Showing 120001 words to 123000 words out of 124388 words
Chapter 41 - HALIN GIRMA Book Complete by Hafsat Rano .pdf
bada sa'a."
" Amin, alfarma nake nema wajen ka."
" Habawa, wane mutum, ka fadi ko menene kake so, an gama kawai."
" Bashir kenan, toh Nagode. Dama so nake idan Allah ya kaimu bayan Magriba kaje ka dauki
matar ka ku tafi gida, shi aure daka gani ya wuce duk in da kake tunani ko hasashe, hakuri
shine ribar zaman dan haka ka ajiye duk abinda ya faru a baya, ka fuskanci rayuwar ka."
"In Sha Allah an gama, dama so nake ita da mahaifiyar ta su fuskanci rayuwar yadda take."
"Zuwa yanzu sun gane ai na sani, kaje ka dauki iyalin ka."
"Zanje in sha Allah, nagode Allah ya kara girma."
"Amin nagode."
Sallama sukayi ya ajiye wayar, dama yana son yaje ya tafi da ita dan ya gane yadda ta damu ta
dawo ko da text message din da take masa, shima kuma abinda yake so kenan, abu daya ya
saka shi delay shine kayan dakin da ya saka akayi mata masu kyau daidai kudin sa, sai sabon
gidan da Moh din ya bashi a lokacin bikin me kyau madaidaci two bedroom da falo da kitchen
sai parking space, wanchan gidan da aka kaita hayar sa suka karba amma ba shine ainahn
gidan da ya bashin ba.
 Kayan duk sun zama ready an saka komai an kwaso kayan kitchen dinta an zuba mata gidan
yayi kyau daidai gidan amarya. Shi kansa yanzu yake jin sa a angon na gaske, bayan doguwar
dambarwar da suka sha da hajjajun sa karshe dai sun rabu bayan ya dawo ya tarar da ita suna
aika-aikar su da kawayen ta, da yayi magana ta taso masa kamar zata dake shi, karshe ma
tace ya saketa ta gaji da auren sa, ta samu wani sabon saurayin me jini a jika, da farko yayi ta
mata magiya akan tayi hakuri amma fafur taki, sai kawai ya danne zuciyar sa ya saketa, aikuwa
yana sakin nata yaji wani sakayau kamar an zare masa wani mugun nauyi, sai ya hau tunanin
ta yadda akayi ma ya aure mace irin ta bayan ya san abinda take aikatawa, abu daya ya sani
shine kwadayin abun duniya ne ya kwashe shi har ya yarda ya amince ya aureta, bayan ta jika
shi da kudi masu yawan gaske.
Text message Moh ya turawa Iman yace ta fadawa Zeenat ta shirya zaizo bayan sallah,
aikuwa tayi mata forwarding text din tana gani kuwa ta kirata ta dinga mata godiya. Dakin Mama
ta wuce ta sameta a zaune ta rafka tagumi yadda abubuwan suka sauya mata a lokaci daya
shine yake bata mamaki, ba tun ranar ta gano Abba so yake ya maida auren su da Maman
Iman ba, sai yau ta gasgata hakan da yace mata ya tafi Abuja. Karamin hauka tayi masa amma
yayi biris yayi tafiyar sa.
Ko da Zeenat ta zo mata da labarin zuwan Bashir din sai taji dadi, a kalla zata huta da
maganar yan gidan da ma makwafta akan zaman Zeenat din a gidan.
"Sai ki hau shiri ai, kafin yazo, kinje kin shantake a asibitin da tun dazu kika dawo ai da kin yi
shirin da ya kamata."
"Anya ma asibitin kawai kika je?"
"Eh mama, chan naje likitan ne be zo da wuri ba."
"Toh sai ki shirya." Tace mata
"Toh."
Daki ta koma ta dan harhada abinda zata hada, ta zauna tana lissafin awowin da suka rage, sai
ga Mama ta shigo da Madara a kofi me dumi ta bata tace ta shanye, ta karba ba musu ta
shanye tas ta bata kofin ta fita.
