Showing 45001 words to 48000 words out of 124388 words

Chapter 16 - HALIN GIRMA Book Complete by Hafsat Rano .pdf

11 Mar 2025

7883

suka dinga insisting yasaka suka karba dan
kar suga kamar sun raina musu ne.
Suna gama fita daga gidan masu kawo kayan Zeenat ta shigowa, mata ne kwantsam masu
mugun yawa, masu goyo ne, gasu nan harda wanda suka ciko bus suka zo. Ana kokarin daga
Mama a maida ta cikin daki sanarwar zuwan su ya katse su, a sanyaye suka dawo suka zauna,
suka shigo bayan an matsar da kayan Iman an tura wasu dakin Abba da dakin Maman. Da kallon bakin ciki Mama take bin su, kamar ta tashi ta hau bugun su haka taji, yaran da
suka zo dasu suka dinga ihu na goyen sai da aka sakko su, na hannu kuwa suka hau wasa a
falon. Gaisawa akayi suka gabatar da kansu, kafin ma su dire sunan Zeenat din Mama ta ja
numfashi da take jin kamar zai fice daga jikin ta.
"Kuyi hakuri asthma ce da ita nema take Kuma ta tashi tun dazu, tashi Yaya mu shiga ciki ki
huta."

Aunty Maimuna kanwar Maman tayi saurin rufawa ta janye Maman dan ta hango matsala
babba, kamar ma kokawa take da numfashiin ta. Suna shiga dakin ta kurma ihu, ihun da kowa
ya ji shi, da tayi sauri ta saka hannu ta rufe mata baki

"Haba Yaya Hajara, ai sai aji kunya, dan Allah kiyi hakuri."

"Kutmar uban hakuri, kike ce min nayi hakuri? Bayan kinga abinda ya faru? Kinga yadda
Ibrahim ya munafurce ni da yan uwansa? Bayan duk halaccin da nayi musu ? Amma kike cewa
nayi hakuri, ke kinsan me nake ji? Innalillah, wayyo Allah na."

" Ni dai kiyi hakuri, ko ma menene ki bari a gama taron nan, kinga mutane zasu tafi dake a
baki."

" Taro? Ke kina ganin za'a cigaba da taron nan?"

" Toh me za'a yi Yaya?"

" Ba zai yiwu ba, wallahi sai dai a fasa auren, amma ba zan bari bakin ciki ya kashe ni ba a
banza." Sai ta sake fashewa da kuka, kuka irin wiwi din nan da kana gani zaka tabbatar da ba
karamin kuka mutum yake ba. Duk yadda Aunty Maimuna taso ta bata baki tayi hakuri ta kasa,
sai kawai ta fito ta rufo mata kofar ta dawo wajen bakin, lokacin har an soma bud'e kayan,
akwatu na guda hudu sai kit daya, da kayan ta masu kyau daidai da tsarin akwatunan, amma
ganin da mutane sukayi wa kayan Iman ya saka zasu ga na Zeenat din kamar bola, a daddage
kowa ya kalla, suka dauko dubu ashirin suka ce gashi nan ta kai dinki ba'a samu an dinka ba
saboda kurewa lokaci. Daga haka sukayi musu sallama aka je dakin Mama a dauko ragowar
kayan da suka rage ta ce idan an basu ko ruwa ba'a za'a basu ba, da k'yar Aunty Maimuna ta
bata hakuri aka saka musu ruwa da lemo a bayan mota suka tafi.

Daya bayan daya yan uwan Abba suka zo suka kwashe kayan iman suka maida su bangaren
Gaji a cewar su kar bakin ciki da kishi ya saka Mama ta saka wuta ta kona su.
Hauka hauka Maman ta soma da suka shigo, kowa yayi mata banza suka dinga dariya suna
yada mata da magana, suka kwashe komai suka yi tafiyar su. Jiki a sanyaye kawayen Mama
suka dinga sulalewa suna guduwa kowa burin sa ya isa gida ya bada labarin abinda ya faru.

Zeenat na wajen saloon suna ta waya da Bashir kiran Maman yake ta shigowa tana kin
dagawa, da dai taga kiran ya ishe ta sai tace ya bari ta daga wayar Maman, katse nasa kiran
tayi ta daga na Maman.

"Kina gidan uban wa wai?"

"Mama kinsan fa ina saloon."

"Toh ki bar komai kike ki taho gida, kizo yanzu ki same ni."

"Mama ban gama ba, kuma kinga zamu je mu siyo head din da zan saka da dinner da Bashir
daga nan..."

"Bashir din yaci abu ta kaza uban sa, na rantse da Allah kika bari man da awa guda baki dawo
gida ba, sai kinga yadda zan miki" tana kaiwa nan ta katse kiran, saroro Zeenat din tayi rik'e da
wayar cike da mamakin Maman.


