Showing 99001 words to 102000 words out of 124388 words
Chapter 34 - HALIN GIRMA Book Complete by Hafsat Rano .pdf
tabbatar da su kadai sun isa su tarwatsa duk wani farin cikin sa. Matsala daya da ya
samu, bashi kadai ne yake son ganin bayan sa ba, nasa kawai yafi zafi ne, sai ya hada guiwa
dasu, yayi amfani dasu wajen samun abinda ya samu akan sa, ya kuma tabbatar da babu wata
alaka da zata sake hada su a nan gaba, ya datse duk wata hanya da zasu neme shi.
  Ta jima tana bacci sosai, Ummimi dake durkushe a gabanta tana kuka sosai taga ta motsa,
ta cigaba da motsawa tana yamutsa fuska kafin ta bud'e idon ta da kad'an kad'an da sukayi
mata matukar nauyi, saman dakin ta fara kalla, sai kuma ta shiga jujjuya idanunta tana son
gano a in da take, da sauri ta yunkura zata mike, Ummimi ta taimaka mata tana rik'e ta
"Karki tashi da sauri jiri zai iya daukar ki, ina tunanin sun zuba miki magani ne.". Ta fad'a cikin
muryar kuka
"Ina ne nan? Me muke anan Ummi?"
"Ni ma ban sani ba, wanda kukayi magana dashi, shi ya kawo mu nan, sun sato mu!"
"Musaddik?"
"Eh."
"Innalillah wa inna ilaihi rajiun." Ta furta a hankali, kanta da yake jujjuyawa ta saka hannu ta
dafe, amai ne taji yana taso mata, ta yunkura da nufin tashi amma kafin ta kai kofar har ta soma
aman, wanda babu komai a cikin sa sai zallar ruwa, tun tana yi har ta koma kakari kasancewar
babu abinda yake cikin ta tun safe, rik'e ta Ummimi tayi tana kuka, tana jera mata sannu, sai da
taga ya lafa sannan ta taimaka mata ta maida ita gefen tabarmar da ta tashi,
"Bari na samo miki ruwa, sannu."
Ta tashi ta fito, su biyu ne a zaune suna karta, suna ganin ta suka tashi
" Ruwa take so dan Allah. "
Da Ido sukayi wa juna signal, kafin daya daga ciki ya shiga wani daki, ya dawo da ruwa ya mik'a
mata, ta karba ta juya ciki, ta tarar da ita tana ta juyejuye akan tabarmar, ta rik'e cikin ta da yake
murda mata kamar zata amayar da kayan cikin ta. Dagota tayi, ta bata ruwan ta kuskure bakin
ta, sannan ta sha, ta koma ta kwanta tana sake rik'e cikin ta.
  ***Kwanan Zeenat biy babu Bashir babu alamar sa, Abba kuma ya zuba musu Ido be sake
cewa komai ba, ko Mama be sake mata maganar ba, shirun nasa yayi masifar bata tsoro, dan
bata san me yake shiryawa ba, ranar suna zaune Zeenat din na cin wainar fulawa, ba wani
dadin ta take ji ba amma itace kadai take mata dadin ci, sai nama da tuwo idan ta same su
kamar wata tsohuwar mayya, jigum jigum suke kowa da abinda yake damun sa. Kofar falon ce
ta bud'e duk suka kalli kofar a tare, Abba ne ya shigo, ya wuce dakin sa, k'asa k'asa Zeenat din
tayi masa sannu da zuwa be ma ji ba, ya shige jimawa kadan ya fito, ya dubi Mama da tayi
tsam tana kallon sa yace
"Tunda har ban isa na saka ko na hana Zeenatu abu a gidan nan ba, kin nuna min ban isa ba
tun fil'azal, na bar miki ita, idan har tana so mu shirya da ita lallai ta koma dakin ta, ke kuma,
hakuri na ya gaza, kije gida kya dawo duk sanda kika shirya gyara auren yarki, idan har
Zeenatu bata koma dakin mijinta ba, toh zaman mu ba zai cigaba ba. "
Daga haka ya saka kai ya fice, ba don darajar yaran dake tsakanin su ba, ba kuma don darajar
zaman da tayi dashi na dadi a baya ba, da zai sauwake mata ne kawai, amma hakan ba zai
yiwu ba, har yanzu yana sonta yana kuma son ta gyara halayenta.
  Tashin hankali ba'a saka maka rana, da girman ta da komai gotai gotai zai ce taje gida,
zagaye ta dinga yi a falon kaamar tayi hauka, duk tsawon shekarun da sukayi da Ibrahim be
taba nuna mata ko yatsa ba, sai gashi a yanzu da girma ya soma hawa kansu, tayi abinda gaba
daya mutuncin ta ya zube a idon sa, har yana cewa zaman su ba zai yiwu ba.
