Showing 108001 words to 111000 words out of 124388 words

Chapter 37 - HALIN GIRMA Book Complete by Hafsat Rano .pdf

11 Mar 2025

7868

din da ta fito dasu ranar da zata tafin gasu nan a saman gado, be san me yasa
abubuwan suka juye masa a yadda be yi zato ko tsammani ba. Wayar sa ce tayi kara, ya dauka
yana kallon sunan, Bubu ne
"Menene alakar Kamal da batan matar ka?"

"Barka da rana Bubu..."

"Barka dai, ya mukaji da alhinin? Allah ya bayyana su cikin koshin lafiya."

"Amin ya Allah."

"Ina jin ka, menene alakar Kamal da batan matar ka?"

Saman goshin sa ya shafa kad'an, kafin yace

"Bincike ne ya kawo hakan Bubu."

"Shikenan, Allah ya sa muji alkhairi."

"Amin ya Allah." Yace sannan sukayi sallama.
   A tsammanin sa Musaddik zai neme shi da zarar gari ya waye, ya kuma rakashi duk wani
waje da zai je, amma kuma ga mamakin sa sai gashi har rana ta daga babu ko waya daga
gareshi, bayan yafi kowa sanin muhimmancin da Iman take dashi a wajen sa, shine mutum na
farko kuma na karshe da ya yarda dashi kaf duniyar nan idan ka cire mutane hudu mafiya
kusanci dashi, Ammin sa, Takawa, Aji da Bubun sa, bayan su be yarda da kowa ba sai
Musaddik wanda ya yarda da tsantsar kaunar da shi ma yake masa, fiye da wadda shi yake
masa, say da yawa Musaddik ya sha shiga rigima saboda shi, ya kuma sha shiga tashin hankali
saboda shi, amma kuma ya kasa gane dalili daya, da zai saka Musaddik din kasa jajanta masa
kamar yadda ya saba a baya, duk wani abu masa tare sukeyi.
   Tashi yayi yana dan zazzagaya dakin, yana so ya dauke tunanin daga zuciyar sa,yana so
yayi wa Musaddik din uzuri a karo na farko kasancewar dan Adam ajizi ne, watakila wani uzurin
ne ya danne wannan din. Wayar sa ce tayi kara, ya matsa yana dubawa, sakon text message
ne from an unknown number, da sauri ya dauki wayar yana dubawa.
_"Ka shirya?"_

Da sauri ya maida masa reply

"Waye kai, me kake so?"

Sai da aka dau lokaci sannan akayi reply da wata number daban

"Ashe har kana da lokacin tsayawa tambayar waye bayan rayuwar matar ka da ke cikin hatsari."

"Ina zamu hadu? Ka dawo da ita nayi maka alkawarin zan kawo maka kai na da kai na."

Nan ma sai da aka sake daukar lokaci kafin yayi masa reply da wata number daban kuma

_"Idan na shirya zan neme ka, karka bata lokaci wajen tracking din number, ba zaka taba samu
ba." _

Kiran number yayi da sauri, amma sai yaji ta a kashe, ya bi sauran layukan da sukayi magana
suma duk a kashe, text message ya turawa CP na numbers din dukka.
    Kira ne ya shigo wayar sa daga gate din gidan, kamar be zai daga ba sai kuma ya tuno da

zuwan su Habib, dagawa yayi suka tambaye shi ko yasan su, yace a farsu su shigo brothers din
Iman ne, da haka ya kashe ya sauya rigar sa zuwa mara nauyi saboda zafin da yake ji.

***Dagata Ummimi tayi ta taimaka mata bayan ta gama amai, ta gyara wajen ta dawo ta
tsugunna a gabanta tana mata sannu, da kai ta amsa mata, ta rufe idon ta hawaye ya gangaro
mata. Shigowa sukayi su hudu, shine a gaba suna bin bayan sa, ya zo gabanta ya durkusa ya
saka hannu ya dago kanta.
"Fine Lady." Ya shafi gefen fuskar ta, ta saka ragowar karfin da take dashi ta ture shi, ya
tuntsure da dariya yana kallon ta

"Ga Dr nan zai duba min ke, dan ina tunanin nine zan maye gurbin Capt bayan na aikashi
barzahu, kina da kyau."

