Showing 87001 words to 90000 words out of 124388 words
Chapter 30 - HALIN GIRMA Book Complete by Hafsat Rano .pdf
zata huta ba har sai sun iso.
Dagawa tayi daidai lokacin da ya fito daga shi sai gajeren wando, faffadan kafadarsa ta kalla da
take a mummurde, ta sauke kanta tana jin wani yanayi da bata san na menene ba, a gabanta
ya tsaya yana rik'e k'ugu, yana, hannun sa daya rik'e da karamin towel, ganin ta dauke kai
kamar bata ganshi ba, ya saka shi yarfa mata ruwan da yake hannun sa a fuska, yi tayi kamar
zata tashi amma da daure ta cigaba da wayar, ta bawa Mamman hakuri yana ji ta gama ta ajiye
wayar tana tashi da sauri.
"Kinyi kyau Matar Muhammad."
"Nagode." Tace a kunyace bubbude hannayen sa yayi, ya ja baya yana tattare fuskar sa.
"Shirya ni..."
"Na'am?"
"Eh ki shirya ni, ki shafa min mai ki saka min kaya..."
"Kamar dan baby?"
"Toh da mene? Ai babyn naki ne ni."
Dariya ta saka tana sake gyara zaman ta
"I'm serious fa, kinga we are running late, kar suyi ta jiranmu."
Ganin da gaske yake, ya sakata tashi ta dauko man, ta shiga shafa masa yana lullumshe ido,
da gangan ya dinga sata komawa baya yana cewa be yi ba, nan fa. Da dai daga alamun so
yake ayi tayi sai ta tattara man ta mayar, ta dauko masa suits din da ta gani tare da abayar ta,
ta mika masa ya noke yana sake bararrajewa. Girgiza kai tayi, ta shiga saka masa, yana sake
narke mata kamar wani karamin yaro a gaban mahaifiyar sa, sai data gama tas ya rage saura
necktie sannan ya karba ya karasa sawa a gaban mirror, ya kalli kansa yana hango ta ta cikin
mirror din,da hannu yayi mata alamar tazo, ta tako ta tsaya daga kuibin sa, ya matso da ita
jikinsa yana kara kansa a jikin fuskar ta.
"Perfect!" Yace yana dariya, wayar sa dake kusa da wajen ya dauka, yayi musu hoto me kyau a
gaban mirror din, sannan ya daga kiran da George yake masa.
"We are on our way."
Kawai yace ya katse kiran, ya rik'e hannun sa cikin nata suka fito, duk da suka hauro reception
din suke shan kallo, tana jin shi yana jan tsaki k'asa-k'asa har suka shiga wajen da yake a cikin
hotel din ne dalilln da ya saka ma suka sauka anan din kenan saboda already an riga anyi
booking dakin tun kafin ranar ma. Duk in da suka wuce sojoji ne a tsaitsaye sun yi shirin ko ta
kwana, cikin girmamawa suke gaida su, har suka kai babbar kofar shiga wajen.
 Â
  Wata iriyar kunya ce ta dabaibaye ta lokacin da suka shiga wajen, mutane ne masu yawa
kai kace wani gagarumin biki ake, kowacce kofar shiga wajen dankare take da jami'an tsaro, ji
tayi ido yayi mata yawa, gashi duk sun tashi da shigowar su. Mafiya yawancin su ba hausawa
bane, sai yan daidaiku da tayi hangowa daga in da take. Wajen zaman su waitress dake tsaye a
wajen ta nuna musu, basu wuce chan ba kai tsaye sai da suka je wajen manyan kusoshin, suka
kwashi gaisuwa in da taga yayi wata irin gaisuwa tasu ta daban, sannan suka samu wajen
zama suka zauna sai a lokacin ya sakar mata hannu.
"Sannu Amarya!"
Wata bahaushiya a kusa da ita tayi mata magana, amsawa tayi tana maida mata murnushin da
tayi mata, sai kuma suka gaisa da sauran matan wasu hausawa wasu ba hausawa ba, kafin
kuma a fara gabatar da abinda ya hada su.
 Captain Is'mail ne a gaba gaba akan komai shi da George, su ne ma organizers din event din
shiyasa ko zama sun kasa yi, har sai da lokacin cin abinci yayi sannan suka zauna shima na
wucin gado,ana gama ci aka cigaba da gudanar da event din. Sun sha kyaututtuka sosai har sai
da Iman ta gaji da karba, idon ta yayi nauyi kwanciya take so kawai yayi, yana lura da ita, yasan
ba karamin aikin su bane su kai fiye da biyu a wajen babu kuma wanda zai damu, ita kuwa
akwai rashin sabo, tashi yayi yana zura hannunsa cikin aljihun wandon sa, ya nufi wajen da
Is'mail yake ya jashi gefe, yayi masa magana kana ya dawo wajen zaman sa ya zauna. Sai da
aka kara kamar mintuna ashirin sannan isma'il din ya bada sanarwar amarya bata jin dadi zata
je ta huta, da haka suka samu suka sulale daga wajen suka nufi masaukin su. Dukkan su a
gajiye suke dan haka babu abinda suka kara bayan sauya kayan jikin su sai bacci, cikin
kankanin lokaci bacci yayi awon gaba dasu.
