Showing 42001 words to 45000 words out of 50228 words

Chapter 15 - Rayuwata ce book Complete by Khadeejah sani (journalist).pdf

Advertisement

da lahiya nagode Miki matata takaina Allah ya biya Miki bukatunki yahadaki
Alkairi aduk inda kike yarabaki da duk sharrukan duniya ameen" yakarasa fada Yana sakar min
kiss sannan yace
"Tashi muje muyi break tun dazu mom ta aiko Mana da abinci inata jiranki Baki farkaba"
Mikewa nayi Ina fadin
"Ayyah dama tashina kayi ai kokuma kaci abinka Naga Rana tayi sosai ai"
"Ai bazan iya ciba batare da keba nifa cin abinci tare da matata shine Abu na farko da nakeson
yazama kamar farillah atare dani insha Allah"
Murmushi nayi kawai,
Muka karasa kan daining din nan nafara kokarin saving dinmu yace nabarshi na huta
aikinshine wannan,

Bayan mungama haka muka dawo muka zauna afalo munata fira Wanda kusan shine Mai
yintama,
Muna hakanne Sai mukaji ana nocking din kofar falon hakan yasakashi dagani daga jikinshi
yaje yabude,
Muryan Ayshat naji hakan ya sakani saurin tashi Ina fadin
"Shinema Sai yanzu zakizo ko?"
Shigowa tayi suna gaisawa ta harareni tana fadin
"Ai wallahi badaban ya takura Wai nazoba da bazaki ganniba"
Kallonta nayi tare da zama kusa da ita sannan nace

"Saboda me to?"
"Saboda nabarku kusha amarcinku karna takuraku" dariya nayi sannan nace
"Kindai Rana kawai zakicemin"
"Eh narama" kirana naji yanayi Wai agaban Ayshat mah baby yake cemin abin yabani kunya na
kalleta dariya tayi tace
"Gulma tashi kije Zaki wani Kama kallona to meye hakan?"
Tashi nayi Ina fadin
"Zakiyi bayanine Bari nazo"
Dakinshi na shiga kawai jinayi ya jawoni jikinshi Yana fadin
"Baby zandan fita zanje gida da asibiti don jiya nayiwa wani tiyata bankara zuwa na dubashiba
Kinga gwara naje Naga jikin nasa ko?"
"Eh gaskiya hakane Allah ya tsare agaidamin da mom kafin nazo"
"Zataji Yar gidan mom" karasa maganar yayi da hade bakina da nashi Saida ya tsotse janbakin
dake bakina sannan yace
"Alhamdllh" tare da Kara gyara jikinsa, Nima na daidaita nustsuwata sannan muka fito a tare,
Ayshat na zaune nan yayi mata sallama ya fita nikuma nazauna kusa da ita Ina fadin
"Me Kika tahomin dashi?"
Rike Baki tayi tare da fadin
"Kardai harkin Sami abun daga abunnan" dariya takeyi nikuwa kallonta nayi azuciyata nace
dama ana ganewa Ashe ai bansaniba saikuma na tuna haryanzu tafiyata Bata dawo daidaiba
don haka na Kara hade Rai nace
"Banason hakafa malama"
Dariya takeyi sannan ta bude Jakarta tare da Ciromin kula tace
"Gashinan danbune Nima mamarsu Mahmud ce ta kawominshi Ina niyyar tahowa saina dibar
miki" karba nayi cikin zumudi Ina fadin
"Wayyo Dadi yaushe rabona Dana cishi dama"
Kallona kawai takeyi tana wani rausayar dakai alamar tausayi na bata,
Ajiyewa nayi nace
"Sai anjima zancishi ba yanzuna"
Murmushi tayi sannan tace
"Uhm hajiya kawas anzama mata" kallonta nayi sannan nace
"Banason wulakanci wai yauna farayin aurene dazaki wani dameni da magana"
Kallona tayi tace
"Lallaima yarnan kina nufin aurenki na baya Dana yanzu Zaki hadashine wallahi kinsan kema
akwai banbanci idon Kuma Babu kifadamin inaji"
Banza nayi da ita natashi nashiga kitchen Kara dumama mata ragowar kaza nayi sannan nafito
mata da ita nace
"Nasan dai wannan kikazo kici gashi Nan Allah yasa na rage Miki" kallona tayi tana dariya
sannan tace
"Tab wallahi karya kikeyi yanda Kika cita jiya da dare akasha amarci Nima haka nacita Kuma
muka Kara Shan wani amarcin dazaki wanice ita nazo naci"
Dariya nayi sannan nace "Aidai nice amarya duk abinki kekin tsufa gashi nan harda baby anan"
nafada Ina nuna cikinta dariyar itama tayi tana shafashi tace

