Showing 3001 words to 6000 words out of 124388 words

Chapter 2 - HALIN GIRMA Book Complete by Hafsat Rano .pdf

Advertisement

11 Mar 2025

7942

abincin ta sannan ta kwanta bacci. Sai da rana ta soma dagawa sannan ta koma ta
daura girkin rana,ta gama kafin lokacin tafiya islamiya, ta dauki na Gaji ta kai mata ta sake
zama tana jiran lokacin ya cika.

"Yaki takwara ta, zo nan." Gajin tace tana daga zaune a in da take

"Me yake damun ki?"

"Na'am?"

"Fad'a min idan kina da wata matsala ne, na dade ina lura da yanayin rashin walwalar ki, sai dai
na kan dauki hakan a matsayin halitta, amma kuma jiya sai abun yazo kaina, na dinga tunanin
ko dai kina da wata damuwa ne? Da kika kasa sanar wa wani kika barta a ranki."

"Babu komai Gaji, yanayi na ne a haka amma ni babu abinda yake damuna."

"Kin tabbata."

Daga mata kai tayi tana jin kamar ta saki kuka, ga dama ta samu amma bata da ikon furta wa,
toh tace mene ma wai? Hakan ba shi zai hana Mama ta daina muzguna mata ba, Kai tsaye zata
kare kanta da zarar Gajin ta tuhume ta karshe kuma abun ya koma kanta kowa ya cigaba da
mata kallon marar kirki ko kuma wadda bata san halacci ba. Shiyasa ta zabi yin shiru kawai dan
fadar ba zata sauya komai ba, su duka sun yarda da Maman yarda irin ta ban mamaki.

"Ai nasan bangaren Hajara baki da wata matsala dama, na dai zata ko damuwa ce dai irin ta
rashin maman ki kusa dake, duk da bani da haufi akan kulawar da kika samu iyakar abinda zaki
samu kenan ko da ita mahaifiyar taki ce."

"Haka ne." Tace a kasalance

"Yawwa ki dinga dan daurewa kina shiga cikin yan uwanki kinji? Zaman shirun da kike babu
dadi."

"In sha Allah zan gyara."

"Yawwa... Haka nake son ji."

"Ya batun yajin aikin nan kuwa? Kun dauko karatu tiryan tiryan yajin aiki ya tsaidaku da tuni
wata maganar ake ba wannan ba."

"Wallahi shiru ba labari, muna dai ta addu'a Allah ya sa a daidaita."

"K'asar nan kenan ai, dan karatun ma yanzu nema ake a hana dan talaka yin sa."

"Wallahi."

" Allah yayi mana maganin abinda yafi karfin mu."

" Amin ya Allah!"

" Shiyasa nace duk ku fidda mazaje kawai da zarar wadanchan sun tafi kuma azo ayi naku
zaman haka nan ba zai yiwu ba."

Shiru tayi gabanta ya fadi, bata son taji ana maganar auren su, gashi kuma taga alamar ba za'a
dauki lokaci ba za'a ce su fidda mazaje, ya zatayi da ranta? Da ganin suna makaranta yasa
maganar ta lafa amma yanzu yajin aikin da aka tafi da ba'a san ranar dawowa ba ya saka
iyayen nasu yanke shawarar suma su aurar dasu kawai sai karasa karatun a dakin su.    Tashi tayi tayi ma Gajin sallama ganin lokaci yayi, taje tayi alwala ta saka Hijab dinta ta fito,
a falo ta tarar da Mama tayi saurin tsugunnawa ta gaishe ta

" Mama barka da gida."

" Saura idan an tashi ki tsaya shiririta a hanya ko ki tsaya gidan Gaji karki zo kiyi abinda ya
dace, jiya kam kinci darajar babanku yana nan."

"In sha Allah." Tace sannan ta mike ta fice Maman ta rakata da harara.

****Sati biyu tsakani aka fara bikin gidan nasu, duk yadda taso gujewa wasu abubuwan amma
Maryam bata barta ba, komai idan za'a yi sai ta sakata a ciki, haka kunshi da gyaran kai tare
suka je da wata kawar Maryam din.
  Alhamis suka fara bikin, a compound din gidan Anty Mabruka sukayi bridal shower iya su da
kawayen su, juma'ah akayi kamu asabar aka daura aure hade da yini, lahadi aka kai kowacce
gidan ta.
   Ranar litinin suka tashi gidan da sauran bakin da basu riga sun tafi ba wanda yawanci
dangin Gaji ne, a babban kitchen din gidan suka hadu aka hada breakfast Masa da miyar
taushe, har rana tayi sosai basu kammala ba hakan ya sake haifar mata da wata irin gajiya
bayan wadda take fama da ita, tasan halin Mama sarai idan ta makale taki fitowa ayi aikin da ita
duk da akwai masu yi din amma dolen ta ne ta fito, duk da hakan ba karamin taimaka mata yayi
ba wajen gogewa da kalolin girke-girke mabanbanta. Sannan uwa uba girkin mutane da yawa
wanda ba kowa bane ya iya.
   Da saurin ta, ta karasa dakin su, ta kwanta a gefen gadon saboda wani irin sanyi da take ji
alamun zazzabi ne ke neman rafke ta, rawar sanyi ta fara hakoranta suka shiga haduwa waje
daya, ta saka hannu da k'yar ta jawo bargon Zeenat din ta lulluba.
   Shigowar ta kenan ta tsaya daga kofar

