Showing 33001 words to 36000 words out of 124388 words

Chapter 12 - HALIN GIRMA Book Complete by Hafsat Rano .pdf

Advertisement

11 Mar 2025

7964

zuwan nasu da komai akan
maganar sai dai baya samun ta a waya wajen kwana uku kenan, yasan tana business sosai
kamar ma tana fita kasashe saro kayayyaki shiyasa yayi tunanin ko kila bata k'asar ne.
Kallon wayar tasa yayi, har lokacin haushin Maman yake ji musamman abubuwan da ya gano
akan irin rikon da tayiwa Fatiman tsawon lokaci be gane komai ba, har Marwan ya titse ya
tambaya ya kuma gaya masa komai abinda ya sake daga masa hankali sosai kenan. Kiran ne
ya sake shigowa ya daga ba dan yaso ba, dan dai kawai be san ko wani abu bane emergency
ya taso, sallama tayi ya amsa ciki ciki. Dama tasan za'a rina shiyasa kawai ta tafi kai tsaye akan
dalilin kiran

"Dama Zeenat ce ta ce na sanar da kai iyayen Bashir zasu zo gobe idan Allah ya kaimu."

"Su bari jibi gobe Yaya yana da abinda zai yi."

Yace mata kai tsaye

"Amma da ka barsu sunzo goben ba dole sai wajen Yayan ba ai."

"Haka tsarin mu yake tun farko, babu Kuma dalilin da zai saka na chanja yanzu dan anzo auren
nawa yayan, idan har ba zasu iya bari sai jibin ba sai ki nema musu wanda zasu gani a goben."

"Abin be kai haka ba ai, Allah ya kaimu jibin."

"Amin."

Yace ya katse kiran yana Jan tsaki, wato duk dadewar ka da mace ba zaka taba sanin wasu
daga cikin halayen ta ba har sai abu ya faru, lallai. Shi kadai yake ta wannan tunanin har
lokacin da zai kwanta yayi, ya kwanta da addu'ar Allah yasa komai ya tafi dai-dai goben.

***Duk cikin su babu wanda ya makara, suka tashi aka hau gaggayara gidan harabar da lungu
da sako su Habib suka taimaka aka tsaftace ko ina, dama dai a gyara yake saboda takanas aka
dauki me aikin kula da wajen amma duk da haka idan suka tuna bakin da zasu zo sai suga ya
kamata a sake gyara ko ina. Wajajen sha biyu cikin jagorancin Musaddik suka iso, cikin manya manyan motocin alfarma da
aka rubuta Emir Kano 1 guda biyu sai guda biyu dauke da tambarin Adamawa Palace.
Cikin kankanin lokaci unguwa ta dauka, mutane suka dinga lekowa daga gidajen su dan
tabbatar da abinda yaran su suka je suka fad'a musu, kowa ya leko sai ya rik'e baki cikin
tunanin abinda ya kawo irin mutanen gidan.
Cikin matuakr girmamawa Abba suka karbe su, sai dai sunyi tunanin zasu gansu a matsayin
mutanne da basu kai ba ko kuma level dinsu ba daya ba, amma sai suka ga akasin haka, cikin
girmamawa, karamcin da dattako suka zo musu, suka nuna Halin Girma, halin babban gida
babu fariya ko nuna su din wasu ne, cikin tattautasa harshe da girmamawa suka nemarwa dan
su kuma jikansu Muhammad auren Fatima. A take Abba yace an bashi. Su kuma nan take suka
gabatar da ranar da suke so a saka, babu musu nan ma Abba ya amince suka tsaida wata daya
kachal, shi din ma saboda Muhammad din ne ya bukaci haka, amma idan sune toh sati biyu
zasu saka.
Babu wani bata lokaci abinka da manyan mutane, masu Halin Girma, suka yi komai cikin sauki
sannan da zasu tafi suka gabatar da kyaututtuka daga iyaye da kakannin Muhammad din da
yake cikin al'adarsu idan za'a zo neman auren. Tarin kayan da suka kasance mota guda sai da
suka bawa su Abba mamaki, a gefen Abba aka ajiye mukullin motar nufin su har da motar da
duk abinda yake ciki kyauta ce ga sirikar Sarki Ahmad Santuraki, da iyalan gidan sa kafin
zuwan ta, sannan suka yi musu sallama suka tafi.


