Showing 18001 words to 21000 words out of 50228 words

Chapter 7 - Rayuwata ce book Complete by Khadeejah sani (journalist).pdf

Ahaka nagama namaidasu inda suke sannan nafito,
Bansameshi afalonba don haka nashiga daki Ina zaunawa naji ya kwadamin Kira tashi nayi
nafito nace gani kallona yayi yace
"Okay kazantarce Zaki farayinta acikin wannan tsararen gidan nawa to Maza kije kiyi wanka
kafin ranki yabaci" komawa nayi dakin nashiga toilet don nayi wanka,

Bayan nayi wanka nasaka Kaya Mai kawai nashafa ajikina da duk yakemin zafi har wani wurin
yayi shatin duka,
Daukar magani nayi nasha sannan nakwanta Ina tunanin da ace inagida yanzu banma
tashiba tunda Sai wurin takwas muke tashi ranarda Babu makaranta Amma yanzu no babuni
Babu bacci kenan,

Ina haka bacci barawo yayi gaba dani Saida nayi Mai isata sannan natashi don kaina Ina tashi
naduba Naga karfe goma tashi nayi da sauri nashiga toilet nawanke bakina nafito,
Fall nayi saina samu ankawo Mana breakfast daga gidansu yaron na zaune Mai suna
mashkur sa,an mahbub ne Nan yagaidani yace
"Anty tundazu nazo inata sallama naji shiru Dana shigo sainaga kina bacci Kuma Naga Babu
motar Yaya yafita shine nazauna jiran tashinki" murmushi nayi nace
"In Banda abinka mashku ai dakasani katasheni, ya gida ya mama da baba?"
"Lafiya kalau suke suna gaidaki Kuma mama tace Wai karkiyi girki na Rana da dare har zuwa
sati zata dunga Aiko Miki dashi"
"Allah sarki mama aikuwa nagode kafada mata nagode sosai" Nan mukayi fira dashi dakko
faranti nayi nadibi abincin tare da tea din da aka hado dashi naci Shima nazuba Masa yaci
kunsan abin yaro koyaci aguda baiki ka Kara masaba,

Bayan nagama tashi nayi nadakko want abun najuyewa Yaya nawanke kwanonin nabashi
yatafi dasu,


Hakama da Rana aka kawomin abinci alokacinne Kuma kawayena sukazo Nan mukasha Hira
sunata tsokanata Wai kodai kodai sunga nacanja azuciyata nace nasha duka dai,
Haka muka wuni dasu Sai bayan magriba sannan sukace zasu tafi cikin kudin da Muslim
yabani da do akko dubu daya nabasu kudin mota kowanne mamaki yakeyi Wai Ina nasami kudi
haka nidai shiru nayi dasu Sai Daya daga ciki maisuna aysha tace
"Kuma dawata tambaya ta rainin wayo mace da mijinta kuce Ina tasami kudi lallaima to nibari
nabaku amsa mijintane ya ajiye mata saboda Baki masu zuwa" dariya nayi nace
"Yawwa tawan kinbasu amsa daidai kuwa" dukkansu mamaki sukeyi haka muka rabu kamar
nabisu suka tafi sukuwa kowacce da tunanin dama itace ta auri miji kamar haka data huta,

Har aka kawo abincin dare baidawoba hakan Kuma yayimin Dadi naci abuna nabarmasa nasa

anan falon nakoma daki nayi Shirin bacci kulle kofar nayi na kwanta tare da dakko wayata Ina
kokarin Kiran Innarmu tashiga Nan tadaga muka gaisa tare da dantaba fira kadan,



*******************


Bangaran su Yaya kuwa bayan ankawo amarya mutane suntafi Innarmu tanata sallamar bakinta
itama amarya da kawayenta suna cikin dakinta kawayen amanarya sunata shewarsu irin ta
yanmatan amarya,
Wurin Taran dare suka yimata sallama suka tafi nan tazama saura ita kadai,
Yaya kuwa Sai wurin Tara da rabi sannan yashigo don dama yafada mata shifa Babu wasu
abokai dasu rakoshi shiyasa itama tace basaisun tsayaba,
Yana shigowa dakin Innarmu yafara zuwa ya ajiye mata kullinta sannan tayimasa nasiha Mai
ratsa jiki bayan tagamane tace yatashi yaje Allah yabasu zaman lafiya,
mikewa yayi yashiga dakin nata zaune take bakin gado fuskarta rufe da mayafi zama yayi
kusada ita tare da bude mata fuska Yana murmushi,
Itama murmushi tayi don ita to kuka batayiba sosai,

