Showing 48001 words to 51000 words out of 124388 words
Chapter 17 - HALIN GIRMA Book Complete by Hafsat Rano .pdf
me kyau fatar ta sai
glowing take kamar fuskar ta taji labari.
  Tun da aka soma mata gyaran jiki ta tabbatar da komai nata ya sauya, hatta lallen da aka
yi mata da gyaran gashi na daban ne, bata kara tabbatar da gatan da take dashi ba sai a event
din da aka yi jiya taga tarin mutanen da suka zo domin ita, kowa don ya ganta kawai. Tasha
kyaututtuka daga kawayen Mummy da yan uwa kowa burin sa ya yi mata abinda zai burge
mummy din.
 Sosai kuwa Mummy taji dadi ba kad'an ba, duk kuwa da miskilancin ta amma sai da yanayin
ta ya sauya sosai.
  Bayan an yi taron an gama ne da daddare take bawa Iman din labarin yadda akayi suka
rabu da mahaifin ta.
"Kinsan aure rai ne dashi, idan lokaci yayi sai an rabu, amma har gobe ina son mahaifin ki,
kaddara ce kawai ta raba mu, a lokacin alhajin mu yayi fushi sosai akan auren da mukayi ba da
sanin kowa ba. Alhajinmu me kudi ne sosai kuma dan siyasa ne, yana matakin senate president
a lokacin, hakan ya saka dole Ibrahim ya sake ni akan kar abinda mukayi ya shafi mutuncin sa,
dan wasu ba zasu taba yarda da cewa munyi aure ba, ko bayan an haife ki nan ma yace a dole
dole sai ya karbi yarsa, ya rik'e ta dan baya son ko kad'an mutuncin sa ya tabu. Hakan ya saka
Ibrahim yin fushi, ya karbe ki ya kuma yi alkawarin ba zai bani ke ba, nasha kuka nayi ta rokon
sa ina masa magiya karshe yayi min alkawarin idan da rai da lafiya zai kawo ki idan kin isa
aure."
" Amma fa ko bayan nan Alhaji yazo daga baya yayi regretting abinda yayi har ya nemi Ibrahim
din da kansa ya kuma roke shi ya bashi ke, dan a lokacin girma yazo gashi yana son gyara,
Mamma ce babbar mu gashi har lokacin Allah be bata haihuwa ba ,amma sai Abban naki yaki
yace yayi hakuri ba zai iya ba."
" Ni banga laifin shi ba dan nasan shi da Zuciya idan har aka taba shi,karshe dai nima nayi aure
bayan na kammala wani course da nake na auri wani dan siyasa Babba, na dade sosai a gidan
kafin karshe Allah ya bamu haihuwa daya, na haifi yan biyu Amaan da Amaani, daga nan kuma
sai muka rabu."
Shiru Iman tayi tana harhada maganganun.
"So kinga kowanne bawa baya wuce kaddarar sa, ni dake haka kaddarar mu take, dole ne
kuma mu karbe ta hannu bibiyu mu gode wa Allah."
"Haka ne mummy, wallahi na zata so Amaan yaran Mamma ne."
Murmushi tayi
"Yaranta ne kam, tunda dai ni ban wani san komai akan su ba, Itace komai dinsu, Allah be bata
haihuwa ba shiyasa ta dauki son duniya ta dora akan su."
"Hajiya fa?"
"Step Mom dimu ce,itace ta haifi Zayd."
"Allah sarki tana da kirki."
" Sosai, kirkin ta yayi yawan da karyar mutum ya shigo gidan nan yace ba ita ce ta haife mu ba,
ita ta kula da koman mu, Itace kuma a matsayin mahaifiyar mu har gobe."
" Ashe akwai step moms masu kirki?"
" Akwai su da yawa Iman, ba dukka aka taru aka zama daya ba, wasu kuma zaki ga yaran ne
basu da kirki sam, sun takura mata sun hana ta sakat, komai dai da kika gani akwai good side
dinsa akwai bad side haka rayuwar take."
" Haka ne." Tace tana tuna Mama da Zeenat
Shirya ta aka yi cikin wasu yan ubansu kaya, kayan da ta tabbatar ba kananun kudi aka kashe
wajen samar dasu ba, komai na jikin ta unique ne, me kyau da ya dace da ita. Sarkar gold din
da Mummy ta siya mata Mamma ta saka mata, sannan ta zaunar da ita a gefen gado ta dauko
mata abinci, ta zauna da kanta ta taimaka mata ta ci dan ta tabbata idan suka tafi babu batun
cin wani abinci a wajen amarya. Ci tayi sosai sannan ta dauko wayar ta tana duba misscalls ko
ya kirata, be kira ba, ajiye wayar tayi akan cinyar ta har lokacin tafiyar su yayi, text message ta
tura masa ta saka wayar a jaka suka fito gaba daya, wajen Hajiya aka kaita tayi mata nasiha
sosai kafin su nufi airport da su Ya Mubarak da sauran jama'ar da zasu halarci daurin auren, sai
kuma su Amaani, Mamma da yan uwan su da zasu je a karasa bikin da su a matsayin dangin
Mamanta.
