Showing 75001 words to 78000 words out of 124388 words
Chapter 26 - HALIN GIRMA Book Complete by Hafsat Rano .pdf
zai iya hakura ba.
 Ji tayi an matso ta sosai, tsoron ta ya karu zuwa sanda taji yana jujjuyata, kuka ta saka masa
bil hakki da gaskiya dan tayi masifar tsorata da abinda ya faru,
"Dan Allah kayi hakuri."
Ta hau bashi hakuri ganin ya dauki hanyar da yar kwakwalwarta ta gaza dauka balle ta gane
karatun. Tsayawa yayi chak da abinda yake, ya soma lallashin ta cikin kalamai masu dadi da
kwantar daa hankali, a hankali ta dinga samun nutsuwa har ta dawo da nutsuwar ta, ta saduda
ta saddakar ta mika wuya, domin dama ance shi aure yakin mata ne, toh tabbas wannan yana
daya daga cikin manya manyan yakin matan. Ba zata iya cewa ga kalar wahalar da tasha ba,
duk da yayi matukar kokari wajen ganin bata sha wahala sosai ba, amma kuma dole ne, sai dai
a hankali a hankali komai zai daidaita haka rayuwar take haka kuma kowa yayi har ya saba. Ita
dai bata san sanda wani baccin wahala ya kwashe ta ba, a hakan ba tare da ta gyara ba, sai
chan cikin dare ta farka ta zame jikin ta, ta wuce toilet ta gyara kanta sosai sannan ta dawo
dakin ta kwanta tana shigewa jikin sa, sake rungume ta yayi tsam a jikinsa bacci ya sake awun
gaba da ita.
  Da yake tafiyar wuri zai saboda ogan sa da yake son gani, ya saka yana sallar asubah yayi
mata sallama ya tafi, kamar ta hanashi tafiyar haka taji amma bata nuna ba, dan ta lura da
muhimmancin tafiyar tasa shiyasa ma bata nuna damuwar ta ba, bayan gari yayi haske sosai
Ammi ta aiko aka tafi da ita chan shashen ta, daga nan kuma aka kaita ta gaida Bubu, ya saka
musu albarka sannan ya hada da nasiha akan rayuwar zaman aure wadda ba zaka taba iya
gane ta ba sai ka shiga cikin ta.
 Sai dare ta dawo bangaren ta, tayi wanka ta dauki waya da nufin kiranshi sai ga kiran nashi
ya shigo, sunyi exchanging text message amma basuyi magana ba tun da ya tafi, whatspp yace
ta hau ya kirata video call suka dade suna waya, kamar kar su rabu da k'yar suka hakura suka
kwanta. Kwana biyu da tafiyar sa, babu wani abu da suka samu daga ita har Muhammad din, duk da
yace yana kokarin sa daga chan din ma amma sam hankalin ta ya gaza kwanciya, gaba daya
bata cikin hayyacin ta kwata kwata dan ko sunyi waya korafin ta kenan.
Duk shirin da ya kamata Laila tayi taa gama, ta saddakar dole ne ya aure ta, dan bashi da
wata hujja duk wata hujja ma bata bar mishi ba, shiyasa take shirin ta hankali kwance kuma
shiri gagarumi dan biki zatayi na kece raini, ita kanta Kilishi sai ta zama yar kallo, amma kuma
ita kanta tana son auren ya yi wu, dan rashin samun mafitar Muhammad din shi zai taimaka
sosai wajen cikar burin ta, dan ta riga ta gama aikawa duk wasu manyan masarautar sakon
abinda muhammad din yayi, ta kuma san ba zasu taba bari a zaba musu muhammad din a
matsayin shugaba ba.
Ana gobe wa'adin da Bubu ya gindaya masa ya dawo, shi kansa ba a nutse yake ba amma
yayi kokari sosai wajen kwantar mata da hankali. Takanas yaje ya samu Aji sukayi magana be
baro wajen Ajin ba sai dare sosai, yayi tunanin ma zai tarar tayi bacci amma sai ya ganta a
zaune tana jiranshi. Tsokanar ta ya hau yi har sai da ya tabbatar ta manta, suka kwana cikin farin ciki sai dai
asubah nayi duk jikinta yayi sanyi, duk abinda take yana kallon ta, ya kuma kara tabbatr da da
gaske tana son shi tana kuma kishin shi sosai, sai dai bata son ta nuna kishin nata a fili, ta
barshi a zuwan kawai tana tayashi ne. Da wuri ya shirya ya fice ta biyo shi har kofa kafin ya fita,
ta rik'e shi sai hawaye, janta yayi zuwa falon ya rarrasheta ya samu da k'yar tayi shiru ya fice
yana waya da Musaddik.