"Me ya faru kuma?" Ta Tambayi kanta cike da mamaki.

Safa da Marwa Mama ta dinga yi a daki tana jiran Zeenat, ko sama da kasa zata hade ba zata
yarda ayi auren nan ba, tasan idan ita kanta Zeenat din tazo taga abinda ya faru zata ce ta fasa
ne, shege matsiyaci dama munafurtar su yayi kenan.

" Yaya Hajara da kin zauna kin nutsu, tashin hankali ba zai gyara komai ba."

" Ba zaki gane halin da nake ciki ba, ba zaki gane ba, ina cikin tashin hankali, bayan kunyar da
nake ciki." Ta fad'a tana cigaba da zagayen, idanun ta ya kada yayi jajur taci kuka ta godewa
Allah. Jugum sukayi kowa da abinda yake rayawa a ransa. A haka Zeenat ta shigo ta same su,
Mama tayi kanta da sauri ta fizgo hannun ta da sauri.
" Kika ce min talaka ne, kayan jikin sa ma a yayyage, daga gani bashi da komai."

"Waye? Wai Mama menene ya faru?"

" Ubanki, bake ce kika ce min wanda yazo neman auren Iman talaka bane?"

" Eh Mama, dan baki ganshi ba."

Dundu Mama ta kai mata ta goce cikin bacin rai tace

" Toh dan ubanki dan sarki ne."

" Sarki!!!" Zeenat ta fad'a da karfi tana zaro ido






*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*

_1aHALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107
1/21/22, 12:57 - Buhainat: Halin Girma
    17

Hafsat Rano

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇�_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇�_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇�_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_con
tent=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator
=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLo
SKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇�_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

****************

"Sarki!" Ta zaro ido cikin tsananin kaduwa

"Laifin ki me, duk laifin ki ne, da baki yi min karya ba, da baki boye min abinda kika gani ba, da
nasan abinda ya kamata nayi tun a lokacin."

"Haba Yaya Hajara, komai fa da kika gani ya faru toh dama chan haka yake a rubuce."

" A ah Maimuna, wannan kam sakaci na ne, ni ce duk na jawo komai, gashi yanzu bansan
yadda zan ba, komai ya kwabe min."

" Hakuri kawai zamuyi mu tayasu da addu'a, kudi ba shine kwanciyar hankali ba,rufin asiri 
shine, idan har Bashir din zai kula da ita ai shikenan, a hankali sai suyi kudin su."

" A ah, ba zai yiwu ba, shegen yaron nan da har zai iya yaudarar mu, ya ha'ince mu ke kinsan
ba mijin kwarai bane, dole Dr yazo a sake sabon zama, wallahi ba zan bawa yata mayaudari
ba."

" Toh wai yama akayi? Kika ganshi a fakiri sannan kuma ya koma dan sarki? Ta yaya hakan ta
faru? Bayan babu wani abu da ya nuna hakan tun farkon zuwan sa?"

" Salamu alaikum." Habib ya yi sallama kafin ya shigo dakin, su i su ne a ciki shiyasa ya shigo
kai tsaye, ya gaida sisters din Mama sannan ya kalli Zeenat dake gefe tana matsar kwalla, yayi
kwafa ya zauna akan kujerar gaban mudubi yace

"Kiyi hakuri Mama dan Allah, amma ni da kaina na fad'a miki Bashir ba mutumin kirki bane,
yanzu dai hakuri kawai za'a yi tunda lokaci ya riga ya kure, dan Allah karki yiwa Abba wata
magana kinsan dai ba zai saurara ba, dan Allah ki kwantar da hankalin ki, kiyi musu addu'a
arziki ai na Allah ne. "
Wani kallon banza Mama tayi masa, kafin ta nuna masa kofa

" Fice ka bani waje bana bukatar maganar ka. "

Mikewa yayi, yana jin babu dadi abinda Maman take yi, tun daga irin rikon da tayi wa Iman din
wanda sun sha haurawa sama a kai idan yayi mata magana, daga baya sai ya daina kawai ya
watsar amma kuma ya kan yawan yiwa abokin sa sadeeq maganar ta akan zai bashi Iman din
saboda yadda yaga zaman da take yana so yaga ta samu yanci, akwai ranar ma da hira ta saka
ya kwashe komai ya sanar wa sadeeq din duk da yasan kamar tonawa mahaifiyar sa asiri yayi
amma kuma ya zai? Baya jin dadi sam.

  Kofar ya ja musu ya bar gidan ma gaba daya dan ba zai zauna ya cigaba da kallon bacin rai
ba. A waje suka hadu da Abba ya aike shi karbo wasu kaya sai kawai ya biya ya dauki sadeeq
suka wuce tare.
  
