Showing 51001 words to 54000 words out of 124388 words
Chapter 18 - HALIN GIRMA Book Complete by Hafsat Rano .pdf
ta cigaba da yi amma sam ya hanata damar hakan, sai ma sake manne ta da
yayi sosai da jikin sa suna shakar kamshin juna. Luf tayi ta daina motsawa kowa na sauraron
bugun zuciyar dan uwan sa. Wajen minti daya suna a haka kafin ya saketa yana jan ta suka
zauna a saman kujerar, ya rik'e hannayen ta yana kallon cikin idanunta
"I promise you ba abinda kike tunani bane, zan miki bayanin komai amma ba yanzu ba, yau
ranar farin ciki ce, let's not discuss duk wani abu da be shafi ranar ba kinji matata? "
Turo bakin ta sake yi, ya saka hannu ya shafa yana murmushi
" I love that. " Saurin rufe fuskar ta tayi kunya na kamata
" Itama kunyar duk ina so, komai ma ni so nake kinji? Amma dai ki ajiye mana zuwa sanda
zamu tare a gidan mu, ko nawa ne zan biya na siya. Bana so a samu matsala dan zai iya yin
abinda ban shirya ba. "
Da sauri ta gyara bakin ta, ta kuma gyara zama tana matsawa kadan, matsowa yayi ta sake
matsawa ya sake matsowa kafin ta samu damar sake matsawa ya saka hannu ya tokare ta, ya
matso da fuskar sa daf da tata, tayi saurin runtse idon ta tana jin kamar zata saki fitsari. Light
kiss taji yayi mata a saman idonta dake a rufe. Â Â A hankali ta bud'e idon ta, tayi saurin rufewa ganin yadda nasa ya sauya sosai.
" Amm.. amm muje kaga su Mamma da yan uwan mummy, sai Gaji da sauran yan uwan Abba
ko? "
" Hmm. " Yace yana jan ajiyar zuciya
" Tohm bari na kira Musaddik yazo. "
Tashi yayi tsaye, ita kuma ta dukar da kanta k'asa, murmushi ta samu kanta da yi, tayi saurin
katse shi ta sake saukar da kanta dan kar ya gani.
Dawowa su Musaddik sukayi, su Zahra da aka samu sabbin samari suka shiga ciki don sanar
da shigowar su Mubamamd din.
  Ta bangaren Gaji aka fara, akayi hotuna sosai da kowa da kowa, sannan aka dawo in da
su Mamma suke nan ma akayi musu, sai sauran mstan gidan da jikoki da sauran yan uwa da
abokan arziki har ma da makwafta da suka shigo ganin kwaf.
 Â
***Yadda Zeenat ta koma zaka rantse tayi shekara tana jinya, gyaran gashin ma da aka yi duk
ya hargitse kamar ba'a yi ba, ta tada aljanu yafi kala biyar duk da muryoyi kala kala akan suns
gargadin in dai aka sake aka kai ta gidan sai sun kashe ta.
  Ko da Mama ta kira Abba ta fad'a masa cewa yayi karya ne, ya kashe kiran dan yana cikin
mutane ne, amma kuma sai ya dinga jin babu dadi yana kuma tausayawa Zeenat din sosai,
amma ya zai yi? Su suka jawa kansu duk da ba irin muna musu da be yi ba.
  Kayan kitchen su Aunty Maimuna suka dauka, suka kira Bashir din dan ba ma a samu
damar zuwa an yi jeren kitchen din ba. Cewa yayi zai aiko a tafi dasu, ba'a dade ba kuwa sai ga
wani saurayi yazo a golf irin ta hayar nan, dole suka saka Habib bin bayan su da wasu kayan
bayan ya dauko yar kurkura dan yawan kayan kadai sun isa a yiwa wasu amaren biyu amfani
dasu bayan Zeenatun.
  Sanda suka shigo unguwar gaban kowa ya hau faduwa, basu gama shiga masifa ba sai da
suka ga kofar gidan da aka tsaida, katuwar kwatar dake kwance a kofar gidan ce ta fara tsorata
su. Haka suka daure suka fito ya bud'e musu gidan suka shiga.