  Da wuri ta tashi, ta shirya ta zauna tana duba lokaci, baccin sa yake tsakanin sa da Allah
tun bayan dawowar sa sallar asubah gashi ta matsu ta ganta a gidan, gashi babu alamun zai
tashi har past 10, an kawo musu breakfast daga reception din taci kad'an ta ajiye masa sauran
ta cigaba da zaman jiran sa. Wasa wasa lokaci ya dinga ja, babu abinda yake sai chanja
kwanciya da juyi daga nan ya koma nan cikin jin dadin baccin. Ganin da gaske ba zai tashi ba,
ya sakata zuwa daidai saitin kansa, ta dan rankwafa da niyyar tashin sa, hannu takai kan sajen
fuskar sa, ta taba kadan, juyi taga yayi ya sake maida kansa dayan barin, sake durkusowa tayi
ta bayan nasa ta kai hannun ta jikin sa, kam taji ya riko hannun ya makale shi tsakanin hannun
sa da jikin sa, ja tayi taji ya makale shi kam, gashi sauran kad'an ta fado kansa gaba daya,
dayan hannun ta saka ta taba shi,
"Please ka tashi zamu makara."
"Uhum..." Yace cikin muryar dake cike da nauyin bacci, ya sake kankame hannun nata a jikinsa
wanda ta jawo mata fadawa kansa ta gefe daidai saitin bayan sa.
  Sun jima a haka tana jin shi yana fitar da numfashin bacci, kafin yayi motsi ya bud'e idon
sa da suke cike da bacci sosai, ya juyo bangarenta yana sakin hannun nata.
"Ka tashi dan Allah."
"Um um..."
"Ka manta zamu fita?"
Da kai ya amsa mata da eh, kokarin tashi tayi zaune ya daddanne ta, ta hanyar dora kafarsa a
jikin ta
"Kinsan fa jiya bamuyi wani bacci ba, please muyi bacci idan muka tashi sai mu fita."
"Past eleven fa, please please please."
"Ohhhh! Ni dai gaskiya, gaskiya bacci nake so nayi, anjima sai muje idan mun tashi, bari kiga."
Ya sake kadannade ta da kafafun nashi da sukayi mata nauyi ta kasa janye su,gani tayi yana
maida idon sa zai rufe tayi saurin rik'e fuskar sa
"Dan Allah!"
"Shikenan." Yace yana sauke kafarsa, ta samu ta mike tana murmushi
"Amma da sharadi, ke zaki min wanka ki shirya ni, ki kuma bani abinci a baki."
"Ahhhh." Ta bud'e baki cike da mamaki
"Fine, bari na koma bacci na sanda na gama mun fita."
Da sauri ta rik'e blanket din da zai sake rufa
"Zanyi."
"Good girl."
 Yace yana mata murmushin mugunta. Janye blanket din tayi, ya zuro kafafun sa k'asa yana
mika mata hannu, kama hannun tayi ya tashi, yayi kamar zai fadi ya fado jikin ta, nauyi sosai
taji, amma ta daure dan taga take taken sa zai iya cewa ya fasa, a haka suka isa toilet din, ya
zauna a gefen bathtub din ta hada ruwan, ta dauko masa brush da toothpaste ta matsa masa ta
bashi, kin karba yayi ya bud'e mata bakin wai tayi masa, sake mika masa tayi ya noke yana
tashi alamun zai bar toilet din, da sauri ta riko shi, ya koma ya zauna ta fara yi masa, dariya ce
take kamashi amma ya kanne, yadda ta daddage kawai zai baka dariya, hannun sa ya dora a
saman nata ya karbi brush din, ya karasa, ya bata ta cilla shi a dustbin din toilet din daga nan
tayi hanyar fita
"Kina fita zan fito nima."
Tsayawa tayi ta dawo tana tura baki, ya hau cire kayan sa a gaban ta, tayi saurin juyar da kanta,
murmushi yayi ya shiga ruwan da yayi masa daidai da yadda yake so, sai data tabbatar ya
shiga ciki sannan ta juyo tana cigaba da dauke kanta ta dauko sponge da sabulu ta bud'e ta
ajiye a dan wajen da aka tanada, zama tayi a gefen bathtub din, taki kallon gefen sa ta juyar
da kanta gaba daya hanya, bata yi aune ba taji ya jawo ta cikin ruwan, ta saki kara, ya hade
bakin su waje daya ya hana karar tata tasiri.