***Har dare Abba be shigo ba, idon Mama kamas tana jiran sa, Zeenat ma idon ta biyu sun
shirya samun Abban ita da Maman ayi magana dan da gaske take ba zata kuma auri Bashir ba
yanzu, musamman bayan taga kayan da aka ce wai nata ne, toh wai mana, dan bata saka rai
ko hasashen irin su ba ko kad'an.    Kamar Abban yasan za'a yi haka yaki shigowa da wuri har sai da suka soma kosawa, gaba
daya duniya bata musu dadi sam, Bashir sai kiranta yake amma sam taki dagawa dan bata da
lokacin sa balle ta wayar sa.
   Wajen sha biyu Abba ya shigo bayan ya gama kallon kayan iman din a bangaren Gaji duk
da be iya kallon komai ba sama-sama shima don sun matsa masa ne, Gaji ce ta kirashi daki
tace ko me Maman zatayi kar ya yarda ya biye mata, ayi a gama komai lafiya shine kawai.
   Yana shigowa ya gansu a falon Zeenat na rakube a k'asan kujera tana cigaba da matsar
kwalla, yi yayi kamar be gansu ba, yayi hanyar dakin sa Mama tayi saurin tare shi

"Dr."

"Kinga dai a yadda na shigo kinsan akwai gajiya, ki bar duk wata magana zuwa gobe da safe
idan ALLAH ya kaimu."

"Ba zai yiwu ba, idan na bari aka kai gobe na samu matsala, yanzu zamuyi ta mu san abinda
muke ciki."

Kada kansa yayi ya dawo ya zauna sannan yace

"Ina jinki."

"So nake a fasa auren Zeenatu, ba zata auri Bashir ba."

Wani banzan kallo Abban yayi mata, kafin ya hade rai sosai yace

"Ashe ma ke mahaukaciya ce ban sani ba Hajara, Ashe baki da tawakkali ma, ashe ma baki
san komai game da rayuww ba, bari kiji."

Ya juyo yana kallon ta

"Dama shi sharri dan aike ne da kike ganin sa, duk in da yaje sai ya dawo, dan haka Wallahi,
Wallahi kinji ma rantse ko?"

" Ba zan karya alkawari na ba, ba kuma zan zama mutumin banza ba, sai dana jaddada muku
ke da ita gata nan, nace kunji kun gani? Sai yanzu da ya rage yan awowi shine zaku zo min da

maganar banza? Saboda bansan me nake ba ko?"

" Idan kana kaunar Allah Dr ka rufa min asiri a fasa auren nan dan Allah!"

" Lallai Hajara kin haukace, wallahi babu abinda zai hana auren nan sai dai idan cikin mu biyu
babu wani, ko ni na mutu ko ita Zeenat din ta mutu, amma in dai da ranmu da lafiyar mu wallahi
sai an yi, kinji ma na gaya miki."

" Abba dan Allah kayi hakuri, wallahi zan iya mutuwa."

" Allah ya jikan ki."

Ya tashi yayi shigewar sa daki ya saka key kar ma ta samu damar biyo shi dan a yadda ya
hangi tashin hankali a idon ta, zata iya jure su kwana a tsaye akan maganar da babu komawa
baya.

Wani irin marayan Kuka Zeenat ta fashe dashi, bata san ba son Bashir take ba, kwadayin abun
sa da kuma kishin Iman ya sakata ganin kamar son nashi take, sai yau ta gane kawai bakin
cikin da take wa Iman ne ya sakata amince dashi.
  A zaune suka kwana, babu kalar tunanin da Mama batayi ba akan washegarin, har da tunani
ko ta dauki Zeenat ta gudu da ita? Kafin gari ya gama haske tuni hayaniyar gidan ta cika ko'ina
wanda ta tabbatar da gangan suke yi don a kular da ita.
   Da k'yar taayi sallah ta saka Zeenat ma tayi lokacin yan uwa har sun tashi sun fara gyara
shashen Maman.
   Dakin Abba Mama ta shiga, ta same shi ya fiddo sabbin kayan sa da zai saka ya ajiye a
saman gado, yana waya da Maman Iman, duk da ta shigo amma be daina wayar tasa ba, ya
cigaba da yi mata bayani

"Masu zuwa daurin auren su taho da ita, kinga anan dinma za'a so a ganta, in yaso daga nan
sai a wuce kawia da ita."

"Owk shikenan."

Ta amsa sannan ta kashe wayar. Haushi ya sake turnuke mama amma ta share dan ba abinda
ya dameta bane a yanzu, matsalar da take ciki yanzu tafi wannan.

"Ina kwana?" Ta durkusa a k'asa ta gaishe shi,

"Lafiya lou." Ya amsa a gajarce yana cigaba da duba sakwannin wayar sa.

