Showing 27001 words to 30000 words out of 50228 words
Chapter 10 - Rayuwata ce book Complete by Khadeejah sani (journalist).pdf
*Comment*
*&*
*Share*
*By*
*Khadeejah (Ummu Fu'ad & Afnan)*
* RAYUWATA CE*
*Na*
*Khadeejah Sani (Journalist)*
*KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
* My mom inatayaki murnar fara sabon littafinki Allah yabaki ikon fadakarwa, Allah ya kara
nisantaki da makiya, Allah ya kiyaye gabanki da bayanki mamana takaina, book dinki mai suna
ITACE KADDARARMU Yana fadakarwa Yana nishadantarwa Allah yakaro Miki basira Mai yawa
my mom SAMEERA HAROUN Ina sonki sosai sosai*
*45_46*
Haka yayita bayani bansan me yake fadaba Saida naji nafisa nayimin magana sannan nadawo
daidai,
Zaunawa tayi munata fira da ita muna cikin hakanne mukaji sallamar mama don haka tamike
tayi waje da gudu tana murna nidai nabita da kallo don rayuwarta tana masifar birgeni tayi
dacen miji Mai kaunarta gashi tana ganin iyayyenta dukkansu uhm Allah sarki ni ga maraici ga
wannan kalar rayuwar danake ciki Allah ya hadani dashi *rayuwata ce* haka Allah ka rangwanta
min haka Allah yasa na dandani farin ciki nima kodan na farantawa mahaifiyata rai,
Sallama sukayi adakin hakan ya daukemin tunanin danakeyi na amsa shiguwa tayi na saki
fuskata Ina mata sannu da zuwa karasowa tayi dakin ta zauna Nan nagaidata tana
tambayataba jiki nace dasauki,
Innarmu ce tashigo dakin sunata firarsu ta duniya nidai nayi tagumi Ina zaune ga jikina namin
ciwo gakuma tunanin da yayimin yawa,
Muna haka har baba yazo Nan akayimasa iso yashigo yazauna gaidashi nayi nan yayimin ya
jiki na amsa sungaisa da Innarmu Sai Kuma mukaji sallamar yaya,
Sallamar tasa danaji Saida gabana yafadi don bazan taba mance wannan mummunar
muryarba shigowa yayi daki tare da zaunawa daga gefan kujera daga kasa Yana gaidasu
yawani sunkuyar da Kai kamar mutumin kirki, Nafisa ce ta gaidashi nikuwa ko kallonshi banyiba
na juyar da kaina Ina kallon gefe guda, Hada Ido mukayi da Innarmu ta wullamin harara nagane abinda take nufi don haka nakara
hade rai sannan nace
"Ina yini"
"Lafiya kalau ya jikin?"
Banza nayi dashi bance komaiba Sai baba yagyara zama yace
"Masha Allah gamu dukkanmu mun hadu Amma banga khalil ba Yana Ina haka?"
Innarmu ce tace "Yana kan hanyar dawowa don lokacin dawowarshi yayi yanzu" kafin baba
yayi magana Sai mukaji sallamar Yaya yashigo dakinmu yakaraso don yaga takalman mutane
Kuma yaga na maza don haka yagane ko babane yazo,
Shigowa yayi da sallama Nan suka amsa ya gaidasu dukkansu sannan ya zauna Nima sannu
da zuwa nayimasa yace
"Ya kikaji jikin naki yanzu kindaina jirin?"
