Showing 111001 words to 114000 words out of 124388 words
Chapter 38 - HALIN GIRMA Book Complete by Hafsat Rano .pdf
sauran operation da suka taba zuwa, yau abun nasu ne, su aka
taba kai tsaye shiyasa kowa yake ji kaamar abin ya shafe shi sosai, cikin kankanin lokaci suka
isa saboda masifar gudun da suke, barbazuwa sukayi a dajin kamar yadda yake according to
plan. A daidai lokacin Dr da zai kawo maganin ya iso, tana kwance kamar kullum ta gama
galabaita sosai ya shigo rataye da jakar sa, tana ganin sa ta mike da sauri, bata ma san tana da
ragowar karfin nan ba sai data ganshi, ya ajiye jakar ya ciro magungunan a ajiye su, sannan ya
koma gefe ya tsaya yana jiran shigowar ogan, jim kadan sai gashi ya shigo, ya duba
magungunan yayi masa bayanin yadda za'a sha.
"Tashi!" Ya daka mata tsawa yana tamke fuska
"Dan Allah kayi hakuri, dan Allah."
"Wallahi sai kin sha."
"Dan Allah kayi hakuri." Ummimi tace tana kuka
"Shut up munafuka, idan na sake jin bakin ki sai na sheke ki har sai kin daina numfashi. "
Gefe ta koma jikin ta yana ta rawa, bindiga ya ciro ya nuna Iman dashi
"Karbi kisha kafin na harbe ki. "
Hannu ta miko ya zuba mata, ya kafe ta da jajayen idon sa, yana nuna ta da bindigar, ta sha
sannan ya juya yana murmushin mugunta ya fice likitan yabi bayan sa. Dakin da ya ajiye
Musaddik da driver ya shiga, ya tarar da Musaddik din a kwance amma kuma sallah yake daga
haka, kwafa yayi ya fito bayan ya rufe kofar, yazo wajen yaran nasa da suka cika harabar wajen
dauke da manyan bindigu cikin shirin ko ta kwana.
"Zan shiga na kwanta, ku kula sosai bana so a samu matsala."
"An gama Oga."
 Suka hada baki wajen fad'a, ciki ya shiga su kuma suka cigaba da tsaiwa a wajen.
 Zagaye gaba daya dajin sukayi, kowa ya kama stand dinsa, Moh da sauran zaratan sojojin
suka kutsa kai ciki, sai da suka dan shiga sosai sannan suka hango bukkokin dake wajen,
wanda suka tabbatar da nan suke. Sake rarrabuwa sukayi waje waje, suka sake zagaye
bukkukin. Â Sai da suka gama shiryawa tsaf, sannan Moh ya basu signal na su yi attacking dinsu, nan
fad'a musu ta sama ta ka, nan suka rikice suka shiga kokarin maida martani, sai dai yawan
Jami'an tsaron ya ninninka yawan su,. Cikin baccin da ya soma dauke shi yaji alamun
yamutsewar wajen, kafin ya kai ga mikewa aka bugo kofar dakin aka shigo, Moh ne a gaba
yaran sa na take masa baya, dukkansu a shirye suke su bada rayuwar sa dan ceto Madam din
Oga. Kasancewar be shiryawa zuwan su ba, sai ya zama kamar sun ci galaaba akansa ne,
babu bindiga ba babu komai a hannun Moh, ya matse shi a jikin bango ya shiga bugun sa, bugu
ba na wasa ba, sai da yayi masa laga-laga ya sake shi cikin jini ya fadi kasa, ya bi ya take
kansa da kafarsa cikin tsananin bacin rai ya soma magana.
"Kafin kaga karshe na, ni zan ga karshen ka da duk wanda ya goya maka baya..."
" Oga an samu Madam, she's bleeding so badly." Da sauri ya juya yabi bayan dan sanda da ya
shigo, ya bar yaran nasa da JABIR.