Kallonta yayi tare dayiwa Allah godiya Daya mallakawa mishi mata kamar wannan,
Mikewa sukayi sukayo alwallah sukayi sallah sannan yayi musu addu,a sosai yakama kanta
yayi sannan suka faracin kazar Daya shigo da ita kunya ta hanata ci sosai don haka kadan taci
tatashi tace takoshi,
Shima tashin yayi tare da tattare kayan yakai cikin firinji yadawo toilet tashiga ta wanke baki
tafito Shima shiga yayi Amma Saida yayi wanka sannan yafito kasa kallonshi tayi har yasaka
sleeping dress yazo kusa da ita yace
"Ganaki kayan tashi kisaka saikizo kikwanta nasan agajiye kike"
Tashi tayi tadauki kayan tayi toilet don tasaka.




*Comment*
*&*
*share*


*By*


*Khadeejah (Ummu Fu,ad & Afnan)*

*Comment*
*&*
*Share*



*By*

*Khadeejah (Ummu Fu ad & Afnan)*





[9/14, 8:08 AM] Hayat: *ν ½νΉ†ν ½νΉ† RAYUWATA CE*ν ½νΉ†ν ½νΉ†


*Na*


*Khadeejah Sani (Journalist)*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*ν Όν΅Ώ31 _ 32*



Saida nayi musu wani kalolin abincin sannan nafito musu dashi, suna Nan sunata aikin da
sukaga afimusu nashige abina,
Daki nakoma nakwanta asaman gado tare da dafe kaina dakemin wani irin ciwo rufe idona
nayi ina tunanin wannan rayuwar,
Sundauki lokacin sunata firarsu inajinsu sai zuwacan naji sunkoma daki saikuma naga anturo
kofar dakina,

Mikewa nayi da sauri tare da kallonshi yawani hade rai yace
"Kitashi kije kikarasa gyaran falon sannan kiwankemin motata tafita sosai ki gogeta saikuma
wankin da na ajiye Miki Yana Nan afalo Shima kiyishi kafin mutashi daga bacci don yau bafita
zanyiba sai anjima zankai dear unguw" yana gama fadar haka yayi waje mikewa nayi jikina duk
yayi sanyi dajin irin wannan muguntar shikenan nazama yar aikinshi kenan kuma harda wankin
mota toni inama nataba wani wankin mota ko ganin yadda akeyi bantababa balle nace nakoya
anan,

Fitowata daga daki naga wani abun mamaki kayanshine kala uku saikuma gajeran wando
guda hudu harda Wanda yasaka jiya da yazo da yarinyar Nan dama nayau Dana gani ajikinsa
saikuma kayan danaganta dashi jiya na bacci dakuma nadazu sai pants dinta Suma kallon
kayan nayi kawai sainaji wani kuka yazomin yanzu ace mijin da nake aurene yazo da wata
karuwa gidana sannan sugama iskancinsu abani kayanta ace nawanke ai wannan bakaramin
rashin mutuncineba gaskiya,
Gyaran falon nayi nadauki kayan nayi waje wankin nafarayi sannan nakoma wajen motar
nama rasa mezan fara kallon motar nakeyi sai kawai naje nadakko ruwa acikin bokiti na ajiya
nadakko wani bokitin karami na ajiyeshi omo na kada nasami wani abun nafara wankewa
inatayi harna gama nazo nadauraye sannan nadauki duster nagoge, Saida naga Babu ruwa ajiki sannan nabarshi nakoma daki,
Lokacin Dana koma har biyu tawuce toilet nashiga nayi wanka nayi alwallah nadawo nayi
sallah sannan macanja Kaya nashirya kwantawa nayi duk agajiye nake banajin Dadin jikin
gabaki Daya don haka nakwanta shiru Ina haka bacci yayi gaba dani,

