Showing 12001 words to 15000 words out of 124388 words
Chapter 5 - HALIN GIRMA Book Complete by Hafsat Rano .pdf
da yar ta ta.
"Bari na shiga ciki Anty." Khalil yace yana mikewa, ta daga masa kai kawai ya wuce ya barta
tana cigaba da tunanin yadda zata bullowa al'amuran.
***Tana zaune a falon Gajin tana tunanin abinda ya faru tsakanin shi da Uncle Khalil, wayarta
dake saman cinyarta tayi kara, ta kalli wayar ganin bakuwar number ya saka ta tashi, ta wuce
zuwa bedroom din Gajin ta daga tana zama a gefen gadon ta
"Assalamu alaikum." Tayi sallama cikin muryarta da tafi komai tafiya dashi, lumshe idon sa yayi
ya bud'e a hankali ya amsa sallamar ta ta
"Wa alaikisalam..."
"Ina wuni?" Ta gaishe shi jin muryar sa
"Lafiya lou Mi Love, na barki lafiya?"
"Alhamdulillah." Tace a kunyace ganin shi kai tsaye yake maganar sa.
" Kina jina Zahraaah na? "
" Na'am?" Tace tana mike kafafunta
" A zahirin gaskiya ba da wasa nazo ba, da gaske nazo neman auren ki ba kuma naso a dauki
wani dogon lokaci in sha Allah, ni din dai ba wani bane kin dai ganni, bawan Allah ne me neman
amincewar Fatima Zahra, ina fatan zaki bani dama dan Allah!"
" Hmm..." Ta sauke ajiyar zuciya maganganun sa na taba ta, me zata ce toh? Da gaske take jin
ya kwanta mata duk da taga alamun ba wani shi nne dashi ba, amma sai taji yadda yake abu
kai tsaye ya birgeta sosai, babu karya straight kawai yake maganar sa, bayan haka da gaske
take son matsawa daga wajen Mama, ko ba komai ta samu yanci itama.
"Baki ce komai ba?"
"Allah ya shige mana gaba, Allah ya zaba mana abinda zai zamar mana alkhairi gaba daya."
Wani irin dadi yaji ya shige shi, ya rufe idon sa, ya dau yan sakanni yana jin sonta na sake
ruruwa a zuciyar ta, yana tuna tsawon lokacin da ya dauka yana dakon soyayyar ta, a lokacin
da shi kansa be san me ake nufi da so din ba.
 Mahaifiyar sa 'ya ce ga sarkin Kano kuma shi jika ne a gidan, hakan ya saka yake da alaka
me karfi da garin na Kano duk da mahaifin sa da mahaifar sa Adamawa-Yola ne, rayuwar sa
bayan ya tasa yayi ta ne tsakanin Kano da Adamawa, shiyasa babu in da be sanin a Kanon ba,
yake kuma jin kamar yafi zama comfortably a Kanon, musamman da bashi da son hayaniya
sosai sai nan din yafi zamar masa peaceful wajen hutawar sa.
  Akwai ranar da ya fito shi da abokin sa Musaddik, suna tafe a mota hanya ta biyo dasu ta
area din su Fatima, a lokacin ya ganta duk da lokacin ba ta kai yanzu ba, be kuma taba jin
abinda yaji akanta, shiyasa ya nace a lokacin suka yi ta bin ta har suka ga gidansu, suka kuma
yi tambaya akan ta da komai. A lokacin yaso ya shigo da karfin sa, sai dai wani labari da ya
samu ya sauya masa tunani da shawara, ya kuma yanke ma kansa shawarar da yake ganin
itace zata daga masa darajar ta, a ranar da gaskiya ta bayyana.
 Musaddik be aminta da shawarar ba duba da gidajen da Muhammad din ya fito, amma haka
ya kafe akan bakansa, shiyasa ma kawai Musaddik din ya kyale shi amma fa kullum cikin masa
korafi yake.
  Bangaren aikin sa zai iya cewa yana cikin yan gata da sai abinda suka zaba da inda suka
zaba zasu zauna, kasancewar gaba daya k'asar babu in da kakan shi mahaifin Ammi zai nemi
alfarma ba'a masa ba, sannan gefe guda mahaifin sa yayi sunan da zaka yi mamaki sosai.
 Duk da hakan be daina aikin sa ba, sai dai babu wani matsi ko takura tun ma be kai matakin
captain ba, balle yanzu da yake da rank me girma.
"Kinsan me?"
Yace yana gyara kwanciyar sa sosai, sanda Musaddik ya murda handle din dakin ya shigo
bayan yayi knocking ya bashi izinin shigowa.
"Ya Iman Abba na kira." Marwan ya fad'a mata yana tsaye a gefen ta, hannun sa ta riko shi
kuma yace
"Yaya Iman ki gaida min da Abba, idan kin dawo ki kira ni please, zan fad'a miki wani abu."