Har akayi sallar magriba aka idar da wajen minti talatin be zo ba, ta gama matsuwa Mama na
lura da ita, ita mamaki ma take yadda ta juye lokaci daya.
Ana idar da sallar isha'i ya aiko yaro wai Zeenat tazo inji Bashir, da sauri ta mike Mama ta
harare, ta koma jiki a sanyaye ta zauna
"Je kace ya shigo wai."
"Hankalin ki ya dawo jikinki kinji? Wannan rawar kan ta mecece? Anya ma yaron nan haka ya
barki kuwa?"
"Mamaaaa."
"Ba wasa nake ba, ki nutsu ki dawo nutsuwar ki wannan rawar kan babu abinda zata jawo miki
sai raini wajen namiji, kayi biris da harkar namiji ma amma be fasa gasa ka ba, ina ga kana
rawar kafa akansa? Daga cewa gashi sai ki mike kina barin jiki ke me miji ko? Toh ki shiga
taitayin ki."
"Mama ai ba laifi bane, tunda shi din miji na ne."
"Inyeee Zeenatu?"
Ta fad'a cike da mamakin Zeenat din, sallama yayi a kofar, kafin ya shigo sanye cikin shadda
sabuwa kar, sai kyalli take da kamshi, cikin ido suka kalli juna da Mama, ta kauda kanta haushin
shi na tike ta, sai ta ga ma kamar da gayya yake wani irin murmushi.
" Mama ana gaishe ki." Zeenat tace jin Maman bata amsa gaiswar Bashir din ba
" Lafiya lou, ya gida." Harara ta watsa wa Zeenat din ta dauke kai kamar bata gani ba, sai ta
tashi tsam ta tayi hanyar barin wajen tace
" Ku gaida gida."
" Mun gode Mama
Yace yana hayewa kujerar, tashi Zeenat tayi tabi bayanta dan yi mata sallama, ya bita da kallo
yana kara bararrajewa a saman kujerar.
Suna shiga Mama ta turnuke ta da fad'a, ta inda take shiga ba tanan take fita ba, tayi mata
tatas saboda bakin ciki, karshe tace ta bata waje. Sallama tayi mata bata amsa ba, sai ta tsaya
taki tafiya tana kallon Maman
" Uban me kika tsaya kina yi anan? Ko jiranki zai yi? "
" Naga kina fushi ne, kiyi hakuri dan Allah ko na hakura da tafiyar kawai tunda naga kamar
bakya so. "
" Inji uban wa nace bana so? Yadda ma kike rawar kafar nan ko bana so zaki hakura ne? "
" Eh. " Ta daga mata kai
" Ke ni karki rainan hankali, wuce kibi mijinki Allah ya bada zaman lafiya. "
" Amin. " Ta amsa hakan ya sake tike Maman. Ta juyar da kanta sai da Zeenat din ta fita sannan
ta zauna cikin rashin sanin abinda kuma ya kamata tayi. Gashi dai a karshe abinda tayi ta yi
akan Zeenat din duk ya tashi a banza, gashi ta rasa damar ta a wajen Abba wanda ba zata taba
dawowa ba, karshe kuma yar ta zabi mijinta akan zaman gidan nasu.
***Da dan gudun Amaani da Amaan suka tare shi, kamar sun sanshi tun da dadewa, kamar sun
saba dashi. Yana da son yara ko dan saboda be haifa da yawa bane, Amaani sak Fatiman sa
sai dai ita bata da hayaniya da kwarafniya irin ta Amaani din, kamar yadda mahaifiyar su take
haka take itama a nutse tun tana karama har kuma girman ta. Su suka jagorance shi zuwa ciki, ya zauna yana tuna shekarun baya da ya kasance a same
wajen, a lokacin da yazo su kayi magana da Alhaji, kamar a lokacin komai yake faruwa.
