Showing 114001 words to 117000 words out of 124388 words
Chapter 39 - HALIN GIRMA Book Complete by Hafsat Rano .pdf
ya fita, ya shiga mota ya nufi station din. Direct office din CP ya
wuce ya samu DSP yana press conference akan case din, kokarin fita yayi amma babu dama
sun riga sun ganshi, sukayi masa cha kuwa kowa na son masa tambayoyi, be basu dama ba
dan yanzu ba wannan ne a gaban sa ba, da kansa zai shirya ya basu lokaci amma ba yanxu da
be ma san me yake masa dadi ba sam. Hakuri aka basu, aka kuma sallame su sannan ya samu
ganin CP din sukayi magana, ya kuma shiga wajen da aka ajiye Jabir din. Yayi matukar laushi
sosai saboda ba karamin duka sojajin nan sukayi masa ba, dama yasan ba zasu kyale shi ba,
hakan ba dan dai basaso a samu matsala ne amma tsaf zasu iya kashe shi a wajen.
  Baya jin a yanzu akwai wata halitta da ya tsana sama da Jabir din, shiyasa ya tsaya daga
kofar be shiga ba, dan idan ya shiga zai iya shake shi har sai ya daina numfashi. Wani dan
sanda ne a gaban sa rik'e da wani katon katako, yana masa tambayoyi, sai kuma wasu yan
sandan suma daban daga gefe cikin fushi suke interrogating dinsa yana rokon suyi hakuri.
Juyawa yayi ya bar wajen ya koma suka karasa magana da CP sannan ya bar station din ya
dawo asinine, in da ya wuce kai tsaye wajen Musaddik, ya samu dakin da yan sanda suna
daukar bayanai daga wajen sa, wucewa yayi ya koma bangaren Mahfuz da har yanzu ba'a saki
gawar sa ba, sai an gama bincike tsaf sannan za'a basu suyi masa sutura. A chan ya zauna
tare da su Habib dasu Abba har bayan Magriba sannan aka basu gawar tasa, suka dauke ta
suka nufi gida da ita don yi masa sutura a mika shi gidan sa na gaskiya.
  Zuwan su ya saka gidan rikicewa, dama kowa ya iso ana zaman jira cike da alhini, ba
karamin taba kowa mutuwar tayi ba, nauyi da kunya ya Moh shiga ciki, sai yake ganin kamar shi
ya jawo, da be saka shi a cikin maganar ba, da duk hakan bata faru ba, a daren aka hada shi,
aka kuma rakashi gidan sa na gaskiya. Allah sarki.
Mutuwa darasi ce babba, Rayuwa bata da tabbas, Allah ya bamu ikon amfani da lokacin mu
kafin ya kure mana,Allah kasa mu cika da imani. Amin ğŸ˜
 Â
Â
***Wani irin juyawa cikin Samha yayi lokacin ta samu labarin an kama Jabir, tsoron ta daya kar
sunan ta ya shigo ciki, itace ta bawa Jay din shawarar kidnapping Iman din, kuma ita kadai ce
tasan plan dinsa duk da itama bata san amfani yayi da ita ba. Wayar ta ce tayi kara da take
gefen ta,dan tsorata tayi, sai kuma ta kai hannu ta dauka tana kallon number, Kamal ne yake
kiranta, dagawa tayi ta saka wayar a handsfree
"Ashe dama abinda zaku aikata kenan ke da dan iskan chan shine kuka shigo dani ciki kuka
samu duk wani bayani akan shi, daga karshe kuka watsar dani."
"Ai kai ba karamin kidahumi bane, idan banda gara irin ka, waye yake da amana a wannan
zamanin, kowa kansa ya sani bari kaji, dan haka karka dameni ka kyale ni naji da abinda yake
damuna."
"Ai wallahi kadan kika gani, asirin ki ya gama tonuwa dan na gama zayyane komai a gaban yan
sanda, abubuwan da kuka sakani nayi duk na fad'a sai ki jira hukunci, wallahi ko shi MOH ya
kyale ki wallahi ni ba zan kyaleli ba kinji na rantse!"
Kit ta kashe wayar ta jefar da ita,
"Wannan wacce irin masifa ce?"
Da sauri ta ja jakarta ta fito, bata tarar da maman ta a falo ba dan haka tayi saurin ficewa ta
dauki mota ta bar gidan, tana tafe tana gwada kiran Laila amma bata dagawa, ta rasa abinda
yake mata dadi, sai kawai ta wuce gidan ta sameta suyi magana ko zata taimaka mata, amma
tana zuwa gate sai aka hanata shiga, tayi mamaki sosai hadda fitowa tayi musu bayanin kanta,
amma kemaimai suka hanata bayan sun tabbatar mata da sun gane ta, umarni ne aka basu kar
su sake barin ta, ta shiga masarautar.