Kasancewar ranar ne ranar da Bubu ya shirya ranar da zai sauka ya bawa muhammad mulkin
duk da shi Muhamamd din bashi da masaniya, sai ya zama na gaba daya masarautar ta cika
sosai da manyan mutane, tun a daren jiya wasu suka iso. Hakan ya jawo bubu ya shiga busy
sosai, sai da suka hadu da muhammad din a masallaci yace ya same shi karfe takwas na safe
a bangarensa. Shiyasa ya shirya ya fita da wuri, ya kuma same shi yana shiryawa,. Kai tsaye
Bubun ya tambaye shi idan yana da wata magana akan abinda ake tuhumar sa? Kai tsaye yace
bashi da wata hujja da zai kare kansa, amma yasan be aikata abinda ake zargin sa ba, shiru
Bubu yayi dan yadda maganar ta karade ko ina har kunyar fita yake a yau, sallamar sa yayi
kawai ba tare da yace komai ba.
Fitowar Bubu ya saka kowa nutsuwa, fadar tayi tsit bayan ya zauna, wanda suka sanshi suna
kallon shi zasu gane ransa a bace yake,limamin babban masallacin Masarautar ya saka aka
kira masa shi gaba, ya matso gaba, Bubun ya bada umarnin za'a daura auren Muhammad da
Laila. Nan da nan fad'ar ta dauki hayaniya, kowa na kokarin tofa albarkacin bakin sa!
*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)Â s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
2/3/22, 21:11 - Buhainat: Halin Girma
   28
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇�_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇�_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇�_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_con
tent=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator
=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLo
SKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇�_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
******* �
Jan kafa ta dinga yi har zuwa wajen da jakar ta ke ajiye, ta hau zazzage ta ko Allah zai sa taga
wayar ta, tun da tazo gidan bata sake ganin wayar ta ba, gashi tana matukar bukatar tayi
magana da Mama, ji taka kamar mutuwa zatayi saboda azabar wahalar da take ciki. Bata ga
wayar ba, sai yan kayan ta da Bashir din ya dauko mata daga wanchan gidan da yafi mata nan
sau dubu duk kuwa da rashin haduwar gidan amma chan a kalla zata samu yancin ta, ba kamar
nan da take xaune karkashin matar Bashir din ba.
 Kwanciya tayi a tsakiyar dakin, tana cigaba da rera kukan ta, har zuwa lokacin da taji ana
taba kofar, kafin ta bud'e ta zuro kanta
"Uban me kike wai har yanxu baki fito kin yi ayyukan ki ba?"
Ta tsinkayi muryar ta har cikin kwakwalwarta, matsawa tayi amma bata tashi ba, shigowa tayi a
fusace ta mik'ar da ita, ta k'wala ihu cikin azaba tace.
"Dan girman Allah kiyi hakuri bani da lafiya."
Da sauri ta saketa, ta ja baya tana kare mata kallo
"Kutmar U! Ni Bash zai munafunta? Kan bala'i amma wallahi sai na yi masa rashin mutunci, dan
wulakanci duk yadda nake kaff-kaffa amma sai da ya zagayo ya taba yarinyar na? Ni xai zawo
wa raini!"
Kamar wadda ake hankadawa ta fice da sauri, Zeenat na jinta tun daga kofar ta fara k'wala
masa kira, baya kasan da ta barshi haka kuma baya sama ya riga yasan abinda ya aikata
shiyasa ya bar gidan. Sake dawowa tayi dakin ta tashi Zeenat din tsaye da karfi
" Tunda har kin iya kwana da miji sai ki fito kiyi aiki, babu wani langabewa da zakiyi wallahi sai
kin min aiki."
"Dan Allah kiyi hakuri wallahi zazzabi nake ji, jikina duk ciwo yake."
"Hehehe..." Ta saki shewa tana mata kallon banza gami da tafa hannu
"Idan kinga na kyale ki sai dai idan mashasharar mutuwa naga kina yi, amma wallahi tunda kika
kwana da miji sai kinyi min aiki."
Kuka Zeenat din take da gaske ba da wasa ba, kuma da gaske take zazzabin take ga wani irin
ciwo da ta kasa gane wanne iri ne, a lokacin ne ta tuna wtaa rana ana ruwan sama, haka Mama
ta tursasawa Iman wanke mata wasu kaya masu yawan gaske,sannan tana wankin tana girki
duk kuma a bayan, har aka kare ruwan nan tana kaiwa da komowa ba tare da Maman ta
tausaya mata ta duba halin da zata shiga ba, a lokacin ita tana kwance a daki tana karatun wani
littafin hausa, sai bayan an gama ruwan ne ta fito ta sakawa cikinta abinci ta sake komawa.
  Tulin kayan wanke-wanken da yake gabanta ta kalla, ta sake fashewa da wani sabon
kukan, a hankali ta zauna a gefen dandamalin ta shiga wanke su tana yi tana kuka
shabe-shabe.