Turo kofar da akayi ne ya sakashi waigawa, itace dai a shekarun baya sai dai girma da ya
soma kamata, duk da haka ba zaka taba bata shekarun ta ba, balle har ka kawo ta ajiye
budurwa kamar Iman din, kullum cikin gyara take tsaf. Ko a baya yasan yayi missing mace
kamar ta, sai dai a yanzu sam be zo da wasa ba, da gaske yake wannan karon sai dai duk
abinda zai faru ya faru. Babu gudu ba ja da baya!
"Sannu da zuwa." Tace tana zama a chan nesa da kujerar da yake kai. Sannan ta gaishe shi ya
amsa yana satar kallon ta, shiru suka dan yi kafin ya sake bijiro mata da maganar da ta sakashi
tasowa gari i gari zuwa Abujan, a tsammanin sa sai sun kai ruwa rana zata amince, amma sai ta
bashi mamaki matuka, yadda kai tsaye tace Allah ya zaba musu mafi alkhairi. Da farin ciki ya
baro garin na Abuja, ya dawo ya tarar da Mama bata da lafiya, ya tausaya mata tunda shi
mutum ne me tausayi, har ma ya saka Habib suka kaita asibiti in da aka ce dole ta rage tunani
saboda jinin ta da ya hau sosai, aka rubuto mata magunguna suka tattaro suka dawo gida.
***Bayan sun gama waya da daddare zasuyi sallama yace ta shirye shi gobe yana nan
dawowa, reaction dinta kadai ya gamsar dashi yadda tayi kewar shi. Yana jin yadda take farin
ciki ta cikin wayar sai dai kara irin tata ta hana ta nuna masa, a hakan ma ya gode dan yasan ya
chanja ta sosai daga auren su zuwa yanzu. Sauran chanjin kuma sai a hankali zata saba da
kalolin soyayyar sa masu tsayawa a zuciya.
Neman baccin da take yi tayi ta rasa, ta tashi ta sauka daga gadon ta bud'e wardrobe dinta, ta
hau duba kayan da take ganin ya dace ta saka, sai data dau lokaci tana zaba kafin ta tsaya
akan wani hadadden lace wanda dinkin sa ya fita sosai. Murmushi tayi ta fito dashi ta ajiye a
gefe ta hada da set of jewelries da zasu dace da lace din sannan ta kwanta tana lissafa kalolin
girke-girken da ya kamata ta tarbi mijin nata dashi, da haka bacci ya dauke ta bayan ta gama
hada komai a cikin kanta saura kawai girkawa gobe idan Allah ya kaimu.
Kasancewar tana cikin zumudin dawowar sa yasa ta tashi da wurwuri, ta duba kitchen na
abubuwan da zata bukata wajen girkin wanda babu ta bawa Ummimi sautu suka je da driver
suka sissiyo, sannan suka shiga aikin tare da sauran ma'aikatan dake kula da kitchen din amma
kuma Itace akan girkin sai dai su taimaka mata da dauko wa da mikowa. 2/26/22, 19:09 - Buhainat: *Hafsat Rano*
   _Halin Girma_
      *44*
***Da wurwuri yaso tahowa amma sai case din Kamal da Kilishi ya tsaida shi, sosai Kamal ya
tada hankali a gidan tun bayan da ya tantance ainihin shi din waye, ya kuma gano wambai ne
Mahaifin sa. Baki daya Kilishi ta nemi kwanciyar hankalin ta ta rasa, gashi har lokacin bubu be
ce ga hukuncin ta ba, sannan ita kanta Laila ta birkice mata, babu Moh kamar yadda ta kwallafa
rai, ga bakin cikin cin amanar da Samha tayi mata ga kuma abinda mahaifiyar ta wa mahaifin ta.