" Allah sarki my buy harkinsa ya juya"
"Waini watanshi nawama nagadai kwata kwata watanki biyu da Yan kwanaki"
"Watanshi biyu hajiyata"
"Ohhh Ashe shiyasa kikemin fatan Nima nasamu ko don ke bakisha amarciba Nima karnasha
to ta Allah ba takiba"
Dariya tayi tana fadin
"Insha Allah lokacin da zakiyi wata Tara anan gidan Zaki haihu"
Shiru nayi Ina murmushi don Nima inason hakan harga Allah,

Wuni tayi Sai yamma sannan Mahmud yazo suak tafi suna tafiya Shima yadawo dama Ayshat
saida tagama abinci sannan ta tafi ta jereshi a daining ta gyara gidan yayi tsaf yayi kyau,
Lokacin Daya shigo Ina dakinshi nagama gyarawa Ina jiyo shigowar motarshi nayi saurin
shigewa toilet nahada Masa ruwan wanka,
Shigowa dakin yayi lokacin na fito daga toilet nace
"Sannu da zuwa"
Karasowa yayi ya jawoni jikinsa Yana fadin
"Haka ake taryar miji ai ba daga nesa nesaba" murmushi nayi sannan nace
"Ya mom take"
"Lafiya kalau tace tana gaida diyarta"
"Ina amsawa"
Zaunawa yayi abakin gado hakan yasakani saurin fara cire Masa takalmi da safar kafar,
Bayan na Gama nace
"Ga ruwan wanka can na had a"
"Ai Baki Gama aikinki bah"
Juyowa nayi daga jikin kwaba Ina Shirin debo Masa Kaya nace
"Na,am"
"Eh haka nace nasan kinji abinda nace ai don haka kidawo kikarasa"
"Ai bansan ko mezanyiba"
"Ki karasa aikinki mana, Baki ciremin kayan bah"
Ruke Baki nayi tare da zaro Ido nakasa magana,
Mikewa yayi Naga yayo kaina hakan yasakani saurin fita da gudu nayi dakina dariya yayi
sannan yacire kayan yayi toilet don yayi wanka gashi magriba ya kusa bayaso lokacin sallah ya
kure,

Koda ya fito daga wanka kayan Dana zaba Masa yasaka sannan ya tafi masallaci ba biyo
dakinaba don sauri yakeyi kar atada sallah,


********************

*Agurguje*

Haka rayuwa taci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali da anushuwa muna nunawa juna
kulawa daidai gwargwado har nakoma makaranta munfara exam shine yake kaini yawuce office
dinsa idon nagama naje can nakirashi mutafi gida tare wani lokacin Kuma natafi gida idon ya
kasance ranar zaikai yamma,
Bangaran su Yaya kuwa ababuwa suna tafiya yadda ya kamata anata zuba love saidai shi
gogan naku abin yadameshi gashi hajiyar tasamu ciki tanata faman shagwabewa Sai ita Mai
ciki shine ke Mata girki idon bashine yayiba bazata cishiba Wai bazata iya ciba don haka
yadawo kuku kulluma shine yake mata girki safe Rana da dare ga wani kalar ci da take dashi
yanzu tana Gama cin abinci zakaji tace yunwa takeji,
Hakadai aketa lallabawa tare da ita saidai mutayasu da addu'ar Allah ya Rana lafiya,

