Showing 9001 words to 12000 words out of 55242 words

Chapter 4 - BA DON MACE BA BY FATIMA FANTAH.doc

Advertisement

22 Feb 2025

3656

tuni halayen 'yanuwana a jinsi ya daina ba ni mamaki, kuma tabbas zan yi duk abinda ta ce, har zuwa lokacin da abun ?aunata zai diro duniya, wanda za mu samu a nutse mu nemi mafitar rayuwarmu.
Toilet Win na shige na yi wankana, ina fitowa na wuce Wakina. Mai na soma shafawa, gani na yi gaba Waya jikina ya yi Wan kumburi ba da yawa ba, a kintacena cikina ya shiga wata na bakwai, shuru na yi ina bitar abubuwan da ke kawo kumburi ga mai juna biyu. Numfashi na sauke, domin ban san ta ina zan je asibiti ba, yadda na saba addu'a nake Allah ya raya min abun ?aunata ya kawo mini shi lafiya cikin wannan duniyar tamu mai cike da rikici.

Bayan na gama shiryawa kai tsaye Ipaja na nufa. KuWi ne dubu biyu na ri?o a hannuna domin yin sadaka kamar yadda na saba yi tun da na samu kuWaWen da Yunus ya ba ni.
Inda Maman Nana take zaune na nufa, duk da ba na magana, Maman Nana ta zayyana mani irin halin ?uncin rayuwa da take ciki a lokutan da nake zuwa bara. Na tausaya mata matu?a, hakan ya sa duk lokacin da na zo da 'yan kuWina ita nake ba wa. Kamar koyaushe zuwa na yi na ba ta kuWin. "Ban san sunanki ba har yau, amma yadda kike taimaka mani ni ma ba zan gajiya da yi maki addu'a ba kamar yadda kika bu?ata. Allah ya ba ki mafitar rayuwarki. Hannuwa biyu na haWa alamun yi mata godiya.
Ban jima ba na tashi domin komawa gida, tafiya nake yi a hankali. "Baiwar Allah... Baiwar Allah..." Na ji muryar da na tabbatar mammallakiyarta mace ce na faWa daga bayana. Juyawa na yi domin ganinta, muna haWa na ji gabana ya faWi, zuciyata ta buga da ?arfi. Da ?yar na fizgo numfashina da na ji yana kaiwa da komawa, "Sannu baiwar Allah..." Ta faWa mini cikin tsananin tausayi. "Ai na san ba ki magana, sannu kin ji. Wallahi kullum na zo gurin nan ina tausaya maki matu?a." Ta ?are zancen cikin gurSatacciyyar hausarta da ba ta fita.
KuWi ta mi?a mani, "Ga wannan kin sayi wani abun kin ji." KarSa na yi, na haWa hannuwana biyu ina mata godiya.
"Sai an jima." Ta faWa tare da juyawa ta yi tafiyarta. Ni ma juyawa na yi na tafi. KuWi ne dubu uku ta ba ni. Kai tsaye gida na koma, zaune na iske Saratu a ?ofar Wakinsu tana waya, sam bana jin yaren da take magana da shi wanda nake tsammanin yarbanci ne. Shigewa na yi Waki na Wora girki da nake yi kan murhun gawayi, bayan na Wora na yi alwala domin gabatar da sallar azahar.