  Takanas taje ta samu Bubu ta roke shi akan ya barta ta koma karatun ta dan zaman ta
anan din komai zai iya faruwa,da farko be amince ba sam, yace mata be yarda ba tayi hakuri ta
kawo miji aure zai mata. Sanin bata da wani tsayayye da zata nuna yau yasa ta samu Moh ta
roke shi cikin kwantar da kai tace ya rokar mata Bubun ya barta. Ko da ya samu Bubun da
magana shima fafur yaki, sai da yayi ta masa magiya sannan yayi masa alkwarin duk wani abu
da ya faru shine zai dauki responsibility din, a haka yayi convincing Bubun ya amince yace ta
koma din,amma da sharadin idan yaji wani abu mara dadi ko mara kyau toh fa shi zai kama da
laifi kuma dole ya karbi aurenta.
  Godiya tayi ta zuba masa kamar ta rungume shi haka take ji, har gobe tana son sa, ba
kuma ztaa daina son nashi ba, zatai ta hakura for now tayi concentrating akan karatun ta, ta
samo ta kammala shi kafin tasan kuma me ya kamata tayi kuma anan gaba. Akalla idan tayi
nisa da gida zata manta abinda Kilishin tayi da dan lokaci ta kuma samu damar mantawa da
Moh din shima na wani lokaci hankalin ta ya kwanta ta nutsu waje daya.
 Â
***A daki ya tarar da Ammin tasa, wanka tayi ta gama shiryawa kenan zata fito ta yi breakfast
ya shigo, ta bishi da kallo har ya zauna a k'asa wajen tumtum din da take hutawa idan tana
dakin, ya tankwashe kafafuwan sa sannan ya gaishe ta cike da ladafi. Kusa dashi ta zo ta
zauna tana amsawa, tasan sallama yazo yayi mata tun jiya dama ya sanar da ita komawar tasa
yau ba kuma zai dawo ba sai ya gama da chan din, sannan yazo a shiga bikin nad'in nasa,
wanda tun yanzu Bubun ya soma aikewa da goron gayyata dan taro yake shiryawa na ban
mamaki.
 Â
"Tafiyar ce Babana?"
"Eh wallahi, na zata ma fa baki tashi ba."
"Wa? Ka manta da wuri nake tashi, kwana biyu ne da kafa ta matsa min bana samun bacci
sosai da daddare sai na rama da safe."
Kafar tata ya matsa mata
" Har yanzu tana ciwon?"
" Ta warke yanzu ai."
" Allah ya kara sauki."
" Amin."
" Idan naje sai mun tashi dawowa gaba daya, ina fatan abun da nayi ya dace."
" Kayi abinda ya dace, kuma ka farantawa mahaifi ka da zaka cika masa burin sa, Allah yayi
maka albarka ya baku zuria dayyiba, inaso na goya yan jikokina a bayan nan nawa."
" Dukka ma zamu baki Ammi ta, halak malak. "
" Um um dai Babana, kar kayi alkawarin da ba zaka cika ba. "
" Da gaske nake Ammi. "
"Toh shikenan Allah ya kawo mana masu Albarka. "
" Amin ya Allah. " Ya amsa yana mikewa
" Ammi zan wuce, ayi mana addu'a. "
" Allah ya taimaka ya bada sa'a, a gaida min da yata kafin tazo, zan kira na sake dubata idan ka
sauka. "
" In sha Allah Ammi ta. "
Bin sa tayi da kallo har ya bace wa ganin ta, ta sauke ajiyar zuciya tana jin soyayyar tilon dan
nata, tana alfahari dashi, daya ne tamkar da dubu yana mata biyayya daida gwargwado.
 Be samu ganin Bubu ba, dama sun riga sunyi sallama tun jiya, dan haka kai tsaye mota ya
shiga, karo na farko zaiyi tafiya cikin rakiyar tarin fadawa ba sojoji ba, wani daban yaji, gargajiya
sosai da al'adah irin ta gidan sarauta. Shi kansa shigar da yayi kenan, shiga irin ta Yarima me
jiran gado, a dan kwana biyun da yayi har ya saba da saka kayan , yana kuma jin dadin su dan
suna sake fito da kamalar sa.