*******************


Mungama exam lafiya Alhamdllh munsami hutu Mai yawa tsahon wata uku,
Amma wani ikon Allah ranar da muka gama exam naje gida na yini acan don da safe muka
gama tundaga gida nakejina banida lafiya ahaka na daure har yazo da dare muka taho gida,
Kamar jira muna zuwa Sai sanyi nakeji kafin Yan mintuna Sai zazzabi Nan nafara amai kafin
wani lokaci harna fita Daga hayyacina,
Shikuwa duk yabi ya rude Yama rasa abinda zaiyimin kawai saiya daukeni yasaka amota nan
getman ya budemasa get mukayi waje,
Cikin sauri muka karasa clinic dinsa nan aka fara duba lafiyata tare da yimin gwaje gwaje
Wanda bansan anyi sauranba nidai nasan ansakani nayi fitsari nakasa ko rmtashi zaune shine
ya kaini har toilet din ya sakani nayi yadiba yakaiwa doctor din.



*Comment*
*&*
*Share*


*By*



*Khadeejah (Ummu Fu'ad & Afnan)*




*ν ½νΉ†ν ½νΉ† RAYUWATA CE*ν ½νΉ†ν ½νΉ†

*Na*


*Khadeejah Sani (Journalist)*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*ν Όν΅Ώ73_74*


Kwance nake inata baccin wahala, don Saida akayimin allurar bacci sannan nayishi ganin
yadda naketa amai gashi na galabaita sosai,
Shigowa doctor din tayi office dinsa inda yake tsaye akaina Yana aikin kallona,
Bakin gadon ta karaso tare da fadin
"Congratulation doctor" tana fada ta Mika Masa takardar tana murmushi dubawa yafarayi inda
yaga cikine gareni na sati biyar ai baisan lokacin da ya kwanto kainaba Yana mika godiyarsa ga
Allah murna yakeyi Yama rasa abinyi Sai kudi Mai yawa Daya bawa doctor din data kawo Masa
wannan labari sannan yashige toilet din dake office din yayo alwallah yatada sallar farin ciki,
Bayan ya idarne ya dauki wayarshi yashiga Kiran mom dauka tayi tare da fadin "my son "
Ai ko amsawa baitsaya yiba yafara fadin
"Mom albishirin ki"
Murmushi tayi sannan tace "kome kakeso zan baka son fadamin menene?"
Dariya yayi cikin farin ciki yace
"Baby tanada ciki mom kinganmu yanzu haka muna clinic"
Cikin murna da zumudi tace
"Kai haba my son da gaske kakemin kokuma wasan da kasaba yiminne?"
"Kawai mom kizo kigani da kanki muna office dina saikinzo"
Kashe wayan tayi tare da mikewa tasaka hijjab tayo waje ko driver Bata tsaya kiraba ta shiga
da kanta tafarayin driving da kanta tayo hanyar clinic din,
Bangarena bansan abinda yake faruwaba,

Kamar kiftawa saiga mom acikin office din tashigo cikin sauri lokacin shikuma ya kwanta a
gefena yanata shafamin ciki Jin anbude kofar yasakashi tasowa da sauri mom din da yaganine
yasa shi sakin dariya Yana cewa

"Ohhh mom irin wannan sauri haka" dariya tayi tace
"My son jika wasane ya jikin nata Allah sarki baby sannu kinji kalli yadda ta rame dama Bata
da lafiya ne?"
"A,a wallahi mom ko daya harfa taje tayi exam yau suka gama shine nace tawuce gida zuwa
yamma naje na dakkota, lokacin da naje muka taho take cemin batajin dadi" nandai ya Bata
labarin duk abinda ya faru har zuwa yanzu,
Kasancewar mom doctor ce saita kalleshi tace
"Yanzu abinda za,ayi kasaka mata ruwa insha Allah tana tashi zataji dadin jikin"
Yadda tace hakan akayi,
Tashi yayi yace "mom Bari nayi sallahr magrib don namanta banyi wallahi gashi Naga Isha,I
takusa"
Dariya tayi tana fadin
"Ohhh my son irin wannan zumudi haka ya Kuma da ranar da yazo ko tazo duniya?"
Dariya yayi sannan ya shiga toilet din office din,

