Showing 105001 words to 108000 words out of 124388 words

Chapter 36 - HALIN GIRMA Book Complete by Hafsat Rano .pdf

11 Mar 2025

7882

ne ya shigo wayar sa daga gate din gidan, kamar be zai daga ba sai kuma ya tuno da
zuwan su Habib, dagawa yayi suka tambaye shi ko yasan su, yace a farsu su shigo brothers din
Iman ne, da haka ya kashe ya sauya rigar sa zuwa mara nauyi saboda zafin da yake ji.

***Dagata Ummimi tayi ta taimaka mata bayan ta gama amai, ta gyara wajen ta dawo ta
tsugunna a gabanta tana mata sannu, da kai ta amsa mata, ta rufe idon ta hawaye ya gangaro
mata. Shigowa sukayi su hudu, shine a gaba suna bin bayan sa, ya zo gabanta ya durkusa ya
saka hannu ya dago kanta.
"Fine Lady." Ya shafi gefen fuskar ta, ta saka ragowar karfin da take dashi ta ture shi, ya
tuntsure da dariya yana kallon ta

"Ga Dr nan zai duba min ke, dan ina tunanin nine zan maye gurbin Capt bayan na aikashi
barzahu, kina da kyau."

"Dr matso, a duba min da kyau idan har ciki ne, a cire shi ko ta yaya ne, ba zan iya jure ganin
sa ba, kaga auren mu ba zai dau lokaci ba idan aka cire shi."

Matsawo likitan yayi, ya bud'e idon ta, sannan ya taba goshin ta, ya dauko wata roba a cikin
kayan sa ya mikawa Ummimi.

" Gashi fitsari zatayi."

Kin karba tayi, na bayan ya daka mata tsawa, ta karba da sauri tana daga Iman din, dukkan su
hawaye suke amma babu me bud'e baki yayi musu saboda tsoro. Tare sukaje tayi fitsarin suka
fito ta dawo ta kawo masa, ya karba a wajen ya duba, ya kuma tabbatar da ciki ne, yan
tambayoyi yayi mata akan period dinta ta amsa tana kuka.
"Ciki ne oga, na sati shida."

"Ya za'a yi dashi?"

"Ba zai wahalar fita ba, tunda karami ne. Yanzu dai zan dawo sai nazo da maganin da zata
sha."

"Yayi kyau, rakashi yaro." Rik'e masa jaka wanda aka kira da yaro yayi suka fita, sannan shi ma
suka fita.

"Hello... Samha baby." Ya fad'a da yaji ta daga wayar

"Eh tana hannu har yanzu."

"Eh ya tabbatar da ciki ne, amma za'a cire shi tunda baki da bukatar shi."

"A ah... Babu fa abinda zan yi wa masoyinki, kawai wata yar harkalla ce zamu karasa ta. "

" Yawwa toh" tace tana jin dadi.

" Sai mun sake magana ko? "

" Amma ai bana samun ka kwata-kwata a waya, me yasa?"

" Babu komai, idan akwai bukatar muyi magana ni zan kiraki da kai na."

" Shikenan."

Dariya yayi sosai bayan sun gama maganar, be san bata da tunani ba kwata-kwata sai yanzu,
amfani yayi da ita ya samu abinda yake so, ba kuma zai kyale wanda ta kwallafa rai akai ba, ba
zata taba samun cikar burin ta ba in dai yana numfashi.

***A waje ya tarar da su Habib din bayan ya gama parker motar, ganin tare suke da Gaji ya
sakashi saurin karasawa ya taimaka mata ta fito, sannan suka gaisa ya saka aka rakata ciki su
kuma yace su biyo shi garden dake baya. Kujeru ne a wajen, ya zauna sannan suka zauna
suma, yana karantar yanayin Mahfuz din, sai a lokacin yayi masa kallon tsaf, ya kuma fahimci
hakan yanayin sa ne, ku kuma yanayin environment din da ya taso kamar yadda Habib yayi
masa bayani dazu.