  Tun daga airport ya fara cin karo da abinda ya tsana da sarauta, yadda ake kokarin kaiwa
kasa wajen gaishe shi, har ga Allah baya so kuma dole zai san yadda zai ya hana irin wannan
gaisuwar. Basu jima da zuwa ba jirgin su ya tashi zuwa birnin na Kano, in da ya tanadi kalolin
soyayyar da zai bajewa sahibar tashi, kafin ya dawo ya karbi sha'anin mulkin da baya jin zai
rage masa wani abu daga cikin irin rayuwar da ya tsara musu, sai dai yasan dole sai ya dinga
raba lokacin da mutane, amma haka zai yakice ya dinga yin abinda ya dace.
 Â
***Tun da taga komai ya gama haduwa sai abinda ba za'a rasa ba, sai ta bar musu sauran aikin
su karasa ita kuma ta haye sama don yin wanka ta shirya tarban mijinta. So take ta burge shi
sosai, duk da ita din ba gwanar kwalliya bace amma zata kokarta, sannan zata cire kunya ta
rungume mijinta taji dumin jikin sa sosai. Â Â Wanka tayi ta sake wanke bakin ta tas, sannan tayi amfani da mouth freshner me kamshi
ta kuskure bakin sannan ta fito tayi zaman shiryawa a gaban mirror. Ta dan dau lokaci tana
shiryawar duk da ba wani make up tayi ba, amma tayi kyau ainun. Kayanta da ta turara akan
kabbasa ta dauko ta saka, sannan ta sake bin jikinta da turarurruka masu sanyi da dadin
kamshi. Samun kanta tayi da yin murmushin yadda ta fito tayi fes, sai taga har wani fari kamar
ta kara tayi fresh da ita.
  Zama ta cigaba da yi a saman nata tana dakon zuwan sa. Waya ta dauko da nufin kiran
Mummy sai taji karar zuge gate din gidan, ta fasa ta tashi da sauri tayi wajen window ta daga
tana kallon motocin da ke shigowa suna samun matsuguni a cikin gidan. Motar da yake ciki ta
zubawa ido, a hankali ya zuro kafarsa cikin takalmin sa da akayi da zallar fatar damisa, daga
yanayin takalmin nasa ta gane irin shigar dake jikin sa, tun kafin ma ya gama fitowa ta gama
wassafa yadda kayan suka karbe shi.
  Kamar wanda aka ce ya daga kai zuwa saman, sukayi ido biyu tana leken sa, da sauri ta
saki labulen sanda ya kashe mata ido daya gami da murmushin sa me tarin bayanai a cikin sa.
  Gaban mirror ta koma ta sake fesa turare sannan ta shafa khumra me kamshi a tafin
hannun ta, ta dauki flat shoe me kyau ta saka ta sauko k'asa. Tana saukowa yana shigowa
falon. Tsayawa yayi a kofar ya toge ya bud'e mata hannayen sa, cikin sanyin ta, ta tafi zuwa
gareshi, ta fad'a jikinsa ya rungume ta yana jujjuyasu a wajen, kamshin turaren ta na ratsa
kofofin hancin sa.
"Ya Allah, ashe haka nayi kewar ki?"
"Um... Barka da zuwa yallabai."
Tace tana dago kanta daga jikin sa
" Barka dai gimbiyar Muhammad."
" Muje ciki?"
" Bismillah... Ladies first "
ya matsa yana nuna mata hanya, yana so ya more kallon tafiyar ta. Bata kawo komai ba tayi
gaba ya bita yana murmushi, a tsakiyar falon suka yada zango.
"Wash." Yace yana taro ta jikin sa, ta zame tana masa dariya
"Wanka ko lunch?"
"You." Ya kashe mata ido, dariya kawai