yaran suka ce, "Wuta muka ga tana ci babban yaya."
"A ina," ya tambaye su da mamaki.
"A can," suka haWa baki wurin faWa.
Cikin al'ajabi ?ayyabu ya ce, "Wuta a wurin nan, to wuta cikin dajin nan ai sai dai wutar daji ko? Amma bari mu gani." Ya ?are zancen yana tafiya don ya tabbatar da abin da suke fada. Tunkarar wurin ya yi, sai dai ji ya yi wani irin tsoro ya dirar mashi hade da tashin hankali. Wani abu ya hade kutt cikin makoshi wanda bai san dalilin zuwan shi ba, a hankali ya fara karanta ayatul kursiyyu a bayyane da duk ayoyin neman tsari da suka fado bakinshi. Ji ya yi kamar an daka mashi tsawa ana kiran sunanshi cikin wani irin mummunan amo, "Innalillahi wa inna ilaihi raji un!" Ya fada ba tare da ya yi baya ba, Bismillah ya yi cike da kwarin gwiwa ya cigaba da tunkarar wurin yaran Malam na bin bayanshi. Wani katon dutsi ya gani wanda ga alamu Wauko shi aka yi aka aje a wurin, le?awa ya yi inda ya ga hayaki na fitowa daga karkashin dutsen, sai daga gefenshi kwarya ce zaune dangal-gal duk da ba tarde zaune take kamar haka Allah ya halicce ta a wurin, duk da ba a kan wuta take ba a cikinta ruwa ne ke tafasa suna fitar da wani siraci. "Lahaula wala kuwwata!" ?ayyabu yake maimatawa yana ambaton sunayen Ubangiji. Baya ya yi da hanzari yana fadin wannan ya fi karfina sai dai na fadowa Malam Babba. Baya ya yi a guje yayin da sauran yaran Malam suka firgita suka fishi gudu. Da karfi ya ji ana kiran sunanshi sam bai juya ba sai kara kaimin gudunsa da ya yi domin ya fado ma Malam Saleh abinda maganansa suka shaida. Ji ya yi kamar wani abu ya ja shi ta baya hakan ya yi daidai da faduwarsa kasa wanwar kamar wanda aka ja da igiya.


SH 10

Yun?urawa ya yi da niyyar tashi sai dai sam hakan ya gagare shi, sunayen Allah da ayoyinsa kawai yake ta ambata cikin rikicewa da yanke ?aunar cewa ya yi mummunan gamo a cikin gonar. Yaran Malam suka ?ara gudu don su iske Malam Saleh su sanar da shi abinda ke faruwa da Malaminsu ?ayyabu. A rikice Waya daga cikinsu yake furta wallahi an tafi da Babban Yaya, ganin yadda ake jan shi kaman ana jan wasu kaya, a ruWe ya ?arasa wajen Malam, cikin shesshekar gudun da ya sha ya soma ba wa Malam labarin dukkan abinda idanuwanshi suka shaida mashi game da ?ayyabu, Malam bai jira ya ?are zancen ba ya ce, "Ta ina abun ya ja shi? A ina kuka ga dutsen?"
"Ta in ne Malam." Yaron ya faWa yana nuna mashi hanyar. Gaba Malam ya yi ya bi hanyar ba tare da wani tsoro ko shakku ba, tunda ya tunkari wurin ya soma ganin ana siddabaru, sam bai damu ba sai ayoyin ?ona aljanu yake jawowa yana karantawa don yana da tabbacin aljanu ne suke webuwa a wurin. Tafiya yake har sai da ya isa inda dutsin yake, daidai wurin da yake hayaki da ?waryar da ruwa ke tafarfasa cikinta, abun ya ba shi mamaki sai dai ya basar ya fara neman inda ?ayyabu ya ma?ale. Kiran shi ya yi da ?arfi, amma sam babu shi babu alamarshi, dube-dube Malam Saleh ke yi a zagayen wurin, kamar an jeho ?ayyabu daga sama ya gan shi gabanshi tamkar matacce baki da hancinsa suna fitar da jini. Da sauri ya tsugunna yana, "?ayyabu,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login