Murmushi tayi me sauti yana jiyo ta
"Ok bye." Ta ajiye wayar ta rik'e hannun Marwan din suka fito a tare..
"Yaushe Abban ya dawo?"
"Be dade ba, yana falo yana cin abinci."
"Owk." Tace suna karasawa.
" Abba barka da gida."
" Barka da Uwata, na dawo ban ganki ba, da zan fita ma ban ganki ba, shiyasa nace ya kira min
ke."
" Ina wajen Gaji Abba."
" Eh haka maman ku tace, amma ai na ganki dai ko?"
K'asa tayi da kanta Mama ta karbe
" Tafi son zaman chan yanzu ai."
" Kuna shan hira da Gaji kenan ko?" Yace yana murmushi
" Ko kuma tafi jin dadin tayi wayarta a chan ba, ko 'yata?"
Maman tace cikin son a sako zancen Moh, shiru kawai Iman tayi Abba ma ya girgiza kansa
kawai
"Allah ya kyauta, kinci abinci dai ko? Nasan ki da wasa da cikin ki."
" Naci Abba."
" Toh karbi nawa ki kara, nasan ba da wani yawa kika ci ba." Ya tura mata plate din gabanta
"Maza kirawo min zeenatu Marwan."
Gaban Mama ne ya fadi, ta zamo daga kujerar tana sakin salati a ranta. Tana gyara daurin
dankwalin kanta ta shigo falon, ta zauna a kusa da Iman ta gaida Abban.
"Abinda yasa na kiraku ke da yar uwarki, akan maganar yaran da suke zuwa wajen ku ne, duk
da shi wanda yake zuwa wajen Uwata bansan shi ba, inaso ki sanar dashi yazo yaga Yaya kafin
ya cigaba da zuwa."
Abincin da ta diba ta hadiye da k'yar gabanta na dukan uku uku.
"Ke kuma..." Ya nuna Zeenat
"Ki kawo wani daban ba yaron nan Bashir ba, ki sake dubawa a cikin sauran ki nemo wanda ya
dace da nasabar gidan nan, me Halin Girma mutumin kirki, kinji na fad'a miki."
Waro ido tayi cikin tashin hankali ta kalli Abban
" Hakan shine abunda ya kamata muyi a matsayin mu na iyaye, dan haka kiyi hakuri."
Tashi yayi, ya kalli Iman da tayi tsam a wajen, ya juya ya kalli Mama yayi mata alama da ido
sannan yace
" Na fita!"
Da k'yar Mama ta bud'e baki tace
" Adawo lafiya."
" Allah ya kiyaye Abba." Iman tace yana kokarin fita
" Amin." Ya amsa kafin ya fice gaba daya.
Wani kallo Mama tayi mata, tayi kwafa ta mike sannan ta kalli Zeenat da ta soma kuka wiwi tace
" Ki same ni a daki."
Kamar wadda zata fadi saboda kuka haka ta tashi, ta kusan fadowa Iman din aka, a ranta tana
jin babu abinda zai hana ta auren Bashir, duk tashin hankalin da za'a yi sai dai ayi shi, amma
babu wanda zai hanata abinda zuciyar ta take so.
***Cikin wani yanayi bayan ya gama jin komai ya gaida Abban da ya fito, yayi masa adawo
lafiya sannan ya juya zuwa wata hanyar ya fasa shiga dakin. Idan har abinda yaji gaskiya ne,
wannan me zubin yan boko haram din aka bawa damar turowa kenan, ba zai taba yarda yayi
biyu babu ba, ba aiki ba Iman, shi zai fara isa wajen Yayan idan yaso ayi wacce za'a yi, yasan
ba zasu taba hanashi ba, domin shi ya chanchanta ba wani bare ba, da ba'a san daga ina yazo
ba.
***
Tashi zaune yayi zaune bayan ya ajiye wayar, ya kalli Musaddik da ya zauna a gefen sa
"Ya akayi ne?"
"Na shigo kana ta waya"
"Eh wallahi, ni da Wifey ne."
"Wifey kuma? Yaushe kayi aure ba labari?"
"Bana son iskanci, kasan wa nake nufi ai."
"Toh ai sai kace aljanar ka da ka nacewa, amma kace wifey bayan bamu shafa fatiha ba."
Jefa masa dan pillow din da yake kusa dashi yayi
"Dan iska, ka jira ka gani ai."
"Wai karo maka yaran ka akayi ne? Naga gate din naka ya sake cika ga wani uban iyayi kamar
basu san mutum ba?"
"Sai hakuri kawai, ya ake ciki ne?"
"Normal, shiru ne ko ina, ya ka baro su Ammi?"
"Lafiya lou wallahi, Bubu yayi min maganar aure ai, nace zan zo musu da magana in less than a
month, kafin nan mun gama daidaitawa da Wifey."