"Dan Allah Dr kayi hakuri, hannun ka baya taba rubewa ka yanke ka yar, kar ka hukunta yar ka
akan laifin da ni na aikata, naji duk hukuncin da zaka yi min kayi min amma dan Allah a fasa
auren nan."

" Kinsan Allah?" Yace yana ajiyewar wayar hannun sa

" Ba zan fasa auren nan ba, iyayen yaron nan sun zo na karbi maganar su nayi komai har sun
kawo lefe sai yau ranar kawai kice a fasa? Nace musu me kenan? Tun farko ban fad'a muku
ba? Ban nuna muku illaar abinda kuka nace akai ba, kuka nuna min ku ba zaku fasa ba, har
kika saka zeenatu ta watsa min k'asa a ido ina mahaifin ta, ko da ace Bashir yaron kwarai ne
idan nace ta hakura dashi ba zaki taimaka wajen ganin ta yi min biyayya ba? Amma me kikayi?
Sannan sai yanzu, sannan zaki zo min da maganar banza, ya kike so nayi?"

" Dan Allah nidai kayi hakuri ka yafe mana,dan Allah ka taimaka."

" Wallahi Hajara babu abinda zan iya akai, kinji ma na rantse, ki barni dan Allah."

Zama tayi dabas a k'asa, sai kuma ta tashi da sauri ta fice ta nufi shashen Gaji, ta same su a
falon yan uwa ana ta shewa, ta wuce su zuwa ciki kamar wadda ta zare. A k'asa ta tsuguna ta
gaida Gaji wanda rabon da tayi haka an dade.

" Dan Allah ki taimaka ki saka baki Dr ya fasa auren nan, wallahi idan akayi auren komai zai iya
faruwa, nasan ke kadai yake jin magana dan Allah."

" Yana ina?"

" Yana gida, dan Allah ki taimaka min."

" Kije kice idan ya gama ina neman sa, Allah ya kyauta ya rufa asiri, sai a hakura kawai."

Tashi tayi da sauri, ta manta ko godiya bata yi ba, ta fice kowa ya bita da kallon mamaki cike da
jin haushi. Ko da ta fadawa Abban be ce mata komai ba, da ya fito ya shiga wajen Gajin bata yi
masa maganar ba, ya gaisa da kowa sannan yayi breakfast da masa ya wuce wajen yan uwan
sa.   
***Daren ranar Moh be runtsa ba, duk wasu bakin da zasu iso sun gama isowa a lokacin kowa
an sama masa masauki na alfarma. Abokan sa da sukayi karatu tare suke kuma aiki tare sai dai
kowa wajen da take daban ne suka sauka a cikin gidan a bangaren Moh din, kafin a daura
auren su wuce adamawa sannan su sake dawowa Kanon saboda events din da za'a yi a
Kanon.
   Raba dare sukayi ana hira, anan suke fad'a masa suma fa sun shirya masa kayataccen
bikin sword crossing amma a abuja saboda suna so manyan su na wajen aiki su ma su zama
sun samu halarta. Abubuwan sun so suyi ma Moh yawa saboda shi dai tsakanin sa da Allah zai
fi so ace da an daura auren kawai su yi tafiyar su shi da ita,amma kowa kokari yake ya shirya
wani abu da zai sake rik'e su, shi dai kawai dan kar ya fito fili yace baya so ne, amma har ga
Allah da kowa ya hakura.

   Da suka tashi da safe ma wasu suka dora da hirar in da Musaddik da wasu ciki suka tafi
karasa abubuwan da basu samu gamawa ba, duk da sai bayan sallar juma'a za'a daura auren
kuma komai da ya kamata su yi an ma riga an gama amma suma zasuyi nasu kokarin ko yaya
ne.     Tun wajen sha biyu Takawa ya saka aka kira masa Muhammad, ya same shi da manyan
mutane har da Mr President sai Bubu da tasa jama'ar. Aji dan tsoho ma ba'a barshi a baya, yaji
dadin ganin su musamman Aji da be saka ran zuwan nasa ba. Bin su yayi daya bayan daya ya
gaishe su dukka, kowa ya kawo kyautar bangirma ya damka masa, harda masu blank cheque
duk dan a birge Takawa.
   Godiya yayi musu dukka ya koma wajen jama'ar sa, suka dauki duk abinda zasu dauka
suka wuce gidan Moh din dake Lamido Crescent yadda zasu fi yin komai a tsare.
  

***Wanka na wajen uku kenan idan tayi ta gama da wannan hadin ruwan sai Mamma ta sake
bata wani, gaba daya wani irin sulbi fatar jikin ta take yi, tayi wani irin haske

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login