  Sai da ta gama komai ta gyara gidan tas sannan ta samu ta sakawa cikinta ruwan tea da
take jin shi kadai zata iya sawa a cikin, ta koma daki ta kudundune tana jin sanda Hajiyar ta bar
gidan cikin rakiyar kawayenta. Bayan kamar minti goma sha biyar da tafiyar ta, ta tashi ta dauki
jakar hannun ta, da mayafi ta fito ta nufi hanyar gate din gidan, fatan ta kawai ta bar gidan idan
har ta fita toh babu ita babu auren Bashir ko me za'a iya sai dai ayi amma ta gama auren. Har
taje gate din bata ga kowa ba, haka babu me gadi a wajen tayi saurin isa kofar ta kama ta bud'e
ta, sai taji ta a rufe, ta ja da dan ragowar karfin ta amma still ko motsi kofar batayi ba, tana haka
ne sai taji alamun ana saka key ta waje, kafin ta iya barin wajen har Bashir ya shigo sanye da
sabuwar shadda kunnen sa makale da waya yana magana yana dariya sai dayan hannun nasa
rik'e da wayar ta da leda me tambarin sahad stores.
"Zan kiraka oga, nagode sosai." Ya katse kiran yana dubanta
"Ba dai guduwa zakiyi ba?"
"Ban sani ba." Tace tana matsawa gaba tana cigaba da kokarin bud'e kofar dan da ya shigo rufe
tayi yayi
"Muje ciki kiji."
"Babu in da zani, na gama zama a bakin gidan nan, da muguntar matarka, wallahi gidan mu
zani ba zan iya ba."
"Naji toh, amma kizo muje kinga na siyo miki chocolates masu kyau da gasasshiyar kaza, da
yogurt."
"Da yake ka samu mayya ko? Toh ba zan koma ba wallahi."
Sai ta fashe da kuka da karfi, da sauri ya toshe mata baki, ya sungumeta tana ihu be ajiye ta ba
sai da ya kaita dakin, sannan ya dire ta, gani yayi idan ya biye mata zata tara masa mutane.
Yana ajiyeta ya zauna a gefe yana bud'e ledojin
" Nasan kinsha wahala jiyan nan, taso kisha fresh yogurt din nan zaki ji dadi."
Banza tayi masa ta cigaab da gursheken kukan ta. Ci ya hau yi yana kallon ta, yana jin da zata
yarda da ya sake zuwa karaye, amma yasan yadda ta sha wahalar nan zai yi wuya ta amince
masa, yaga kiran Hajiya wajen sau goma amma be daga ko daya ba, dan yasan kwanan
zancen yanzu ma sai da ya tabbatar ta bar gidan sannan ya shigo, da ace Zeenat din zata
amince masa da lafiya lou, shiyasa ma ya tsaya yayi mata siyayyar yasanta da shegen
kwadayi, amma sai yaga ko kallo be isheta ba daga shi har kayan hannun nasa. Sai da ya
kusan cinyewa sannan ya tuna ya rage mata, ya mike zai fita ta tsare shi
" Bani wayata."
"Hauka nake? Kije ki kira min ruwa kenan, ai kinga na baki wayar nan ko? Toh nasan me na
taka in da ko kinje sai kin dawo da kafarki."
Matsar da ita yayi ya fice yaje ya dora ruwa, yayi zafi ya juyo mata a wani babban bawo ya kai
mata toilet ya dawo ya sake sungumarta tana dukansa da komai ya kaita, ya danna ta ciki ta
dinga ihu tana tashi amma sai da ya daddanne ta har ta hakura ta zauna, sannan ya fito ya
barta a ciki, ya nufi gate ya samu me gadi ya dawo ya ja masa kashedi akan kar ya kuskura ya
barta ta fita sannan ya fice daga gidan da baya saka ran dawowar shi sai dare yayi sosai
saboda Hajjajun sa da yasan ta tama zata kare masa tanadi tsaf dan ba abinda ta tsana kamar
tarayya ita da wani akan abu guda!
***Tana zaune ya dawo daga sallar, ya chanja kayan jikin sa zuw doguwar jallabiya maroon
colour me kyau, bata kai masa har k'asa ba, tashi tayi suka hadu a hanya sannan suka karasa
tsakiyar falon, ta wuce zuwa dining area din ta dauko warmers din ta dawo ta jere su a k'asan
bayan ta ciro table mat ta shinfid'a akan carpet din
"Me yasa zaki bawa kanki wahala bayan duk wannan aikin kina da wadanda zasuyi."
"Ban iya zama haka nan babu aiki ba wallahi, ni nama sallame su tun dazu nace su je zan
neme su."