"Dr matso, a duba min da kyau idan har ciki ne, a cire shi ko ta yaya ne, ba zan iya jure ganin
sa ba, kaga auren mu ba zai dau lokaci ba idan aka cire shi."

Matsawo likitan yayi, ya bud'e idon ta, sannan ya taba goshin ta, ya dauko wata roba a cikin
kayan sa ya mikawa Ummimi.

" Gashi fitsari zatayi."

Kin karba tayi, na bayan ya daka mata tsawa, ta karba da sauri tana daga Iman din, dukkan su
hawaye suke amma babu me bud'e baki yayi musu saboda tsoro. Tare sukaje tayi fitsarin suka
fito ta dawo ta kawo masa, ya karba a wajen ya duba, ya kuma tabbatar da ciki ne, yan
tambayoyi yayi mata akan period dinta ta amsa tana kuka.
"Ciki ne oga, na sati shida."

"Ya za'a yi dashi?"

"Ba zai wahalar fita ba, tunda karami ne. Yanzu dai zan dawo sai nazo da maganin da zata
sha."

"Yayi kyau, rakashi yaro." Rik'e masa jaka wanda aka kira da yaro yayi suka fita, sannan shi ma
suka fita.

"Hello... Samha baby." Ya fad'a da yaji ta daga wayar

"Eh tana hannu har yanzu."

"Eh ya tabbatar da ciki ne, amma za'a cire shi tunda baki da bukatar shi."

"A ah... Babu fa abinda zan yi wa masoyinki, kawai wata yar harkalla ce zamu karasa ta. "

" Yawwa toh" tace tana jin dadi.

" Sai mun sake magana ko? "

" Amma ai bana samun ka kwata-kwata a waya, me yasa?"

" Babu komai, idan akwai bukatar muyi magana ni zan kiraki da kai na."

" Shikenan."

Dariya yayi sosai bayan sun gama maganar, be san bata da tunani ba kwata-kwata sai yanzu,
amfani yayi da ita ya samu abinda yake so, ba kuma zai kyale wanda ta kwallafa rai akai ba, ba
zata taba samun cikar burin ta ba in dai yana numfashi.

***A waje ya tarar da su Habib din bayan ya gama parker motar, ganin tare suke da Gaji ya
sakashi saurin karasawa ya taimaka mata ta fito, sannan suka gaisa ya saka aka rakata ciki su
kuma yace su biyo shi garden dake baya. Kujeru ne a wajen, ya zauna sannan suka zauna
suma, yana karantar yanayin Mahfuz din, sai a lokacin yayi masa kallon tsaf, ya kuma fahimci
hakan yanayin sa ne, ku kuma yanayin environment din da ya taso kamar yadda Habib yayi
masa bayani dazu.

"Ta yaya zaka iya taimakawa?" Yace bayan ya gama nakaltar yanayin sa, gyara zama yayi
sosai, yayi murmushi sannan yace zai masa yan tambayoyi,da ka ya amsa masa ya bashi go
ahead.

"Babu wani message ko kira da ka samu daga wajen kidnappers din?"

"Akwai."

"Zan iya gani?"

"Why not?" Ya mik'a masa wayar, ya karba ya duba messages din dukka, ya jima yana sake
dubawa kafin ya mik'a masa wayar sa

"Kayi tunani sosai, wanene kake da matsala dashi, irin wadda kasan lallai da zai samu dama
akan ka zai iya aikata maka komai?"

"Babu shi, bansan waye ba gaskiya."

" Babu ko old friend? Ko abokin aiki?"