"Ta yaya zaka iya taimakawa?" Yace bayan ya gama nakaltar yanayin sa, gyara zama yayi
sosai, yayi murmushi sannan yace zai masa yan tambayoyi,da ka ya amsa masa ya bashi go
ahead.

"Babu wani message ko kira da ka samu daga wajen kidnappers din?"

"Akwai."

"Zan iya gani?"

"Why not?" Ya mik'a masa wayar, ya karba ya duba messages din dukka, ya jima yana sake
dubawa kafin ya mik'a masa wayar sa

"Kayi tunani sosai, wanene kake da matsala dashi, irin wadda kasan lallai da zai samu dama
akan ka zai iya aikata maka komai?"

"Babu shi, bansan waye ba gaskiya."

" Babu ko old friend? Ko abokin aiki?"

Shiru yayi cikin tunani

" Think... "

_" Zan dawo komai daren dadewa, sai na dauki fansa akan ka, ko da zan karar da komai da na
mallaka ma duniya sai na maida rayuwar ka abun kwatance! "_

"JABIR! " Yace yana mikewa tsaye da sauri, tashi Mahfuz yayi shima yana kallon sa

" Waye shi. "

" Aboki na ne, abokin aiki na ne. "

" Recently na samu labarin ya zama babban terrorist kuma yana da connection da manyan
k'asar, bayan shi bana tunanin akwai wanda zai bukaci rayuwa ta, babu. "

"Ya akayi na manta? Ya akayi? "

" Kasan in da za'a same shi? "

Girgiza kai yayi,

" Ban sani ba. "

Komawa sukayi suka zauna, Mahfuz ya ciro biro da paper ya rubuta wani abu, daidai lokacin da
Moh ya daga wayar Musaddik yace ya same shi a garden, yana ajiye wayar sai gashi ya
zagayo dama chan yana cikin gidan, da kallo Mahfuz ya bishi kafin ya karaso wajen yace

"Waye shi?"

"Best friend dina ne."

"Ok." Yace a gajarce ganin ya karaso, ya mik'a musu hannu suka gaisa amma da ya bawa
Mahfuz hanun sai ya rik'e hannun nasa har sai da suka kalle shi dukka, sai ya saki yana
murmushi ya jingina da kujerar da yake kai, wani kallo Musaddik yayi masa ya zauna yana
maida hankalin sa kan Moh.
"I'm very sorry Capt..."

"Babu komai, nasan wani uzuri ne dakai." Ya katse shi kafin ya karasa.

"Babu wani progress ko?" Yace

"Babu."

"Allah ya bayyana su."

"Amin."

"Ya aiki?" Mahfuz ya tambayi Musaddik unexpectedly

"Aiki Alhamdulillah."

"Wanne aiki kake?"

"Harkar kwangila, kaifa?"

"Detective!"

Wani kallo Musaddik yayi masa, yayi shiru,.sai kuma ya kalli Moh

"Naga kamar kana da baki, dama inaso muyi maganar flash din nan ne tunda naga ka dawo."

"Flash?" Mahfuz yayi karaf ya tambaya

"Let's talk about that later." Moh yace sai ya mik'a wa Musaddik hannu

"Suna ina?"

Sosa kansa yayi

"Dalilin da yasa kaga kamar ina janye kaina a case din nan kenan, wallahi bansan ya akayi ba,
na rasa su gaba daya."

"What!"

"Kayi hakuri,ranar da aka sace wayata aka hada dasu gaba daya, bansan ya zan maka bayani
ba, nasan kuma muhimmancin flash din a wajen ka, shiyasa na kasa nutsuwa."

Murmushi kawai Mahfuz yayi, ya dire pen din hannun sa akan dan deborin da yake gaban sa,
ya dora hannun sa akai ya jingina yana masa kallon tsaf.

" Idan nace wani abu zaka yarda dani?"

Girgiza masa kai Moh yayi dan maganar batan flash din ba karamin bashi mam I'llaki tayi ba.

"Ina bukatar yara hudu cikin yaranka na gate."