SH 5


G.R.A
MODOJI


Sallama ta yi cikin falon gidan, a guje Badiyya ta fada jikinta, tana faWin oyoyo Mom. Sai da ta gama murnar ganinta sannan ta sake ta. A shagwaSe ta ce, "Mom..."
"Na am diyar Mom, duk kin bi kin Waga mani hankali." Turo baki ta yi, "Mom ba ki san yadda na gaji da jinyar nan ba, a ce mutum koyaushe yana barci, ko ya tashi fa kaman wanda ya sha kayan maye, a daddafe yake komai sai kuma ya koma ya cigaba da barcin, Wallahi ba ki ji yadda na gaji ba."
Murmushi Mom ta yi. "Ke ki kwantar da hankalinki, aikin ne da yawa shi ya sa aka Wauki lokaci."
"Amma yanzu komai ya kammala ko My Mom?"
"Komai ya kammala, ke dai mu je daga ciki."
"Yawwa Mommyna." Badiyyah ta ?are maganar da murnarta. Takawa suka yi a nutse suna mai da yadda aka yi har suka isa bedroom din ta da ke saman bene. Zama ta yi kan gado ta ce, "Mom ya ake ciki? Na fa ?agara na ji yadda aka tsaya."
"Kwantar da hankalinki, bari ki gani." Hannu ta sa cikin haWaWWiyar hand bag Winta ta fiddo wani magani. "Karbi wannan, yanzu da yake barcin nan kawai ki bude kwalbar ki saita daidai hancinsa, da zaran ya sha?a zai mance da komai kuma zai tashi daidai yadda yake, wannan gane-ganen da yake yi da abubuwan da yake ji duk zai daina, haka aka tabbatar mini."
"Yawwah Mom, ki ga fa tafiyar mu bai fi saura sati daya ba amma mutum baya hayyacinsa kamar mahaukaci, wallahi Mom ba ki ji yadda na gundura ba, kuma wallahi ba na so a ce ba mu samu damar yin tafiyar nan ba, ai ni aka fasa an tafka mini babbar asara."
"An tafka maki, ko an tafka mana, ke mu je maza ki sha?a mashi, ya mike ya warware a yi tafiyar nan." Karbar maganin ta yi ta ce, "Haka ne Mom, ba a bori da sanyin jiki, yanzun nan zan je na shaka mashi shi."
"Allah sarki, mu je in gan shi." Mikewa ta yi suka isa bedroom dinsa tare da ita, kwance yake yana baccinsa a nutse,. Badiyya ta ce, "Mom kin gan shi ko ya tashi da ya sha magungunan nan sai ya koma barcin. Kwana nawa ana abu daya, kuma abun ko sauki baya yi abun har mamaki yake ba ni ma fa. Uhmm, ba na gaya maki ba aiki da 'ya'yan Malaman zaure akwai wahala an ba su sun ci sun sha, dubi fa gumurzun da muka sha kafin a zo nan."
Wani motsi ya yi tare da juyawa, cikin ?araji ya furta, "Ummaaah! Lilbirrah!" Badiyya ta ru?un?ume uwar, sake maimaita sunayen ya yi guda biyu. Badiyya ta saki Mom tana wi?i-wi?i da idanuwana tana kallonta. "Ke Badiyyah da ma haka yake wannan abun?" Mom ta fada a firgice. Kada kai ta yi, "Bai taba haka ba Mom, hasali ma yana dan tuna abubuwa amma bai taba ambatar sunayen su ba." Dukar da kanta ta yi kasa, "Innalillahi, Mom kwalbar ta fashe." Ta ?are maganar a firgice. Zaro ido Mom ta yi, "?auki abun ki shafa a hancinshi, dauki ki shafa mashi na ce. Kin san nawa na biya kafin a yi mini wannan aikin dubu dari biyu da hamsin na bayar, haba Badiyya ya za ki saki kwalbar?"
"Mom wallahi tsoro ya ba ni, ban san ma ya faWi ba." Dukawa ta yi ta dauko kwalbar, abinda ke ciki mai kamar mai ya zube, sai dai Wan abunda ba a rasa ba. Matsawa ta yi inda ya koma barcinshi bai san suna yi ba, hannu ta sa ta lakaci maganin da ke ciki a hankali ta goga mashi a hancin. Juyawa ya yi tamkar yana sane da me aka shafa mashi, ya ?ara buWe ?ofofin hancinsa ya sha?a.
"Yawwah aiki ya yi dama haka Boka Rigijim ya ce zai yi." "Wai Allah Alhmadulillah, ai Mom hankalina har ya tashi, a ce ya tashi da wadannan mutanen a bakinsa ai kashinmu ya bushe kuma.
"?an buhun uba, yanzu kai da su Ummah kuma sai lahira kwa haWu." Badiyya ta faWa. Dariya suka yi gaba daya.
"Yawwah, komai ya kammala bara na tafi."
"Yanzu Mom komai lafiya?"
"Na ce maki garau zai tashi, ai mu dama mun san daga inda abun yake, saboda haka an ?aras." Dariya ta kuma yi, ta ce to Mom Allah ya kiyaye, sai kin ji ni zancen tafiyarmu. Tare suka fita suna kara tattauna abubuwan da suke son cimmawa a gidan Abu?alib.