"A,a Yaya haryanzu inayi"
"Okay Allah yakara sauki ai Sai ahankali zakiji daidai"
Bangaran mama kuwa dadine ya isheta don atunaninta ko cikine gareni don haka tafara
washe bakin tana fadin
"Ayyah sannu mamana Allah yakara sauki"
Ameen nace sannan dakin yadauki shiru can baba yace
"To naji abinda yafaru sannan inason ganin takardar Daya rubuta mata"yayane yamike yaje
dakinshi ya dauko yakawo Mai nan baba yafara karantawa afili aikuwa mama naji abinda yace
na bani da iddarshi takara rabga salati tana tafa hannuwa,
Saida baba ya nisa sannan yajuya bangaran Yaya yace
"Inaso ka maimaita abinda kafada Mana dazu agabanta don inason naji abinda ka aikata"
Nan yafara kame kame yama rasa abinda zaice ahakadai yafara bada labarin Daya bawasu
mama agida dafarko nayi mamakin yadda yazauna yake fadawa iyayensa abinda ya aikata,
saidai Kuma naji yacanja hanya yadda yaki fadin kawo karuwar tasa,
Yanata zubo musu karya akaina nidai inatajinsa kallonshi kawai nakeyi nama rasa abinyi har
yakai karshe, Kuma maganar datafi ko wacce batamin rai inda naji Yana fadin
"Banyi niyyar sakintaba Amma abinda take fadamin aranar yasakani na saketa zagina tayitayi
tana fadamin magana tana zagina harda idon na haifi cikin uwata da ubana nasaketa nikuma
shiyasa na saketa, Amma don Allah kuyi hakuri kuyafemin nasan na aikata abinda ba daidaiba
kugafarceni insha Allah hakan bazai Kara faruwaba"kallonshi kawai nakeyi nama rasa abinda
zance don abin yabatamin rai juyowa baba yayi kaina yace
"Kinji abinda yace keme zakice"
Banyi niyyar fada musu komaiba Amma tunda haka yakeso Dole zan fadani Kuma bazan boye
komaiba don haka namike zaune nafara Basu labarin duk abinda yafaru har zuwa yadda
mukayi da karuwar tasa da fadan damukayi nayi nasara akanta dakuma dukan dayayimin da
korata dayayi yabani takarda nakare da fadin "Wallahi wallahi wallahi banyimai karyaba ko nafadi San Rainaba duk abinda nafada shine
abinda yafaru Kuma wallahi tunda nake tare da Yaya bantaba zaginsaba kawaidai na fada
masane karya Kara zagin iyayena don ba sa,anninsa bane"
Dakinne yayi shiru saini daketa kuka kawai zuwa can baba yace
"Kanajin abinda tace ko kanada ja akan hakan?"
Girgiza kanshi yayi kawai baice komaiba,
Hakan yasa mama fashewa da wani kukan tace
"Dama irin abinda kake aikatawa kenan irin rayuwar daka zaba kenan, haka kadinga
cuzgunawa yarinyar nan dama, bawar Allah tana zaune dakai bisa biyayya amma kai kanuna
kawuce kayiwa mutane biyayya, yanzu haka kazaba zina! Zina!! zina!!! Innalillahi wa'inna
ilaihirraji'un........"kukane yaci karfinta tamike tayi waje batare data karasa maganaba , Innarmu ce tabi bayanta itama tana share hawayan tausayina,
Kallona baba yayi yace
"Allah ya saka Miki don nidai bazan taba nema maka gafarar abinda kayiwa marainiyar Allah
bah, Allah kuma yabaki lafiya Allah yahadaki da miji nagari ba irin wannan shashashanba
sakarai, Allah yayi miki albarka ya inganta rayuwarki"
"Ameen baba nagode Allah yakara girma" amsawa yayi da amin sannan yaciro kudi yamikawa
nafisa daketa kuka yace
"Mika mata tasiya wani abun Allah yakara sauki"
Yana fadar haka yayi waje,
Yayane yatashi yabi bayansa itama nafisa tamike tayi waje tare da mikomin kudin,
Komawa nayi na kwanta nayi kamar banganshi zauneba Saida yadauki lokaci sannan yamike
zai fita kallonshi nayi nace
"Allah ya shirya mazinata yasa sugane hanyar gaskiya, Kuma inaso kasani duk abinda kayimin
