Showing 33001 words to 36000 words out of 55242 words

Chapter 12 - BA DON MACE BA BY FATIMA FANTAH.doc

Advertisement

22 Feb 2025

3636

da al'ajabin abinda suke yi. Gabansa ya faWi lokacin da ya kalli ?ofar Wakin Ummansa, rufe yake gam. Bakinsa na rawa ya ce, "Baba, ina Ummana, ina Lilbirrah ina Rumaisa suke? Duk suna ina Baba, na ga ba su nan kuma ba su fito ba. Baba wai me yake faruwa ne?"
Malam Abdulhadi ya ja dogon numfashi, muryarsa a disashe ya ce, "Abu?alib, kana nufin duk ba ka san me ke faruwa ba? Kana nufin duk abinda ka aikata ba a hayyacinka kake ba?"
"Baba me na yi? Me na yi wai? Na ga Jabir yana kuka, ga Anti ma tana min wani kallo, duka kowa kallona yake kamar yau suka fara ganina? Baba me ya faru ne?"
"Abu?alib wannan dogon zance ne."
?asa ya faWi daSas hawaye na biyo kumatunshi, "Baba kenan da gaske na saki Lilbirrah? Kenan da gaske Ummana ta tsine min? Baba me na yi ne haka? Wane irin mummunan zunubi na aikata? Ina Umma take Baba ina Ummana?"
"Ta so mu je Abu?alib," Malam Abdulhadi ya faWa tare da Wago Abu?alib daga zaman cin doyar da ya yi.
?akinsa suka shiga kafin su zauna Abu?alib ya ce, "Baba ina Ummana?"
"Tana asibiti."
A firgice ya Wago, "Tana asibiti Baba?"
"Tana can Abu?alib."
"Me ya same ta to Subhanallahi."
"Ciwon zuciya ne da hawan jini mai tsanani. Baba, ni ne ma silar komai ko?"
"Abu?alib ka nutsu, tabbas an shiga jarabawa kuma muna cikin wani yanayi mu duka. Ka nutsu domin cinye jarabawar nan..."
"Baba to wai me ke faruwa ne?"
KaWa kai kawai Baba ya yi ba tare da ya furta komai ba ya ce, "Tashi mu je asibitin." Mi?ewa ya yi kamar ?aramin yaro yana ta faman sharce hawaye.
Suna isa suka yi kiciSus da Inna Uwale a bakin ?ofa, sakin plask Win ruwan zafin da ke hannunta ta yi ?asa sannan ta yi saurin dafe ?irjinta. "Baban Rumaisa, idanuwana ne ke min gizo ko da gaske Abu?alib nake gani?"
"Inna Uwale, ke ma kina mamakin ganina kenan?" Abu?alib ya faWa yana kallon Inna Uwale.
Juyawa ta yi ta shige cikin asibitin, Umma barci take sai Rumaisa da ke zaune tana karatun Al?ur'ani mai girma. "Rumaisa ga yayanki Abu?alib nan."
Zumbur ta mi?e tsaye, "Inna Uwale da gaske, ina Yaya Abu?alib Win?" Kafin ta rufe baki suka shigo cikin Wakin tare da Abu?alib Win. "A she zan ga wannan ranar kusa haka?" Ta faWa tare da yin hanzarin rungume shi.
?ago ta ya yi shi ma idanuwansa sun cika da hawaye, "Rumaisa don Allah me ya same ni? Me ya samu Ummana? Ina Lilbirrah kuma?"
"Uwale, Rumaisa, kamar muryar Abu?alib nake ji..." Muryar Umma da yanayin rashin lafiya ya sa ta dishe ta ratsa cikin Wakin. Da sauri Abu?alib ya saki Rumaisa, gaban gadon ya yi suka ya tsugunna yana, "Ummana, ba kama ba ce. Ni ne, muryar Abu?alib Winki ce."
BuWe idanuwa Umma ta yi, domin ji take kamar mafarki ne take yi, cikin kasa gaskata ganinsa da take yi, ta ce, "Rumaisa Abu?alib yake min gizo, yanzu na gama jin muryarsa na buWe idanu kuma shi Win nake gani."
Rumaisa ta matsa gab da ita, "Umma ba mafarki ba ne, kuma ba gizo ba ne Yaya Abu?alib ne, shi ne da kansa."
Hawaye suka biyo gefen fuskarta, ta yun?ura da ?yar da nufin mi?ewa, da sauri ya sa hannuwansa ya mi?ar da ita zaune. Baya ya yi nufin yi, da sauri Umma ta ri?e hannunsa, kallonsa take, irin kallon da ke bayyana tsananin soyayya ga wanda ake mashi, kallon da ke nuna kewa da zallan kaWaicin da aka shiga na rashin wanda ake yi ma shi. "Abu?alib..." Ta faWa ta kasa daina kallonsa. Shi ma ita yake kallo, cikin dusasshiyar murya ya ce, "Ummana." Sakin hannunsa ta yi ta jingina da pillown da aka saka a bayanta, juyawa ta yi gefe a dake ta ce, "Rumaisa kin faWa masa sa?ona? Kin faWi wasiyya ta gare shi?"
Gaban Rumaisa ya buga a tare da na shi, bakinsa na rawa ya ce, "Rumaisa wa ce wasiyya Umma ta ba da a faWa mani?"
Kallonsa take tana hangen rauni da tashin hankalin da yake ciki, sannan kuma Umma ta yi umarnin faWa mashi wasiyyar da ta bayar a faWa mashi, tabbas yana bu?atar tallafi yana bu?atar samun sau?i daga goran wahalar da ya afka. Shurun da ta yi ya sa Umma faWin, "Ki faWa mashi, ko da rai ya yi halinsa gare ni na yafe masa duk abinda ya yi mani, amma ba zan amsa mashi maganar shi ba a yanzu, ba zan sake saka shi idanuwana ba har sai ya gano mani Wiyata Lilbirrah a duk inda take cikin faWin duniyar nan, idan har ina raye zan ci gaba da mu'amala da shi ne idan ya dawo da ita gare ni, ya wanke dukkan ba?in fentin da ya yi mata, ya dawo da ita cikin aminci. Wannan ita ce wasiyyata gare shi, ko da na mutu tabbatuwar yafiyata gare shi shi ne cika wannan aikin? Saboda haka ki ce masa ya fita."
"Ummana," Abu?alib ya faWa yana ri?e tafin hannunta. Ba ta juyo inda yake ba, cikin sha?a??ar muryarta ta ce, 'Na ce ka fita, idan kuma kana son ?arasa ni ne ka fi gaba da zama."
Rumaisa ta yi saurin cewa, "Yaya Abu?alib ka yi ha?uri ka fita, zan yi maka bayanin komai, ta ?are zancenta tana hawaye.
Inna Uwale da Baban Rumaisa suka yi saurin cewa, "Umma ki taimaka ki ?yale shi mana, ki mashi uziri."
"Baban Rumaisa idan za ya fita ku fita tare don Allah..."
Sosai Abu?alib ke kuka, ko kaWan ya kasa ko da motsi balle ya tashi daga gaban nata.
"Umma..." Tari ta soma yi, wanda cikin rikicewa da kaunar lafiyar Umma Rumaisa ta ce, "Yaya Abu?alib ka fita zan maka bayani, idan Umma ta fara tarin nan si?ewa take yi."
Mi?ewa ya yi da ?yar ya fita yana jin jiri na Wibarsa, Baban Rumaisa ya bi bayansa, dukansu zuciyoyinsu babu daWi.
Yana fita Umma ta saka sabon kuka, tana tuna abinda ya faru. Inna Uwale ta ce, "Umma ki yi ha?uri ki yafe ma Abu?alib, ki ga yadda ya kasance gare mu ko tunawa da mu ma baya yi, yau ga shi ya zo har inda muke, mu godewa Allah."
"Uwale, kin san wane hali Lilbirrah take ciki? Tana raye ko a mace take? Ba zan kula shi ba kamar yadda na faWa har sai ya mai do ta gare ni."
Rumaisa ta cigaba da share hawaye, tunanin wane hali Lilbirrar ta kasance ya taso cikin ranta.
Inna Uwale ta Wauko rubutun da Malam Saleh ya ba ta, "Umma ga shi Malam Saleh ya ce ki sha." KarSa ta yi kasantuwar dama lokacin garin ya waye, shan shi ta yi kaman ruwa ta koma ta kwanta.