&

ABU?ALIB
Wuraren ?arfe biyar na yamma ya tashi, hannu ya sa ya dafe kanshi da ya yi mashi nauyi, muryarsa a shake ya ce, "Shona& My Shona." Da sauri ta karaso cikin falon. "My Boo, ta fada tana zama gabanshi."
"Wanka nake so na yi." Ya faWa yana kallonta.
"Okay Bubuna bara na hada maka ruwan, ya karfin jikin naka, da sauki ko My boo, sannu ka ji," ta fada tana shafa fuskarshi.
"Na ji sauki sosai, ji nake kamar an cire min kaya, sam bana jin komai cikin kaina."
"Wayyoo dadi, Alhmdlillah. My Boo ya sami lafiya, haka nake ta son ji." Shafa fuskarshi ta yi, Haka nake ta son na ji ka faWa, Allah ya kara maka lafiya My King," bai amsa ba ya zuba mata idanu yana kallonta. Sumbatar gefen kumatunshi ta yi, sannan ta mike ta shiga toilet dinshi, ruwa masu dumi ta hada mashi cikin kayataccen jacuzzinshi, foitowa ta yi ta kalle shi tana murmushi.
"My Boo, na hada maka ruwan." Okay. Mikewa ya yi ya buWe wardrobe yabdauko rigar wanka. Rage kayan jikinshi ya yi sannan ya shige toilet din. Wanka ya yi zuciyarsa tana ta sake-sake da tunane-tunanen da ya rasa madafarsu.
Sai daya gama sannan ya fito, zama ya yi kan kujerar gaban mirror. Lotion din shi ya dauko ya fara shafawa, da sauri ta isa wajen shi ta karSa, "My king ciwon nan naka ya tayar min da hankali." Dan gajeran murmushi ya yi mata, "Ni ma ya ya daga mini hankali My, amma yanzu ji nake na yi garau don ma ciwon kai da nake ji kadan-kadan. Amma kar ki damu fa, i'm feel okay."
"Na ji dadi My, ka warke, yanzu bara na je na hada maka Dining, ka zo ka ci abinci, ina kallon fuskarkan nan mai kyau tana mun murmushi."
Jinjina kai kawai ya yi yana mayar mata da martanin murmushi, tana fita kai tsaye bedroom dinta ta nufa. Waya ta dauka ta kira Mom din, cikin murna ta ce mata "Mom, albishirinki, yadda kika faWa hakan ta kasance ya tashi tangarangam, kamar ba abunda ya same shi."
"Me na faWa maki, ai aikin mutumin nan ?arshe ne, sai ki mai da hankali kuWin aiki har da la'ada za ki wawuro mana."
"Mom ke ma kin san ba ki da matsala." Badiyya ta faWa suna dariya.
Tana ajiye wayar ta fice zuwa dining area, a nutse ya fito ya zauna kan Waya daga kujerun dining Win. "My Boo, har ka fito? Ka ga ban haWa abincin ba ko, ina fitowa na ji ina son zuwa toilet."
"Toilet kuma, Shona za mu ci abincin?"
"Sorry My. Kawai na yi no.1 ne fa."
"Okay. HaWa min abincin ina jin yunwa sosai."
"Okay. Let me do it quickly. Ba za ka jira ba." Kitchen ta shige ta fara harhaWa kayan tana ajiyewa. Bayan ta gama tsaf ta fara zuzzuba mashi, ci yake a hankali. Jefi-jefi take jifar shi da hira, amsawa yake yi kamar baya son magana har ya gama cin abincin gaba Waya.