" Me zasuyi maka?" Musaddik yace ransa a bace.

" Wait and see." Yayi murmushi, shi Moh ba gane kan maganar ba kwata kwata, yayi dai abinda
Mahfuz yace ya kirawo su suka zo, suka tsaya daga gefe, tashi Mahfuz yayi ya zagayo ta bayan
Musaddik,

"Take off your mask!"

"Kamar ya?"

"Me kake nufi Mahfuz?" Moh da shima ya mike ya fad'a cike da mamaki

" This man is deceiving you, ka kalli hannun sa, ka kalli fuskar sa, akwai banbancin skin color,
he's definitely using a mask, idan har ya musa, zan tabbatar maka."

"Noo...you are mistaken, wannan Musaddik ne, trusted friend dina ba zai taba deceiving dina
ba,you cannot accused somebody without a proof."

" Shine zan maka proving yanzu ai, wait and see, guys... Ku rik'e shi."

" Dakata!"

Moh yace ransa na baci, ba zai dauki wulakanta Musaddik yana kallo ba.

"Waye wannan Capt, waye zai zo ya shiga tsakani na da kai?"

"Calm down aboki na, misunderstanding aka samu amma zan masa magana..." Sai ya juya
wajen Mahfuz din

"Let's call it a day, zamuyi magana gobe, Habib ku jirani a wajen mota."

"Muje Mahfuz." Wani kallo yabi Musaddik din dashi, sannan ya juya suka bar wajen da Habib.

Juyawa kan Musaddik yayi da ransa yayi masifar baci, ya shiga bashi hakuri akan abinda
Mahfuz din yayi, yace ya jirashi yana zuwa bari ya sallame su. Yana barin wajen ya ciro waya,
ya kira shi yana matsawa chan gaba.

"Akwai matsala." Yana dagawa yace

"Ya fara suspecting dinka ne?"

"Be fara ba, wani banzan yaro ne bansan daga ina yazo ba, yaso dole sai ya nuna masa
gaskiyar mask da na saka..."

"Ya yadda?"

"Be yarda ba, kasan ya yarda dani sosai, so ba zai taba kawowa ba. "

" You have to be very careful, shi kuma yaron zan san yadda zan yi dashi. "

" Ok sir. " Ya kashe wayar yana juyowa, sukayi ido biyu da Moh da yake tsaye a bayan sa
kamar mayunwacin zakin da ya shekara be ce ba.




***Assalamu alaikum sisters, masu korafi naga wasu daga cikin korafin ku, ina mai baku hakuri
akan matsalolin da aka samu, dan gane da rashin posting halin girma shekaran jiya da jiya,
hakan ya faru ne sakamakon ciwon hakorin da ya matsa min hade da zazzabi, wanda har ta kai
ban iya samun duba sakonni ba balle har na iya zaman rubutu
Duk cikin zafafa biyar babu wadda a cikin mu take jin dadi a duk sanda batayi posting ba, Allah
ne shaida ana iyakar kokari wajen ganin Anyi abinda ya dace. Sai dai idan abu ya sha kan
mutum a ba yadda ya iya. Allah ya huci zuciyar duk wanda ransa ya baci ta dalilin jira ko wani
abu, ba da gangan bane wani lokacin kuma ajizanci ne na dan Adam.
Allah ya rufa asiri ya sa mu gama lafiya
2/21/22, 08:16 - Buhainat: Halin Girma
38

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇�_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇�_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇�_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_con
tent=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator
=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLo
SKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇�_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

****
Zaune yake a office din commissioner of police lokacin da message din ya shigo wayar,
karantawa yayi yana kai karshe ya mike tsaye da sauri.

"Ya akayi?" CP ya tambaya shi yana kallon yana yin sa

"Akwai matsala..." Sai ya mik'a masa wayar ya soma zagaye a cikin office din cikin tsananin
tashin hankali, idan har akwai ciki a jikin Iman toh lallai tana cikin halin tashin hankali, yasan
yadda ciki musamman a watannin farko yadda yake wahalar wa yawa yawan mata suna shan
wahala kafin ciki yayi kwari wasu kamar zasu rasa ransu saboda tsabar wahala. Ya take ciki
yanzu? Me take ci?