kaima zaka hadu da daidai dakai insha Allah, Kuma bazan taba yafe makaba akan zalincin
dakayimin ba har abada, Kai inaso kasani wallahi da ace inada halin dazan kaika court da Babu
abinda zai hanani kaika akwatarmin hakkina, Amma kaje kaida Allah, Allah yana tare dani kuma
nasan saiya sakamin"
Ina kaiwa Nan nashige cikin daki nabarshi Nan tsaye da jajayen idanu Yana kallona,
Wake yayi yasamu harsu Mama sun tafi don haka yayi waje batare Daya yiwa Innarmu
maganaba tana kitchen tana kallonsa Bata tanka Saba yafita,
Alhamdllh jikina yayi sauki don Ina samun kulawa daga bangaran Innarmu, Yaya, Nafisa,
harda mahbub Shima ba,a barshi abayaba don ko makaranta yaje harda tsaraba yake kawomin
Wai Shima kayana dubiya yake kawon,
Muna hakane nafisa tafara zazzabine nice na rakata asibiti gwajin farko aka fada Mana tana
dauke da ciki na wata biyu,
Murna kamar me don lokacin Yaya yayi tafiya bayanan aikuwa nice nafara kiransa nafada
Masa sannan muka dawo gida tanata rokona akan Wai karna fadawa Innarmu nace
"Tab wallahi wasama kikeyi ai kinsan kamar taji tagama" hakan yasakata muna shigowa
tashige daki Wai ita kunya takeji,
Innarmu tayi farin ciki sosai don harda hawayenta tayi na murna tace
"Da babanku Yana Nan yau da bansan kalar farin cikin dazai yiba don yanason yaga jikokinshi
Amma Allah baiyi zai ganiba"
Nima hawayen na share nace
"Allah ya gafarata Masa yasa yahuta"
Ameen ta amsa dashi,
*Agurguje please*
*********************
Hakadai rayuwa taketa tafiya hankalinmu yakara kwanciya sosai don yanzu bana cikin
damuwar komai saidai yawan tunanin masoyina tare da mafarkinsa da nake,
Ana cikin hakanne yau saiga mama tazo gidanmu yau kimanin wata hudu kenan rabonta da
gidan tunda abun Nan yafaru Bata Kara zuwaba Sai yau,
Mungaisa sosai Nana sukafara fira da Innarmu hakan yasa namike zanje dakin nafisa mama
tace
"Mamana zo nan wurinki ai nazo don sauri nakeyi"
Komawa nayi kusa da ita nazauna tafr magana tace
"Mamana inaso kiyi hakuri akan abinda yafaru Kuma kidauka kalar Taki kaddarar kenan, insha
Allah bazaki kara komawa makaman ciyar taba, abunda ke tafe Dani wata alfarma nazo nema
awurinki Ina fatan Zaki karbeta hannu bibiyu, nayi miki alkawarin insha Allah bazaki taba
komawa gidan jiyaba" tana kaiwa Nan tayi shiru nikuwa Banda faduwar gaba Babu abinda
nakeyi jin abinda tace Amma saina dake nace. "Mama insh Allah bazan baki kunyaba indai zan
iya abinda Zaki fadamin din" kamo hanuna tayi tafara fadin
"Inaso zama dake, inason kizama sirikata saidai wancan yakasa cikamin buri na, wannan
daliline yasakani yanke shawarar Kara nemawa yarona Mai hankali da tarbiyya aurenki akaro
na biyu, wannan bakowa bane face................."
*Ikon Allah wai akace nazaune yafadi, agaskiya abin Nan yabani mamaki na ganin yadda
mutane ke neman kudi ta hanyar haramun, hausawa sukace kura dashan bugu gardi da kwace
kudi, muda Shan wahalar zaunawa mubata wanni muna aikin typing Amma Sai asami masu
Saida Mana book, agaskiya abin Nan yabani mamaki, sannan idon writers tace zata maida
book dinta na kudi saikaji ana aiko mata da zagi da bakaken maganganu, wallahi abun Nan
yabani mamaki tare da tunanin Anya kuwa wasunmu zasuga annabin rahama, saboda rashin
imani irin na mutane wani yayi abunsa sannan kadauka kadunga Saida Masa, bayan bafinsa
son kudin kayiba, mumafa munason kudin nan amma mukaga zamu iya rubuta books kyauta,