#HafsatRano
#ZafafaBiyar2021
Not edited
Ignore typos




Masu sharing sannun ku da kokari kunji? Allah ya shirye ku idan masu shiryuwa ne, idan kuma
ba masu shiryuwa bane toh... Kun san sauran dai😀

1/12/22, 21:41 - Buhainat: Halin Girma
    13

*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107* 

I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos.
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1ft46u5twk6r3&utm_content=nj79azb


***Sai da suka ga tafiyar su sannan suka dawo ciki, kowa da abinda yake cin sa a zuciya.
Tabbas sun amsa sunan babban gida, haka sun nuna Halin Girma da dattako na irin manyan
mutane da suka san mutunci da yakana.
Fadar irin tarin kayan da suka zo dashi ba abu bane me sauki, hakan ya dan tarsa tsoro a
zuciyar Abba, yake jin tamkar siyar da Iman din zai yi, wannan uban dukiya a matsayin
tambaya, ina ga idan aka zo auren? Basu da talaucin da arziki zai tsorata su, sai dai dole ne
suyi mamaki ganin uban dukiyar da aka lafto da sunan na Iman din ne, tun daga kan sutura
zuwa kayan kawa na mata, da kyautata gwala-gwalai tamkar ba'a san darajar su ba.
Haduwa suka yi suka tattauna yadda zasu adana komai saboda yadda rayuwar yanzu ta
zama ta rashin tssro, shawarar farko shine su bar maganar tsakanin su domin mata akwai sakin
baki musamamn idan abun da ya sha musu tunani ne, yanzu zasu yi ta kwazozotan sa har
wasu dake waje su samu damar aiwatar da mummunan kuduri akan su. Tabbas shawarar tayi dan da gaske komai na iya faruwa idan maganar ta fantsama shiyasa
kawai a take aka fita da motar da duk abinda yake ciki daga gidan zuwa in da zai fi zama safe
kafin bikin yazo kusa sosai sai ayi abinda ya dace dasu, ko bata kayanta ta tafi dasu tunda
dama su chan babu wani tsoron rashin tsaro ta ko ina zagaye suke da Jami'an tsaro. Karshen
magana kuma ma shi Muhammad din kansa, su ne tsaron ma baki daya. Da wannan shawarar
suka tashi bayan Abba ya sanar musu da zuwan iyayen Bashir a gobe kamar yadda Mama ta
shaida masa.

Sake gwada kiran Maman Iman din yayi bayan ya koma gida, cikin sa'a kuwa kiran ya shiga,
bata wani jima tana ringing ba ta dauka a nutse cikin sallamar ta da muryar da yake jin ta kullum
a bakin Iman din, maganar da sak ta mahaifiyar ta, hatta nutsuwar ta irin ta uwarta ce shiyasa
yake jin ba zai iya mantawa da ita ba ko da shekaru sun ja, duk da yanzu babu batun soyayya a
tsakanin su tun da be riga yasan matsayar da take a yanzun ba ko da aure ko babu, a dai
kwanakin baya ya samu labarin tayi aure har da albarka Yaya a tsakanin su.

"Ina wuni Abban Iman?" Ta gaishe shi jin yayi shiru bayan amsa sallamar ta

"Lafiya Lou Maimunatu, ya gida ya kowa da kowa?"

"Kowa lafiya Alhamdulillah, Iman fa?"

"Tana nan lafiya."

