Showing 90001 words to 93000 words out of 124388 words

Chapter 31 - HALIN GIRMA Book Complete by Hafsat Rano .pdf

Advertisement

11 Mar 2025

7936

a baya da pool daga chan gefe shima, gidan yayi kyau amma yayi girma ace
mutum daya kwal dan ma ma'aikata masu yawa wanda yawanci daga masarauta suke sai
wanda aka turo su daga adamawa. Daki ta koma ta haye gado tayi kwanciyar ta dan bata jin
yunwa tasha cornflakes suna zuwa sai kawai ta kwanta da niyyar ta tashi wajen azahar ta dafa
masa simple dish dan wata gajiya take ji na nukurkusar ta.
   Ta jima batayi irin baccin da tayi ba, ga sanyin AC da kamshin fresheners masu dadin
kamshi da ya cika dakin, hakan ya kara taimaka mata jin dadin baccin sosai har sai da taji ana
mata knocking sannan ta tashi bakin ta dauke da addu'a ta yane kanta ta fito ta bud'e kofar,
daya daga cikin masu aikin ce Atine, ta russuna ta gaishe ta sannan tace tayi baki ne a falo. Ok
tace ta rufe kofar ta koma ta gyara fuskar ta, ta fesa turare ta dauko wayarta ta fito. Yan mata ne
su biyu kyawawa dasu masha ALLAH, suna zaune suna kallon TV ta fito,

"Sannun ku da zuwa."

"Yawwa." Suka amsa a sake, suka gaishe ta sannan suka gabatar mata da kansu

"Fulani ce ta aiko mu, kayan gara ne dangin su alkaki dasu bakilawa da dublan, sai gireba da
sauran su, tace gashi nan zaku iya tayin baki tunda kun dawo."

"Kai mun gode sosai, Allah ya saka da alkhairi."

Ta tashi ta bubbude, ta dawo ta zauna tana murmushi ta sake godiya, aikin gidan mace ne
kayan gara amma basu bari anyi mata ko daya ba, dama tasan dai ko za'a yi sai dai a gayawa
su Mamma suyi mata sai gashi sunce ba sai anyi ba,itama yar su ce kamar Muhammad din.
   Hira sukayi sosai tun tana nokewa har ta saki jiki dasu dan suna da hira ga faram faran
kamar sun saba. Tare suka ci abincin da suka zo dashi alkubus da miyar taushe, suka bita
kitchen da zata yi ma Moh dan abincin sa, suka tayata sai yamma suka tafi, bayan sun mata
alkawarin zasu dawo basa so ya dawo ya same su dan tsaf zai kore su, jin su kawai tayi dan
batayi tunanin zai aikata ba, bata san yadda yake tsare musu gida da daure fuska bane shiyasa
har yake mamaki dan sun ce ba zasu zauna ya same su ba.
   Suna fita kuwa sai gashi ya shigo, yaga fitar motar su amma basu tsaya ba suka kara mai.
Bud'e hannun sa yayi ya tsaya daga jikin kofa, ta tafi a sanyaye ta fad'a jikin sa, ya rungume ta
yana shafa kanta.

"Sannu da zuwa yallabai."

Ta karbi rigar hannun sa suka rankaya cikin falon, sai da ya zauna sannan ya amsa mata
sannun ya dora da

"Baki kikayi?"

"Su umaima ne, daga chan gida aiko su."

"Yan rawar kai, tun yaushe suka zo?"

" Wajen twelve din rana."

" Ah kice kin samu yan hira ko nace yan surutu dan bakin su sam baya shiru."

" Naji dadin zuwan su kuwa, sun tayani hira ai."

" Sun kyauta da suka tafi kafin na dawo, dan tsaf zan saka yarinya frog jump ba abinda ya
damen."

Ya fad'a yana kai cup din ruwan da ta zuba masa bakin sa,

" Da gaske wai?"

" Da gaske mana, suma sun sani ai, kila ma sun fada miki ko?."

" A ah." Tace tana dariya

" Ya yau din? Ya gidan naki?"

" Alhamdulillah, komai yayi Masha ALLAH, Allah ya kara arziki, thanks for everything,

" Amin Amin, I'm glad you like it."

Yace cikin jin dadin addu'ar ta

" I love it!"

" Masha ALLAH."