_ZAFAFA2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D'aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
2/24/22, 08:08 - Buhainat: ©®*Hafsat Rano*
   _Halin Girma_
      *41*
***Ruwa ta fara ambata sanda ta farka, da sauri Mamma tayi wajenta itace take tsaye dama,
Mummy na kan sallaya tana lazimi ta mike da sauri cikin tsananin farin ciki.
"Alhamdulillah." Ta furta tana karasa kusa da Mamma da take jera mata sannu, da ido kawai
take bin su tana son tuna abinda ya faru karshe. Murmushi tayi cikin dauriya tace
"Mamma."
"Na'am Iman, sannu kinji?."
" Alhamdulillah mun auna arziki. " Ta juya tana fadawa Mummy da ta kasa boye farin cikin ta
"Fatima. "
"Mummy. "
" Sannu kinji, akwai abinda yake Miki ciwo? "
Da hannu ta nuna cikin ta, taba cikin Mummy tayi kila saboda wankin cikin da akayi mata ne,
" Bari nayi musu magana tunda ta farka. "
" Bari naje. "
Mummy tace tana yin gaba, ta bar su da mamma tana tambayar ta. Tare suka shigo da nurses
su biyu, mamma ta matsa suka duba ta, sukayi mata tambayoyi sannan suka ce a bata ruwa
tasha da abinci sannan suka fita daya ta sauki file din ta daya kuma ta tafi kawo mata
magunguna daga pharmacy. Â Â Taimaka mata mamma tayi tunda an cire drip din ta kai ta toilet, ta gasa mata jikin ta, ta
taimaka mata tayi wanka da brush kafin ta fito Mummy ta hada mata tea me kauri da kidney
pepper soup da aka kawo daga fada.
 Daure da alwala ta fito bayan ta sauya kayan jikin ta zuwa doguwar riga mara nauyi ta saka
Hijab ta zauna a gadon ta biya bashin sallolin da suke kanta, sai da ta idar sannan ta dan ci
abincin kad'an ta koma ta kwanta lamo tana jin jikinta babu kwari ko kad'an.
  Abba ne ya shigo tare da wasu mutane masu rawani, suka dubata sukayi mata ya jiki
sannan suka tafi, Abba ya rakasu ya dawo ya zauna yana sake dubata. Tsam Mummy ta bar
dakin ta koma waje ta bar Mamma a ciki suna magana da Abban, ya dan jima a ciki sai da yaga
alamar ba zata dawo dakin ba bayan kuma ita ta kirashi da Iman din ta farka sai ya tashi kawai
yayi sallama ya tafi akan zai dawo anjima.
  A waje suka hadu da Mummy din, ya sameta har wajen da take zaunen yayi mata magana,
ta amsa masa sama sama kamar tana jin haushin sa ko wani abu, be gane dalilin ta ba, ganin a
waje ne ga kuma Moh da ya nufo su ya saka shi kyale ta ya tafi, suka gaisa fuskar sa fayau
alamun ya samu labarin farkawar Iman din. Komawa yayi ya raka Abban har mota sannan ya
dawo, ya tarar da mummy da Mamma din duk a waje, kila Mummy din ce ta sanar mata da
zuwan sa shiyasa suka fito ba sai ya shiga su hau fita ba, gaishe su yayi da tambayar ya mai jiki
sannan ya danyi jim a wajen sai da Mamma tace ya shiga sannan ya tashi ya nufi dakin da
daukin ganin ta. Â Â Ko sallama ya maita yayi sai da ya tura kofar ya shiga sannan ya tuna yayi sallama ta dago
daga kwanciyar da tayi ta kalle shi. Da sassarfa ya karasa kuwa, ya haye saman gadon ya
tattaro ta zuwa jikin sa, ya rungume ta tsam damuwar da yake ciki na raguwa. Luf tayi a jikin
nasa tana jin nutsuwar da ta rasa tsawon kwanaki, bata san haka tayi kewar sa ba, sai yanzu
da suke tare, kuka ta saka masa ya sake rungume ta yana jin shima kamar ya rushe da kukan.
Sai da yaga kukan nata na neman zarcewa sannan ya dakatar da ita ta hanya shafa bayan ta
ya shiga magana a kunnen ta
"Shssh... Karki karawa kanki wani ciwon please, you are safe now. Babu wani abu da zai sake
faruwa, I will protect you with my life."
Shiru tayi tana jan numfashi, ya cigaba da shafa bayanta har sai da yaji tayi shiru gaba daya,
sannan ya dago ta daga jikin sa yana kallon fuskar ta, murmushin ya sakar mata ta maida masa
itama.