Ta janibin Abu?alib kuwa cikin wani kalar yanayi ya ce ma Malam Abdulhadi, "Baba wai me ke faruwa? Na gaza gane komai."
"Yanzu mu tafi gun Babanka, shi zai yi mana bayanin komai." Sai da Baban Rumaisa ya kama hannunsa suka tafi zuwa gidan Malam Saleh.

&&&

BADIYYAH

Ganin sam ba ta gabanshi ya ida tada hankalinta, kai tsaye gidansu ta nufa. Tana isa ta iske gidan rufe Maman ba ta nan, sosai ta Wimauta da rashin ganinta ga rashin jinta a waya da ba ta yi ba tun suna Vienna. ?ayan gidansu ta shiga tana yin sallama gidan sun yi bula?ai da ita kamar ba su ga kowa ba. Tsaki ta ja, cikin isa ta wuce Wakin Babansu, waya yake sai da ya gama tsaf sannan ya juyo wajenta, "Baban Nana barka da safiya, ina kwana?"
"Lafiya ?alau," ya amsa a gintse.
"Baban Nana, da ma in ce ina Mom take?"
"Wa ke nan?" Ya tambaya kaman bai taSa sanin wace Mom Win ba.
"Baba, Mama nake nufi."
"Ba ta sanar da ke inda take ba?'
"Eh Baba, yanzun nan na diro ?asar fa."
"Madallah to ya yi. Sai ki je ki iske ta can Shargalle, tana can ai."
Ji ta yi cikinta ya juya, "Baba Shargalle kuma?"
"Ina can ne tushen ku ko? To tana can, sai ki same ta can.
Zaune ta yi kaman an dasa ta, ganin ba ta da niyyar tashi ya sa shi mi?ewa ya baro maga Wakin.
Mi?ewa ta yi a sanyaye ta fito. "Mun huta dai da mugun iri, irin butulci da mugun abu, sai a gaida gida Umma ta gaida Assha." Muryar Waya daga cikin matan gidan ta dake ta, ko juyawa ba ta yi ba ta fice waje.
Ta daWe tsaye bakin hanya nisawa ta yi, "Wallahi ko me ake yi dai yanzu ba zan koma ?auye ba, ta ya zan koma na tashi a tutar babu kenan, ba ni ga tsuntsu ba ni ga tarko, ba zai yiyu ba. Bara na koma gidana, idan na je na nutsu sai na tafi wajen Mama, don haka can zan tafi sai dai komai zai faru ya faru. Napep ta haye ta ba shi umarnin ya kai ta gidan nata da ke Modoji.