&&&&&

Tun bayan komawar su asibiti jikin Umma ya dan yi sauki, har tana iya cin abinci sannan tana iya zama da zuwa toilet. Rumaisa ta kalle ta cikin tausayawa, tabbas Ummah ta hadu da jarabawa da kaddarar rayuwa, wacce ko a mafarki ba ta taSa tunano ta ba.
Abu kamar wasa har an kwashi tsayin watanni shida ciff ba tare da sun kara saka Yayansu AbuDalib a idanuwansu ba, haka sunan 'yaruwarsu Lilbirrah ya zama tarihi daga zuri'arsu, wannan abun takaici ne da ba?in cikinsa ya wuce a kwatanta.
Ummah ta fito daga daki ta nufi toiet a hankali. Kallon Inna Uwale Rumaisa ta yi, cikin sanyin murya ta ce, "Inna ranar nan kika ce za a shiga cikin lamarin nan na Yaya Abudalib, Umma kowa ya yi shuru ya rabu da mu, tamkar ba wanda ya san abinda ya faru, haka za a zuba idanuwa Badiyyah su cigaba da juya Yaya su kaWai?" Numfashi Inna Uwale ta sauke a hankali ta ce, "Ban mance ba Rumaisa, abun yana raina kamar kuWin haya, kuma tabbas zan Wauki mataki ba za mu zauna bisa hukuncin Umma ba, don ba mu san abinda su Badiyya za su yi a gaba ba. Alhamdulillah jikin Umma ya yi sauki, don haka da yamman nan zan shirya in fita idan na fita zan je can Yammawa wurin Malam Saleh, idan an gama abinda ake yi, an Wauki mataki Umma ta san komai."
"Shi ke nan Inna Uwale, amma idan Umma ta sani yanzu akwi matsala."
"Ki kwantar da hankalinki ba wanda zai sani, ba kuma abinda zai faru."
Jin takun Umma ya sa suka yi shuru suka daina zancen da suke yi. Wuce su ta yi ta koma kan gado ta kwanta, kallon Inna Uwale suka yi da Rumaisa, shuru ta yi alamun ba ta ji zancen da suke ba.

&
Inna Uwale tana fita kai tsaye Yammawa ta yi ma tsinke. A kofar gida ta samu Malam Saleh, kasantuwar yana cikin daliabai gaisawa kawai suka yi ta wuce cikin gida.
Inna Uwale suna cikin gaisawa da Sa'adatu matar Malam Saleh ya shigo. Cikin girmama juna suka sake gaisawa.
A hankali ta ce, "Malam na zo ne kan maganar Abu?alib, duk kun yi shiru tamkar Abu?alib ba jininmu ba ne, kun zuba ida kun bar waccen yarinyar ita da mahaifiyarta suna cin karensu babu babbaka."
?an gajeran murmushi ya yi irin nasu na manya, "Uwale, kin faWi jini ga Uba da ya haifi Wansa da kansa? Abu?alib fa Wana ne, Wan da na haifa. Kamar yadda bana mance karatun da ke kaina, sau Waya ba na mancewa da Abu?alib. Kamar yadda kika ce, na bar su ne su ci karensu babu babbaka, na bar su kuma na ga iya gudun ruwansu. Amma na lura ba su san me suke yi ba, kuma ba su san kawaici da kauda kai ba. Saboda haka sun yi nasu, muma za mu yi namu."