" Ya zakayi toh idan aka ce ka turo?"
" Shine matsalar wallahi, amma zan san yadda zan dai."
" Toh Allah ya sa muji alkhairi angon Fatima."
" In Sha Allah." Yace yana dafe saitin heart dinsa, dai-dai lokacin kiran ta ya shigo wayar, yayi
saurin dora hannun sa akan baki alamun Musaddik yayi masa shiru, wurga masa pillow da ya
jefe shi dashi yayi ya fice yana cewa
" Ka same ni a kasa idan ka gama zan kalli laliga."
Da kai ya amsa masa yana kara kiran a kunnen sa
" Nagode sosai da kika kirani, na zata ba zaki kira ba."
" Haba! Zan kira ai."
" Nagode sosai, bari na kira ki toh."
" A ah ba komai, muyi magana akwai kati kar a cinye maka naka kai kadai."
Murmushi yayi me sauti
" Kinga kuma 200 nasa dazu har ta kusa karewa, bari na fita sai na sake siyo ko na 100 ne sai
na kiraki."
" Allah ba sai ka fita ba, ga sanyin nan da ake yi ma."
" Shikenan Nagode."
" Me kikayi a wajen Abba."
" Abinci naci."
" Iyeeeee, yar gata! Har abinci abba ke baki? Allah sarki ni."
" Kaima ai dan gata ne."
" Ni din? Tab ni ba dan gata bane, gashi ke har abinci Abba yake baki, niko kin ganni a dan
shago na sanyin nan duk a kaina zai kare, babu me tausayi na ya bani abinci."
" Allah sarki."
Tace cikin tausayawa, da ace sun saba sosai da tace yazo ya karbi abinci, ta hada masa har da
abin rufar ta idan yaso ita sai ta samu wani wajen Gaji, amma ba zata iya ba, sai kawai tayi
shiru tana tunanin ta yadda zata fad'a masa Abba yace yazo ya samu yayansa.
"Dama... Dama...Abba ne yace."
"Me?" Yace cikin zakuwa
"Wai ka fara zuwa ka samu Abba (Baban yayansu) ka nemi izinin zuwa kafin ka cigaba da
zuwa."
"In Sha Allah zanzo, yaushe ake samun sa a gida?"
"Kamar da yamma haka zuwa bayan Magriba."
" Ok in sha Allah zanzo, nagode sosai da wannan karamcin na Abba, duk da ni din ba kowa
bane, amma har aka bani wannan damar, nagode Sosai."
" Ni dai dan Allah ka daina cewa kai ba kowa bane, a islamiyya an fad'a mana, babu wanda yafi
wani sai wanda yafi tsoron Allah."
" Haka ne, wai kinga ina nufin ni din ba kudi ne dani ba, amma..."
" Kudi ba sune farin ciki ba ai, wadatar zuciya itace mutum, dan Allah ka daina wannan
maganar kana sani jin wani iri."
"An daina ta daga yau, ba zaki sake ji ba, kiyi hakuri idan na bata miki rai."
" Babu komai."
" Yawwa, kiyi min murmushi naji toh."
Shiru tayi
" Kinji mana, pleaseee."
Yace sai kuma yayi saurin daidaita kansa ganin zai zarme da yi mata shagwaba har ta ranfo
wani abu
"Nayi fa, ai baka gani na."
"Tam shikenan, idan naje na nemi izini wajen Abban mu, zanzo na gani a zahiri."
"Uhum." Tace tana jin zuciyar ta na sake nutsuwa dashi, ko ba komai ta samu wani da yake
dauke mata damuwar ta da kadaici
"Bari na barki haka kar na cinye miki kudi..."
"Goodnight, sweet dreams of meeeee."
"Allah ya tashe mu lafiya." Tace tana yin dariya k'asa k'asa
"Amin ya Allah, bye inji turawa."
"Bye." Tace mishi ta ajiye wayar.
"Yess!" Yayi tsalle ya dire kafin ya fice yana saka hannun sa cikin aljihun dogon wandon sa. A
falon ya tarar da Musaddik da tea yana sha, ya zauna ya diba shima yana murmushi.
_"You don make me fall in love, you don make me fall in lov, Baby I love you."_💕
Dariya sosai Musaddik ya saka
" JJC kawai, zaka cika mana kunne da wata wakar ka."
"Idan fitsari abin banza ne, kaza ma tayi mana?"
"Okh haka ne, shikenan ai.Wait and see. Ni yanzu ba wannan ya kawo ni ba, me yasa ka saka
aka dakatar da gayen nan ne?"
Tashi yayi rik'e da cup din yana bata fuska
"Kaga dacewar ya nemi irin abinda nake nema?"
"Kamar ya?"