SH 14


Kamar Ra?umi da akala AbuDalib ya bi bayan Malam Abdulhadi zuwa gidan Babansa Malam Saleh, sun tarar yana zaune makarantar Allo yana fama da dalibai. Bai ji mamakin ganin AbuDalib ba kamar sauran, sai dai ya daga kai ya kalle shi, duk ya firgice ya fice hayyacinsa. Yana isa wurin Malam Saleh ya tsugunna gabansa, hawayen da yake ta faman yi suka cigaba da sauka kan dandamalin fuskarsa, murysa a dishe ya ce, "Baba& Baba na shiga uku, Baba ina cikin tashin hankali& Baba me ya same ni, me ke faruwa da ni?"
Malam Saleh bai ce masa komai ba ya mi?e tsaye ya dago AbuDAlib. Kuka ya fashe da shi sosai, "AbuDalib." Baban ya kira shi cikin taushin murya.
"Na am Baba," ya fada yana fashewa da kuka sosan gaske. Cikin gida suka shiga kai tsaye dakin Malam Saleh suka yada zango. Zaune ya yi ya tisa Abu?alib Win gabansa, kuka yake yana sauke ajiyar zuciya, sai dai ya yi mai isar shi Malam Saleh bai ce mashi komai ba haka shi ma Malam Abdulhadi baban Rumaisa duka idanuwa suka sa mashi, kowa da abinda yake tunani a ransa. Sai da ya nisa ya rage zugin da zuciyarsa ke yi sannan ya samu'yar guntuwar samu nutsuwa, Malam Saleh ya nisa ya soma magana,  AbuDalib, ka nutsu dukkan abinda ya yi farko zai yi karshe, wannan rubutacciyar kaddararka ce, haka Allah ya hukunta maka tun kafin halittarka.
 To ni Baba me ya same ni ne?
 AbuDalib zan so bayyana me ya same ka Win a abunda Allah ya nuna mini, amma na fi son sai gaban Ummanka, domin duk abin nan da ke faruwa babu wanda ya kai ta shan wahala. Kuma idan ta ga komai, watakil za ta karbi uziri har ka samu ganinta.
Baban Rumaisa ya dago a sanyaye,  Ka ji abinda ta fada ne Malam?
Jinjina kai ya yi,  Eh Uwale ta kira ni ta fada mani. Kar ku yi fushi ku karbi uzirin Ummah, tana cikin ?uncin zuciya sosai, 'yarta guda aka salwantar. Sannan kamar yadda ta ce, ka yi kokari ka shiga neman Lilbirrah tana nan cikin ?asar nan, sai dai sanin takamaiman inda take sai Allahn da ya yi ta.
"Baba, to ni me na yi ma Lilbirrah wai da gaske ni na kore ta da kai na? Khouhar Wina...
 Na ce ka bar wannan maganar, na fi so a yi ta duka gaban Umma.
 To Baba. Amma duk me ye silar wannan? Baba wallahi ni ban san na aikata duk abinda ake tuhumata na aikata, wallahi ban aikata ba Baba.
 Abu?alin mu musulmi ne, kyautata zato ga kowane mutum a gare mu wajibi ne, ban san wa zan dauki wannnan laifin na dora mashi ba, amma Allah zai bayyana ko waye ya yi maka wannan abun. Batun ba ka san ka aikata ba, za mu iya karSar uziri saboda ba halinka ba ne.
Baban Rumaisa ya yi karaf ya ce,  Malam, wallahi ni dai ba na raba daya biyu wannan abun daga matarsa ne ita da uwarta. Kuma wallahi kamar yadda ya ce, ni kaina sai daga baya na ri?a jin abinda na aikata kamar al'mara, ka duba sirrin da na ke ri?e da shi shekara da shekaru amma ban bayyana shi ba tsawon lokacin sai yanzu, wannan abun takaici har ina, shi ya sa sam bana ganin laifin Umma...
Kada kai Malam Saleh ya yi,  A ah ba za mu ce haka ba, ba za mu ce matarsa ko wata uwarta ba, ko mene ne gaskiya za ta yi halinta, duk abinda kuka yi ko kuka ji kuma duka gaskiyar nan dai ?wara Waya za ta yi halinta.