Bani na farkaba Sai wurin karfe goma Ina bude Ido naganshi zaune kusa dani Yana ruke da
hannuna murmushi nayi Masa tare da fara yunkurin tashi,
Kamoni yayi ya tadani zaune Yana yimin sannu kaina na rike sannan nace
"Banyi sallah bah"
"Zakiyi ai sannu yanzu meke Miki ciwo?"
"Kaina saikuma bakina Babu Dadi"
"Ayyah sannu Suma zasu daina a hankali"
Mikewa yayi Yana fadin "Bari na hada Miki tea kisha nasan kinajin yunwa"
"Banason tea amai zaisakani" dawowa yayi kusa dani Yana fadin
"Mezaki ci me kikeso?"
"Babu komi sallah nakeso nayi bani ruwa nasha"
"A,a baby kidaure kici wani abun dai please banason zama da yunwa"
Yatsina fuska nayi sannan nace
"Zanci waina da Miya da man shanu" dariya yayi sannan yace
"Ohhh baby kwadayi ko?"
Nima murmushi nayi sannan nace"sallah zanyi"
Kamani yayi Yana fadin "muje kiyi alwallah, waima yanzu Ina za,a Sami wainar Nan da kike
fada?"
"Ana saidawa a bakin layinmu ai"
"Okay Bari inkira yayanmu naji ko zaishigo office yanzu saina bashi sako"
Tsayawa nayi da tafiya nace
"Please karka fada Masa" dariya yayi sannan yace
"Okay angama ranki ya dade"

Alwallah nayi nafito sannan natada sallah
Waya ya dauka tare da Kiran Yaya
Dauka yayi suka Kara gaisawa don Daman sun gaisa dashi lokacin da yaje daukata agida,
"Yayanmu don Allah kafitone?"

"Eh kaganni a kofar gida yanzu zan fito dai"
"Yawwa please ka tahomana da wainar shinkafa da Miya da manshanu a bakin titin Nan
please muna Nan cikin clinic din"
"Okay Babu damuwa Amma lafiya kuwa naji kace Kuna clinic?"
Saida ya kalleni inata sallah a zaune don bazan iya yintaba a tsaye jiri nakeji sannan yace
"Kaganmu wallahi madam ce babu lafiya muna nan"
"Innalillahi meya same ta haka da sauri inace dazu kuka wuce gida meya faru" magana yake
cikin tashin hankali da fargaba ganin hakan ya sakashi fita daga dakin don yanason ya fadamai
abin farin cikin Daya sameshi sannan Kuma ya kwantar Masa da hankali don yaji har muryarshi
ta canja, Nan yafada Masa ai baima Bari ya Gama fadaba yakoma cikin gida da sauri Yana fadawa
Innarmu abinda ya faru murna ta kamata Nan tayimin addu'ar Allah ya saukeni lafiya,
Nafisa dake daki itama fitowa tayi tana murna tare da rokonshi don Allah tazo suje tare,
Kallonta yayi sannan yace
"Taho muje ki tahomin da kullah babbah da karama"
Kallonshi Innarmu tayi sannan tace
"Mezakayi da kula Kuma?"
"Waina za,a siya musu yace"
Nan suka fito nafisa saboda murna ko baby bata daukaba tace tabarma Innarmu ita kafin ta
dawo,

Lokacin da suka karaso harna idar da sallah Ina zaune abakin gadon na dasa Masa rigimar
zansha icream shikuma yace bazansha Abu Mai sanyiba don haka nasami wuri nazauna inata
hade rai shikuma ya shareni Yana danna wayarshi Yana satar kallona,
Shigowar nafisa ruke da kula yasakani yin murmushi nace
"Yawwa maman baby sannu da zuwa"
"Wacece maman baby Kuma bayan ke?"
Kallonta nayi cike da alamar tambaya sannan nace
"Yau kuma nizaki cewa mmn baby Ina babyn take?"
"Tana gida barta nayi acan tunda munyi sabowar baby"
"A Ina kukayi sabuwar babyn?"
Dariya tayi kawai tana fadin
"Kedai sannu Allah ya saukeki lafiya"
Kallon wurin da Muslim yake azaune nayi da niyyar nayi Masa korafin ya fada kawai sainaga
yaya zaune kusa dashi don haka nayi saurin sunkuyar da kaina Ina Wasa da hannuna ni wallahi
kunya nakeji,
Katsemin tunanin yayi da cewa "sannu ya jikin naki Innarmu Tana Miki sannu"
Shiru nayi tare dayin kasa da kaina Ina Wasa da hannuna,
Nan suka zauna sunata fira Sai zuwa can Nafisa tace
"Kinga na manta Bari na zuba Miki wainar kici ko?"
"Yawwa zuba mata please Nima na Sha,afa inata fira"Muslim ne yayi maganar cikin sauri,
Daukar plate tayi ta zuba min aikuwa cikin sauri da zumudi nafara aikawa bakina Ina lumshe
idanu dan tayimin Dadi sosai,