***Tun ranar farko da Bashir ya samu damar shigowa dakin har yayi abinda yayi, tun daga
lokacin duk dare sai ya lallabo, ranar farkon tana jin su suka haura sama da uwargidan tasa

suka fado, sai da k'yar suka daidaita dan shima jan wuya yayi mata ganin idan ta biye masa zai
iya cewa su rabu yasa ta kyale shi, taga kansa rawa yake ya samu yarinya karama shiyasa ta
kwantar da kanta ta cigaba da bin sa tana so taga iyakar limit din iskancin nasa, tasan sarai
yana zuwa dakin da dare amma ta share bata taba nuna masa ba, wani zubin ma akan
kunnenta komai yake faruwa amma ta daure dan plan dinta akansa ba na yanzu bane, shigo
shigo babu zurfi tayi masa sai ya gama sakankancewa zatayi maganin sa.
   Ranar ma kamar yadda ya saba kawo mata waya suyi magana da Mama haka ya kawo
mata, ta karba tana daga kwance da babu wani aiki da takeyi yanzu matar gidan ta rage takura
mata, dattijuwar me aikinta da ta tafi gida ta dawo shiyasa aikin ya rage mata sai dai taci ta
kwanta ga uban kasalar da take fama dashi ga shegen nacin Bashir da yake hanata sakat, tana
shan wuya sosai a hannun sa dan baya daga mata kafa ko kad'an, tun tana masa rashin kunya
har tazo ta kyale shi yayi uwar da zai yi, ranar da zata samu hanya kawai take nema wallahi ta
tafi ba zata dawo ba ko me za'a yi mata kuwa.
  Wayar ya mika mata bayan ya gama amsawa da toh, suka gaisa da Mama ta take fad'a mata
haihuwar Aunty Bilki, tayi murna sosai ana take jin gobe suna kuma a gidan su za'a yi sunan
saboda akwai fili sosai

"Ki lallaba shi ya kawo ki na dai gaya masa."

"Toh shikenan, zan kira." Ta katse wayar ta mika masa

"Dan Allah ka barni naje suna gidan mu gobe."

"Ki shirya da safe zan mika ki sai na wuce garari na, idan na gama sai nazo mu dawo."

Yace ya sa kai ya fice da bishi da kallon mamaki, bata taba tunanin zai yarda haka kai tsaye ba,
murna ta hau yi ta dinga zagaye dakin tana jin kamar wahalar ta, ta kare kenan dan ko giyar
wake take sha idan taje gida ba zata dawo ba sai dai Abba ya kashe ta.
  Murmushin mugunta yayi yana barin dakin, shi kadai yasan tsiyar da ya shirya ya kuma
tabbatar da ko taje gidan toh sai ta dawo da kanta ko Maman ta sakota gaba ta dawo da ita.

***Waya suka gama yi da Ya Maryam ta cigaba da shiryawa a tsanake saboda safiya ce,
sannan yace ta jira shi ya fita toh dole sai ya dawo zata tafi, tana so taga Abban ta da Marwan
da Gaji da sauran yan gidan, shiyasa ta tashi tun wuri ta hau shiryawa yadda zata samu zuwa
da wuri ta dade kuma.    Tana zaune taji shigowar motocin sa, ta yaye curtains din dakin ta ga wasu motoci guda
biyu da bata san su a gidan ba, sakin labulen tayi, ta sake fesa turare ta fito suka hadu a falo.
   Tafi ya shiga yi mata dan ba karamin kyau tayi ba, lace ta saka me orange da black yayi
mata kyau ya dace da kalar ta, zaunar da ita yayi ya dauke ta hotuna masu kyau sannan yace
idan ta gama ta ga driver nan idan yaso zai zo da daddare su dawo tare. Jakar ta, ta dauko ya
rakota har wajen motar ya bud'e mata ta shiga, sannan suka fita daga gidan yana tsaye yana
kallon su. Tasa motar ya fad'a shima ya bar gidan dan yana da important abun da zai yi. A
daidai lokacin Zeenat suka fito da Bashir, ya kunna machine din da ya aro a wajen abokin sa

dan Hajiya ta fita da motar ta, kamar tace ba zata hau ba, sai kuma ta hau dan bata da ko biyar
din da zata dauki adaidata sahu, tunanin idan taje gida ta karbo masa sam be zo kanta ba.
 

_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D'aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107
2/12/22, 11:31 - Buhainat: Halin Girma
      33

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇�_*
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇�_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇�_*
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_con
tent=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator
=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLo
SKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇�_*
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

*******�
A kusan jere suke tafiya da motar Abba da Habib ke ciki shida mama, kasancewar tint ce ya
saka basu gane Iman din bace a ciki, suna shigowa layin su Habib ya sake kallon motar yace

"Ina tunanin fa Iman ce a motar nan."

"Wacce motar? " Mama tace tana waigawa, gabanta ne ya fadi ganin dalleliyar mota a bayan
su,

" Ta ya akayi ka sani?"