" Mama dan Allah kiyi hakuri, zan koma wallahi ba zanzo ku samu matsala da Abba akai na ba,
zan jure koma menene dama ni na jawo ma kaina. "
" Ba laifin ki bane, babu abinda zai faru , sake gwada kiran Bashir din idan be daga ba sai kawai
na saka Habib ya kaiki chan gidan su, daga nan sa neme shi ai dole yazo ya dauke ki."
Da sauri ta dauko wayar, ta kira amma sai taji alamar anyi blocking number, ajiyewa tayi jiki a
sanyaye tana fadawa Maman, kira mata Habib tayi, tace yazo maza gida yanzu duk abinda
yake yi, be dau wani lokaci ba sai gashi, ta fad'a masa abinda take so yayi,yace mata babu
mota Abba ya fita, sakashi tayi yaje ya kira musu napep yazo suka tafi, suka fita ta ja ajiyar
zuciya, ba zata iya jure tafiyar ko ina ba, ta riga tayi girman da zaman gidan su zai mata wahala
sosai, idan kuma ta tafi bata san ta yadda zata dinga ji daga wajen Zeenat din ba.
***Yana zaune bayan sun gama wani taro da sukayi, ba zaka iya tantance yanayin da yake ciki
na bakin ciki bane ko na farin ciki, kiran layin Musaddik yake amma still amsar daya ce, switch
off, sunyi dashi kafin su taso zai kirashi, gashi babu wani isashen lokaci da zasu sake batawa,
su biyu ne suka shigo, suka sara masa sannan suka koma gefe suka tsaya
"It's time sir."
Mikewa yayi be ce komai ba, ya shige cikin dakin, ya dauki jacket dinsa da dayar wayarshi,
sauran kayan nasa sun riga sun fitar dasu tun dazu,gaba yayi suka bishi a baya, yana cigaba
da kiran Musaddik din, ganin da gaske ba zai same shi ba, shiyasa ya sauya akalar kiran zuwa
kiran ta. Jiya basuyi magana ba gaba daya, yasan tana kaiwa yamma a school haka kuma
yasan ta dawo a gajiya, ko da ya kirata no answer sai kawai ya kyale ta, a zuwan suyi magana
a yau kafin ya taho. Ringing wayar tayi tayi ba'a daga ba, bayan ta katse ya sake kira amma still
no answer, sai ya kashe wayar tasa baki daya ya tura ta cikin aljihun wandon sa, sanda suka
karaso wajen motocin da zasu dauke su, tuni duk sun shiga shi kadai ake jira, dama kuma
shine Captain din tafiyar. Yana shigowa duk suka mike tsaya, irin doguwar babbar motar nan ce,
sai da ya zauna sannan duk suka zauna, driver ya jasu suka bar harabar wajen.
  Tun daren jiya labari ya kai fadar Maimartaba na rashin dawowar Iman din daga makaranta
wanda ma'aikatan gidan ne suka kai labarin, kamar wasa da kowa ya dauka, a tunanin su ko
wani wajen ta biya, amma ganin har dare ya soma yi ya saka hankali ya fara tashi, zama ma
neman gagarar Fulani tayi bayan an tabbatar da bata je gidan su ba, ba kuma wani da zata je
wajen sa, number driver da tata duk suna shiga amma kuma babu answer. Waya Maimartaba
yayi a dare ya sanar da yan sanda abinda yake faruwa, a take ya tashi jami'an tsaron ko ta
kwana, suka bazama neman, in da aka samu wayar Iman din da ta driver a cikin makarantar in
da aka ajiye a waje daya cikin wata farar leda.
  Tsawon daren babu wanda ya runtsa a tsakanin su, in da suka gama tabbatar da sace su
akayi, kuka sosai Fulani take tana hango kalar tashin hankalin da muhammad zai shiga idan ya
dawo. Zuwa safiya labari ya fara fita, bayan Maimartaba sunyi waya da gwamna, da wasu
manyan jami'an tsaro, cikin kankanin lokaci labari ya baza lungu da sako na k'asar har ma da
kasashen dake da makfwataka da k'asar.
 Ana zargin an sace matar dan sarkin Adamawa, jikan sarkin Kano babban jami'in sojoji
Captain Muhammad Ahmad Santuraki haka gidajen jaridu suka dinga wallafawa a shafukansu,
nan da nan mutane suka dauka kowa na kokarin tofa albarkacin bakin sa.
_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D'aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇
09134848107
2/17/22, 09:45 - Buhainat: Halin Girma
37
*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇�_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇�_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇�_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_con
tent=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator
=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLo
SKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇�_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
*******�
Cikin matukar tashin hankali Abba ya shigo gidan, bayan abinda ya gani a shafin BBC HAUSA,
ya saka shi matukat kaduwa, idan har suna nufin surukin sa kenan, toh kenan Iman aka sace?