Jinjina kai yayi yana yaba mata, tashi yayi ya tayata suka karasa sakko da sauran kayan,
sannan yayi serving nasu a plate daya, da spoon daya, debowa yayi ya nufo bakin ta yace
"Oya, it's my duty bud'e bakin ki."
Dariya ta saka ta bud'e bakin a kunyace ya saka mata, sannan shima ya diba ya ci dadin girkin
ya ratsa shi, lumshe idon sa yayi ya bud'e yana ware su akanta
"Da gaske kice kika yi abincin nan?"
"Da gaske!"
"Wow... Alhamdulillah Ya Allah, I'm blessed ta ko ina, Allah nagode maka, abincin nan yayi dadi
sosai,Allah yayi miki albarka."
"Amin."
Ta amsa tana jin dadi sosai, babu abinda mace take so irin idan tayi abu a yaba, tana fatan ya
dore har gaba, hakan yana karawa mace karfin guiwa wajen kyautata ma mijinta. Cikin nishadi
suka gama cin abincin, ya sake tayata suka tattare kayan zuwa kan dining din, in da masu aikin
zasu kwashe daga nan zuwa kitchen. Falon suka dawo suka zauna, ya matso kusa da ita ya
ajiye kansa a saman kafarta, yace
"Ina jinki, bani labarin yadda akayi."
Dan muskutawa tayi ya gyara shima, tayi murmushi me sauti ya maida mata yana jan kunnensa
"Na matsu naji!"
"Abinda ya faru bayan ka fita, na dawo daki na zauna ina tunanin mafita, duk tunanin da zanyi
nayi babu wani abu da nake ganin zamu iya rik'e shi a matsayin hujja, duk da haka ban karaya
ba, inaji da yakinin Allah ba zai bata nasara ba, hakan ya saka ni tashi na dauro alwala, nazo
nayi nafila, na sake rokon Allah akan ya taimaka ya bayyana gaskiya, bayan na idar ne kawai
nayi deciding bari na shiga kitchen na ga abinda yake wakana, domin a rayuwa ta kitchen na
daya daga cikin wuraren da ya zama tamkar daki na, domin nayi masa sabon gaske. Na tarar
da ma'aikata da yawa suna ta hada-hadar hada girki, shine na karbi aikin namu, nace su ji da
nasu. Muna aikin ne sako ya iso, a cikin envelope din nan..."
Ta nuna masa tana mika masa
" Flash ne a ciki, wai inji wata mata sanye da nikaf tace a bani, a haka sakon yazo."
Jujjuya envelope din yake a hannun sa, tambarin gidan ne a jikin envelope din, wanda ba kowa
ne yake samun ta ba sai jinin gidan... Cigaba tayi
"Shine nazo na saka a jikin Tv, abinda na gani ya saka ni rawar jiki, nayi sauri na nufi daki na
dauko system dinka da kayi amfani jiya, naci sa'a na sameta a bud'e, na saka flash din a jiki
nayi copying komai a wayata sannan na tura maka, na kuma kiraka da nufin nace ka duba
amma kuma har ta gama ringing baka daga ba, a lokacin babu irin tashin hankalin da ban shiga
ba, na dinga kaiwa da komowa a tsakani ina fatan ka daga wayar ko kuma ka duba sakon kafin
lokaci ya kure. Ganin shiru shiru babu alamar zaka daga, sai na yanke shawarar zuwa da kaina,
har fadar dan ba zan iya jurewa ba, har na dauki abinda zan dauka na fito na kuma kira wadda
zata rakani, sai ga kiran ka."
Zaune ya tashi ya jere da ita akan kujerar, yana cigaba da jujjuya envelope din, yana son gano
wanda zai aiko da sakon, duk iya tunanin sa be samu amsa ba, sai ya ajiye a gefe ya
rungumota jikin sa yana murmushi
"Thank you so much Baby, nagode sosai da kokarin ki."
"U welcome."
"Ashe dai Ashe ana so na tunda har ake kishi na."
"Kishi kuma?"
"Ehen menene? Kishi ne mana, hadda kuka fa daxu da zan tafi, kamar wanda zai tafi filing
daga!"
Sai ya tuntsure da dariya yana gwada yadda ta riko shi, turo baki tayi tana tashi daga kusa
dashi
"Tayaka jimamin abun nake fa, aiko ba zan kara tayaka ba."
" Fadi gaskiya dai, kinga za'a kwace miki handsome mijinki, hankali ya tashi."
" Na shiga uku."
" Ba haka bane? Kinga hanci zur har baka, yarinya taga handsome guy tace idan bani ba sai
rijiyar kusugu."
" Allah kaiko?"
" Ai gaskiya ne, ki rantse ba kishi bane."
Shiru tayi ta kyale shi, ta lura yana da so wasa da tsokanar ta, is like kamar ma yafi jin dadin
sakata a gaba yayi ta tsokana, amma ka ganshi da sauran