Bansan lokacin da suka tashiba kawai jinayi an wankeni da wani Mari daysakani tashi zaune
Ina hawaye yace
"Dan ubanki haka ake wanke mota duk kinbi kinjikemin ita kalli jikina dana zauna yanzu"
yafada Yana juyomin bayansa duk yajike yadora da fadin
"Hakama dear itama duk jikinta yabaci to zakici ubanki wallahi yau....." Karuwar tashice ta
katseshi tace
"Dear rabuda ita kawai tazo muje taciremin kayanan ta canjamin wani kaima tacirema
tacanjama wani aikin da zatayi kenan sannan tawankesu tahada da wadancan kayan ta goge
Mana"
"Yawwa dear kinkawo shawara haka za,ayi wuce muje" wucewa nayi gaba suna biye Dani
abaya har dakin nashi natsaya karasowa tayi tace
"Uhm fara aikinki"
Kallonta nayi nama rasa abinda zanfara yimata don haka nakalleta nace
"Mezanyi to"
"Ciremin kayan zakiyi Mana kicanjan wasu har pant dinama yajike don haka harshi"
Murmushi nayi kawai nasaka hannu nafara zuge zip dinta don doguwar rigace ajikinta nadawo
na cireta nazame pant din nata duk kunya tabi takamani Amma ita Naga ko ajikinta sai firarsu
sukeyi dashi,
Bude jakar kayanta nayi zan dakko mata wasu kayan sainaji tace
"A,a zuki fara ciremasa kayan sannan kidakko Mana wasu"

Juyowa nayi zanfara cirewa Sai naji yace
"Dear kiciremin da kanki wallahi Ina gyamin wannan yarinyar ne shiyasa banaso ta ciremin"
"Okay bara nacirema kekuma dakku kayan"

Juyawa nayi tare dayin hamdala bansan abinda suke yiba najuyo don na ajiye kayan akan
gado kawai Naga nagansu manne da juna sunata aikinsu Sai uban nishi sukeyi saurin dauke
kaina nayi na ajiye kayan nayi waje,

Wanka nayi nayi sallah sannan nafito nadibi abincina nakoma daki nakulle don banaso yazo
yadameni,


***************


Haka rayuwa taketa tafiya kullum akwai kalar rashin mutuncin dazai billomin dashi yau inyayi
wannan gobe wancan ahaka har munci wata Daya da kwanaki yanzu nice kemana girki idon
karuwar tashi taso inagamawa tace baimataba inkuma taso tayi shiru taci idon yatafi office Bata
kulani saidai tashige dakinshi tayi zamanta nikuma nayita aikina, Bangaran su Yaya kuwa anacan anatashan soyayya kamar baza,a mutuba nafisa tasaki
jikinta tana fitowa wurin Innarmu suyi aikin gida don abincin Rana Dana dare tace keyinshi
tahana Innarmu itakuma innarmu tahanat yin breakfast itace take musu,
Dafarko innarmu tasoma anraba girkin tadungayi da kanta amma tace a,a abarshi ahade yafi
don haka sukabar girkinsu ahade,

Acikin kwanakin Nan Naga suncanja want kalar tsarin idon yafita aiki itama saita fita Bata
dawowa sai dare kokuma sudawo tare hakan bakaramin Dadi yayiminba don nasake Koda baki
nayi banata jin tsoran karta fito sugantaba,

Yau zaune nake nagama abincin rana inata kallo kawai saijinayi anshigo da mota kasancewar
akwai get man kallon kofar falon nayi nace araina ko wanene kokuwa shine yadawo yau yanaji
da wani bala,inne bankai da rufe bakinaba kawai naga mahbub yashigo ai tashi nayi cikin
murna natareahi don baitaba zuwaba, "Oyoyoyo my brother kaida waye haka naji mota?" Tunda nasan Yaya bashida mota,
"Nida yayane da anty mukazo gasunan shigowa" ai inajin haka nayi waje da guduna na tarosu
Ina murna Nan suka shigo Ina kusa da nafisa muka gaisa nanfa akafara fira tashi nayi naje
nadakko abincin danayi nakawo nakina nadakko lemukan da akayimin iyaka dasu kullum siya
kirga idon zaifita Wai karnasha Masa tunda ko agida Basha nakeyiba lokacin naji zafin maganar
don haka bantaba tabamasaba sai yau Shima Kuma saboda bakine,
Nacika musu gabansu da kayan motsa baki sannan nazauna munata fira,
Yayane yace
"Waikekuwa yanaga kinrame kinyi wani bakki haka kodai bakida lafiyane" murmushi nayi nace
"Wallahi Yaya lafiyata kalau Nima haka Naga nakoma wata kala Amma Naga nafisa tayi kiba

takara wani haske kodai kodai" gallamin harara yayi yace.
"Sa,ankine Niko?"
Dariya nayi tare da sunkuyar dakai kasa.