SH 6

LAGOS NIGERIA

Karfe sha daya na safe na fito domin tafiya Ipaja, a hankali nake takuna, gangarowar wata mota ya sani Wan dakatawa, duk da ban iya ganin mammallakin motar ba, amma zuciyata na ayyana mini macecina ne. A hankali motar ta rage gudunta lokacin da ta ?araso inda nake, sauke gilashin motarshi ya yi kamar yadda na yi tsammani kuwa shi ne. Cikin muryarsa mai dan kauri ya ce, "Amatullah," Wan murmushi na yi jin sunan da ya kira ni da shi. "
"Ama," ya sake fada yana kallon cikin idanuwana, da sauri na sauke kaina ?asa, gaishe shi na yi cikin yarena na bebenci.
"Lafiya lau," ya fada. Ya kike? Ya kika tashi?"
"Lafiya," na amsa mashi da yaren da nake yi.
"Ya Baby? Shi ma yana lafiya ko?" Kallonsa na yi ?wa?walwar kaina na tsere cikin dogon tunani, karo na farko da irin kalmar ta shiga cikin kunnuwana, ni ce uwa da Uban abun ?aunata, wani bai taSa jingina kanshi da shi ba balle ya tambayi kwana da tashin shi, ba wanda ya taba damuwa da shi, ba wanda ya taba tambayata game da shi ni, ni kaWai nake kulawa da wannan a kan shi. Take na ji idanuwana sun kawo ?wallan, hannu na dora kan cikin lumshe idanuwana na yi hawayen na ?ara malalowa.
"Sorry," da ya fada ta dawo da ni daga duniyar tunanina. hawayen da suka kwararo daga idaniyata. Kallona ya yi cikin tausayi yana kara maimaita sorry. Jinjina kai na yi alamun ba komai.
"Ban san sunanki ba, sai dai na kira ki da baiwar Allah shi ya sa kika ji na kiraki da Amatullah, kuma haka zan cigaba da kiranki har zuwa lokacin da kika yarda kika aminta da ni kika fada mini sunanki ko da rubuce a takarda ne." Bance da shi komai ba, sai aikin saurarenshi da nake yi.
"Kwana biyu ba na nan na raka Babana America wata seminar, shi ya sa kika kwana biyu ban leko ki ba. Kuma idan ba damuwa Amatallah mu je ki kai ni gidan da kike don Allah." Haka nan na ji zuciyata ta aminta da shi, ban yi gardama ba na juya alamun ya biyo bayana. Bai damu ba domin ya san ba lallai na aminta da shiga motarshi ba. A nutse na ci gaba da tafiya da takuna irin na masu juna biyun da suka kusa haihuwa, har muka isa daidai kofar gidan. Fitowa ya yi daga mota ya zagayo inda nake, kada kai ya yi yana jinjina yadda ya ga tsari da yanayin gidan. Ji na yi yana kiran yara da ke wasa can gefe, kayan abinci ya sa suka dinga fitowa da su, tun daga kan karamin buhun shinkafa, galon din mai taliya catton da makaroni da garin kwaki da sauran kayayyaki masu yawa. Sosai na cika da mamaki da al ajabin abinda ya yi.
"Amatullah don't worry for this, ni zuciyata na ayyana mani akwai wani boyayyen labari a tare da ke, kuma tana ayyana mini ke mutuniyar kirki ce sai dai wata kaddara marar daWi has separated you from your bleseed family, so ni na yi niyyah ina so don Allah ki zauna ki kula da kanki ba tare da kin kuma zuwa bara ba, ki kula da kanki kin ji." Jinjina kaina na yi hawaye na kuma wanke fuskata. Kudi ya miko ya ba ni, ban san ko nawa ba ne. "Ki karba mana komai na yi na yi don Allah ne." Nagode na fada mashi cikin yarena.
Juyawa ya yi ya shiga motarshi, har ya bace ma idanuwana ina ganinshi. Juyawa na yi na shiga cikin gidan, dukkan kayan da Yunus ya kawo mini sun shigar da su cikin dakina. Komawa na yi cikin dakin na yi godiya ga Allah tabbas dukkanin tsanani yana tare da sauki, kamar yadda Allah S. Ya ce, "Fa'inna ba'a dal usrin yusra." Duk yadda abubuwa suka yi tsananin sau?i na biyo bayanshi ko su kasance tare.
Dirshan na zauna ina ?ara duba kayayyakin, kaya ne da yawa har da su madara da bournvita da lipton da sauran kayan tea. Sosai na ji dadi har cikin raina. Alkhairi ya same ni dole na faWawa abokin hirata kuma abun ?aunata.
Cikin jin daWi na ce, "Abun kauna, ka ga taimakon Allah ya zo mana ko? Ka gani mun samu har da kayan shayi, abun kauna za mu sha dadi, kuma ba za mu mu ?ara fita bara ba, za mu huta abun ?auna. Za ni huta har zuwa lokacin da za ka iso gare ni, lokacin da zan sa ka cikin idaniyata." Murmushi na yi na shafa ina godiya ga Allah na saukin da ya zo mana lokaci daya. *

&
Cikin shauki ya shiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login