shine wani can banza zaina Saida mana, to indai hakane ku readers zaku dunga siya ai saimu
koma siyarwar kawai, nidai Ina Nan inata tunanin yadda zan maida wannan abun nawa, na
yanke hukuncin zan maidashi Nima na kudi gwara Nima na siyar nasmi kudin tunda baifini
sansuba Amma Ina jiran shawararku readers me kukace akan hakan, ya kuka gani?, Meya
kamata nayi akan hakan?, namai dashi na kudin kokuwa akwai wata hanyar dazanbi wadda
zatafi ba ba wannan ba, Ina jiran shawararku*
*Comment*
*&*
*Share*
*Khadeejah (Ummu Fu'ad & Afnan)*
[10/4, 7:46 PM] Hayat: * RAYUWATA CE*
*Na*
*Khadeejah Sani (Journalist)*
*KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*Masoyana na hakika naga shawar warinku agareni Kuma nagode Allah yabar kauna, dalilin
shawar shawarin Dana samu ta Tex message da WhatsApp message da wadanda suka kirani
nagode sosai Allah yabar kauna, Kuma wannan dalilin yasa nagane Kuna Sona tsakani da
Allah sannan duk Wanda ya daukarmin book yasaida nabarshi da Allah wallahi bazan taba
yafewaba Ina Kuma rokon Allah ya sakamin ya bimin hakkina tundaga Nan duniya, sannan
wannan book zanci gaba da sambado mukushi kyauta batare dakun biyaniba amma insha Allah
book Dina na gaba Mai dauke da tausayi ilimi dakuma tsantsar butulci bazan iya sakinsa
kyautaba duk Mai bukata zai iya nemana nabashi account number yaturo kudinsa sannan
yasamu yanzu haka nafara typing dinsa Amma ban fara sakinsaba,*
*Bayan haka*
*Wadan da suka karbi account number nah sukaimin kyauta nagode Allah yabar kauna kuma
nasan kunasona tsakani da Allah bawai don book dinaba, hakama wasu da yawa daga cikin
fans Dina nasani Kuna Sona Nima Kuma Ina sonku sannan kutayani Mika godiyata ga
masoyana da sukayimin kyuta yau da safiyar Nan Allah yabar kauna ameen*
* Masu zagina Kuma bazan barku abayaba masu cewa dama talaucine yayi Miki
yawa shiyasa kikeson billo da hakan, eh naji Kuma nagode Allah Kuma yabarmin ku kuci gaba
da zagina nikuma naita cigaba Ina barinku abaya, sannan inaso kisani da ace da wannan
rubutun na dogara da wallahi bazan taba kawowa hakaba kisani nayi books ba dayaba ba
biyuba bantaba yunkurin maida book Dina na kudiba Sai yanzu Shima Kuma akwai dalili don
haka please kusan me zakuce banason rashin tunani cikin Al amarina, baya ga haka zagin da
kukayimin bazai taba fitominba don ba akaina aka faraba Kuma ba akaina zaku gamaba,
sannan inaso kusan cewa book Dina na gaba na kudine duk maiso ta siya maraso tabarshi,
nagama magana*♀♀
*47_58*
"Face muktar nasan kinsan muktar ba halayyarshi Daya da Adam ba yanada halayya Mai kyau
ga hakuri ilimi tunani uwa uba Kuma baibar tarbiyyaba don haka nake rokonki dakiyi tunani
akan hakan Yaya Kika gani?"
Ai kwata kwata bazan iya fasalta muku halin da nake cikiba nama rasa abinda kemin Dadi don
haka nakasa magana nayi shiru hakama Innarmu tayi shiru Sai zuwa can naji nafisa tace
"Mama kiyi hakuri da wannan maganar kibarta tadan huta zuwa wani lokaci tayi tunani sannan
tafidda abinda ta zaba"
Shirune ya Kara rsata dakin zuwa wani lokaci sannan mama tace
"Hakane wannnan amma aganina ai baikamata ace tazauna hakaba har na wani lokaci
yakamata asan abinyi"
Nafisance takara magana tace "ai yanzu makaranta ma zata fara zuwa jiya naji yace angama
mata komai zata fara zuwa cikin satin Nan"
"Uhm ai shikenan tunda anfi karfina Amma inaso duk da haka kiyi tunani akan maganata duk
shawarar da Kika yanke kifadamin karkiji kunyata kinji mamana?"