"Kut! Lallai ma." Tace tana karasawa ciki, ta fuzge bargon da karfi

"Dan Allah zee ki kyale ni bani da lafiya." Tace muryar ta chan ciki. Shiru Zeenat din tayi tana
kallon ta, sai kuma ta sakar mata bargon ta juya ta fice daga dakin. Har dare zazzabin be sake
ta ba, babu kuma wanda yazo neman ta. Tayi tunanin Zeenat din zata fad'a wa Maman ne duk
da bata saka rai ba, amma jin shirun ya tabbatar mata da ta fad'a mata dan da ba haka ba da

tuni Maman ta turo neman ta akan wani aikin.
   Wajajen Tara Zeenat ta dawo dakin, ta kalle ta a zaune saman abun sallah ta kudundune,
juyawa tayi ta fita ta dawo da paracetamol a hannun ta da ruwa ta mika mata. Karba tayi da
sauri tayi mata godiya, bata amsa ba ta sake fita sai gata ta dawo da katifar Iman din, ta
shinfid'a mata sannan ta dauko bargon ta, ta dora mata akai ta haye gadon ta kwanta ta rufe
idon ta. Sosai Iman taji dadi a ranta, ko ba komai tayi mata abinda bata taba ba, tashi tayi da
k'yar ta lallaba ta fita kitchen ta hado tea sannan ta dawo ta sha da k'yar ta sake komawa ta
kwanta ta kudundune.
   Kwanan ta uku a haka, har ta soma samun karfin jikinta, Mama ta shigo sau daya ta bata
anti-malaria shima dan tasan Abban zai iya tambaya ne, shima da tasan zai shigo ya duba ta
ne, tana jin sanda take ce masa sun je asibiti ma kuma jikin da sauki.
  
***Karamin daki ne da yafi kama da shago, katifa ce karama irin ta yan boarding school sai
jakar kayan sa a gefe, bayan haka babu komai a dakin sai wani dogon mudubi dake rataye jikin
bangon dakin.
   Tsaye yake a gaban mudubin yana duba fuskar sa dake cike da kasumba ko ina har baka
iya ganin komai na fuskar tasa sosai, kansa rufe yake da katuwar hular sanyi, ya nannade
wuyan sa da abu, kafar sa da hannun sa duk rufe suke cikin hular sanyi, idan ka cire fuskar sa
da itama kasumbar bata wani bari a ganta sosai, babu wani abu na jikin sa dake a bud'e. Kayan
jikin sa a wanke suke tsaf, sai dai sun tsufa sosai, har da wata yar bula a jikin hannun rigar.
   A ko da yaushe yakan tsaya ne a daidai hanyar da take hucewa idan ta dawo daga
islamiyya, amma kuma kwana biyu ya rabu da ganin ta, shiyasa ya yanke shawarar zuwa gida
duk da yasan ba tsarar sa bace amma zai gwada sa'ar sa.
  


*_WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*

*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in
QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na
MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*

*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama
cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*

*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA
ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*

*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*

*_DEEN MARSHALL👉� Mamuhghee_*

*_HALIN GIRMA👉�hafsat rano_*

*_TAKUN SAƘA👉�billyn abdul_*

*_SO DA ZUCIYA👉�miss xoxo_*

*_ƊABI'AR ZUCIYA👉�huguma_*

*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ÆŠAI ÆŠAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI
NAIRA 1K KACAL*

2👉�400
3👉�500
4👉�700
5👉�1000

*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number

08184017082

*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA
SHAIDAR BIYANKU*

09134848107

*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA
MASOYANMU_*����������
#team zafafa biyar
1/2/22, 22:47 - Buhainat: *HALIN GIRMA*

Hafsat Rano

3

****
Tsaye yayi jikin gate din gidan yana kare masa kallo, tunanin ta yadda zai fara shiga yake
musamman da ba sanin sunan ta yayi ba, ya dai saka mata suna da zuciyar sa kuma be taba
yunkurin tsaidata balle yaji sunan ta ba.
  Lekowa maigadin gidan yayi, ganin mutum a tsaye yasa shi fitowa gaba daya

"Sannu." Yace masa yana kokarin daidaita muryar sa

"Yawwa sannu, wa kake nema?" Maigadin ya tambaye shi yana kare masa kallon cikin rashin
sani.