"Akwai wani da kake da matsala dashi banda matsala ta cikin gida?"

CP ya tambaye shi bayan ya maimaita karanta sakon fiye da sau goma, har ya gano abu daya
a cikin sakon, akwai kiyayye me zafin gaske tsakanin duk wanda ya turo sakon, duk wanda
yake son ranka ba karamin kiyayye yake maka.
  Girgiza kai yayi ba tare da yayi magana ba,

"Idan ka gamsu da maganganun da mukayi, lallai muna da bukatar Kamal a binciken mu, domin
idan har ka tattara bayanan baya da na yanzu zaka gane akwai wani abu da yake a boye a
bayan dukkan cases din, case din ka da Laila, evidence din da ya wanke ka, sannan matar ka,
zai iya yiwuwa wani ne da yake son ta tun ba yanzu ba, ko kuma wanda yake da matsala da kai
ne amma shi da kansa yake son daukar fansa shiyasa har yayi kokarin wanke ka a baya, duk
wannan tunani na ne, ban ce ya zama gaskiya ba, amma ina ji a raina, cases din suna da alaka
da juna."

Zama ya kuma yayi a kujerar da ya tashi yana tattare bayanan dukka a kwakwalwar kansa, jiya
baki daya ranar a cikin bincike yayi ta, babu mutum daya da binciken sa ya nuna masa sai
Kamal. Evidence din farko shine sanda ya shiga bangaren sa, sai na biyu da suke zaune suna
magana da wani mutum ya sunkuyar da kansa, wata mace a gefen sa itama babu fuskar ta,
fuskar Kamal din ce kadai ta nuna wanda ya tabbata shi be sani ba, yana kyautata zaton gadar
zare suka danawa Kamal din sukayi amfani da son mulkin sa suka samu abinda suke so
sannan suka yi dumping din sa.

"Duk abinda ya kamata ayi, ayi Sir."

"Zamu fara da Kamal, ina fatan hakan ba zai zama matsala ga Maimartaba ba."

"In Sha Allah." Yace yana mikewa, jiri ne ya debe shi, yayi kamar zai fadi da sauri CP ya tashi
yana riko shi

"Subhanallah, Capt akwai matsala ba, sai ka daure saboda tana matukar bukatar taimakon ka a
wannan gabar."

Gid'a masa kai yayi yana rik'e kansa da yake mugun sarawa, be runtsa ba tunda ya diro garin
Kano, ba kuma yajin idan ka cire ruwa ya sakawa cikin sa wani abu, sai da ya dawo daidai
sannan ya mike yayi masa sallama, ya rakashi da ido yana yaba wa kwazon sa.

***Gidan su Iman din ya wuce kai tsaye, dan sunyi waya da Abba da safe yake ce masa bashi
da lafiya, kamar ma bp din sa ne yayi sama, yasan batan Iman din ne ya saka shi shiga
matsalar.
   A kofar gida ya tarar da Habib da saurayin nan na ranar nan, dauke kai yayi kamar be
gansu ba, sai da Habib din ya taso yazo wajen sa yana kokarin kiran waya.

"Sannu da zuwa."

"Ah... Babban Yaya."

Ya mik'a masa hannu suka gaisa, sannan yayi masa jajen abinda ya faru, suna maganar
Mahfuz ya karaso wajen, ya mik'a masa hannu kansa tsaye, kamar ba zai bashi hannun ba, sai
kuma ya mik'a masa a dakile suka gaisa.

"Zanga Abba."

"Owk Bismillah."

Yayi gaba, shi kuma suka biyo bayan shi tare da Mahfuz har part din su, Abba na kwance a falo
kan doguwar kujera, Mama ta shiga ciki dauko Hijab suka shigo, ya durkusa har k'asa ya gaida
Abban, wanda yake kallon sa ciki da tausayawa, ya ga dauriyar sa sosai dan kana kallon sa

zaka gane yadda ya tabu, ya rame sosai amma be karaya ba, be kuma zauna ba tun da ya
dawo.