 Jini ne sosai yake zuba, da sauri ya karasa gabanta, idon ta da yake kokarin rufewa da kalle
shi. Rawa jikin sa yake ya tallafota jikin sa
" Bude idon ki, dan Allah ki bud'e idon ke, me sukayi miki? Me sukayi miki?"
Karasa rufewa idon sukayi ruf, ya dagata ya fita da ita jikin sa na rawa, idan har wani abu ya
same ta, sai ya karar da dangin JABIR kaf.
_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D'aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
2/24/22, 08:05 - Buhainat: Halin Girma
40
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇�_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇�_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇�_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_con
tent=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator
=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLo
SKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇�_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
****Wasu daga cikin sojin ne suka bi bayan sa, in da sauran jami'an tsaron suka cigaba da
dudduba bukokin har suka samu nasarar ganin Musaddik da driver a wani daki, sai makamai
masu yawan gaske suma daki gida, dukkan su suna bukatar taimakon gaggawa musamman
Musaddik da yake cikin mawuyacin hali. Â Â Karar harbi suka ji, daga baya wanda basu san dalilin harbin ba, a zaton su sun kama duk
yaran JABIR din, da shi kansa JABIR din bayan dukan da Moh yayi masa. Zagayawa baya
sukayi, suka ga mutum a kwance cikin jini, bashi da alamun yana tare da sauran yan iskan
amma kuma basu san me ya kawo shi wajen ba.
"Mu taimaka masa."
"Waye ya harbe shi?"
"Akwai sauran yan iskan a baya, let's check, ku dauke shi ku tafi dashi zamu biyo bayanki. "
" Ok. "
Suka ce suka taimaka masa, da k'yar yake numfashi saboda tsabar wahala, a motar da aka
saka Musaddik suka saka shi, suka bi bayan motar da Moh suke ciki dan basu taimakon
gaggawa. Rik'e yake da hannun ta yana kuka wiwi kukan da ya kasa dauriyar rik'e shi, gani
yake kamar motar bata sauri duk kuwa da irin gudun da suke tsulawa, idan har wani abu ya
same ta, ba zai bar kowa ba wannan alkawarin sa ne.
 Sanda suke karaso asibitin tuni iyayen gulma yan jarida sun iso domin samun na watsawa,
kofar baya suka koma suka bi, suka shiga asibitin dan a yanayin da take ciki ba zai yarda wasu
yan iska su dauke ta a hoto su yada wa duniya ba, duk ma wata gidan jarida ko talabijin da tayi
gangancin haka sai ya yi shari'a dasu. Â Â Da sauri nurses din suka karbeta, daidai lokacin da Babban likita ya karaso cikin tawagar
sauran manyan likitoci mata da maza, aka shiga da ita ciki domin bata taimakon gaggawa.
  Zagaye ya soma yi a wajen cikin yanayi na fitar hayyaci, wayar sa da take ta faman
nemam agaji ya gaza fitowa da ita balle ya iya amsa kiran da ake ta faman doka masa da ba zai
wuce daga makusantan sa ba, bashi da sukunin ciro wayar balle ma ya amsa ta, balle ya iya
wata magana ba tare da yasan halin da Iman din sa take ciki ba. Â Â Â Cikin kankanin lokaci asibitin ya cika da manyan mutane daga masarauta da kuma
gidan gwamnati, Takawa ne ya karaso a karshe ya samu shiga wajen da Moh din yake shi kadai
sai wasu sojoji daga gefe, sauran mutane suna ta dayan bangaren in da aka kai Musaddik da
saurayin da aka harba wanda yake cikin yanayi mara dadi. Â Â Yana ganin Takawa yayi saurin isa gareshi, sai kuma ya ja ya tsaya a gabansa ba, hannun
sa ya kama, ya ji yadda hannun yake rawa sosai kamar wanda yake jin masifaffen sanyi.
"Kayi addu'a muhammad, babu abinda zai faru kaji?"