Shiru yayi cikin tunani

" Think... "

_" Zan dawo komai daren dadewa, sai na dauki fansa akan ka, ko da zan karar da komai da na
mallaka ma duniya sai na maida rayuwar ka abun kwatance! "_

"JABIR! " Yace yana mikewa tsaye da sauri, tashi Mahfuz yayi shima yana kallon sa

" Waye shi. "

" Aboki na ne, abokin aiki na ne. "

" Recently na samu labarin ya zama babban terrorist kuma yana da connection da manyan
k'asar, bayan shi bana tunanin akwai wanda zai bukaci rayuwa ta, babu. "

"Ya akayi na manta? Ya akayi? "

" Kasan in da za'a same shi? "

Girgiza kai yayi,

" Ban sani ba. "

Komawa sukayi suka zauna, Mahfuz ya ciro biro da paper ya rubuta wani abu, daidai lokacin da
Moh ya daga wayar Musaddik yace ya same shi a garden, yana ajiye wayar sai gashi ya
zagayo dama chan yana cikin gidan, da kallo Mahfuz ya bishi kafin ya karaso wajen yace

"Waye shi?"

"Best friend dina ne."

"Ok." Yace a gajarce ganin ya karaso, ya mik'a musu hannu suka gaisa amma da ya bawa
Mahfuz hanun sai ya rik'e hannun nasa har sai da suka kalle shi dukka, sai ya saki yana
murmushi ya jingina da kujerar da yake kai, wani kallo Musaddik yayi masa ya zauna yana
maida hankalin sa kan Moh.
"I'm very sorry Capt..."

"Babu komai, nasan wani uzuri ne dakai." Ya katse shi kafin ya karasa.

"Babu wani progress ko?" Yace

"Babu."

"Allah ya bayyana su."

"Amin."

"Ya aiki?" Mahfuz ya tambayi Musaddik unexpectedly

"Aiki Alhamdulillah."

"Wanne aiki kake?"

"Harkar kwangila, kaifa?"

"Detective!"

Wani kallo Musaddik yayi masa, yayi shiru,.sai kuma ya kalli Moh

"Naga kamar kana da baki, dama inaso muyi maganar flash din nan ne tunda naga ka dawo."

"Flash?" Mahfuz yayi karaf ya tambaya

"Let's talk about that later." Moh yace sai ya mik'a wa Musaddik hannu

"Suna ina?"

Sosa kansa yayi

"Dalilin da yasa kaga kamar ina janye kaina a case din nan kenan, wallahi bansan ya akayi ba,
na rasa su gaba daya."

"What!"

"Kayi hakuri,ranar da aka sace wayata aka hada dasu gaba daya, bansan ya zan maka bayani
ba, nasan kuma muhimmancin flash din a wajen ka, shiyasa na kasa nutsuwa."

Murmushi kawai Mahfuz yayi, ya dire pen din hannun sa akan dan deborin da yake gaban sa,
ya dora hannun sa akai ya jingina yana masa kallon tsaf.

" Idan nace wani abu zaka yarda dani?"

Girgiza masa kai Moh yayi dan maganar batan flash din ba karamin bashi mam I'llaki tayi ba.

"Ina bukatar yara hudu cikin yaranka na gate."

" Me zasuyi maka?" Musaddik yace ransa a bace.

" Wait and see." Yayi murmushi, shi Moh ba gane kan maganar ba kwata kwata, yayi dai abinda
Mahfuz yace ya kirawo su suka zo, suka tsaya daga gefe, tashi Mahfuz yayi ya zagayo ta bayan
Musaddik,

"Take off your mask!"

"Kamar ya?"

"Me kake nufi Mahfuz?" Moh da shima ya mike ya fad'a cike da mamaki

" This man is deceiving you, ka kalli hannun sa, ka kalli fuskar sa, akwai banbancin skin color,
he's definitely using a mask, idan har ya musa, zan tabbatar maka."

"Noo...you are mistaken, wannan Musaddik ne, trusted friend dina ba zai taba deceiving dina
ba,you cannot accused somebody without a proof."

" Shine zan maka proving yanzu ai, wait and see, guys... Ku rik'e shi."

