Showing 57001 words to 60000 words out of 124388 words
Chapter 20 - HALIN GIRMA Book Complete by Hafsat Rano .pdf
da ya shirya ba.
  Jikinta ne ya hau rawa tayi kokarin hanashi amma sai ya sake matso da fuskar ta sosai,
ya tallafo ta ta baya ya sakata a jikin sa ssosai ya cigaba da aikin sa. Ta saman bayanta taji
yana neman abu, har ya kai wajen da zip din ta yake, ya shiga jan shi zuwa k'asa, da sauri ta
rik'e hannayen nasa tana girgiza masa kai hawaye har ya fara sauka a idon ta.
"Pleaseeeeee." Ya furta cikin muryar da taji kamar ba tasa ba, ta shige ciki sosai.
"Dan Allah kayi hakuri." Tace tana sake rik'e hannun nasa, dan taga kamar ma baya gane me
take cewa.
  Wayar sa dake cikin aljihun wandon sa ce tayi kara, ya janye ta yana murmushi ya ciro
wayar yana daidaita kansa.
"Zan kira ka Bashir."
Kawai yace yana kashe kiran. Lokacin ta koma ta zauna tana kokarin daidaita kanta dan ba
karamin yanayi ta shiga ba.
  A gabanta yayi kamar kneel down, ya tallafo fuskar sa yana mata kallon tsantsar kauna,
turo baki tayi ta harare shi ya tuntsure da dariya
"Pretender kawai."
Ya saka hannu ya lakaci gefen hancin ta, murnushin ita ma tayi ta juyar da kanta daga kallon sa
abinda ya faru yana cigaba da haskawa a idon ta.
"Kaje anan kiran ka."
Tace ganin yaki tashi ya kuma hanata sakat da kallon sa da idon sa da suke sake bata tsoro a
game dashi.
"Kora ta kike? Wallahi sai naki tafiya na kwana anan din dama ai daki na ne."
" Ya hakuri ni dai dan Allah."
" Matsoraciya, kin fiye tsoro wallahi."
" Tsoro ai halak ne." Tace tana dariya
"Inyee kinyi baki haka? Yarinya zaki maimaita maganar nan ne, for now zan barki amma
gaskiya zan dawo, kice ma su Amaani su kwana dayan dakin ke kadai zaki kwana anan, kinga
dama akwai secret door dita kawai sai na shigo mu sha soyayyar mu."
" Tab!"
" I'm serious
 Â
 Â
#Rano💕
#Rano💕
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)Â s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
1/31/22, 19:12 - Buhainat: Halin Girma
   21
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇�_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇�_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇�_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_con
tent=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator
=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLo
SKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇�_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
**************
Ta kofar ya koma ya fice bayan ya tabbatar da ya isar mata da sakon da yake son isarwa, yana
kallon yadda tayi laushi sosai ta bishi da kallo har ya fice gaba daya.
  Kai tsaye wayar sa ya dauka ya kira Bashir, ya daga yana tafiya zuwa shashen Takawa
dan yana son ganin shi
"Ya akayi Bashir?"
"Barka da warhaka Ranka ya dade"
" Barka dai, ya taro?"
" Mun gode Allah, an kawo amarya yallabai."
" Yayi kyau, Allah ya baku zaman lafiya, ka kula da ita sosai kar naji wani abu mara dadi, karka
kuma taba yarda mahaifiyar ta ko wani yace zai taka ka akan matar ka."
" In Sha Allah ranka ya dade, hakan ba zata faru ba."
"Yayi kyau, sakon ka na wajen Musaddik."
Godiya ya hau yi dan dama abinda ya saka kiran kenan. Cilla wayar yayi a aljihu sanda ya isa
sashen Takawan da ya zata ya jima da isa a adamawa.
***A tsorace take tun bayan da mutane suka yaye, yan matan biyu da aka barta dasu suma
basu wani jima ba suka cikawa wandon su iska dan ba zasu iya zaman ba, babu kalar ma da
bata yi musu ba akan su zauna amma suka ki, a cewar su idan suka zauna basu san uban da
zai maida su gida ba su ba samari masu mota ba ga unguwar da shegen nisa kafin kaje titi.
Haka tana ji tana gani suka yi tafiyar su suka barta. Tasha kuka kuwa kamar ba zata mutu, ta
dinga tsinewa Bashir albarka taji kamar ta gudu ta bar garin ma baki daya.
  Tana nan a zaune cikin duhu taji ana saka mukulli a kofar gidan, tashi tayi da sauri tana
zaro ido,a duhu take dan dama da wayar ta, ta haska kuma babu charge ta mutu tun dazu.
  Shigowa yayi yana haske gidan da wayar sa, ya shigo ciki ya dalle ta, tayi saurin kare
fuskar ta tana cewa
"Waye!" A tsorace
"Amarsu ta ango."