  Sai da suka bata lokaci mai tsawo a ciki sannan suka fito, ta dinga turo baki tana jin kamar
tayi masa kuka, ta riga ta gama shiryawa tsaf har kayan da ta saka dama su tayi niyyar sawa
amma ya jawo sai ta sake sabon shiri, a wajen shiryawar ma haka tayi ta fama dashi da ya
janye mata towel ta nan sai ya janye mata ta nan haka dai yayi tayi har sai data gama cika fam,
zata fashe kafin ya kyaleta su shirya a nutse.
  Kasancewar ciki da falo ne dakin, sai tayi ficewar ta, ta barshi a ciki yana karasa shiryawa
ta hada masa breakfast din ta ajiye da yazo ci kawai zai yi su tafi. Da waya a makale a kunnen
sa ya fito, yayi zaman amsa wayar da ta fuskanci da Musaddik suke magana, sai da ya gama
wayar tsaf sannan ya jawo abinci ya soma ci a yangace kamar ba jiran sa take ba, bata dai ce
komai ba, ya gama duk bata lokacin da zai yi, sannan ya tashi yana goge bakin sa da tissue.
Tashi tayi itama dama tayi ready har da jakarta a kusa da ita, gaba yayi ta bishi a baya, ya
murda kofar sojan da yake jiran sa a wajen ya karbi Notepad da wayoyin sa, shi kuma ya zuba
hannuwan sa a aljihu suka shiga takawa zuwa wajen da aka tanadar domin parking motoci.
  Bud'e mata kofa yayi, ta shiga ya rufe sannan shima aka bud'e masa nasa bangaren ya
shiga suka fita daga harabar hotel din!
Bashin Jiya....so sorry banajin dadi ne
_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D'aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
2/12/22, 11:07 - Buhainat: Halin Girma
   32
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇�_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇�_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇�_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_con
tent=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator
=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLo
SKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇�_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
*******�
Address din drivern ya dinga bi har suka isa gidan, tun kafin motar ta gama daidatuwa a
harabar gidan take kokarin fita, chapko ta yayi yana bata fuska
"I'm jealous!"
Da mamaki dake kallon sa
"Yes I'm jealous, I want my share of love too, inaso naga same action na murna anytime mukayi
nisa da juna, inason soyayya, inaso a gatata ni, aji dani sannan a damu dani please."
Dariya ma ya bata, ya saki hannun ta yana sake bata fuska shi a lallai yayi fushi, girgiza kanta
tayi cikin muryar lallashi tace
"I'm so sorry toh, kawai I'm eager ne, ban wani zauna dasu sosai ba, shiyasa kawai."
"Shikenan reason din?"
"Shikenan, ko baka so naga Mama ta? Kullum fa kai kana tare da Ammi fa, nifa?"
"Ba haka bane, banda Mummy ai nake nufi, Mamma, Amaani, Amaan and rest, su nake kishi
dasu."
Dariya ta sake yi, ta rik'e kofar ta bud'e, ya zuba mata ido kamar bashi da niyyar fitowa, sai da
tayi masa alamar da hannu sannan ya bud'e ya fito ta dayan side din, yana karewa gidan kallon.
  Kofar shiga part din suka nufa, yana biye da ita a baya hannun sa sakaye a cikin aljihun
sa, daf da zasu kai kofar ta bud'e, Amaani ce a gaba da shegen gudu, tayi kanta tana ihun
wallahi itace, kamar zata kada ita, sai da k'yar ya nutsu tana numfarfashi, hango shi da tayi a
baya sai kawai tayi wajen sa , ta rik'e masa hannu ta fara zuba masa surutu kamar tayi shekara
da sanin sa. Cike da sha'awa yake duban ta, ta rik'e shi gagam har ciki tana bashi labarin da be
gane kan sa ba.
 Mamma ce ta fito daga wani corridor, tana sanye da lullubi akanta, fuskarta cike da farin cikin
ganin su,
"Sannun ku da zuwa."
Tace sanda ta karaso falon, idon ta akan Iman dake zaune da Amaan a kusa da ita. Russunawa
yayi cikin ladabi ya gaida Mamma din, a daidai lokacin Mummy ta fito itama, ya gaishe ta a
kunyace dan kallo daya yayi mata yaga tsantsar kama da Fatin sa, amsawa tayi ita din ma a
yanayin kunya irin tamu wadda aka gada tun iyaye da kakanni. Iman ce ta gaishe ta, ta amsa
daga tsaitsaye ta juya ciki, murmushi kawai Mamma tayi dan tasan yadda ta matsu da zuwan
nasu, amma ba zata taba nunawa ba, yadda tayi zaka dauka ma bata damu ba sam,nan kuwa
tsantsar kara ce irin tata da har take nema tayi yawa.