Da ka ya iya amsa masa, sai a sannan ya ga su Abba, ya matsa ya gaishe su, dukkanin su
suna cikin tashin hankali, Abba kamar bashi ba saboda tashin hankali, sun riga Takawa zuwa
wajen amma ba'a barsu sun shigo ba saboda tsoron da yake wajen sai da Takawa yazo sannan
suka samu shigowa. Sunyi waya da Maman Iman din tun dazu ya kuma san zuwa yanzu sun
karaso amma ba lallai su shigo kai tsaye ba, sai ya dubi Muhammad yace
"Mahaifiyar ta suna waje, nasan ba za'a barsu su shigo ba."
"Bari naje." Ya fad'a yana yin gaba, daya daga cikin sojan ya bishi suka tafi tare, daga chan
baya ya hango su a tsaye suna magana da wani Soja da yaki fafur barin su, su shiga wajen,
ganin Moha da kansa ya nufo wajen ya saka sojan sake kallon matan.
"Alhamdulillah." Mamma tace tana share hawayen ta
Bud'e musu sojan nan yayi tun ma kafin ya karaso, dan yayi masa alamar ya barsu, suka shigo
suka sameshi, ya gaishe su, sannan suka tambaye shi Iman din, Alhamdulillah kawai yace suka
bishi zuwa ciki duk jikin su ya kara sanyi sosai da lamarin.
  Be barsu sun karasa wajen da su Takawa suke ba kasancewar duk maza ne, sai yasa aka
kawo musu kujera suka zauna shi kuma ya karasa ciki.
  An dauki tsawon lokaci kafin likita guda daya ta fito, har zata wuce sai ta ga Takawa, da
sauri ta je ta durkusa ta gaishe shi, sannan tace suna kokarin su in sha Allah babu matsala,
sannan ta je ta dauko abu ta dawo ta koma ciki.
   Sun iya iyakar kokarin da zasuyi wajen ganin sun tsaida cikin amma kuma hakan be
yiwu ba,saboda karfin maganin da aka bata ba zai bar cikin ba, Allah yaso babu wani illa da
yayi mata bayan fitar da cikin. Wankin ciki suka hada sukayi mata sannan aka saka mata drip
saboda ta rasa ruwa sosai a jikinta tsawon kwanaki tana amai sannan babu abincin da take ci.
Numfashin da take fitar wa ne kadai zai baka tabbacin tana da rai bayan haka babu wani abu
na jikinta da yake motsi, tayi fayau kamar ba ita ba, sai uban fari da tayi kamar babu
wadataccen jini a jikinta.
  Tura ta akayi zuwa dakin da aka kwantar da ita, sannan Drs din suka fito wajen da su
Takawa suke, suka kwashi gaisuwa sannan sukayi bayanin yadda al'amarin ya kasancewa pills
din da aka bata ne yayi karbi sosai, jiri ne ya kwashi Muhammad yayi kamar zai fadi wani
bafade yayi saurin taro shi, ya rik'e shi jikin sa. Hakuri kowa na wajen ya dinga bashi, kafin a
bada damar a shiga a ganta, Takawa ne ya fara shiga sannan su Abba suka shiga tare dasu
Mummy, sannan suka fito aka bar Muhammad din ya shiga. Tunda ya shigo ya hangi yadda
take fitar da numfashi a wahalce, jikin sa ya kara sanyi sosai, shine duk ya jawo mata wannan
matsalar tana zaman zaman ta. A da ya dauka matsalar sa kawai gidansu ne, shiyasa gaba
daya ya taso da tsanar mulki tun bayan da yaga abinda ya faru da Baban su Laila lokacin bashi
da wani girma sosai amma hakan be bar kwakwalwar sa ba, ya taso da tsanar mulkin da ganin
cewa duk wata masifa tana cikin gidan sarauta.