Wani abu ne ya tokare mata a makoshi jin muryar sa, tayi kansa da sauri ta hau kai masa duka
tana kuka
"Allah ya isa ban yafe maka ba, Allah ya isa."
Rik'e hannun nata yayi da karfi ya juyar da ita ta dawo tana jingina da bayan sa
"Ni kike wa Allah ya isa? Lallai ma yarinyar nan."
"Allah ya isa na fad'a mugu, macuci maha'inci."
Juyo da ita yayi ransa na soyuwa amma ya danne kamar be ji komai ba, ya dalle mata baki da
bayan hannun sa, yayi murmushi yana sake haske ta
"Duk abinda ma zaki ce ki fad'a amaryata."
Kuka ta shiga rusa wa da karfi, ganin zata iya jawowa a jiyo su a makota ya sakashi jawota ya
shiga sumbatar ta, ta dinga dukansa tana harbin sa a kafa amma ko a jikin sa, sai da ya gajiyar
da ita sosai sannan ya saketa yana murmushin, a kalla ya rage zafi dan yasan ba lallai Hajjaju
ta yarda ta barshi ba. Â Â A wajen ta duk'a tana kuka, ta dinga jin kamar ta mutu ta huta da abinda take ji, tana jinshi
yana waya har ya gama kafin ya dagata tsaye ya rik'e hannun ta a cikin nasa su shiga barin
gidan.
  Mota ce a kofar gidan irin wadda yake zuwa wajen ta zance, bud'e mata gaba yayi ta shiga
ya rufe sannan ya zagaya ya shiga mazaunin driver ya tada motar suka bar unguwar.
  Tafiya sukayi da dan nisa har suka iso unguwa, gangarawa taga yayi zuwa wata doguwar
hanya suka dinga tafiya kafin su isa kofar wani babban gida, horn taga yayi da sauri me gadin
ya bud'e gidan ya shiga da motar ciki. Tunanin ta ne ya tafi wani waje daban, ko dai Bashir
gwada ta yake yana so yaga yadda zatayi idan ya kaita wanchan gidan shiyasa ya kai ta? Ko
kuma dai duk shiri ne. Murmushi ya sakar mata ta cikin hasken da ya hasko cikin motar bayan
ya tsaya a gaban ginin gidan.
  Sauri taga yayi ya bud'e motar sanda wata babbar mata hamshakiya ta nufo su cikin wata
irin kwalliya, ta sha ado sosai tana walwali, katuwar gaske ce dan zatayi biyu ko ma ukun Bashir
din idaan aka hade shi da Zeenat din waje daya.
  Kafin ta kai ga garasowa Bashir din ya isa wajenta. Yayi kamar zai zube a k'asa a
gabanta, ta riko shi tana masa murmushi, ware ido sosai Zeenat tayi tana tunani toh ko Maman
shi ce? Karasowa tayi daidai kofar da Zeenat din take ciki ta bud'e mata tana sakar mata
murmushi
"Amarya."
Ta kira ta tana sakin hannun Bashir din ta kama na Zeenat din tana jawo ta daga ciki.
"Sannu da zuwa kanwata, sannu sannu."
"Kanwata?"
Zeenat ta maimaita sunan tana bin Bashir da kallon neman karin bayani amma sai taga ya
fuske kamar be ganta ba. Takawa suka shiga yi har zuwa cikin gidan wani babban falo da yasha
kawa sosai. Wasu mata ne hamshakai suma kamar matar farkon suka tarbi Zeenat din suna
tafi, ita dai Zeenat gaba daya kanta ya kulle jira take su samu kebewa da Bashir ta tambaye shi
me yake faruwa. Zaunar da ita matar tayi ta ja hannun Bashir din sauran mstan suka hau shewa
da dariya, bin su Zeenat tayi da ido har suka haura sama, zuwa anjima kad'an sai gata ta sakko
ita kadai babu Bashir din cikin shigar kayan bacci ta karaso falon ta kalli sauran matan tace
"A rakata dakin ta ko?"
"An gama Lay, an gama."
Suka tashi gaba daya, daya ta kama Zeenat din suka nufi wata hanya da take a bayan kafar
benen dake falon, wani dogon corridor ne suka bishi har zuwa bayan dakunan gidan, sai wani
daki guda daya a wajen da kofar sa tana kallon kofar da suka fito, nan taga an bud'e, sannan
sun shiga gaba daya ciki. Â Â Katifa ce a k'asa karama kamar ta yan boarding sai wata karamar kujerar roba fara, suna
shiga kamar jira dama suke matar da ta shigo da ita ta wurgar da ita a saman kujerar har sai da
kanta ya bugu da bango, tayi kara saboda zafin da taji kafin wadda suke kira da Hajiya Lay
(Layuza) ta rankwafo akanta tana mata kallon tsana tace
"Ke dan yar iska ce ke, har kin isa mu hada miji daya? Kin isa nayi sharing dake? Karamar
yarinya da bata fi sa'ar yata karama ba, kece kishiyata ko? Toh ni ko a zamanin kuruciya ban
zauna da kishiya ba balle yanzu da nasan ciwon kaina nasan abinda nake so, dan haka nan
dakin da nake ajiye masu aiki nane kuma na sallame su dan yanzu basu da amfani, sai ki
cigaba daga in da suka tsaya, shara wanke wanke, wankin undies dina da girki, komai ma dai
da kika sani."