  Mintuna kad'an suka isa dasu Kanon, dan ma basu taho da wuri ba, Abba ne ya saka aka
je aka taho dasu daga airport din, aka sauke su a bangaren Abba babba, ita kuma Iman aka
wuce da ita ta gaida Gaji sannan suka shiga wajen Mama.
  Gabanta ya fadi tun shigowar su, ko wanka bata yi ba, duk da ta dan samu nutswa bayan
ta samu Gaji, tana da yakinin zata hana Abban kuma ya hanu, amma kuma jikin ta duk yayi
sanyi tana dai zaune ne tana kallon kowa, masu kaya-kaya ma a cikin yan uwan ta haushin su
take ji, gani take ai kamata yayi su tayata alhini. Kawayen ta kuwa da sun kirata take dagawa
tace an daga bikin zata neme su, abinda bata sani ba zance ya gama zagaya ko ina wasu ma
da gayya suke kiran dan su tabbatar.
Gaishe ta Iman take amma ta tsura mata ido ta kasa amsawa, tsabar bakin ciki ta kasa boye
shi, mamakin yadda yarinyar ta sauya take, Ashe haka take da kyau bata sani ba? Ko Kuma dai
yanzu ne kyawun ya fito. Kayan jikin ta kawai ta kalla tasan an kashe kudi, idon ta ya sauka
akan sarkar wuyan ta, tana ta sheki da kyalli kana gani zaka gane zallar gold ne. Tari ne taji
kamr zai sarke ta, duk suna lura da ita da suka ga kamar bata hayyacin ta sai kawai suka tashi
suka koma in da aka sauke su.
Lokaci lokaci Iman na kallon wayar ta, ta matsu suyi magana ta san halin da ake ciki, ba zata
kirashi ba dan tasan yana cikin hayaniya amma taso ko yaya ne ya kirata.
  Daidai lokacin da aka saka na daurin auren yayi, ta kwanta kawai lamo tana jin faduwar
gaba, wani iri kamar tace ta fasa, ba'a gidan ake daura auren ba, a babban masallacin Kano ne
da yake kusa da gidan sarki shiyasa basu san abinda yake faruwa ba.
  Ji tayi gidan yayi tsit, kamar babu mutane, ta dinga jin wani tsoro tsoro yana shigar ta,
Mamma ce ta taba ta, tayi mata murmushi tace
"Kowacce mace ta kan ji irin haka idan za'a daura mata aure, kiyi addu'a kinji yata?"
Da kai ta amsawa Mamman, ta soma karanta hasbunallahu wa ni'imal wakil, a hankali taji
nutsuwa na saukar mata. A daidai lokacin suka ji karar tsayawar motoci, kafin gidan ya kaure da
wata irin guda me karfin gaske.
 Wani maroki ne me muryar tsiya, ya shiga kirari cikin muryar sa da ta shiga har
kwakwalwarta, ta tsaya chak da tunanin abinda kunnen ta yaji
"Alhamdulillah, Allah mun gode maka, an daura auren Yarima Muhammad da amaryar sa
Gmbiya Fatima, dan sarki jikan sarki, kuma sarkin gobe idan Allah ya kaimu."
Farin ciki ne ya kama su Mamma suka hau murna, bata fuskantar komai, a daidai lokacin sakon
sa ya shigo wayar ta,
"Duba whatsapp dinki amarya tah."
Da sauri ta shiga whatsapp din har ta mantawa bata kunna data ba ,kunnawa tayi messages din
suka shigo tayi saurin bud'e nasa. Hotuna ne masu yawa, ta hau bud'e su tana kura idon ta,
hoton farko ya saka numfashin ta tsayawa na dan sakanni
"Capt Muhammad Ahmad Santuraki."
Yayi captioning hoton, yana sanye da nadi irin na sarauta, da kunnuwan sa guda biyu a sama
da yake nuna yadda tsarin sarautar take, gaba daya gani tayi an sauya mata shi,shine sai wasu
abubuwan da yawa da suka dauke ta zuwa wani tunani na baya tana kokarin alakanta
abubuwan da tayi ta shakku akan sa. Kwanciyar fatar sa, da yadda yake magana yana bata
mamaki matuka.
Sauran hotunan ta shiga bubbudewa, duk akwai shi aciki tare da manyan k'asar da ma ketare,
hoton sa da Takawa da yadda Takawan ya rik'e shi says alot. Ji tayi gaba daya ya goge mata
hadda, ya bar kanta blank bata ma san wanne irin tunani zatayi ba.