Innalillah wa inna ilaihi rajiun,tashin hankalin da ba'a saka maka rana. Sauri sauri yake yana
kokarin isa bangaren Abba babba, kiran Mummy ya shigo wayar sa,
"Shikenan." Ya furta
"Sun samu labari kenan, ta tabbata da gaske ne."
Ya sake fad'a sai kuma ya daga wayar yana kokarin daidaita tashin hankalin da yake ciki.
"Hello Abban Iman, abinda nake gani a news gaskiya ne?"
"Labarin da nake samu yanzu kenan, yanzu muke shirin tafiya dan samun sahihancin labarin, ki
kwantar da hankalin ki, in sha Allah babu wani abu da zai faru."
"Innalillah wa inna ilaihi rajiun." Ta furta tana sakin kuka
"Zan tawo yanxu.."
"Sai kin zo." Ya katse kiran da sauri yana shiga ciki, a tsaye ya tarar da Abban yana kaiwa da
komowa, yana shiga Abba Musa da Abba Kabiru suka shigo, babu wata magana da suka tsaya
yi suka fice da sauri, suka dauki hanyar gidan sarki, dan anan ne kawai zasu samu gaskiyar
abinda suke so suji, da Abba Musa yace su kira Muhammad din amma kuma sai suka fasa
suka ga gwara su je din kawai ba lallai shima ya iya daukar waya ba. Â Haka sukayi, cikin tsananin tashin hankali suka isa gidan, bayan sun gabatar da kansu aka
shigar dasu har in da maimartaba yake, babu wasu mutane sai makusantan sa, suna jimamin
abinda ya same su haka bakatatan, sannan lokaci zuwa lokaci suna communicating da chan
police station din, duk da babu wani labari akai, dan duk wanda yayi aikin yayi masifar kwarewa
wajen gudanar da plan din nasa dan be bar duk wata hanya da za'a neme shi ba, amma duk da
haka ba zasu karaya ba, zasu yi iyakar kokarin su dan ganin an samu so cikin kankanin lokaci.
  Labarin da su Abba suka samu yayi masifar sake daga musu hankali dan har kwalla sai da
Abba yayi ba tare da kowa ya lura, yadda ake bada labarin rashin imanin masu kidnapping din
nan kawai yake tunawa, ga iman sam bata da hayaniya, zata cutu ainun a wajen su sai dai
fatan Allah ya bayyana ta cikin aminci da koshin lafiya. Â Suna zaune jugum kowa yana tunanin yadda Moh zai idan ya dawo, ya ci karo da wannan
mugun labarin duk uban tsaron da yake ganin ya zuba a gidan sa, lallai addu'a ce kawai mafita
a wannan zamanin, dan a duk in da mutum yake ba wai ya tsira daga sharrin su bane.
  Haka kawai yaji kamar bashi da lafiya, duk daukin da yake na zuwa gida ya ganta bayan
tsawon lokacin sai yaji kamar duk guzarin sa na barin sa. Tun a airport din yaga kamar
ma'aikatan na kallon sa, kallon da ya kasa gane na menene, sai kawai ya kyale hakan a wani
dalili nasu da suka sani. Daga nesa ya hango motocin sa, suna jiran isowar sa, dora jacket
dinsa yayi a saman kafadar sa ya shiga takawa zuwa wajen su dan basu ganshi ba. Sai da ya
kusa daf dasu sannan suka ankara, duk suka taho da sauri kowa na kokarin riga dan uwansa
isa, kayan hannun sa suka karba, aka bud'e masa motar ya shiga ya zauna.
"Muje mana." Yace ganin yaki tada motar
"I'm sorry sir." Yace sannan ya tada motar suka bi bayan su sauran. Sake neman layin
Musaddik yake a lokaci daya yana neman nata amma duk magana daya ce, switch off, kansa
ne ya daure sosai ta yadda za'a ce basu da charge a wayar su kuma tun jiya, be san me yasa
ba, sai kawai yaji kamar babu lafiya.
"Me ya faru?"
"Na'am?"
"Kaji ni ai, what's going on!"
"I'm very sorry sir, bamu san yadda akayi hakan ta faru ba, amma we are trying our best kuma
gaba daya k'asar ma."
"Ban gane ba, me kake nufi?"
"Kayi hakuri sir, in sha Allah za'a gansu."
" Nace maka me ya faru? Me kake nufi?" Ya fad'a a tsawace yana tasowa kamar zai dake shi
"Kayi hakuri sir, ana neman Madam da driver ta da House help din, tun jiya basu daw...**
" What!!!" Ya fad'a da karfi
"We are very sorry sir!"
" Wannan zancen banza ne, zancen wofi, menene amfanin ku? Nace menene amfanin ku?"