  Babban tashin hankali sanda suka shiga gidan suka tarar da kayan da suke gidan da
Bashir din yace ya saka mata kaya kar ayi komai, su kansu kujerun bayan yadda aka daina
yayin su, ba set bane dan babu three seater ko kankantar falon ya hanata shiga ko kuma ba'a yi
da ita ba oho. Â Â Sanda suka shiga kitchen din sai da suka kusa kurma ihu, kwatan kwatan abinda Maman
ta siya ba zai shiga kitchen din ba. Babu wanda yake wa wani magana a cikin su, suka saka
abinda zai iya shiga kitchen din da ko kitchen cabinets babu, sauran na amfanin suka saka
mata a cikin sip dan wannan ba za'a kirashi da wardrobe ba sai da sip😢😂 ragowar kayan
suka juya dasu cike da tunanin yadda za'a kare da Mama. Babu maganar uban kayan turaren
wutar da ta siya wajen hadaddiyar me turaren wutar nan*yerwa incense and more.*
   Shigowar su kenan suka tarar ana ta hotuna da Iman, jiki a sanyaye suka wuce
bangaren Maman suna taraddadin yadda za'a kwashe. Mama ma jin ance sun dawo ta yi
zumbur ta tashi, sai dai tun kan su gama zama ta san da matsala.
  Aunty Maimuna ce ta jata daki tayi mata bayanin komai sai ragowar kayan da tace an loda
su a motar Aunty Muhibba dan kar a shigo dasu saboda yan saka ido.
  A k'asa dirshan ta zauna, ta cire dan kwalin ta da take jin yayi mata nauyin gaske saboda
yadda kanta ke masifar sarawa
"Amma Bashir ya cuce mu, ya cuci rayuwata, yanxu dan Allah wannan abun kunya da me yayi
kama? Na shiga uku."
Ta jefar da hannun ta gefe,
"Be kyauta ba gaskiya, ha'inci ne wannan kuma, sam be kyauta ba."
Aunty Maimuna dake kokarin bata baki ta fad'a duk babu dadi
" Allah ya isa ban yafe ba wallahi,shege macuci. "
"Kiyi hakuri Yaya Hajara, cuta dai Bashir ya riga yayi mana ita sai dai muyi hakuri, mu lallaba a
kai ta idan yaso daga baya idan hankalin kowa ya dauke sai musan abinda ya kamata. "
Wani kallo tayi mata, kamar ma ta rufe ta da duka take ji
" Sai bayan an kai ta ya gark'ama mata ciki sannan ne kike tunanin zai rabu da ita? "
" A ah Yaya, kinga wai ai dai yanzu daga daure aure yau ai ba za'a ce ya saketa ba, kinga
hakan ai kema zai iya baki matsala da Dr. "
" Matsala ta nawa kuma? Ni yanzu ya riga ya fita daga kaina, ta yata kawai nake, dole na bata
farin ciki ko ta halin Kaka. "
Shiru kawai Aunty Maimuna tayi dan ba kuma tasan yadda zatayi ta bawa Maman hakuri ba.
Aunty Muhibba ce ta shigo, tace maman ta tashi ta gyara jikinta Iman da mijinta zasu shigo.
Kamar ta danna ma Aunty Muhibban ashar taji dan dai akwai kunya tsakanin su kasancewar ta
matar babban wansu, dole ta tashi ta wanko fuskar ta a bathroom ta shafa mai da yar hoda ta
saka kwalli sannan ta fito.
***A zaune take ta tankwashe kafar ta akan dan carpet din da yake jikin gadon dakin, ranta a
bace yake tun bayan da ta samu labarin auren da Yarima Muhammad zai, taso ta tada hankalin
ta amma Kilishi ta hanata, yanzu gashi tana ji tana gani an daura.
Â
"Laila!"
Ta kira sunanta tana daga zaune a gefen makeken gadon ta, da ido ta kalle ta ba tare da ta
amsa ba, ta mike tsaye. Sanye take da doguwar gown ja, sai gashin ta da yake a tattare a waje
daya da yasha gyara na musamman.
"Yaushe zaki koma?" Ta ta da tambayar bayan tasan amsar da zata bata. Da ido ta sake
dubanta, ranta na sake baci tace
"Na dawo kenan."
Da sauri ta mike daga gishingid'ar da tayi, ta dauka zata ce mata soon zata koma kamar yadda
take bata amsa a ko da yaushe idan tayi mata maganar komawar.
"Kinsan me kike cewa? Ba zaki koma ba? Me yasa?"
"Ba zan koma ba har sai na samu cikar burina. Ni ce na chanchanta da zama a wajen da aka
bawa yar talakawa, wadda bata da komai da kowa. Yarima nawa ne ni kadai babu kuma wanda
ya isa ya dakatar dani."
"Har ni?" Tace tana zaro ido cikin mamaki
"Duk wanda yayi kokarin shiga hanya ta, ko waye kuwa, ko da Bubu ne!"
Tsam kilishi tayi a in da take tsaye ta kasa cewa komai. Tana son Laila tamkar yadda take son
Kamal,sai da tafi son Kamal ya gaji ubansa akan yadda ita Lailan take so. Sai dai idan taga da
gaske Kamal ba zai samu sarautar ba, toh zatayi duk yadda zatayi ta samu Laila ta shiga
rayuwar Muhammad din. Â Â Juyawa Lailan tayi cikin takun ta na isa, ta bar dakin. Da kallo Kilishi ta bita ta girgiza kai
"Ba zan taba barin ki da tsarin ki ba har sai na ga da gaske plan dina ba zai yiwu ba, wanda
bani da shakku, Kamal shine zai gaji ubansa a ranar da suka shirya bawa dan gatan dan
nasu. Maimartaba da kansa zai yi fushi dashi, fushi irin wanda be taba yi ba!"