" Dakata!"

Moh yace ransa na baci, ba zai dauki wulakanta Musaddik yana kallo ba.

"Waye wannan Capt, waye zai zo ya shiga tsakani na da kai?"

"Calm down aboki na, misunderstanding aka samu amma zan masa magana..." Sai ya juya
wajen Mahfuz din

"Let's call it a day, zamuyi magana gobe, Habib ku jirani a wajen mota."

"Muje Mahfuz." Wani kallo yabi Musaddik din dashi, sannan ya juya suka bar wajen da Habib.

Juyawa kan Musaddik yayi da ransa yayi masifar baci, ya shiga bashi hakuri akan abinda
Mahfuz din yayi, yace ya jirashi yana zuwa bari ya sallame su. Yana barin wajen ya ciro waya,
ya kira shi yana matsawa chan gaba.

"Akwai matsala." Yana dagawa yace

"Ya fara suspecting dinka ne?"

"Be fara ba, wani banzan yaro ne bansan daga ina yazo ba, yaso dole sai ya nuna masa
gaskiyar mask da na saka..."

"Ya yadda?"

"Be yarda ba, kasan ya yarda dani sosai, so ba zai taba kawowa ba. "

" You have to be very careful, shi kuma yaron zan san yadda zan yi dashi. "

" Ok sir. " Ya kashe wayar yana juyowa, sukayi ido biyu da Moh da yake tsaye a bayan sa
kamar mayunwacin zakin da ya shekara be ce ba.




***Assalamu alaikum sisters, masu korafi naga wasu daga cikin korafin ku, ina mai baku hakuri
akan matsalolin da aka samu, dan gane da rashin posting halin girma shekaran jiya da jiya,
hakan ya faru ne sakamakon ciwon hakorin da ya matsa min hade da zazzabi, wanda har ta kai
ban iya samun duba sakonni ba balle har na iya zaman rubutu
Duk cikin zafafa biyar babu wadda a cikin mu take jin dadi a duk sanda batayi posting ba, Allah
ne shaida ana iyakar kokari wajen ganin Anyi abinda ya dace. Sai dai idan abu ya sha kan
mutum a ba yadda ya iya. Allah ya huci zuciyar duk wanda ransa ya baci ta dalilin jira ko wani
abu, ba da gangan bane wani lokacin kuma ajizanci ne na dan Adam.
Allah ya rufa asiri ya sa mu gama lafiya
2/21/22, 08:16 - Buhainat: Halin Girma
39

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇�_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇�_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇�_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_con
tent=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator
=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLo
SKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇�_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

****

"Capt... Yaron nan ya bata min rai, ya za'a yi ya zarge ni haka?"

Sassauta fuskar sa yayi, ya dafa shi

"Karka damu yarinta ce."

"Naga alama, waye shi? Aina yake?"

"Bansan shi ba, abokin Habib ne I guess!"

"Amma ka barshi ya zage haka, naji ma kamar hausar shi bata fita."

"Eh, born and raised a UK ne, dole zaka ji banbanci, anyways ya wuce na masa fad'a kuma."

"Shikenan, yanzu menene next? Da ya kamata muyi?"

Daga kafada Moh yayi cikin halin ko in kula yace

"Babu komai for now, muna cigaba da addu'a."

"Bari na wuce, I'm sorry akan maganar missing files din nan."

"Karka damu."