Gaba daya kwakwalwar Zeenat ta gaza gane me matar take cewa, ji tayi kamar wani yare take
mata na daban da bata sanshi ba, ta dinga jujjuya kanta tana son gasgata abinda taji akan
Bashir din, yana da mata dama? Mata babba kamar wanna da ta yi sa'ar uwarsa? Abba ne ya
fado mata, sanda ya kirata yake mata magiya kamar ba Mahaifin ta ba, ya kaskantar da kansa
yana rokon ta akan ta rufa masa asiri ta hakura da Bashir amma ta shafawa idon ta toka, ta
kekeshe kasa tace taji ta gani, yanzu ta yaya hakkin Abban ta zai barta? Tun a ranar farko ta
fara fuskantar wannan tashin hankalin.
  Firgigit tayi sanda taji saukar abu kamar ruwa asaman fuskar ta, ta saka hannu ta shafa da
sauri tana daga kanta
"Kinji abinda na fad'a miki ko?"
A hankali ta daga kanta alamar eh, ta daka mata tsawa tace
"Baki zaki bud'e kiyi min magana bana son rainin wayo."
"Naji." Tace tana barin kwallar da ta taru a idonta ta shiga sakkowa saman fuskarta. Dariya suka
kwashe da ita, suka juya suka fita suna cigaba da zantuttukan su mara sa dadi ji.
***Bangaren amarya Iman kuwa komai na tafiya daidai, ta dade batayi bacci ba tana tunanin
Moh da kalar soyayyar sa me tsayawa a zuciya, koman sa abin so da birgewa ne tun daga
maganar sa har yadda yake tafiyar da ita. Da k'yar ta samu bacci ya dauke ta bayan ta gama
tunanin nasa. Tun asubah da suka farka basu koma ba, kana jin yadda hayaniya take tashi a
masarautar kasan akwai gagarumin shirin da ake yi. Shiryawa suka hau yi ita ta fara wanka
sannan su Khadija suka yi. Suna fitowa falon suka tarar da abinci a jere na alfarma yana jiran
su, nan suka hau kai suka ci suka yi nak, sannan aka turo tafiya da Iman din shashen Fulani.
Alkyabba aka sake saka mata sannan suka fito kanta na k'asa tana jin yadda take shan
gaisuwa kamar ta tsaya ta amsa amma yan matan nan sunce mata ksr ta tsaya amsawa haka
sarautar take.
  Da murna Fulani ta tarbe ta yau din ma, ta saka aka kaita har uwar dakin ta in da mutane
suka dinga shigowa suna ganin ta wanda suke da kusanci da gidan. Ta jima sosai anan har
suka soma jin tashin kidan kwarya in da adaidai lokacin su Mamma suka iso sai dai babu
Mama, gaisuwa aka sake kafin a rakasu in da ake kidan kwaryar aka nuna musu wajen zaman
su, kafin daga bisani a rako Iman din wajen itama.
  Da yamma kuma aka dawo ciki aka sake shiryawa in da aka nufi hall din dan gabatar da
bikin da kuma kyaututtukan da aka shiryawa Iman din.
 Sakon Maimartaba ne ya samu Fulani akan yana son ganin Matar Muhammad din dan a yau
zasu wuce komai dare, mamaki ya kama Fulani dan a yadda suka shirya kwanaki uku zasuyi a
nan din kafin su tafi adamawar, bata sani ba Muhammad din ne da kansa yaje ya samu
Takawan ya roke shi akan a rage bidiar dan shi kam ya gaji sosai, take kuwa ya amince har ma
ya sanar da Bubu tun a daren jiyan.
  Maimakon a wuce da ita hall din sai aka fara kaita wajen Takawar. Kanta a k'asa sosai
kwarjinin sa ya cika wajen ta yadda kowa ya kasa sakewa, nasiha ya soma yi cikin maganar sa
da ta saka jikin kowa mutuwa, yayi musu fatan alkhairi sannan ya kare da sake jan hankulan
mutane akan yadda rayuwar ta zama, basu dade a wajen ba, suka fito kowa na yaba karamci
na Maimartaba da ya karbe su hannu bibiyu ba tare da nuna banbanci ko wani abu ba.