Dariya ta saki ta koma ta zauna tana harda kafarta, indai tana numfashi Muhammad ba zai taba
sarauta ba wannan alkawari ne da tayi wa kanta.
****
  A gajiya Bubu ya dawo, shiyasa be samu ganin kowa ba ya shige turakarsa. Tun da wuri
Ammi ta shirya tana jiran sa dama,aiko yana dawowa ta tafi dan tana so su karasa maganar da
ya fara yi mata ranar basu samu damar gamawa ba
  Har ta karaso ta zauna be bar kallon ta ba, babu wani babban chanji akan sanin da yayi
mata a dah da nayi yanzu, jikin ta me kyau ne zaka rantse bata ajiye garkamemen saurayi
kamar Muhammad din ba.
"Barka da zuwa gimbiya a fad'ar Ahmadu."
Yayi mata kirarin da ya saba mata tun zamanin kuruciyar su. Dariya tayi ta zauna tana dora tray
din da ta shigo dashi a saman table.
"Sannu da zuwa, kun sha gajiya. An rabu da taro lafiya da kowa?"
"Lafiya Alhamdulillah, Takawa yayi matukar kokari sai dai muci Allah ya saka masa da alkhairi."
"Ai dama yace shine uba, kuma shine kuma kaka, mu yan kallo ne kawai."
Murmushi Bubu yayi yace
"Gaskiya kam ga zahiri nan mun gani ai."
"Allah ya basu zaman lafiya, har na matsu su tawo nan wallahi."
Hannu ya kai saman hancin ta ya lakace mata fuska yace
"Ko kunya, dan farin."
"Kuma dan auta ba."
Sai suka saka dariya a tare.
"Allah dai ya basu zaman lafiya da zuria dayyiba, kwanan nan zaki ga yan duguiw duguiw suna
yawo a tsakiyar masarautar nan, lokacin na dawo gida nima na huta kamar Aji, kinga sai kawai
na dinga kallon su ina jin dadi."Â
" Allahu ya sa, Allah ya nuna mana. "
" Amin. " Yace yana hasaso lokacin idan da rai da lafiya
" Ka gama yanke shawarar nad'in ranar juma'a din? "
" Haka muka tsara da Aji kuma na sanar da Takawa shima yayi na'am da hakan. "
" Kana ganin babu matsala? "
Rik'e ta yayi a jikin sa, yasan me take tsoro take gudu kuma
" Babu komai in sha Allah, babu abinda zai faru. "
" Aikin sa fa? "
" Ajiye shi zai kinga ba zai yiwu a hada ba ai. "
" Amma... "
" Ki tayashi da addu'a har ma dani din ma, idan ban ajiye mulkin nan ba hankali na ba zai taba
kwanciya ba. "
" Allah ya nuna mana, Allah yasa ayi lafiya a gama lafiya. "
" Yawwa ko kefa, addu'ar kenan. "
#Rano💕
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)Â s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
1/25/22, 10:41 - Buhainat: Halin Girma
   19
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇�_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇�_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇�_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_con
tent=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator
=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLo
SKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇�_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
**************
Ta cikin ido Moh ya kalli Mama da ya lura kamar tsaiwar na neman gagarar ta tunda aka fara
daukar hotunan, gashi sai dauka ake an ki dainawa itama a cikin yanayi take da saura kad'an ta
zube a wajen idan aka cigaba da daukar hotunan. Sai da ya tabbatar da tayi masifar kaiwa
karshe har tana neman fito da abinda yake zuciyar ta ne sannan yace ya isa haka, tayi saurin
fadawa daki babu ko magana, hannun Iman din ya kama a gaban kowa, suka juya suka bar part
din yana jin a kalla Mama zata yi hankali, a kalla zata san rayuwa da yadda take juya wa bawa.
  Tafiya sukayi bayan sun yi sallama akan zuwa magriba za'a zo a dauki Iman din. Sake
chanja kaya tayi zuwa wasu kayan na daban, suka zauna cikin yan mata da sauran yayan da
aka ma aure a family aka dinga hira cikin farin ciki. Bata saka musu baki sai dai tayi murmushi
musamamn da ya zama kusan rabin maganar akan zaman aure ne wanda take jin kamar wasu
maganganun sun girmi kanta.