Shiru sukayi baki daya, kowa da kalar tunanin sa a ransa, shine ya katse shirun ta hanyar cewa

" Inaso zan kawo miki ita kamar yadda nayi miki alkawari idan auren ta ya tashi, ta samu miji
har an tsaida rana wata daya, in sha Allah a tsawon wata dayan nan zata zauna a wajenki, a
matsayin ki na mahaifiyar ta sai kiyi duk abinda ya dace, kiyi hakuri da Kaddara, kiyi hakuri!"

Wani irin yar taji har cikin kanta, Iman dinta har ta girman da zata yi aure, rayuwa na gudu
sosai, tana tuna lokacin da ta dawo masa da ita, da irin tashin hankalin da ta shiga a rashin ta
wanda bata taba tunanin zata dawo daidai ta cigaba da rayuwa ba, a lokacin tunani take
rayuwarta ta kare gaba daya, amma kuma sai gashi ta cigaba da rayuwa duk da babu ranar da
zata fito ta fadi bata tuna yar tata ba, amma ya zatayi? Mutane na fifita al'ada akan addini. Ta
sani sarai uwa ce taka da ikon rik'e yarta har zuwa aurenta, tare da sharadin kula da duk wata
bukatar ta daga mahaifin ta, sai dai idan anji tsoron tarbiyyar da zata samu a wajen uwar, toh
amma a lokacin wa take dashi da zai tsaya mata? Bayan iyayenta da take ganin su a matsayin
gatan ta sun kekashe kasa sun ki amincewar da rikon nata a wajenta? A lokacin da akwai
karancin shekaru a tare da ita, amma da ace yanzu ne, babu me raba ta da yarta kuwa, duk
yadda zatayi zatayi ta tabbatar da ta rik'e ta a wajen ta. Ta bata kulawa da dukkan gatan da take
bukata.

"Allah ya sanya alkhairi, ya nuna mana lokacin."

Kawai tace dan bata kuma san me zata ce masa ba, taji dadi da ma ya cika alkawarin sa, zatayi
kokari a dan zaman nan ta koya wa yarta kaunar ta da sabawa da ita da yan uwanta, sannan ta
nusar da ita rayuwa da yadda zata kula da auren ta. Sallama sukayi da alkawarin ana gobe zai
kawo ta, zai kira ya sanar mata. Godiya tayi masa dan har gobe tana ganin kima da mutuncin
sa, mutum ne shi na gari, me kirki da son iyalin sa.

Bayan gama wayar da sukayi ne zuciyar sa ta gwada masa kiran Zeenat ya sake gwada
tankwarata, idan Allah ya taimake shi ta hakura sai yafi kowa murna, dan yanzu bashi da
babban tashin hankali kamar auren zeenatun da yake da yakinin zai iya zamar mata wani
Babban tashin hankali a gaba. Kiran nata yayi, tana dagawa yace ta matsa daga wajen kowa zai yi magana da ita, da ido ta
kalli Mama dake zaune ana maida maganar auren Zeenat din da Hajiya ta fice zuwa tsakar
gidan.

"Abba na fito."

"Yawwa zeenatu, magana nake so muyi a matsayi na, na mahaifin ki, kin san dai ba zan taba
zabar miki abinda zai cutar dake ba, ba kuma zan ga cigaba a gareki na dakushe ki ba, ina
neman alfarma, kiyi hakuri da Bashir ki kawo wani ba shi ba,nayi miki alkawarin tsaya miki
kinji?"

Gabanta ne ya fadi, a tunanin ta an gama wannan babin, sai gashi Abban ya dawo da shi yana
kuma kokarin daure ta da jijiyoyin jikinta.

" Kina jina zeenatu?" Ya sake fad'a cikin yanayi me wahalar fassarawa
Shashekar kuka yaji, ta fashe da kuka cikin muryar kukan tace

" Dan Allah Abba kayi hakuri?"

"Ai ba laifi kikayi min ba Zeenatu, alfarma kawai nake nema a matsayi na, na mahaifin ki."

"Abba dan Allah kayi hakuri, wallahi ba zan iya hakura da Bashir ba."