" Number na duba. "

Ya amsa mata yana tsayawa a daidai kofar gidan, daidai lokacin motar Iman din itama ta tsaya,
yayi daidai da isowar Zeenat a saman machine din Bashir. Mutuwar zaune Mama tayi ta kasa
bud'e murfin motar balle ta fito, idon ta yana kan motar da ta gama gane wacece a ciki, ta saitin
ta Bashir ya zagayo bayan ya faka machine din, ya leko yana cewa
" Sannu da zuwa Mama. "

Wani abu taji, ta kalle shi a kaikace kamar ta falla masa mari, tayi dauriya ta danne zuciyar ta ta
amsa tana jan kofar ganin yana kokarin bud'e mata, matsa wa yayi ta fito idon ta akan Zeenat
da tayi wani irin haske, hasken da tana kallon ta, ta gane na menene, kamar wadda aka sage
wa guiwa haka ya shiga jan kafarta zuwa cikin gidan, suka rufa mata baya a jere Iman din na
magana da Zeenat da take ta kokarin maida hawayen da take jin zasu zubo mata wanda bata
san dalilin su ba

"Ashe zaki zo?" Tace a sanyaye

"Wallahi, ya gida? Ko waya bamuyi ba."

"Wayata ta lalace ne. "

" Ayya." Kawai tace suka karasa ciki, nan da nan mutanen dake harabar gidan sukayi kan Iman,
kowa so yake ya ganta, duk sun rude babu wanda yabi ta kan Zeenat, ganin haka yasa ta
sulale ta gudu bangaren su, ta samu Mama a zaune tana kuka wiwi, kukan bakin ciki, kukan
dana sani da aka ce keya ce wadda bata da amfani, ta tuna watarana da aka zo akayi sallama
da Iman, ranar ce ta farko da aka fara zuwa kuma wajen Iman din, tun basu kai yanzu ba, da
kanta ta saka Hijab ta koreshi irin korar wulakanci, ba tare da kowa ya sani ba sai Habib, wanda
bayan ta kore shi ne Habib yake gaya mata waye shi, da kuma gidan da ya fito,. Tun daga
lokacin ta dauki alwashin dakushe Iman din, ta kara maida ita mara yanci cikin rashin sanin
cewa gata tayi mata, babu in da zata shiga rayuwa ta bata wahala musaman irin abubuwan da
suka shafi kula da gida.
   Taba ta Zeenat tayi ganin sai sallama take amma bata amsa ba, firgigit tayi tana dawowa
tunanin ta, suka rungume juna Zeenat din ta fashe da kuka, bata hanata ba, sai da tayi me isar
ta dan tasan kukan zai rage mata abinda take ji, gwara ace kishiyar uwa ke gallaza maka akan
ace kishiyar ka ce zata hanaka sakat da sukuni, abinda tayi ne ya juyo kanta amma ta siga ta
daban, sigar da bata taba tunani ko tsammani ba.
  Yan uwan Abba ne suka biyo Zeenat din har cikin gidan nasu, da mitar me ya faru zata shigo
ta wuce su babu ko gaisuwa, Mama na jinsu bata ce komai ba, dan tasan da biyu suka zo
maganar, tana jin Zeenat din tace suyi hakuri, wanda ya saka su jin nauyi da kunya kuma, suka
tafi cike da borin kunya.   Suna fita Iman ta shigo, ta russuna har k'asa ta gaida Mama kamar yadda ta saba, ko ba
komai ita a uwa take kallon ta, dan itace tayi mata komai na mahaifiya idan aka cire shekarun
haihiwa zuwa yaye, ita ta sani, ko ma menene dai tayi mata wani abu.
  A chunkushe ta amsa, har yanzu akwai haushin Iman din a zuciyar ta, wanda bata jin zata
daina sai ko ranar da ta bar duniya, har gobe tana kallon Iman din ta tuna cin amanar da akayi
mata, wanda take ganin da gaske Itace baa kyautawa ba.
   Ta dan zauna a bangaren nasu, babu me magana a cikin su, sai jefi jefi da suke magana
tsakanin ta da Zeenat wadda take cike da mamakin sauyawarta, tayi sanyi sosai kamar ba ita
ba, ta kuma hangi wani abu a idon ta, da take da yakinin damuwa ce. Tashi Mama tayi ta barsu
a falon tayi shigewarta daki, domin ta samu damar yin tunanin abinda ya kamata tayi akan
auran Zeenat din.
   Bin ta Zeenat tayi, ganin haka ya saka Iman ficewa ta koma bangaren Gaji in da anan me
jegon take, ta shiga yan uwa aka cigaba da kuranta ta da yaba ta, kowa yana so ya samu ya
kafa kansa ganin cewa yanzu ta wuce duk wani matsayi ta kai in da basu taba tunani ba,
shiyasa kowa yake kokarin chusa kansa dan idan wata dama ta taso ko da ta aikin Hajji ne, toh
Iman din zata tuna da mutum.
   Wajen azahar sai ga Yaya Maryam tazo, sai da ta biya ta asibitin da take ANC sannan ta
tawo shine dalilin rashin zuwan nata da wuri. Jan Iman tayi suka koma gidan su, suka zauna su