  Sunyi aiki tare da JABIR zai iya kiransa da abokin sa mafi kusanci dashi a wanchan
lokacin, bashi da hannu a matsalar da JABIR din ya samu daga sama har aka sallame shi aka
kuma karawa Moh din matsayi irjn wanda ya Jabir din ne ya chanchanta, bayan nan duk wata
alaka tasu ta yanke, har ya manta dashi sai lokaci zuwa lokaci yake tunashi,be taba saka wani
abu a ransa game dashi ba, rayuwar sa yake kansa tsaye ba tare da sanin akwai babban
makiyinsa da yake burin ganin bayan sa ba.
  Maganar Takawa ce ta fado masa wadda yayi masa ita dazu kafin ya bar asibitin
_"Ka sani bawa baya taba wuce ko ketare kaddarar sa, dan haka ka dauka wannan din
kaddarar ka ce kayi addu'a Allah ya baka ikon cinyeta. Sanin kanka ne mutum be isa ya hana
ko dakatar da kaddarar ka ba, kafi kowa sanin yaran da suke tare da kai suna tsaron ka gida da
mota ba wai na matsayin da kake dashi bane a aikin ka, alfarma tace ya saka aka baka su har
haka, wanda duk munyi hakan ne saboda mu baka kariya a gida da waje, sai dai yanzu na kara
tabbatar wa babu dan adam din da ya isa ya tsare ka face Allah, kuma duk abinda Allah ya
kaddara zai faru toh fa sai ya faru ko da a gaban idon mutum ne."_
  Gaban gadon ya ja ya tsaya cikin tsananin tausayin ta, be taba kawo tunanin wani abu zai
faru da su haka ba a dan kankanin lokaci nan, ya zata shikenan ta rabu da duk wata matsala
tun da suka riga sukayi auren su, ashe ba haka bane. Hannun wanda babu drip a jiki ya rik'e, ya
zauna a gaban gadon yana karewa fuskar ta kallo, daga gani kasan ba jin dadin baccin take ba,
bacci ne me cike da wahala iri iri.
  Ya jima sosai a dakin, babu motsin komai, kamar babu kowa aciki, knocking akayi, ya cire
kansa da k'yar ya kalli kofar ba tare da yayi magana ba, sai da aka sake kwankwasawa sannan
yace
" Bismillah. " Turo kofar akayi, Zeenat da Habib ne a gaba sai Mam, sai sauran jama'ar gidan da
sai yanzu suka samu damar shigowa wajen, tashi yayi daga zaunen, ya mikawa Habib hannu
suka gaisa, fuskar sa ta dan daga alamun yayi kuka, ya mai jiki yayi masa sannan suka gaisa
da sauran matan, suka fita tare da Habib din waje,
"Ina Mahfuz?"
Yayi karfin halin tambayar sa dan yayi tunanin tare zasu zo. Dan duban sa Habib din yayi kamar
me tunani, sai kuma yace
"Ai tare aka fito dasu daga wajen da Iman din take."
Kallon rashin fahimta Moha yayi masa yace
"Ban gane ba?"
Kwalla ce ta zubowa Habib din yayi saurin sharewa yana daurewa yace
"Dazu da safe ya fito daga gida akan zaizo ya same ka, nace zan raka shi amma ya bari anjima
yace zai gane ma ai, shikenan ya tafi, bansan ya akayi ba, sai gashi shima an same shi a chan
in da Iman din take."
Kafin ma ya karasa tuni Moh ya firgice, yasan an ce akwai mutum uku bayan iman da Ummimi,
daya an harbe shi ma aamma sam be kawo tunanin komai ba, be ma kara tunawa ba saboda
damuwar da ta danne shi, yana so dai yaje ya tabbatar da Musaddik na cikin wadanda aka
samo din amma sai yake ganin kamar idan ya matsa daga wajen ta komai zai iya faruwa.
"Yana ina?"
"Yana chan emergency unit har yanzu bamu ji komai daga garesu ba, su Abba dai suna chan?"