Ya harzuko sai kawai ya taka birki suka tsaya
" Ta yaya akayi tun jiya basu dawo ba, kuma babu wanda zai kirani ya fad'a min? Tun jiya fa!"
" Ohhh... Innalillah wa inna ilaihi rajiun, what's going on, me yake faruwa?"
A cikin tsananin tashin hankali yayi maganar, zuwa lokacin idanun sa sun yi masifar kadawa,
wani abu me karfi yazo ya tsaya masa a makoshi, ya dinga jin kamar ya kamasu yayi ta bugu
har sai sun fada masa yadda akayi suka yi wannan sakacin.
  Basu wuce gida kai tsaye ba, station suka wuce yana ta kiraye kirayen waya cikin karfin
hali, ashe tuni labarin ya kai wa shugaban su har ma da abokan tafiyar sa amma kowa yayi
masa kus, ransa yayi masifar baci, ga wani irin tashin hankali da yake ciki, yana tsoron wani
abu ya faru da ita, ba zai taba yafewa kansa ba, ba kuma zai yafewa duk wanda yake da hannu
a wannan al'amarin ba.
   Duk bayanan da ya kamata ya samu ya samu a station, abu daya ne basu da tabbaci
shine in da suke, dan duk babu waya a tare dasu,sannan an cire tracker din dake hade da
motar ta daina aiki tun daga cikin school din anan ne last location din motar.
  Jiri ne yaji yana kokarin kayar dashi k'asa, da sauri aka bashi kujera ya zauna yana dafe
kansa, wayar sa da take ta faman kara alamun kira ya zaro yana duba number din, Ammi ce tun
dazu take son su yi magana be samu dama ba, yace zai kirata amma kuma yasan ta kasa
hakuri ne, kowa ya shiga tashin hankali da dimuwa kasancewar kuma har an kwana amma
babu wani labari.
  Daga wayar yayi muryar sa a chan ciki, ya gaida Ammin ta amsa cike da tausayawa tilon
dan nata, tasan yana da karfin zuciya da kokarin maida komai ba komai ba a tsawon rayuwar
sa bata ga wani abu da ya gigitashi ya firgita shi ba, amma tasan dole ne wannan tashin
hankalin ba zai iya rik'e shi ba, ba zai iya shanye shi ba ace matar ka na hannun bata gari, ba
kuma kasan abinda zai je ya dawo ba. Lallashi da ban baki ta dinga yi masa, tana so ko yaya
ne ya kwantar da hankalin sa duk da tasan ba lallai ba, yaji ta ne kawai amma bashi da sukunin
nan, yana cikin wasiwasi da tunanin wanda zai aikata masa wannan danyen aikin, idan
kidnapping dinta akayi saboda ransom yasan tabbas zasu neme su a tsakanin kwana uku,
amma kuma idan ba dan hakan bane fa? Tsoro ne ya kara kamashi, ya mike da k'yar cikin
wasiwasin abinda zai je ya dawo, baya fatan wani abu daban ya bullo wanda be taba tunani ko
hasashe ba, a tunanin sa duk wani me matsala dashi ba zai wuce gidan su ba, Kamal da
mahaifiyar su, wambai da sauran masu goyon bayan Kamal din, bayan su, baya tunanin akwai
wani da wata matsala ta hada su da har zai iya yi masa haka.
  Tunanin sa ne ya katse, yana tuna abinda yake cikin flash din nan da ya bawa Musaddik,
yana bukatar sake dubawa ko zai samu wata amsa a cikin video din, amma kuma ya kalla yafi
sau nawa, sai dai kamar akwai wani abu da yake missing, be san menene ba, amma kuma zai
koma baya ya sake dubawa sosai. Tunanin sa ne ya tsaya akan Kamal, dalilin da ya kaishi bangaren sa har ya ajiye masa
wannan macijin robar, babu wani abu da ya dauka bayan wannan ajiyar da yayi,tashi yayi da
sauri
"Tracker ce!"
Ya furta ba tare da yasan a fili yayi maganar ba.
"Me kake tunani?" Shugaban yan sandan yace shima yana tashi tsaye
"Kwanakin baya an ajiye min abu me kama da micijin robar irin na wasan yara a adamawa,ina
kyautata zaton tracker ce a jiki, ya akayi nayi missing step din?"
"Wa kake tunani?"
" Bana tunanin kowa, amma koma waye ne, yana da alaka da wannan case din."
" Ina macijin robar."
" Yana gida!"
" Nan ko adamawa?"
" Yana nan..."
"Ok muna bukatar shi ko zai taimaka mana wajen binciken mu."
" Shikenan."
Hannu ya mik'a masa
" Sai naji daga gareku."
" In sha Allah zamuyi kokarin mu."