Nan fa ake yinta, shiru yayi kamar me nazari shi kuma maigadin ya kafe shi da ido yana son jin
abinda ya kawo shi.

"Am... Amm nazo wajen..."

"Malam Iliya." Zeenat dake fitowa ta kirashi tana leko wa.

"Na'am ranki ya dade!"

"Siyo min kati na 500 kayi sauri dan Allah."

"Yanzu kuwa, ga wani bako nan bansan wajen wa yazo ba dai kin tambaye shi."

Yayi gaba, kallon sa tayi tun daga sama har kasa a wulakanci ta yatsine baki tace

"Wa kake nema kai kuma Malam?"

"Yar uwarki nake nema dan Allah, wata me zuwa islamiya kasan layin nan doguwa haka fara."

"Waye kai a wajen ta?"

Kallon cikin ido yayi mata, ta ja tsaki tana juya fuskar ta

"Ban fiye son kallo ba Malam, ka shigo ciki bari na tura maka ita dama ai sai dai ita din..."

Gaba tayi tana cigaba da sababi

"A kaf gidan nan wa zai kwaso mutum irin wannman dan Allah! Ji shi kamar wani mahaukaci."

Sai ta kwashe da dariya tana sake daga kafa.

A kwance ta tarar da Iman tana danna wayar ta da ba kasafai ta cika wani amfani da ita ba,
yanzun ma wani labari ne yaja hankalin ta a Facebook take karantawa.

" Kina da babban bako a waje da galleliyar ranar nan."

" Waye?"

" Idan kika je idon ki zai gane miki shi."

" Owk."

    Tace tana tashi zaune, har yanzu bata gama dawowa daidai ba amma haka ta karfafa
jikinta tayi ayyukan ta. Hijab ta saka madaidaici akan doguwar rigar jikinta ta fito. Daga chan
hanyar gate ta hange shi a tsaye ya rataye hannayen sa a bayan sa, kansa a kasa yana wasa
da kafar sa.    Dogo ne na ajin farko, jikin sa ko ina a murje babu alamun rama ko kad'an, yanayin shigar
sa bata dace da tsarin zubin halittar sa ba, kafin ta karasa ta gama ayyana shi a ranta. Da
sallama ta isa, ya dago da sauri a lokaci daya kwayar idon sa ta sauka a cikin ta ta, gabanta ne
yayi masifar faduwa, tayi saurin janye idon ta, ta russuna kad'an tace
"Ina wuni?" Lumshe idon sa yayi ya bud'e, fuskar sa dake cike da kasumba ta dan yi fadi
alamun farin ciki, ya tattaro dukkan nutsuwa da jaruntar sa yayi gyaran murya yace

"Kina lafiya?"

"Alhamdulillah." Tace a gajarce ta matsa wajen wasu kujerun roba guda biyu ta dauko daya ta
kawo masa.

"Bismillah zauna kana ta tsaiwa."

Hannun sa ya dora a saman kujerar ta kalli hannun yayi saurin janye shi ya zauna sannan yace

"Kefa?"

Wani dan tudu a wajen ta nuna masa da hannu, ta zauna akai tana jin duk ta takura ganin
yadda yake bin ta da kallo da wasu irin idanun sa da suka sake shiga ciki sosai.

"Na same ki lafiya? Ya gida yasu Mama da yan uwa?"

"Lafiya lou Alhamdulillah."

"Ban gane waye ba amma?"

"Me sonki ne, me kaunar ki da son duk wani farin cikin ki, yan kwanakin nan da na dauka banga
wucewar ki ba, sun zame min kwanaki mafiya muni a rayuwa ta. Na kan zauna a duk yini ina
dakon wucewarki, ban taba yunkurin yi miki magana ba, sai dai zuciya ta, ta gaza dauka har sai
dana biyo bayanki, ina fatan ban takura miki ba?"
Girgiza kai tayi tana jin wani bawai, wai ita ake karantawa wannan kalaman, idan har taji daidai

wato ya dade yana bibiyar ta, bata ma sani ba.

" Kinyi shiru!" Yace yana gyara zaman sa

Shirun ta sake yi dan bata san me zata ce masa ba.

" Nasan dama karambani ne irin nawa, ban kai ajin ko da me wanke miki takalmi bane, kiyi
hakuri idan nayi miki shishigi a rayuwar ki."

" A ah wallahi, ba haka bane ba, a kalla mutumin da yace yana son ka ai yafi makiyinka, nagode
sosai da soyayyar ka gareni."  Tace da sauri sannan tayi murmushi, ji yayi kamar zuciyar sa
zata fito daga kirjin sa, ya danne sosai ya maida mata murnushin

"Nagode Nuryyy... Nagode sosai."