"Akwai labari ne muhammadu?"

"In sha Allah Abba, ana iyakar kokari."

"Toh basu kira ba har yanzu ko?"

"Basu kira ba Abba."

"Shikenan Allah ya dawo mana dasu cikin koshin lafiya."

"Amin Abba"

"Sannu da kokari, kai ma Allah ya biyaka, Allah ya tona asirin azzalumai, tun jiya ban runtsa ba,
na rasa in da zan saka raina naji dadi, shikenan mutun bashi da daraja a k'asar nan tamu? Ace
satar mutum tafi satar kaza sauki? Wannan wacce irin musiba ce... Allahumma ajirni fi
musibati..."
"Allah ya bayyana su."

" Amin ya Allah. "

Suka hada baki gaba daya, shigowar Mama da Zeenat a bayan ta ne ya katse maganar da Moh
yaso yayi, ya dan kalle su sai ya dauke kai ya maida wajen Abba da alamun sa ya nuna yana jin
jiki. Gaisawa sukayi da Mama sama sama tayi masa jaje, sannan Zeenat da gaishe shi itama ya
amsa yana mikewa.
"Bari na koma Abba, duk yadda ake ciki zan kira dan Allah ka kwantar da hankalin ka."

"Shikenan, Allah yasa muji alkhairi."

" Sai anjima." Ya dan kalli gefen da Mama take ya fad'a sannan ya fice Habib da Mahfuz suka bi
bayan sa, sun kusan kai gate din gidan Mahfuz yace

" Zan iya taimakawa."

Tsayawa chak Moh yayi da tafiyar da yake ya juyo.

"Idan har zaka yarda zan iya taimakawa."

"How? Ta yaya?"

"Security ne from an intelligent agency a UK."

"Sounds good."

Moh yace yana dan rage hadewaar fuskar sa. Sai ya bud'e hannun sa alamun babu matsala
yace

"Idan har zaka iya taimakawa, shikenan sai muje ko?"

"Let me freshen up, zan zo daga baya. Ina zan same ka?"

" Habib ka rakoshi gida na, don't take long please."

" In Sha Allah."

Juyawa yayi ya fice su kuma suka koma ciki don Mahfouz ya shirya, anan suka tarar da Gaji a
part din ta saka Abba a gaba tana ta rusa kuka, bata samu labarin ba sai da Moh yazo yanzu
sannan tasan abinda yake faruwa, taji zancen a radio har ta tausaya amma bata kawo Iman
bace ,bata ma fuskanci zancen ba kwata kwata ma gaba daya. Baki Abba yake bata akan tayi
hakuri amma taki, sai kuka take ita lallai sai an kaita gidan Iman din, a dole haka Abba ya saka
tabi su Habib din ko ta barshi ya ji da kansa shima kawai dauriya ce irin ta namiji.
   Yana shiga gidan ya tarar da motocin masarauta, ciki ya shiga kansa tsaye, da mamaki
yake kallon Fulani a zaune a falon nasu, tare da mummy da Mamma sai wasu matan, suna
zaune jingum jingum cikin alhini da jimami, daga gefe hadiman Fulanin ne suma a falon, kallo
daya yayi ma duk matan falon, ya karasa gaban Fulanin ya durkusa ya gaishe ta, ta amsa
muryar ta na rawa alamun  bata dade da gama kuka ba, juyawa yayi ya gaida su mummy
wanda sai a lokacin ya samu ganin su, ta fad'a tayi fayau amma kuma a nutse take sosai, sai
yace ma Mamma ta fita fita hayyacin ta, wuce su yayi zuwa ciki, suka rakashi da kallon
tausayawa.
   Dafe kansa yayi bayan ya zauna a gefen gadon, komai nata yana nan a dakin hatta da
handouts

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login