  A gaggauce akayi taron, saboda tafiyar da zasuyi, sosai iman ta samu kyaututtuka masu
tarin yawa a yan awowin da basu gaza biyar ba, kowa so yake ace shine yafi, kowa so yake ya
burge Fulani da Maimartaba, dan kowa ya san yadda muhammad din yake a zukatansu.
***Motoci ne guda uku suka dauke su zuwa airport din daga su Mamma sai wasu yan uwan
Abba su uku shikenan wanda zasu adamawar, shima saboda bikin da zasuyi ne suma badan
haka ba da babu me zuwa. a lokacin Moh sun dade da isa suna zaune dasu Musaddik ana hira
a wani kebantaccen wuri. Â Â Zuwan su da aka dan suka dauki hanya babu wani bata lokaci. Ita kadai ce a wajenta,
babu kowa a saman duk suna k'asa sai ita kadai kwal har ta dinga tunanin dalilin da ya saka
aka kawo ta nan din ba abarta wajen su Mamma ba. Kamshin turaren sa ne ya amsa mata
tunanin ta, ya karaso ya zauna kusa da ita yana kashe mata ido. Kayan jikin sa ta kalla wanda
suka kasance na sarauta, sai takalmin kafarsa da akayi da fatar zaki yayi kyau sosai shigar
gidan sarauta, babu hula akan sa ya rik'e ta hannun sa, sumar sa ta fulani ta sha gyara ya fito a
bafulatanin sa sosai.
  Shi din ma shigar ta yake kallo, yana kuma yaba yadda komai ta saka sai yaga ya karbe ta
yayi dai-dai da ita.
"Ba magana?" Yace bayan ya gama kallon nata
Mirgina kanta tayi gefe tayi masa murmushi tace
"Sannu da zuwa toh."
"Yawwa."
Yace yana jingina da kujerar jirgin sosai, be sake magana ba sai dai yanayin sa ya nuna mata
kamar akwai damuwa, tasan yadda yake mata dan haka yau din sai taga kamar bashi ba, bata
sani ba ko sarautar ce ta motsa. Satar kallon sa ta dinga yi sai taga ya kulle idon sa yayi kamar
me bacci. Duk sai taji ta takura ta kuma damu, taba shi tayi kad'an, ya motsa amma be bude
idon nasa ba, sai kamo hannun ta da yayi ya sakalo shi ta tsakanin nasa hannun ya harde su
waje daya, kusan rabin jikin ta ya sauka a nasa, bata sake attempting komai ba har zuwa sanda
suka iso jirgin ya sauka suka fito still hannun sa na sarke da nasa.
 Â
***Kafarta a mike take tana sauraron bayanin da take mata, ko motsi batayi ba, kamar bata jin
me take cewa har ta kai karshen bayanin tayi shiru tana kallon ta. Sai da ta dauki lokaci me
tsawo kafin ta gyara zama, ta bud'e hannun ta, ta mik'a mata shi, jikinta na rawa ta ciro kwalbar
da take nannade a gefen zanin ta, ta saka mata a cikin tafin hannun ta. Jujjuya shi tayi tayi a
hannun nata tamkar me son gano wani abu.
"Turare ne ranki ya dade, a jiki kawai ake shafa shi bayan haka babu wani abu."
"Kin tabbatar da abinda kika ce?"
"Allah ya taimake ki, yadda nayi miki bayanin haka yake, yace kar ayi wasa dashi, sannan kuma
kar ayi sakacin da za'a samu matsala."
"Rik'e." Ta mika mata, da sauri ta karba tana damke wa a hannun ta sosai.
" Kin tabbata babu wani abu da ya faru tsakanin su?"
" Na tabbatar, sai da ya nuna min komai kafin ya bani, yau zasu iso sai kiyi kokari kafin su tare a
sabon bangaren su dan naji rad'e rad'in bikin ba zai dau kwanakin da aka tsara ba, bisa
umarnin Sarki."
Murmushi tayi me kyau, ta dawo ta zauna bayan ta ciro wata karamar riga ta karata a jikin ta,sai
kuma ta ajiye tana mikar da hannun ta baya.
" Kinyi kokari, kina da kyauta me tsoka idan har na samu biyan bukata."
" An riga ma an samu gimbiya, ki kwantar da hankalin ki."
"Tukunna dai."
" Me yayi saura? Yan awoyi ya rage miki ki samu abinda kike so gimbiya ta."
Jikin tagar dakin ta karasa, ta daga labulayen tana kallon harabar gidan da yadda hadiman
gidan ke kaiwa da komowa a tsakanin bangaren Moh din da na Ammi, tasan duk shirin tarbar
bakin ake, hankalin kowa ya riga