"Innalillah wa inna ilaihi rajiun, muje."
Sauri sauri ya dinga yi kamar zai tashi sama, idan wani abu ya samu yaron fa? Ya zai da ransa
wai? Ba'a barin kowa ya shiga wajen nasa saboda yadda case din nasa ya zama very
complicated case, bayan sun yi nasarar cire bullets din amma sam jinin ya ki tsayawa, ana kara
wani, wani yana fita, su kansu abin ya basu tsoro ganin yadda yake zubar da jini, shiyasa suka
hana kowa shiga, su Abba da suka dawo wajen tun da suka samu labari jikin kowa ya gama
sarewa da al'amarin Mahfuz din.
  Moh na isa wajen dr na fitowa daga ciki, jikin sa babu kuzari ya nufo wajen da su Abban
suke, ya kalle su daya bayan daya kafin yace
" Sai dai muyi hakuri... "
Wani irin zubewa Moh yayi a wajen, kirjin sa na masa wani irin suya, ashe Ajali ne ya kawo shi
k'asar? Ashe dama shine sanadin mutuwar sa, me yasa yayi masa wannna tsawar, me yasa ya
ci masa mutunci bayan be san wani abu dangane dashi ba,
"Nooo Dr... No be mutu ba, Dan Allah karka ce min ya mutu dagaske, ban kyauta masa ba, be
kamata ya mutu ba, he's innocent be kamata yayi facing irin wannan mutuwar ba, me yayi?
Menene nasa a ciki?"
"Get hold of yourself Capt, kullu nafsin za'ikatul ma'ut, hakikaa kowacce rai sai ta dandani zafin
mutuwa, shi da ya tafi be yi sauri ba, mu kuma bamuyi jinkiri ba, addu'a kawai yake bukata."
Dr yace ya juya ya barsu a wajen, babu wanda ya iya motsi a wajen saboda tsabar kaduwa,
yaro me zumunci me shiga rai, me son yan uwan sa, ya Yaya zataji? Labarin mutuwa irin
wannan mara dadi, kullum korafin ta akan Nigeria shine rashin tsaro, ko waya sukayi ta kan ce
musu Nigeria ta zama abinda ta zama, rai ba abakin komai yake ba. Kullum maganar ta kenan,
tsoron ta kenan, ashe bata tsira ba, Ashe zaman ta a chan bashi ne zai sauya kaddara ba?
Innalillah wa inna ilaihi rajiun kowa yake maimaitawa babu hargitsi ko hargowa, saboda dauriya
irin ta maza, sai dai kana kallon su zaka san mutuwar ta dake su, musamman Habib da Moh,
kafin kace kwabo labarin ya zagaye ko ina, kowa sai da ya tausaya wa Mahfuz irin kaddarar da
ta fad'a masa.
  Zuwan Aji da Bubu ne ya dawo da Moh cikin hayyacin sa, babu hawaye ko digo a fuskar
sa amma ya daku, ya kadu da zaka iya rantsewa ya dade a kwance yana jinya me tsanani.
  Baya magana bayan amsa gaisuwa sai dai kawai ya amsa maka da ka, har zuwa lokaci
itama bata farka ba, yaje yaga Musaddik wanda yake da sauki sai ciwuka a jikin sa yawanci na
duka ne. Sai kuma yunwa da ta ramar dashi sosai, driver da Ummimi babu abinda ya same su
dama su ba sune targets din ba. Â Â Wajen azahar ya dawo dakin da take, har lokacin bata tashi ba, mummy ce kawai a dakin
tana zaune gaban gadon da Iman din take, idon ta yayi ja sosai, addu'a take tofa mata ya shigo
ta tashi a kunyace tana kokarin barin dakin
"Dan Allah mummy ki yi zaman ki, dama nazo na duba ko ta farka ne, zanje station din na
dawo."
Komawa tayi ta zauna shi kuma