Shiru ya biyo baya, ta dinga wasa da gefen Hijab dinta shi kuma yana satar kallon ta.
Nutsuwarta tafi komai tafiya dashi.

"Bari na wuce."

Da sauri ta mike kamar me jiran kad'an,

"Ka gaida gida." Tace tana saurin yin gaba

"Ko zan samu number waya dan Allah?"

Tsayawa tayi ta mika masa hannu, ya shafa aljihun sa dukka

"Kinga garin sauri na manta wayar a daki, amma zan rik'e fad'a min."

"Ok ." Tace ta karanto masa,

" Nagode sunana Muhammad."

" Fatima, ka gaida gida."

Ta juya ta barshi a tsaye a wajen. Sake maimaita sunan Fatiman yayi, ya saki murmushi a
hankali sannan ya juya ya fice daga gidan.


***A zaune a falo ta tarar da Mama na waya, zata wuce ta tsaida ta da hannu ta cigaba da
wayar ta

" Ba za dai ka bar maganar nan ba ko Khalil? Toh shikenan sai kazo din dai ma sake tattaunata,
idan yaso ko a dangi ne sai ka duba sosai ba za'a rasa ba ai."

Amsa ya bata daga bangaren sa, ta ja tsaki tace

" Matsalata da kai kafiya wallahi toh sai anjima, sai kazo din."

Ta kashe wayar ta dangwarar da ita a gefen ta

" Na rasa shegen taurin kai irin na Khalil wallahi, sam baya kaunar ya ganni cikin farin ciki,
mtsw."

Ta sake jan tsaki a karo na ba adadi.

" Daga ina kike?"ta jeho mata tambayar bayan ta riga ta san inda take.

" Wani ne yazo dama."

" Waye shi?"

" Bansan shi ba nima, wai a bayan layi yake."

" Toh kina jina? Idan zaki yiwa kanki kiyamullaili ki rik'e shi hannu bibiyu toh, idan kuma kika yi
wasarairai da shi shima ya gudu kamar sauran, sai ki zauna muyi ta jerawa a gidan nan,tunda
dai bakin hali ya hana samarin zama kowa yazo sai ya tafi."

Bata dago ba, bata kuma ce kala ba, tana jin Maman tana kuma ajiye kowacce magana a
mazaunin da ya dace, sai da ta gama yi mata cin fuskar sanann tace

" Khalil zai zo gobe, babu ruwanki dashi da shiga harkar sa, ko falo bana so naga kina kaiwa da
komowa har ya tafi, zan fi so ki tattara ki koma wajen Gaji da zama aikin ma na yafe miki, idan
ya gama kwanakin ya tafi shikenan, bana son daukar magana dan shi ba kunya magana yake ji
ba, kinji dai na gaya miki."
" In sha Allah."

" Jeki."

Tashi tayi ta bita da kallo ranta na tafasa, da gaske take kishi da ita dukda bata zauna da
mahaifiyar ta ba, amma duk sanda ta kalle ta sai ta tuno abinda ya faru.


****A guje suka taso ganin ya fito, ya nufi wajen da jerin motocin ke fake suna jiran sa, ransa a

bace yake da kiran amma bashi da ikon kin amsawa, dole ya ajiye shirin sa a gefe ya kirawo su
domin ba zai taba yarda da shigar masa shirin sa ba. Shiyasa su kansu basu da yakini ko
masaniyar komai, dan ya tabbatar da zasu taimaka wajen lalata masa shirin sa. Dan su din
basu da ikon kansu sai abinda aka gindaya musu.
Bud'e masa bayan motar daya daga ciki yayi, ya russuna kad'an sannan yace


"We are very sorry sir!"

Be tanka masa ba, ya shige cikin motar ya jingina bayan sa da kujerar ya lumshe idon sa.

"Oga Main house zamu?" Yayi tambayar yana tada motar


"Lamido Crescent!" Yace yana sake rufe idon sa.

Chan suka wuce direct, suna isa ya fito ya shige ciki, tun daga falo ya fara wurgi da kayan jikin
sa, ya rage daga shi sai boxer da farar singlet, kallon kansa yayi a jikin tangamemen mudubin
dake tsaye kikam a falon, ya juya ya sake juyawa sannan ya wuce zuwa cikin bedroom din sa.
Wanka ya fara yi a gurguje sannan ya fito ya shirya cikin shigar babbar riga da jamfa da
wando farare kal, sau cikin sa ya jawo ya ajiye a gefe ya fara saka farar socks a ciki sannan ya
saka ya fito rik'e da babbar rigar a hannu.
Zama yayi sannan ya danna remote din kofar, da sauri suka shigo su biyu, ya mik'a wa daya
babbar rigar, karba yayi ya taimaka masa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login