  Gabatowar la'asar ya sake saka Iman din a cikin yanayi fargaba, irin wanda ake ji idan za'a
rabu da gida. Tashi tayi ta ja Khadija suka fita zuwa shashen su, tana son ganin Zeenat sannan
tana son daukar wasu abubuwan a dakin su.
  Shigowar su ya saka kowa na falon bin su da kallo, kai tsaye dakin Mama ta wuce Khadija
na binta a babu yadda zatayi. Kusan zabura mama tayi ganin ta, ta tamke fuska tamau tana jin
haushin shigo mata da tayi a halin da take ciki. Har kasa ta duk'a, ta gaida Maman sannan ta
gaida su Aunty Maimuna. Duk sun amsa banda Maman da tayi kamar bata ji ba, tashi tayi
bayan nan ba tare da wata magana ba ta wuce zuwa dakin su. Tayi mugun mamakin ganin
Zeenat din, sai taji tausayin ta ya kama ta, ta durkusa a gabanta tana tuna lokacin da ta taimaka
mata da bata jin dadi.
"Zeenat?"
Ta kira sunan ta, sai a lokacin ta san sun shigo dakin ma. Da ido tabi Iman din kamar taga
sabuwar halitta,
"Iman?"
"Na'am, baki da lafiya ne? Kin ganki kuwa Zeenat?"
"Bani da lafiya Iman, bana jin dadin komai, wallahi bana son auren nan gashi an riga an daura,
tsoro ma nake ji kar naje na aikata wani abu mara kyau."
" Me ya faru? Me yasa bakya so?"
" Bashir karya yayi min, babu gaskiya a maganar sa, bashi da komai fakiri ne wallahi."
Shiru Iman din tayi dan bata san me zata ce ba, tunanin yadda akayi hakan ta faru take, sai dai
bata san yadda zata dauki maganar ta kuma ajiye ta ba. Kuka Zeenat din ta sake fashewa dah,
kuka dacin da take jin sa a chunkushe a makoshin ta. Baki Iman din ta dinga bata, ta samu da
k'yar tana maida numfashi. Tashi Iman din tayi ta duba wajen da ta ajiye jakar islamiyyar ta, ta
dauka sannan ta sauki abubuwan da tasan zata bukata ba kaya ba. Khadija ta bawa ta tafi kai
mata wajen Mamma sannan ta dawo ta cigaba da kwantar wa da Zeenat din hankali.
  Kamar ba Zeenat ba da take taka Iman din tayi mata duk wulakancin da ta ga dama, tayi
laushi sosai,har tana dora kanta a kafar Iman din.
  Wayar hannun ta ce tayi k'ara, Moh ne yake kira, dagawa tayi tana tashi daga gaban
Zeenat din
"Amaryata."
"Umm." Ta turo baki, dariya yayi sosai kafin yace
"Ki cigaba da turo bakin nan, babu ruwana aka samu matsala wallahi"
Murmushi ta samu kanta da yi, ta jujjuya kanta tace
"Kaiko?"
"Me nayi?"
"Ba komai."
"Sharri kawai zaki min dan kin ganni bawan Allah."
"Nima ai baiwar Allah ce."
" Na yarda kuwa, are you ready?"
" Mefa?"
" Shigowa fadar Moh."
" Ummm."
" Get ready kinji? Yanzu zasu zo, kwana biyu zuwa uku zamuyi anan sai mu wuce adamawa."
" Adamawa?" Tace tana zaro ido
" Calm down, zan miki bayanin komai."
" Shikenan." Tace a sanyaye
" That's my wife, Allah yayi miki albarka."
" Amin." Ta amsa tana sakin murmushi a hankali.
Kashe kiran yayi, Zeenat ta bita da kallon sha'awa, tana hango tsantsar dacewar da Iman din
tayi, gashi ita ta tashi a tutar babu.
"Zeenat bari na tafi, zamuyi waya in sha Allah, kiyi hakuri dan Allah ki kwantar da hankalin ki."
Jumbur ta mike, ta rik'e jikin rigar ta tana goge kwallar da ta zubo mata
" Dan Allah Iman karki tafi ki barni, wallahi ba zan iya zama da Bashir ba."
" Me yasa? Bakya son sa ne wai dama?"
" Wallahi bana son shi, ko kad'an wallahi laifin Mama ne."
" Iman!" Taji muryar Mamma a kofar dakin tana kiran ta, juyawa tayi ta fita tana kallon Zeenat
din cikin tausayawa
" Ke kuma daga zuwa daukar abu sai ki zauna? Kinga ai lokaci yayi ko?".
Bata ce komai ba sai kawai tabi Mamman suka bar bangaren, ranta babu dadi ko kad'an.
  Wanka mamma ta sake sata tayi, kayan da zata chanja ta tarar a dakin, an turara mata su
da turarurruka masu dadin kamshi. Tana shiryawa tana tunanin