" Me yake miki ciwo yanzu? "
" Kai na.. " Tace a hankali
" Sannu zai daina a hankali, komai zai wuce, ba zan sake tafiya ba barki ba nayi miki alkawari
nan."
Maida kanta tayi jikin sa ta kwantar ya gyara mata kwanciyar yadda zata ji dadi, ya saka hannu
yana mata tausa a hankali.
 Sun dade a haka har sai da akayi knocking a kofar, ya zameta ta kwanta sosai akan gadon
ya sauka sannan yace
" Bismillah a shigo."
Bataliyar yan gidan su ce, tun daga kan su Ya Maryam da matan gidan hadda Dadah da wasu
ma da be san su ba, a gurguje ya gaisa dasu ya bar musu dakin dan dakin ma yayi musu
kad'an.
  Dakin da Musaddik yake ya wuce, ya sameshi a zaune ya gama cin abinci, yayi fes dashi
jikinsa kuma yayi kyau, kanin sa ne yake kula dashi suka gaisa da Moh din sannan ya basu
waje dama yana so yaje ya siyo abu a shop sai yayi amfani da damar ya tafi.
"Jikin ka yayi kyau sosai friend."
"Wallahi Alhamdulillah, mun gode Allah, ya jikin Madam din?"
"Itama Alhamdulillah wallahi, ta samu sauki."
"Masha ALLAH. Allah ya kara mana lafiya baki daya. "
"Amin, ka tabbata kana cikin abokai na gari, Allah ya hada mu tare a inuwar al'arshi, bansan da
wanne baki zan gode maka ba, ban kuma san da wanne ido zan kalle ka na gode maka ba, ta
ya akayi na kasa ganewa? Na kasa banbance ka da wani daban? How long ka zauna a wajen
sa.? "
" Mu daina tunawa dan Allah, tunda ya shigo hannu shikenan nasan dole zai girbi abinda ya
shuka. "
" Still dai inaso nasan komai... "
" Ka bari mu koma gida, zan baka labarin komai, for now kayi fucusing akan case din cikin gida,
yau saura kwana uku su juya komai, kana bukatar gabatar da evidence din nan."
" Haka ne, kuma abinda ya faru yanzu ya saka na kara jin kowanne abu akwai good side da bad
side dinsa, abinda na tsana nake ganin shine kawai matsalar ta, har naki bin umarnin Bubu
akai,shi zan yi facing yanzu, zan karbi abinda ya zama mallaki na, zan farantawa mahaifi na
kamar yadda ya dade yana burin ganin ranar. "
" Da gaske kake? "
" Da gaske nake. "
" Kai masha ALLAH, Bubu zai fi kowa murna shi da Aji. Dama a komai alkhairi ake nema ba son
zuciya ba,nayi murna sosai aboki na, Allah ya baka sa'a. "
" Amin. " Yace yana daukar ledojin maganin sa
" Kana shan magungunan nan kuwa?"
" Ina sha. "
" Good, da baka sha da sai na saka ka... "
" Frog jump. " Ya karasa masa suka kwashe da dariya suka tafa
" Wallahi ka raina ni, Capt guda, Capt Muhammad Ahmad Santuraki, babu wani respect ko? "
" Ayi hakuri tsohon Capt! "
Duka ya kai masa a kafadarsa, ya goce suka sake kyalkyalewa da dariya.
***Baki daya ta rasa abinda yake mata dadi, ta rasa in da zata tsoma ranta taji sanyi, cikin
jikinta yayi masifar takura mata, babu abinda take so take kulafuci sai mijinta Bashir, takanas ta
aika aka samo mata irin turaren da yake amfani dashi amma duk a banza, watarana sai ta shiga
daki tayi kuka gashi Abba yayi shiru da maganar, ko dan abinda ya faru a kwanakin ne? Babu
irin kiran da batayi wa Bashir amma sai yace mata ta kara jira zaizo,. Takanas ta samu Mama a
daki da ita ma kanta ta gaji da zaman Zeenat din ta kuma damu da shirun da Abban yayi dama
Bashir din. Da kallo ta bita har ta zauna a kusa da ita, tun ma kafin tayi magana ta riga tasan
me ya kawo ta
"Yau zan samu Abban ku da maganar, ni kaina hankali na ba akwance yake ba, kema kuma
duk alamu sun nuna dakin mijinki kike so, ki tattara ki koma Allah ya baku zaman lafiya, me
afkuwa ta riga ta afku shiyasa yayi biris damu shima Bashir din yasan ya gama damu, sai ki
koma kawai ya zamuyi?"
"Nima dama maganar da nazo muyi kenan."