Sunjima ana sosai sannan Yaya yashiga ciki don yayi aikin da yakawoshi Sai wuraren
shabiyun dare sannan suka tafi don haka Nima nace mutafi aikuwa yace a,a Sai Ankara
karamin wani ruwan naji dadin jikina sosai zuwa safiya saimu tafi rigima nasaka akan nidai
kawai mutafi gida hakan yasakashi tashi Dole mukayi waje, Muna fitowa cikin clinic din duk Wanda ya ganmu saiya tsaya ya gaidashi tare da yimasa
congrat ni abunma har mamaki yabani ganin yadda lokaci daya har kowa yaji,

Mundauki hanyar gida ne nasaki kuka kallona yayi cikin tashin hankali yafara jefomin tambaya
yace
"Meya faru wani gurin ke Miki ciwo menene fadamin please?"
Kallonshi nayi nace
"Don Allah kasiyamin ice cream wallahi jinake idon banshaba bazan iya komaiba please katai
makamin don Allah" nakarasa maganar da sakin wani kukan
Hakan da yaganine ya sakashi cewa
"Shikenan zan siya Miki" godiya nayi Masa,
Munje wani guri ya tsaya yashiga saigashi da leda ice cream neh guda biyu aciki Nan nashiga
murna nabude Daya nafara shanshi kafin mukarasa gida harna shanye don haka nafara kokarin
bude dayan hanani yayi yace
"A,a Wanda kikasha is okay kibar wanna Nima nasha ko?"
Daga kaina nayi sannan muka shiga cikin gidan,


*********************


Alhamdllh iya kulawa dai Ina samunta awurin mom kizo Innarmu Yaya uwa uba kokuma nace
Mai gayya Mai aiki ba,a magana agurinshi don har hutu ya dauka na kuka Dani shine dafamin
wannan dafamin wancan kuka dani hatta wanka inda Yana gida banayi da kaina saidai yayimin,
Cikin hakanne Kuma muka cinye hutunmu Wanda lokacin cikina Yana wata hudu da sati biyu
aikuwa Nan yasaka rigimar bazan komaba Wai ahakura da makarantar Sai bayan na Yaya
yaron ko yarinyar sannan nashiga wata,
Nan Nima nace banyardaba Abu kamar Wasa Sai gamu da zuwa wurin Innarmu itama goya
Masa baya tayi hakan yasa nayi fishi nafito daga gidan natafi gidan mom Nan naje nasameta
zaune afalo tana ganina tafara murmushi tace
"Diyata sannu da zuwa kinji kina fama da kanki Kika iya tahowa Kuma bashine ya kawokiba
sannu kinji?"
Nan nagaidata saikuma nafara tunanin abinda zance mata don abindai akwai kunya ace
nakawo mata karar danta,
Fira mukayi sosai zuwa can nayi karfin Hali nafada mata abinda yake take Dani Nan tashiga
fada tana cewa
"Ai wannan maganar banzace mata nawa keyin karatu da ciki saike zai Hana" Jin nasami
karbuwa yasakani cewa
"Mom kumafa wanna kawar tawa matar Mahmud itama ciki gareta akma shine nizaice Wai

saidai nadaina gashi Ina nce2"
"Rabu dashi kinji karatu kamar kinci gaba dayi haka kawai ahanaki karatunki"
Murmushi nayi nan mukaci gaba da firarmu,

Shikuwa ban garanshi Yana ganina natashi na fito alamar nayi fishi Sai Shima ya tashi yafara
sallama dasu Innarmu yafito ganin bai ganniba yasakashi yin murmushi ya hawo motarshi yayo
gida don yasan nan zantaho

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login