"Ba'a takara da Sarki, be chanchanci karawa dani ba, bashi da qualities din da zai iya neman
auren ta, cika bakin sa ya saka na nuna masa iyakar sa, anyways warning ne kawai, zan sake
gwada hankalin sa , idan yayi hankali fine, idan be ba kuma sai muje a haka, sai a karbi
application din wasu."
Gid'a Kai Musaddik yayi be sake cewa komai ba, yasan waye Moh, yasan bashi da matsala ta
kowanne bangare, amma bashi da dadi idan har kayi crossing din sa, zai nuna maka shi din
babba ne a cikin manya!
"Ka fahimta dai ko?"
"Yes Captain!" Ya mike sannan ya sara masa.
"Aje waya!" Yace masa suka kwashe da dariya a tare.
HALIN GIRMA
Hafsat Rano
WAIWAYE......ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*
*ZAFAFANKU BIYAR 🔥🔥🔥🔥sune suka sake dawo muku da wasu nau'in
QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na
MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*
*_SANIN HALI.....yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama
cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*
*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA
ƘWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*
*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*
*_DEEN MARSHALL👉� Mamuhghee_*
*_HALIN GIRMA👉�hafsat rano_*
*_TAKUN SAƘA👉�billyn abdul_*
*_SO DA ZUCIYA👉�miss xoxo_*
*_ƊABI'AR ZUCIYA👉�huguma_*
*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN ÆŠAI ÆŠAI HAR BIYAR...ZAKU SAMESU AKAN KUDI
NAIRA 1K KACAL*
2👉�400
3👉�500
4👉�700
5👉�1000
*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA
SHAIDAR BIYANKU*
09134848107
_*HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA
MASOYANMU_*����������
#team zafafa biyar .
___________
1/6/22, 17:52 - Buhainat: *HALIN GIRMA*
      7
*Zafafa biyar na kudi ne, idan kina so ki karanta ki tuntubi 08184017082 or 09134848107*Â
I'm on Instagram as @zafafabiyar5. Install the app to follow my photos and videos.
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
***
Kukan ta ne yake karuwa Mama na tsaye a kanta, ta ja tsaki tace
"Bana son shirman banza kina ji na? Akan namiji zaki zauna kina rafka wannan kukan kamar
uwarki ce ta mutu ko ubanki?"
"Mafita nake so mu samawa kanmu, saboda anga zaki huta shine aka shiga aka fita ake so ayi
mana bakin ciki, idan ba haka ba, me ya kawo wadannan zantukan?"
Cikin kuka tace
"Wallahi Mama nasan Iman ce taje ta samu Gaji da maganar tunda dama ita yace yana so ai,
shine dan taga wanda yazo wajen nata talaka ne shine zata min bakin ciki, toh wallahi babu
wanda ya isa ya hanani auren Bashir, naji na gani kowanne hali ne dashi."
Shiru Maman tayi tana kallon yar ta ta, idan har ta bari maganar ta sha ruwa akwai matsala,
sanin cewa Zeenat din ba wani farin jini bane da ita, dama dai jamaar Iman din ne tun farko take
sanin yadda zatayi, dole ta san abinda ya kamata amma duk da haka ba zata nunawa Zeenat
din komai ba
" Kina jina? Ki tashi ki tafi dakin ku, ki daina wannan kukan tunda ba ubanki bane ya mutu, zan
san yadda zanyi komai ya daidaita."
Da bayan hannun ta ta goge kukan, ta fice tana rangaji, tana sake kudurewa a ranta babu gudu
babu ja da baya a auren ta da Bashir din.
 Tana isa daki ta tarar da missed calls din sa, ta bi kiran da sauri tana sake daidai ta kanta.
" Gani a waje." Yace tana dagawa.
" Mu hadu a bayan layi akwai matsala karka zo gida."
" Me ya faru?" Yace a kidime.
" Babu komai gani nan zuwa."
Kashe wayar ta, tasan zai ta tambayar ta menene gwara kawai taje suyi magana su sama wa
kansu mafita dan ba zata iya hakura dashi ba.
Â
Ficewa tayi ta kofar kitchen bayan ta gyara fuskar ta, ta bar gidan cikin sauri tana tsoron
haduwa da Ya Habib ko wani.
 A chan bayan layin ta hange shi jikin motar sa, a tsaye yake yana ta jijjiga jikin sa daga gani
baya cikin nutsuwar sa, tana isa ya juyo da sauri.
" Lafiya baby?" Yace yana riko hannun ta. Kuka ta saka da sauri yace
" Na shiga uku, me ya faru?"
" Abba ne yace wai na rabu da kai, wai yayi bin..."
" Shisshsh..." Yace da sauri yana dora hannun sa a saman bakin ta
" Kinsan dai hakan ba gaskiya bane ko? Sharri akayi min ko menene akace domin a hana mu
aure, duk wanda ya yi min wannan