Da kallo ya bishi har ya fice daga wajen, ya daga waya ya kira waya, sukayi magana sannan ya
kashe. A kalla Mahfuz ya zama wani haske a binciken sa, kowa da yanayi da tsarin aiikin sa, ya
san aikin sa sosai ya kuma masifar burgeshi, he's smart and intelligent daga ganin shi,kuma da
yake akwai banbancin yadda k'asar mu take da tasu sun fi mu skills da kayan aiki.   Shugaban su ya kira, ya fad'a masa abinda ake ciki, ya kuma tabbatar masa da zasu yi duk
yadda zasuyi, a yanzu za'a binciki layin mudassir din a nan za'a gane da wadanda yake waya,
yana ajiye wayar ya kira Ammi sukayi magana sannan ya kira Aji da yake ta avoiding kiran sa
tun ranar, yana dagawa kuwa ya haushi da fad'a akan kin daga wayar sa da yayi, hakuri ya
bashi kawai sukayi magana ya kashe.
  Bayan kamar awa daya aka kirashi, ya shirya a gurguje ya fita cikin tawagar yaran matasan
sojoji, kowanne a cikin su a kalla zaka gane babu sauki a tattare dashi, bakin glass ne a fuskar
Moh, baka ko ganin kwayar idon sa. A wani waje suka hadu, ya tarar da taron jami'an tsaro
birjik kowannen su cikin shiri, babu kalar da babu na jami'an tsaro tun daga kan police, DSS,
civil defense, uwa uba sojoji. Gaisuwa ya dinga amsawa daga kananan ma'aikata har ya karasa
wajen manyan da suke kasan wata rumfa suna magana. Details din bayanan da aka samu ta
wayar Musaddik din suke dubawa, in da ya nuna babu wata waya da yake yi illa da mutum uku,

Moh din sai wata number da take kiran sa kullum a private number sai kuma Samha Bello
Turaki, da Kamal Abubakar Santuraki
   Kansa ne yayi masifar daurewa, menene alakar Samha a cikin case din? Karba yayi ya
sake dubawa sosai ya tabbatar da abinda yake a rubuce. Yasan Laila ce take son shi ba Samha
da take kawarta ba,menene akalar Samha da Iman dinsa da har za'a hada kai da ita a sace
ta?be san dalili ba,  abu daya ya yarda dashi, dukkan su anyi amfani dasu ne, domin a samu
galaba akan sa, su kuma idon su ya rufe, suna son ganin bayan  din suka fadawa gadar zaran
JABIR!

"Mun gabatar da duk binciken da zamuyi akan shi, mun kuma tabbatar da ba Musaddik bane,
yayi amfani da fuska ne, sannan yayi amfani da wata na'ura da take kwafar murya, wadda take
da masifar tsada Kuma alamu sun nuna ya jima tare da kai, ba zaka taba ganewa ba idan har
ba sani kayi ba, Musaddik yana da kusanci da kai shiyasa har sukayi amfani dashi wajen
samun kanka, da weakness dinka, sai kuma dan uwanka  Kamal da suka taimaka musu don
cimma tasu bukatar da hadin guiwar Samha da bamu san wata alaka dake tsakanin ku ba."

"Layin  da yake private mun saka an bud'e mana shi, kuma mun tabbatar da ana kira da layin
ne daga wani bangare ma dajin falgore! "

"Yana ina yanzu? "

" Yana ciki, idan an gama shiryawa shine zai shige gaba, kaine team captain din da zai
jagoranci tafiyar daga bangaren mu. "

" Ok sir! "

Yace yana sara masa, wucewa yayi zuwa in da aka ajiye fake Musaddik din, yana so ya
tantance banbance banbancen dake tsakanin sa da Musaddik dinsa da ya kasa ganewa, yana
durkushe a k'asa bayan dukan da ya sha, ya tabbata dai da JABIR ya tantance shi sosai kafin
ya kawo shi, dan hatta tsawo da yanayin sa irin ma Musaddik din ne, fuskar sa ya dago, ya kare
masa kallo zuciyar sa na tafarfasa, kamar zai daure amma sai ya k'asa, ya dunkule hannu ya
naushe shi a baki, nan da nan kuwa sai jini, ya saka kafa ya hambare shi. fitowa yayi ya tsaya a
filin yayi bayanin yadda zasu yi idan sun isa, duk suka amsa suka shiga motocin su a gurguje
suka dauki hanyar dajin falgore.
    Gudu suke kamar zasu tashi sama, haka suke a duk sanda suka fita operation amma
kuma na yau yasha banban da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login