"Ai na sani, oh Zeenatu ana son miji. "
Da sauri ta rufe idon ta, ta tashi ta bar dakin a kunyace, ita kanta bata san menene ya hau
kanta ba, yadda take ji idan bata koma ba, komai zai iya furuwa da ita. Ga wani masifaffen son
cikin jikin ta da take ba zata so ya taso ba tare da mahaifin sa ba, ta taba karanta wani littafi da
yarinyar ciki tayi gangancin kashe aurenta ashe akwai ciki, karshe haka ta haife dan a gida
kuma ta cigaba da rainon sa a cikin bakar wahala, gashi duk wanda yazo auren ta sai yace ba
zai rik'e mata da ba.
  Text message ta sake tura masa na ban hakuri, kamar yadda take masa kullum amma
baya reply, ko ranar da yazo gaisuwa gidan taso suyi magana amma kemaimai ya ki bata dama
karshe ma ya daga wayar Hajiyar sa yayi tafiyar sa ya barta a wajen.
*Adamawa-Yola*
Ayi maneji😢😢🙌
_ZAFAFA2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D'aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
2/24/22, 08:09 - Buhainat: ®*Hafsat Rano*
   _Halin Girma_
      *42*
***
*Adamawa-Yola*
Dukkan su sunyi shiru da abinda yake sak'awa a rai, idan har ta tabbata Muhammad yana da
evidence akan su, toh gaba daya lissafin su ya sauya. Amma kuma akwai abin mamaki ace
yasan komai tsawon wannan lokacin amma be taba fadawa kowa ba, hatta mahaifiyar sa da
yafi kusanci da ita akkowaan kowa. Â Â Sanarwar shigowar sa masarautar ya sake saka su cikin tashin hankali, rige rigen lekawa
suke kowa yana so yaga da wacce yazo, ba karamin kaduwa sukayi ba ganin shi cikin shigar
saurata yayi masifar kyau, ya dauki wani siririn glass fari ya dora akan fuskar sa, murmushi ne
kwance a fuskar tasa yana tafiya irin ta kasaita. Fada ya wuce kansa tsaye, bayan ya tabbatar
da an gama tattara duk wasu masu fad'a aji na masarautar tasu, shi kanshi Bubu a cike da
Mamaki yake musamman da irin hakan bata taba faruwa, ba ruwan Muhammad din da harkar
cikin gidan balle har ya nemi ganawa da manyan fadar.
  yadda ya shigo fadar kai tsaye ya saka wasu da yawa daga ciki yin mutuwar zaune, sakon
shi ya iso musu tun kafin ya karaso. Wajen da ya saba zama ya samu ya zauna bayan ya
kwashi gaisuwa. Su hudu suka shigo a tare hadda Kamal, suka samu waje suka zauna, daga
nan bubu ya soma magana cikin nutsuwa da makasudin taruwar su a wajen.
"Mun taru ne domin danmu Muhammad yana da bukatar ganawa da manyan masarautar
saboda muhimmiyar maganar da ta kawo shi, wadda muke kyautata zaton zata kawo cigaba a
masarautar tamu baki daya."
Mikewa tsaye yayi ya sake gaisuwa sannan ya soma magana idon sa fes akan wambai da
jama'ar sa.
"Tsawon lokaci na dauka ina bin diddigin mutuwar marigayi tsohon sarki. Duk da karancin
shekarun da nake dashi a wanchan lokacin amma ban manta ba, ban manta fuskokin mutanen
da sukayi sanadiyar mutuwar sa ba."
Hayaniya ce ta cika fadar kowa na kokarin tofa albarkacin bakin sa cikin tsananin mamakin
maganganun Mohammad din wanda shi kansa Bubun be san da wannan maganar ba.
Murmushi ne a kwance a fuskar sa yana karanta tashin hankali dake kwance a fuskokin su, tuni
suka fara jikewa da gumi cikin yanayi na wahalarwa
" Wacce irin magana ce wannan yarima?"
Gyara tsaiwar sa yayi, ya sake kafe su da ido yace
"Ayi min afuwa, na dauko maganar daga sama, sai dai ba kai tsaye nazo da maganar ba sai
dana tabbatar da ina da gamsashiyar shaida wanda zasu zama madafa a gareni."
Babu be tanka ba, ya dai zuba masa ido yana kallon sa yadda ya dake ya sake burgeshi, ya
kuma ji a ransa lallai Muhammad ya shiryawa koma menene ,yadda ya dade yana nuna halin
ko in kula da harkar gidan sai ya dauka be san komai ba, ashe yana sane har yana kokarin
samun hujjar da zai tsayawa wan nasa da ya tabbatar da akwai wani bayanin a cikin labarin
mutuwar tasa.