Kamar saukar aradu haka Abba yaji, ya dafe kansa ya shiga karanto innalillah wa inna ilaihi
rajiun, babu babbar jarrabawa irin yayanka suyi rashin sa'ar miji, duk abinda yaje ya dawo dole
kana ciki, kamar ka saida akuyar ka ne tazo tana ci maka danga, baya fatan hakan ta faru ga
ita, shiyasa tun farko ya hakurkurtar da zuciyar sa be ga laifin ta ba sai na Mama, amma yanzu
ya tabbata abinda Zeenat din take so shi Maman take goyan ba, dama mafiya yawan lokuta
uwa na tafiya ne da ra'ayin yarta.

"Shikenan zeenatu, duk abinda yaje ya dawo karki kuka da kowa, ki kuka da kanki."

"Abba dan..." Kafin ta kai karshe ya katse kiran, Jan kafarta tayi ta koma ciki tana jin a ranta tayi
abinda ya dace, a kalla ta yi kokarin kare soyayyar ta ko ba komai idan akayi auren Abban zai
hakura ya sakko.

"Lafiya?" Mama tace tana kallon ta.

"Ya kukayi da Baban naki? Maganar dai ce ko?"

Da kai ta amsa mata da eh, tsaki Maman taja

"Shine kike kuka ko me? Ni wai Zeenat asiri Bashir yayi miki ne? Da bakya ganin kowa da
komai sai shi?"

Kanwar Maman Atika ta fad'a cikin bacin rai

" Ni banga wani abun naci a Bashir din nan ba, tunda mahaifin yarinyar nan baya so toh a
hakura mana? Iyaye maza sun fi mu tunani da hangen nesa."

"Toh Atika ya za'a yi? Shi ma fa duk zuga ce wallahi, ai da be san da hakan ba sai bayan yaga
mijin da yar lelen tasa ta samu, shikenan kuma sai kananan maganganu bansan daga ina ba,
amma ina kyautata zaton daga wajen Gaji ne, dan ita kadai ce take sauya musu tunani da raayi
dukkan su, ita kuma na tabbata munafurcin Iman ne dan ko yaushe tana wajen ta."

"Duk wannan ta tunani ne Yaya Hajara, bamu da tabbas din hakan, kinga dai yadda Dr ya dage
ya kamata ace kin bashi dama kinji ta bakin sa akai."

"Kyale shi kawai, zai sakko ne."

"Me yace miki?" Ta tambayi Zeenat din tamkar abin be dameta ba.

"Cewa yayi nayi masa alfarma na hakura da Bashir."

"Ehen kinji? Har ya saukar da kansa a matsayin sa na mahaifi yace yana neman alfarma kema
Yaya Hajara kinsan da matsala."

" Me kika ce masa ke kuma?" Taki amsa atikar ta tambayi Zeenat din.

" Hakuri na bashi." Tace tana rakubewa a gefen Hajiya da tunda aka fara maganar bata saka
musu baki ba sai lokacin

" Gaskiya da kun hakura kun bi zabin Ibrahim, a kalla shi namiji ne yafi mu dukka tunani da
hangen nesa."

" Hajiya toh ya za'a yi? Lokaci ya riga ya wuce bata kula kowa sai shi, yaushe zata fara daga
farko kafin ma ta samu saurayin su fuskanci juna a zo maganar aure."

" Duk wannan me sauki ne akan ka dauki dan ka, ka kaishi inda zai Sha wahala."

" It's better to marry late than to marry wrong." Atika tace tana girgiza kafarta

" Khair in sha Allah, babu abinda zai faru."

Maman tace a kasan zuciyar ta tana jin tsoron abinda zai je ya dawo, ita kanta ta fara tsoron
yadda Abban ya kafe ta tabbata akwai babban dalili, amma kuma ta Ina Zeenat din zata fara?
Hasalima bata da farin jinin samarin duk asalin su Iman suke so sai ita maman tayi amfani da
wannan a juya mata kansu zuwa Zeenat din dan ba zata iya gani Iman din tayi aure musamman
auren babban gida ita kuma Zeenat din na zaune a gida.