Wasu mata ne suka dinga shigowa, wanda kana ganin su zaka san su din hadimai ne daga
gidan sarauta, duk suka taru waje daya cikin girmamawa suka hau gabatar da kansu.
Kayan hannun su Mamma ta saka suka ajiye a gefe sannan ta aika wata bangaren Gaji akan
wasu suzo a cikin dangin Abban, hakan ya bawa Iman damar sulalewa ta shige dakin Umma,
sannan ta kira Ya Maryam ya waya tace dan Allah tazo dakin Umma. Sai gata tazo har da
saurin ta, murna fal fuskar ta dan suma ba karamin mamaki suka shiga ba. Hotunan ta soma nuna mata, sannan ta hau mita kamar zatayi kuka, katse ta Ya Maryam tayi,
"Yarinya kad'an ma kika gani, sai kin ga uban lefen da aka kawo miki, wallahi Iman Allah ya baki
miji, miji na kere sa'a me sonki tsakani da Allah, kinyi sa'a, halin ki ne ya jawo miki amma."
"Amma me yasa zai rufe ni?"
"Haka tasa salon soyayyar yake, kin ganshi kuwa? Salo,aji kyau ga kudi."
Turo baki Iman tayi, ta rasa me ma zatayi, Itace zata shiga gidan sarauta? Sarauta ma babba
irin ta Kano? Katse mata tunani yayi da wani sakon nasa
"Meet me a seat room din Abba, na matsu na ganki, I want to feel you right close to me."
Da sauri ta kife wayar,. Maryam da taga komai ta kyalkyale da dariya
"Su Iman an shiga sahun manya, jeki dan Allah yaji duminki, halal dinsa ce ke yanzu ehe."
Duka ta kai wa Maryam din ta manta ma basa yar haka da ita, ta sake kwanshewa da dariya
tana tsokanar ta
"Saura kije ki dinga wannan nuku nukun naki, tashi ki sake gyara jikin ki, bari naje na karasa jin
drammer da ake a gidanku, Zeenat na chan ta tada aljanu wai ba ta yarda ba, kinsan an riga an
daura itama."
"Kamar ya?" Tace cikin mamaki
"Jeki ke dai wajen aikin Allah, bari zan baki labari in details."
Ta juya da sauri ta fice bayan ta sanarwa da Mamma cewa Iman zata je yarima na seat room
suyi hotunan tarihi.
Rano💕💕
#Note edited
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)Â s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_1aHALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
1/21/22, 12:58 - Buhainat: Halin Girma
  18
Hafsat Rano
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇�_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇�_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇�_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_con
tent=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator
=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLo
SKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇�_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
**************
Shigowa Mamma tayi, ta same ta a tsaye ta ma rasa abinda zatayi. Hannun ta, ta kama ta
zaunar da ita, ta bud'e jakar da suka zo da ita ta ciro turare me dadin kamshi na daban ta fesa
mata, ta duba fuskar ta sannan tace
"Ki kwantar da hankalin ki dan Allah,bari na duba kayan da yan matan nan suka kawo, ba za'a
rasa alkyabba ba. "
Fita tayi sai gata ta dawo tare da daya daga cikin yan matan, ta russuna har k'asa ta gaida Iman
din da gabatar da kanta da sunan ta Ummimi sannan ta matsa daga gefe,
" Tashi ta taimaka miki ta saka miki. "
Mamma tace tana murmushi, wani banbarakwai Iman taji, ta tashi cikin sanyin jiki yarinyar ta
hau saka mata alkyabbar cikin k'warewa. Ji take tamkar mafarki, kamar zata farka taga komai
yana yadda take. Har ta gama gyara mata, ta kawo sauran kayan ta sassaka mata ta fito sosai
a gimbiyar ta mamaki be bar ta ba.
 Â
  Khadija da Zahra ne suka shigo, kusan sa'annin Iman din ne a family, doki ya saka su
zuwa suka Iman din suma su bawa idon su abinci, suna shigowa dakin suka ganta cikin shigar
da tayi masifar mata kyau, shigar alfarma.
  Hoto Zahra ta ciro waya ta hau daukar ta, kala kala har da videos dan dole ne yau
followersa dinta na Instagram su kara kiyayarta.
  Kiran ta ya sake yi dan da gaske ya matsu ya ganta, irin matsuwar ba don idon sirikai ba,
da dumbin jama'a da sai dai kawai ta ganshi a duk ma in da take.
  Mamma ce ta dakatar da hotunan haka, tace suyi mata rakiya zuwa in da Muhammad din
yake, ko tace Yarima Muhammad dan sunan kam be chanchanci a dinga fadar sa haka nan kai
tsaye ba.
  Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, haka ta tashi tana turo baki. Tare suka fito da biyu
daga cikin hadiman yan matan nan, suna daga bayan ta suna take mata baya, domin da gaske
Ammi tayi musu gargadi akan surukarta ta, su kula da ita da komai nata
  Suna zuwa daf da seat room din suka soma jin hayaniyar maza,amma ba irin hayaniyar
da zaka ji ba irin ta wasu mazan marasa aji da tsari. Hayaniya ce ta nuna farin cikin su da taya
murna cikin ilimi da wayewa. Ji tayi kamar ta koma da baya, dan yadda ta tsani taro na maza
har ya zama tana ciki, bata san kalar kunyar da zata sha ba, dan da alama dukkan su masu
surutu ne. Bata dai ji muryar uban gayyar ba, ta kamo addu'a ta soma yi har ta samu nutswar ta
"Iman." Ya kirata yana karasowa wajen, tare suke da Habib da abokin sa Sadeeq. Murmushi
tayi masa
"Uncle Khalil, ashe kazo."
Murmushin yak'e ya maida mata, ya tuna da warning din da Moh ya kada masa, duk da yayi
kokari matuka be saba ka'ida ba, yanzu ma dole ce ta sakashi zuwa tun da dai ba zai ki zuwa
daurin auren Zeenat ba.
"Nazo Iman, Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya."
"Amin."
Ta amsa a ciki tana jin babu dadi, lokaci daya yanayin sa ya sauya, yayi saurin barin wajen
yana yin gaba, suka gaisa da Sadeeq da Ya Habib sannan suka wuce zuwa in da zasu.
  Sallama Ummimi tayi daga kofar, ta sanar da zuwan Iman din kamar yadda yake a tsarin
masarauta, murmushi Moh yayi me aji, ya mike da kansa yana hararar su Ja'afar
"Amaryata tazo dan Allah muna bukatar privacy."
Dariya suka kwashe gaba daya, ya hade rai da gaske ba da wasa ba,su ka hau tsokanar sa
amma yayi fumfurus yace wallahi sai sun fita. Musaddik ne yace
"Ai ka bari ta shigo mu gaisa ko? Sai mu fita daga baya."
Da kai ya amsa ya koma ya zauna yana jin rawanin da ke kansa ya soma gundurar sa. Shigowa
sukayi bayan sun saka Iman din a tsakiya, idanun ta da tayi kokarin saukar dasu k'asa sosai
suka shiga cikin nasa, da sauri ta dauke idon ta, ta zauna su Zahra suka sakata a tsakiya.
Gaishe su sukayi suma suka amsa sannan suka gaisa da Iman din da take amsa musu ciki ciki
dan ji take kamar ace fit ta fice saboda tsoro.
"Capt. Lets snap please."
Wani abokin sa Gbenga yace yana kallon sa
"Ok sir." Yace yana tashi, taimaka mata Zahra tayi, ta isa wajen da yake a tsaye, daga gefen sa
ta tsaya, sai taji kamar ana saka abu ana bubbuge mata kafafunta. Hannun ta taji yana laluba ta
cikin babbar rigarsa, ta daga kai da nufin kallon sa, shima a lokacin kallon ta yake, Ja'afar yayi
sauri ya dauki scene din, hoton yayi masifar kyau, duk suka hau yabawa. Â Â Masifaffiyar kunyar da take ji ta hanata sakewa sam, duk da haka an dauki hotunan sosai
sun fita, banda camera man suma wayoyin su duk babu na banza.
  Wani irin laushi hannun sa da yake cikin nata taji,ta tuna kullum cikin safar hannu yake
zuwa mata, duk sanda zata ganshi hannun sa da kafar sa, na sakaye, sai yanzu ta gani dalilin
nasa na yin hakan.
 Mammatsa mata hannun ya dinga yi, ya hanata sakat ya sakata a wani irin yanayi me
wuyar fassarawa, gashi ya saka shi cikin rigar yadda ba wani wanda zai lura, sai da aka gama
hotunan tas sannan suka fita suka barsu da nufin idan sun gama gaisawa sai su fito a shiga
cikin gidajen ayi sauran hotunan a cewar Musaddik. Â Â Kamar me jiran kiris kuwa, suna gama ficewa ya saka dukkan karfin sa, yayi hugging dinta
kamkam yana sauke tagwayen ajiyar zuciya.
 Â
"Alhamdulillah." Ya furta yana murmushi
"Mrs Muhammad Ahmad Santuraki."
Ya rada mata a kunnenta, ture shi tayi tana turo bakin ta gaba, ya tsaya yana kallon ta dan be
taba sanin ta iya shagwaba ba sai yanzu
"Me yasa kayi haka?"
Tace cikin dan daga murya ita a dole ya bata mata rai, riko ta yayi da sauri ya dora hannun sa
akan lips dinsa yace
"Shssh... Ba'a dagawa miji murya babu kyau."
Kokarin ture shin