*Comment*
*&*
*Share*


*By*


*Khadeejah (Ummu Fu,ad & Afnan)*
[9/15, 7:16 AM] Hayat: *ν ½νΉ†ν ½νΉ† RAYUWATA CE*ν ½νΉ†ν ½νΉ†


*Na*

*Khadeejah Sani (Journalist)*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*ν Όν΅Ώ33 _ 34*



Fira mukeyi cikin kwanciyar hankali can nace
"Au namanta Yaya yaushe kayi mota bansaniba Babu labari?"
Dariya yayi yace
"Kindai ganta baki ganetaba ta Muslim ce yasaka drive dinsa yakawomin Wai narunga anfani
da ita kafin yadawo, saboda ajiyan karfe ba,a hawa yanada matsala" lokacin Daya Kira sunansa
Saida gabana yayi mummunar faduwa don kusan kulluma sainayi kukan rashin mutum Mai ilimi,
mutumnci, sanin yakamat, nutsuwa, uawa uba kuma tarbiyya saurin dauke tunanin dayayimin
karan tsaye nayi tare da zabga uban murmushi Wanda ake cewa kafi kuka ciwo nace
"Ayyah Allah sarki yaya Muslim ashe kunayin way dashi" don dama agaban Innarmu da Yaya

haka nake fadamasa amsa yabani yace
"Aikuwa ko jiya munyi waya yacemin ya wajenki nace kina can bantaba zuwaba shine yace
gaskiya ban kyautaba nasamu jiyan nazo nace yayi hakuri saidai zuwa gobe"
"Allah sarki bawan Allah ashema shine yasakaku zuwan Nan da kukayi"
"Aikuwa dai don wallahi idon ta nine bayanzu zanzoba saidai baby tazo itada mahbub"
"Ai gashinan yayana yasakaka zuwan dole dai"
"Kuma Allah dandai Ina masifar ganin girmansa yasa nazo da Babu inda zani cewa kawai
zanyi Masa nazo kina gaidashi dondai bazan iya yimasa hakaba don daima yanzu nasan Yana
makaranta ko compan ninsa Dana kirashi kungaisa Amma darensu yakusa bari kafin mutafi
nakira mikishi" Cikin farincikin nace "yawwa Yaya dakuwa ka kyautamin wallahi"
Nafisace wadda tundazu taketa kallonmu muna Bata Sha,awa jitake dama yayantane yake
zama haka suyi fira datafi kowa Jin dadi Amma shi sai shegen girman kantsiya da jijjida Kai Sai
masifar tsiya tace
"Uhm uhm naga alamar kunmanta danima gabaki daya awurin Nan alama ko?"
Murmushi nayi nace
"Habadai na isa namanta da matar yaya babba ai ban,isaba wallahi"
Dariya shikuma yayi yace
"Kekuwa yaushe rabon da muhadu kusan wata da sati Daya kenanfa ai dole azanta"
"Ummm gaskiyane to Nima bari nakira nawa yayan yadawo guda muyi hira tunda naga Bata da
alamar kiransa"
Kallonta nayi nace
"Kirashi da kanki ai kunfi kusa"
Dariya tayi tare da daukar wayarta tafara kiransa tashi tayi tabar wajen don tasan indai
takirashi da zagi yake farawa don haka ta tashi karma yabata kunya,
Firarmu muka Dora da Yaya nace
"Ni Yaya naga haryanzu bakaci komaiba Dana ajiye muku gwara nafisa Tasha lemo taci
abincin kadan"
Murmushi yayi yace
"Ke akoshe nake Amma bari nasha lemon kawai"
Dauka yayi yanasha kallonshi nayi azuciyata nace
"Hmmm bakasan akalar cin mutuncin da akayimin ba akan wannan abin banzan daba damuna
yayiba kwata kwata" maganar da yayine yadawo Dani yace
"Yada kallo haka konima nayi kibarne bansaniba" dariya nayi nace
"Wallahi kayi kiba sosai bakaga yadda kakomaba harda wani tunbi kayi" dariya yakeyi yace
"Lallaine yarinya kinrainani da yawafa nine nayi tunbin?"
Nima dariyar nayi nace
"Eh Mana kaga yadda kadawo ne?"
"A,a banganiba saike sa idunawa" dariyar nakarayi nace
"Yaya wallahi jinake kamar karku tafi dama harda Innarmu kukazo dayau naji dadin dayafi
haka" kallona yayi yace
"Kefa dadina dake bakida wayo wani lokacin shikenan Sai mutaho harda Inna saidai wata
ranar nakawo miki ita ta yini idon nadawo daga aiki nabiyo muwuce gida"