Shi ko AbuDalib sauraren su kawai yake, zuciyarsa tunani take kala-kala wanda rabinsa yana wajen Khouhar Winsa.
"Baba, to ya za a yi har Umma ta zo mu ji abinda ke faruwa, ta yi fushi da ni sosai, kuma ko zan tafi neman Lilbirrah sai Ummana ta yafe mini."
"Idan ta ji sauki za a sallame ta a asibitin, to da zaran sun sallame ta Win sai a yi komai a gama."
"Amma Malam, ni na san Umma ba za ta yafe mana ba har ta koma gidana ba."
"Za ta koma Malam Abdulhadi, kai dai a yi hakuri a bi komai a hankali."
AbuDalib ya dago kansa da ke du?e cikin sauri, "Baba kenan Ummana ba ta gidan ma, to tana ina?"
"Tsawon watanni bakwai kenan ba ta nan."
Malam Saleh ya ce, "Wni gida suka koma ita da Rumaisa nan wajen tudun 'yan lihidda."
"Umman nawa, a gidan haya?" AbuDalib ya faWa cikin takaici.
"Ka nutsu ka daina zantukan nan komai zai wuce. Kar ka sa ma kanka hawan jini mana da ?ananun shekarunka."
"To Baba." Sun tattauna sosai kafin daga bisani Malam Andulhadi ya mi?e ya tafi gida shi kuma Malam Saleh ya tafi wajen Walibai. Zamewa Abu?alib ya yi ya kwanta ?asa cikin Wakin. Sai yamma ya farka daga barcin da ya yi nasarar sace shi, salloli ya yi saurin bayarwa saboda lokaci ya yi nisa. Bayan ya gama sallolin Malam Saleh ya shigo Wakin, "Sannu ka tashi ko, ina ta ?o?arin tashinka ka yi Sallah amma ko motsi baka yi."
Murmushin ya?e kawai ya yi, "Ka Wauki abincin gaya nan ka ci ka ji ko."
Kallon shi ya yi, "Baba Wallahi ni ko yunwa bana ji, na manta rabon da na zauna ma ko abinci na ci."
"To ka ci wannan ko yaya ne, tuwo ne zai maka sau?in ci."
"Na?oshi Baba." Malam Saleh bai kuma ce mashi komai ba ya ?yale shi.
"Yanzu tun da ka Wan huta, ka je gida ka huta, ka ga daga saukarka airpot ba ka huta ba, ka je ka yi wanka ka canza kayan jikinka."
Mikewa ya yi a sanyaye ya fice, yana fita maimakon ya tafi gidansa sai ya wuce asibitin da Ummansa take. A waje ya samu Rumaisa, saukin da Umman ta ji ya sa ta Wan sakewa har ta fito wajen Wakin. Tana ganinsa ta mike ta zo inda yake, "Yaya..." ta fada tana kallonsa.
"Rumaisa, ya jikin Ummana, zuwa na yi in sake ganinta."
"Da sauki sosai, tana shan rubutun nan da Baba ya kawo mata ta ce mana sai ta ji kaman an zare mata kaya a jikinta, ta ji sauki sosai."
"Ni so nake in ganta Rumaisa."
"Yaya AbuDalib, Umma tana kewarka sosai, amma kuma& " ta dan yi shuru.
"Amma kuma me Rumaisa?"
"Halin da zuciyarta ke ciki na rashin sanin inda Yaya Lilbirrah take da kuma irin kazafi da bakin fentin da aka yi mata shi ne ya hana ta karSarka, kuma Yaya duk da akwai lauje cikin naWi, Umma gani take kai ne ka yi komai."
"Rumaisa a faWa mani me na yi?"
"Yaya... Ni dai kawai kar ka damu Umma ta ji dadin dawowarka, dawowarka cikin family na tabbata tana cikin farin ciki. Nisawa ya yi, har a lokacin zuciyarsa karye take, "Rumaisa wai me ya faru ne, me ye na yi da kowa baya son faWa mani, na san dai ko mene ne na tafka babban kuskure."
"Yaya bayanin me ya same ka dogon labari ne."
"Ba za ki fada min din ba,"
"Uhmm, yadda ka ce Yaya tabbas ka aikata babban kuskure... To ni me zance ma wai, ko ma dai mene ne wannan munafukar matar taka ita ce silar komai."