  Abinci aka shiga jere musu, yayi mata alama da ido akan tafiya zai, ya dauki bottle water
guda daya ya mike yayi musu sallama akan zai dawo, mamma ce ta hau korafin me zai sa ba
zai tsaya yaci abinci ba, hakuri ya bata akan zai dawo akwai wanda yake jiran sa ne. Shikenan
tace ya fice ta harari Iman
"Haka ake wa miji? Tashi mana kije kiji."
Tashi tayi tana dariya, ta bi bayan sa ta same shi har ya kai wajen mota, tsayawa yayi ganin ta
fito ya choge jikin motar sai data karaso sannan ya shiga, ya sauke glass din motar yana kallon
ta
"Kwana zanyi ko?"
"Inji waye? Da yamma zan dawo zuwa magriba."
"Dan Allah..." Girgza mata kai yayi tun kafin ta karasa.
"Zaki dawo next time, sai na dawo bye."
Ya daga glass din ta dan ja baya tana kallon motar har ta fice daga gidan, kamar zatayi kuka
haka taji, taja kafarta a hankali ta koma ciki ta samu Mamma ta zuba mata abincin mummy
kuma ta dawo falon ta zauna tana wa Amaani fad'a akan rawar kanta.
  Taji dadin zuwan ta gidan sosai, kamar tayi ta zama haka taji, amma tasan tun da yace zai
dawo toh zai dawo din, amma taso ya barta ko zuwa da safe ne sai yazo su tafi ko ya turo a
dauke ta.
 Ta idar da sallar magriba kenan a dakin Mummy, Amaani ta shigo tace ya dawo, har ga Allah
taji babu dadi, ta tashi ta nannade sallayar ta ajiye a gefe ta zauna a saman sofa tana ciro
wayarta. Tana zaune har wajen minti talatin babu wanda yazo kiranta, har ta kishingida sai ga
Mamma ta shigo, tace ta tashi su tafi yama fita,
"Na zata zai barni na kwana."
"Kul... Dududu yaushe akayi auren? Kar ma ki soma yi masa maganar kina ji na? Watarana da
kanki zaki zo ma"
" Wuce muje kar suyi ta jira." Tace tana sakata a gaba suka fito falon, uban kaya ne jibge a
gefen falon dangin su shinkafa kayan abinci dai masu yawa, Mummy na zaune tana juya kudi a
hannun ta
" Kinga wahalar da yayi ko? Kiyi masa godiya nace ba za'a karba ba amma ya dage dole." Tayi
maganar tana ajiye kudin a saman center table, bin kudin Iman tayi da ido wanda a kalla zasuyi
hundred thousand, sai kayan abincin da yake a dankare awajen, jinjina kanta tayi cike da
mamakin sa, ko alama be nuna mata ba balle ta gane shirin sa, dadi ne ya kamata ta fito bayan
sun yi sallama da Mummy tana zuba masa ido ta cikin hasken compound din gidan, duk da
motar tint ce, amma tana iya hango inuwar sa, cike da karsashi ta karasa wajen motar, dai-dai
lokacin da kofar ta bud'e, ta shiga da sallama tana dagawa su Iman hannu.
  Suna fita daga gidan ya matso kusa da ita cikin lallashi yace
"I'm sorry na hanaki kwana, kinga gobe da wuri zamu tafi amma next time da kaina zan kawo ki
har sai kin gaji."
"Laa ba komai fa, dama wasa nake yi, su Mamma ma ba zasu barni ba ai, wai dududu yaushe
akayi auren?"
"Haka suka ce ko?"
"Eh..."
"Yawwa kin gani."
"Babu komai fa, ni nama manta ma ma na tambaya, I'm sorry."
Ta kama kunnenta, zare hannun nata yayi yana jawo ta jikinsa.
" Thanks dear."
****
Washegari suka dauki hanyar Kano, tun kafin su isa an gama gyara musu gidan su, dama dai
ba wani baci yayi ba saboda akwai masu aiki da kula da gidan banda sojojin da suke waje suna
gadi, suna isa ya fice tare da Musaddik, anan ta tarar da uban kayan lefen ta, tayi zaman kallon
su cike da mamaki, idan kaya na yawa toh ita dai sun mata mugun yawa, ya zatayi dasu? Shine
kuma har da siyan mata wasu kayan saboda dai ba'a san wahalar kudin ba. Gajiya tayi da kalla
ta saka masu aikin suka kwashe su, suka maida su wani daki guda kafin ta kira Mamma taji
abinda ya kamata tayi dasu da mutanen da ya kamata a bawa.
  Slippers ta zura ta zazzagaya gidan nata, wanda yasha kaya na alfarma, har da wani
babban garden