***Da sauri ya karasa part dinsa yana jin kayan na masa nauyi sosai, yau tun safe Bubu ya Aiko
masa da kaya sannan ya bukaci ganin sa a kofar part dinsa dan shiga tawagar sa zuwa Fada,
haka ya tashi ya shirya ba dan yaso ba ya fita. Tun lokacin sai yanzu ya samu dawowa part din
sa, yana shiga ya hau cire kayan yayi wurgi da rawanin yana jin shi sakayau. Allah Allah yake
ya samu feedbacks din aikin da ya saka Musaddik sai gashi kuwa ya kirashi adaidai lokacin,
dagawa yayi yana rage daga shi sai singlet da boxer kasancewar zafi ya fara hurawa kadan

kadan ba kamar kwanakin baya da ake sanyi sosai ba.

"Gani fa ga mutumin ka." Musaddik yace yana dagawa

"Da gaske? Sharp sharp haka? Ok bari na kiraka Video Call."

Ya katse sannan ya kira video call, a daidai saitin fuskar Bashir Musaddik ya saka wayar yadda
yana dagawa Moh zai fara ganin sa. Yana durkushe tamkar me neman gafara, wata dariya ce ta
zowa Moh, yayi murmushi kawai yace

"Oga Bashir barka da warhaka."

"Dan girman Allah ranka ya dade kayi hakuri, wallahi bansan gidan da kaje Neman aure bane
nima naje, wallahi kuskure ne kawai amma kayi hakuri."

"Ai ba laifi kayi ba Bash, ni hakan yayi min dadi sosai, kuma ina tayaka murna, kaga ni da kai
mun zama yan uwa tunda zamu auri yan uwa."

"Tuba nake ranka ya dade!" Yace yana kasa da kansa

"Dago kanka bash, bafa wani laifi kayi ba, aiki nake so na baka, bana son kuskure ko kadan a
ciki, idan har kayi min yadda ya dace akwai babban tukuiwaci."

"Hakan shi yafi komai sauki a wajena ranka ya dade, fadi ko menene ."

"Yaushe za'a je tambyar maka auren?"

"Gobe ne ranka ya dade, amma idan kace a fasa na fasa wallahi."

Girgiza kai yayi

" Ba za'a fasa ba, Ina so idan sun je su nemi a saka musu wata daya!"

" Wata daya!" Ya zaro ido

" Wata biyar nace ko shekara, ban shirya ba wallahi,dan dai bana son na rasata ne."

" Ba zaka taba rasata ba, ni zan maka komai na auren tun daga lefe har gidan zama zan baka,
ni dai kawai kayi duk abinda nace kayi."

Dukawa yayi jiki na rawa

" Nagode nagode Allah ya kara girma, zanyi duk abinda kace, ba zan yi komai ba sai da sanin

ka."

" Good, yanzu aikin me kake?"

" Buga buga kawai, sai kuma aiken Hajjaju idan ya tashi."

Dariya sosai Moh yayi, ya hangi tsantsar mutuwar zuciya da son zuciyar a tattare da Bashir din,
mikar da yan yatsun sa yayi baya, ya dawo dasu gaba suka bada sauti kafin ya katse dariyar
yana zama so serious.

" Abinda nake so kayi min, zaka ji daga bakin Musaddik, bana son kuskure ko kadan, komai Ina
so ya tafi cikin tsari , Ina so gobe ka dauki hanyar Katsina, zan aiko maka da sako ka kaiwa
Gimbiya Zeenatu, hakan zai sake goge shakku ko wani tunani akanka."

" Nagode ranka ya dade, nagode nagode."

" Karka damu, kai dai kayi abinda nace, bana son kuskure ko kadan!"

" Da yardar Allah zaka same ni da bin duk umarnin ka. "

Daga masa kai Moh yayi sannan yace

" Guy!"

" Yeah Captain!" Musaddik yace yana matsawa daga wajen da Bashir din yake

"Ka kula dashi sosai dan dan iskan kansa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login