Kallonta nayi nace "insha Allah zan fada Miki mama"
Firarsu suka cigaba dayi nidai natashi nayi waje don cigaba da aikina,
Koda najicmaganar makaranta nayi mamaki don bansan da itaba don haka Saida nabari mama
ta tafi na tambayi nafisa Nan take fadamin ai Yaya yadade Yana nemamin makaranta Kuma
Alhamdllh lillah nasami fce zanyi nce insha Allah bangaran English Islamic Nan naita murna
nace "To ai Naga banyi jamb dinba duk da nabiya kudin Ina gidan Yaya aka zana banjeba"
"Ai yasaka an zana Miki Nima naso nayi Amma yace a,a Wai bayanzu zan cigaba da karatuba
kema dandai kinriga kinbiya kudin jamb dinne yace kema ba karantun zakiyiba kawaidai don kar
ayi asarane yasa yayi Miki, lokacin da hakan ta faru Sai ya fara nema maki school ammafa
cewa yayi soyake yayimiki bazata don haka karki nunamai kinsani Nima badan abunda Naga
Yana Shirin faruwaba dazu Allah da Babu yadda za,ayi kiji daga bakina Sai dai abakinsa" dariya
kawai nayi cike da farinciki Nan mukaci gaba da firarmu nida ita,
Sai bayana kwana biyi sannan Yaya yazo yasameni rike da wayata Ina chatting yace
"Kishirya gobe Zaki fara lecture insha Allah ga temitable dinki nan saiki duba, kishirya da wuri
na saukeki" murna nakeyi nama rasa bakin godiya nace
"Aikuwa Yaya nagode Allah yabar zumunci Allah ya biyaka da gidan aljanna nagode Yaya
sosai bansan da bakin dazanmaka godiyaba Amma Babu abinda zance saidai Allah yabarka da
masoyiyyarka yakara dakon kauna tsakaninku" dariya yayi yace
"Keko Allah ya shirya minke" dariya nayi Nima Nan natashi nafara tsalle na nunawa Innarmu
godiya tayi Masa itama shidai yayi waje Yana dariyar murnar da yaga inayi,
***************
Alhamdllh haka nafara zuwa makaranta cikin sa,a na hadu da kawata goda Daya Mai mutunci
sunanata Ayshat muna zaune cikin mutunta juna da daraja juna,
Ahaka mukayi exam munyi huru munkoma makaranta,
Alhamdllh exam ta fito munsami abinda mukeso don dukkan subject din da nakeyi dukkansu
daga A Sai B nasamu hakan yayimin Dadi sosai,
Yau kimanin watana Tara kenan da fitowa daga gidan Yaya Kuma yayi daidai da cikin nafisa
wata Tara don haka mukafara shirye shiryen tarbar baby ni maman baby inata sayan kayan
baby don yanzu inayin Sana,a sosai Ina Saida atamfa da mayafi hijjab da jakunkuna, don haka
bana rasa kudi a hannuna,
Yauma kamar kullom na fito daga lecture naji karar wayata dakkowa nayi Naga Yaya ke kirana
don haka nayi saurin dauka Ina fadin
"Asslm baban Yaya ya yaudin?"
"Lafiya Lau ke nafisa ta haihu yanzuma muna asibiti " ai bansan lokacin da nasaki karaba Ina
muna nace
" Wanne asibiti kike ganina zuwa yanzun Nan kuwa"
Katse wayan nayi tare da mikewa nace
"Ayshat kinga bazan tsayaba lecture din malamin nanba Sai gone matar yayace ta haihu
yanzu" dariya tayi sannan tace
"A,a kice sis anyi baby anzama mom" dariya nayi Ina fadin "kedai Bari ni wallahi nama manta
ko tambayar me tabaifama banyi, Kinga natafi Sai munyi waya"
Sallama mukayi na Kama hanyar asibiti
Zuwana keda wuya na samu har anfiddo da ita dakin hutu Nan nadauki baby girl Ina kallo
nace
"Innarmu Kinga yarin yarnan kamarmu Daya da ita ko?"
Dariya tayi tace
"Ohh waima ni kike tambaya ke bakisaniba kenan?"
Dariya nakarayi nace
"To Bari naji baban baby me zaice shi, Yaya Dani take kamako?"
Dariya Shima yayi yace "lallaima yarinya Dani take Kama bakeba" bata Rai nayi nace
"Nidai nidai Dani take kama" nakarasa kamar zanyi kuka,
Dariya sukayimin gabaki dayansu nan muka karasa dakin,
Kwance take tana bacci don haka muka Sami guri muka zauna nidai pic nafara yiwa babyna
sannan na daukemu tare Innarmu ce tace
"Mawota haka ta huta kinbi kinhanata hutawa"