"Da ma haka Baba ya ce, Wallahi sai na rabu da ita yau, yau dinnan Rumaisa."
Kallon shi take kamar zararre, "Yaya ka bari ka tabbatar tukuna, don Allah kar ka kore ta yanzu ka bari gaskiyar da ita kanta ba za ta yi mata musu ba ta bayyana sannan."
"Sai na rabu da ita na ce maki Rumaisa." Takawa ya yi cikin firgicin da yake ya isa bakin windown Wakin da Umma ke kwance, zaune take suna ta labarin da bai san ko me suke fada ba ita da Inna Uwale, ji ya yi zuciyarsa ta yi kewarta sosai, idanuwansa suna kallonta kamar sun jima da yawa ba su yi tozali da ita ba. Tuno maganganun da ta yi mashi yake yi, yana jin kanshi na sarawa. Umma ta lura da ana leke ta tagar, mikewa ta yi ta zo wurin don tabbatarwa, ido biyu suka yi da Abudalib din ya kasa Wauke idanuwansa daga kanta, "Ummana! Don Allah ki yafe mani."
Baya ta koma, "Ummana ni ne Abu?alib Winki fa..." Cik ta tsaya ta juyo tana kallonshi, "Abu?alib Wina... kai ne fa kuma na san kai ne, kai ne dai da na bawa amana ka ci, kai ne da na ba ka yarda ka ha'ince ni, ka karya al?awarin da muka yi da kai, ka salwantar min da 'yata guda wacce nake so fiye da kowa a rayuwata. Lilbirrah, Lilbirratah ban san inda take ba, tana a raye ko a mace cikin lafiya ko akasin haka, cikin ?oshi ko yunwa duka ban sani ba. Ta ya zan so sake haWa ido ma da kai, fuskarka ba?i take min kamar gawayi ko kaWan bana son ganinka, haskenka Waya ne wurina ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login