"To Allah yakaimu" nafisa ce tadawo tazauna kusa da Yaya tace
"My love kaji Yaya yace Wai aiki yayi Masa yawa shida gida Sai dare bazai samu dawowaba
dawuri"
"Ayyah Allah baiyi zaku haduba sai wani lokacin"
Fira mukeyi har akayi sallahr la,asar don haka Yaya yafita masallaci dake layinmu mukuma
muka shiga dakina donyin sallah,


Bayan mun,idar muka zauna acan munata fira da ita har lokacinda yadawo yace tafito suwuce,
Munyi sallama da ita awurin mota ta shiga sannan muka tsaya da Yaya nace
"Yaya waya nakeso Mai kyau zandunga chat da ita don Allah inada kudi zanbaka kasiyamin ko
gobene idon kadawo daga aiki saika bani don Allah" kallona yayi yace
"Dama naga alamar bakwayin zaman lafiya da mijinki Amma zamuyi maganar Sai nadawo jeki
dakko dubu goma saina cika miki nasiya Miki Yar dubu talatin ko talatin da biyar"
Harna juya saiyace
"Kezo nakirashi kugaisa Kinga namanta ko?"
Murna nayi dajin hakan don dama Yana Raina maganar kawaidai nayi shirune Kuma shiyasa
na kawomai maganar siyan wayar donya tuna,

Gaisawa sukayi sannan yace gani Nan yamikomin na juya nayi gidan Ina cewa
"Yaya bari nakawo kudin yanzu"
Gaidashi nafarayi ya amsa sannan yace
"Ya guda da maigidan gidan naki?"
Cikin sanyin murya da rawarta nace
"Lafiya kalau ya karatun"
"Alhamdllh yanajiki haka bakida lafiyane?"
"A,a lafiyata kalau mekaji"
"Kifadamin gaskiya wallahi acikin kwanakin Nan inaji ajikina akwai abinda yake faruwa dake
Kuma bamai Dadi bane shiyasa na takurashi yazo yaga lafiyarki"
"Uhm Babu komi yaushe zaka dawo?"
"Babu rana saina kammala karatu Nanda shekara da rabi insha Allah"
"Allah ya kaimu yabada abinda ake nema yasa anyi asa,a"
"Ameen kema Allah yabaku zaman lafiya kidunga yiwa mijinki biyayya kinji Nafeesat nasan
kinada tarbiyya da ilimi to don Allah kikara akan wanda nasanki dashi kinji?"
Kuka nafara tare da fadin
"Insha Allah zanyi yadda kace nagode Allah yabaka mata tagari kamar yadda kake nagari"
inakaiwa Nan nakwashe wayar tare da goge fuskata nafito daga falon don dama nashiga harna
dakko kudin nafito,

Tsaye na taddashi kamar yadda nabarshi na mikamai wayar tare da kudin nace
"Yaya nasan abubuwa sunma yawa ga dubu talatin nan kasiyamin wayar kacikamin sauran
nagode Allah yabar zumunci" kallona yayi kamar zaiyi magana saikuma yafasa yace ameen,

Komawa nayi na yiwa nafisa godiya tare da Bata wani sirrinmu aleda nace zamuyi waya nan
tafara godiya shikuwa mahbub bashi kudi nayi nace yakaima Innarmu sannan Shima nabashi
dubu daya,

Ina Nan tsaye harsuka bar gidan kukane yaci karfina nakoma ciki,
Ina shiga naci Karo da jarkokin lemon da sukasha guda uku murmushi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login