isu matasa aka hau hirar aure da yadda rayuwar auren take ma baki daya, sosai Iman take
daukar haske, tana karuwa da wasu abubuwan tunda sun fita jimawa, bata saka musu baki ba,
a tunanin Yaya Maryam ma bata jin su, nan kuwa ta haddace komai akanta.
  

***Tare suka shigo da Musaddik, wanda kallo daya zaka yi musu kasan a gajiye suke sosai,
babu wanda yayi magana sai da suka huta sannan ne Musaddik ya mika masa wayar sa da ake
ta faman kira tun suna hanya, karba yayi ya daga yana kishingid'a a saman kujerar

"Ya akayi? Kun duba yadda abun ya samu kansa a cikin part din?"

"Mun duba dukka CCTV footage na gaba daya area din, bamu ga kowa ba a kusa da wajen ma,
har zuwa kofar shiga shashen, falon kuma babu CCTV kasan, time da za'a saka kace baka so. "

" Na sani, shikenan ba damuwa. "

Yace yana zare wayar daga kunnen sa, ya ajiye yana murmushi wanda ya saka Musaddik
kallon shi

" Akwai wanda yake so yayi wasa da hankali na, ko ma waye yasan babu cameras a ciki, target
din su iya na wajen ne kawai. "

" Me kake tunani? "

" I can't say exactly, amma dai akwai wani abun daban ba sarauta ba, ko ma waye yana da
matsala da aure na, ba sarauta ba. "

" Laila fa? "

" Ba ita bace. "

" Toh me zasuyi benefiting anan, ban gane komai ba. "

" Guy, baka san wanne irin mutane ne suke zagaye da gidan nan ba, da kuma kudurin kowa,
zaka sha mamaki amma. "

"Ka sansu? "

" Almost.. "

" Then why are you allowing them to walk over you? Bayan kana da duk damar da zaka yi musu
abinda zakayi to get rid of them. "

" Ba zai yiwu ba, this is not a military war, wannan fad'an ba ma makami bane, ko na gwajin
kwanji ba, sai ka zama very very careful da duk moves dinka, akwai bakin ciki a gidan sarauta,
akwai kyashi, da hassada. Masu son kujerar ba mutane bane yan kad'an, suna da yawa kuma
kowa zai iya komai domin ganin ya samu abinda yake so"
Gid'a kai Musaddik yayi yace

" It's harder than i thought. "

Murmushi Moh yayi, ya hade hannuwan sa waje daya, suka fitar da sauti me dan kara, ya mike
yana zuba hannayen sa cikin aljihun sa

"Muje naga Takawa."

"Owk." Yace ya mike suka fita

***Be samu ganin Takawar ba kamar yadda ya saka rai, ya zauna zaman jiran sa dan yana so
ya nema masa alfarma akan tafiyar da za'a yi akan wani aiki gashi har da sunan sa, baya son
yayi nisa da gida dan a kalla zasuyi wata guda cif, yasan idan ya samu Takawar ya kira waya
za'a iya cire sunan sa, duk da tun daga last yace ya daina nema masa alfarma, tun da shi yaji
ya gani dole ne yabi dokar aiki, sai gashi ya dawo yanzu be kuma san yadda zata kaya musu
ba, shi kansa kunyar neman alfarmar yake amma kuma baya son tafiya ya bar Iman ita kadai
bata gama sanin komai ba.
   Har sukayi la'asar suka dawo Takawan be dawo ba, cigaba da zaman jiran sa sukayi
Muhammad har da dan baccin sa,ya bar Musaddik yana kallo dan dama shi mayen kallo ne. Sai
goshin Magriba sannan suka ji dawowar sa, alwala suka daura suka fita zuwa masallaci aka yi
sallah,.    Yadda ya dawo da irin wannan lokacin dama babu wani zama da zai kara direct ya wuce
gida dan yana bukatar ya huta sosai.
   Shawara sukayi akan kawai su dawo gobe da wuri kafin ya fito zaman fada. Da wannan
shawarar sukayi amfani suka tafi, suka wuce kai tsaye gidan su Iman daukota. A ransa ya
kuduri zai kaita ya nuna mata dakin da ya zauna har ya kwana aciki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login