Showing 24001 words to 27000 words out of 50228 words

Chapter 9 - Rayuwata ce book Complete by Khadeejah sani (journalist).pdf

kuka salati ya
dauka Yama kasa bude takardar Sai zuwacan ya bude tare da karantawa afili hakan yasa nafisa
dake zaune taji aikuwa tanajin abinda yace tamike tayi dakinta da gudu tana rusa kuka kamar
ranta zaifita Wanda baisaniba Sai ya rantse ita aka aikowa da sakin, Innarmu ce takara fitowa tana fadin
"Haba nafisa yazakizo kisamu gaba kiyita kuka batare dakin fada Mana abinda yake faruwaba"
kallon yayanmu tayi tace
"Au ashema kashigo gatanan tun magriba tazo taki fadar komai gashi Nan yanzu har takwas
da rabi tayi tana Nan zaune inda take" kallon Innarmu yayi cike da tausayi sannan yayi mata
bayani kallona tayi tace
"Allah ya kyauta tashi muje daki kiyi wanka ga ruwan zafican" mikewa nazoyi nakasa don
dukkan jikina ciwo yakemin hakan data ganine yasakata kamani mukayi daki mukabar Yaya
Nan tsaye don yagane dukana yayi kafin nataho ga fuskata Nan duk tabi ta kunbura,


Bangaran nafisa kuwa tana shiga daki tadauki wayarta tafara neman wayar babansu tana shiga
yadauka tare dayin sallama,
Kukan da takene yasakashi yin shiru sannan yace
"Mamana meyafarune haka kike irin wannan kukan?"
Cikin kuka tafara fadin "shikenan yajazamin baba yanzu za,a sakeni Nima sallahi ya saketa
nasan bazai cigaba da zama daniba Yaya yasaki anty Nafisa nashiga uku"
Cikin firgici yace
"What? Mekikace yasaketa garin Yaya yaushe metayi Masa?"duk yajera mata wadan nan
tambayoyin,

Cikin wani kukan tace
"Wallahi baba bakaga yadda yayi mata dukaba duk fuskarta jini yabata takunbura tazo gidan
tanata kuka, munyi mata tambayar duniya amma takiyi mana magana saida yaya yadawo
sannan tabashi takardar yana dubawa yaga sakinta yayi kuma saki uku" tana kaiwa nan takara
fashewa da wani sabon kukan, Shirune ya ratsa wayar zuwa Dan lokaci sannan yace
"Shikenan ai kiyi hakuri Bari nakirashi naji ba,asi" kashe wayar yayi,
Kiran wayar yayan yaketayi Amma tashiga bai dagaba don haka yafadawa Mama abinda ke
faruwa mama harda kukanta don abin yabata mata rai baba tashi yayi yace
"Bari naje gidan nashi nasameshi naji ba,asin abinda yafaru" Allah ya kiyaye hanya tayi masa
yatafi.


Bangaran su yayan kuwa abinda yasa baiji Kiran wayarba tunda yadawo daga masallaci ta
tsareshi a falo da rigimar itafa saiya aureta don tagaji da wannan rayuwar (kunsan nafisa tayi
mata zancen zai auri wata ya koreta shiyasa ta canja shawara tace ya aureta)
Hakan data fada kuwa ba karamin murna yayiba Nan suka Gama yanke hukuncin gobe zata
koma gidansu afara Shirin biki,
Rigar dake jikinta ya daga tare da tura hannu cikin rigar Yana taba bobos dinta don bakaramin
burgesho sukeba dondaima bawani girma garesuba yadda yakeso yaji sun cikamasa hannu,
Yade bakinsu sukayi guri guda Yana tsotsar harhsenta kamar yasami sweet nandai suka fara
lulawa duniyar tasu cikin hakan sukaji ana kwankwasa kofar falon don Allah yasosu akulle take
tashi yayi Yana tsaki yakoma yazauna duk yafita daga hayyacinsa itacema take cikin nata
hankalin don haka tamike ta tafi tana fadin "Wayene muna cikin Jin dadinmu yazo yaruguza mana" bude kofar tayi tare dabin dattijon da
kallon rainin wayo tajuyo tace
"Baby taso kaga wani tsohone yazo kila Yan neman maulane zuka sallameshi please" tafada
tana komawa cikin falon,
Tasowa yayi Yana cewa "waye yake neman shiga hakkina Ina gab da lulawa duniyar datafimin
kom..........." Maganarce ta tsaya wuri Daya lokacin dayaci Karo da baba hatta numfa shinsa
kasa daidaitashi yayi saboda tsoro da fargaba tare da tunanin mazai biyo baya.




*Comment*
*&*
*Share*



*By*

*Khadeejah (Ummu Fu,a & Afnan(*





[9/21, 7:47 AM] Hayat: *ν ½νΉ†ν ½νΉ† RAYUWATA CE*ν ½νΉ†ν ½νΉ†


*Na*


*Khadeejah Sani (Journalist)*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*Masoyana kuyimin afuwa na rashin jina kwana biyu da kukayi, kusan jiki akace da jini Sai
ahankali, gashi Nan kunsamu nayi amma saidai nace kuyi hakuri nasan yayi muku kadan babu
yawa ayimin afuwa my fans*


*ν Όν΅Ώ41_42*


Bayan nayi wanka nakwanta zazzabi ya rufeni Innarmu ce tahadomin tea tare da zaunawa
bakin gado tace
"Tashi kisha tea da magani ko kyaji Dan kwari ajikinki" tashi nayi da wuya tare da jingina jikin
filon da Innarmu tasakamin na jingina sannan nafara magana cikin hawaye nace
"Don Allah Innarmu kiyi hakuri karkiyi fishi Dani wallahi balaifina bane shine ya........" Dagamin
hannun da tayine yasakani yin shiru Ina raba idanu tafara magana tace
"Banason Jin abinda Zaki fadamin kawai Ina Kara yimin addu,a Allah yasa hakane yafi mafi
Alkairi, ni bandauki wani abuba kawaidai nadaukeshi amatsayin ke wannan shine irin naki
kaddarar Kuma Ina rokon Allah yabaki ikon cinyeta, don haka banason Jin komai kawai kisha
tea din nan da magani kwanta Allah yabaki lafiya"
Bangaran Yaya kuwa Koda yashiga daki yasami nafisa zaune tana kuka yazauna kusa da ita

tare da fadin
"Meyafaru Kuma kike kuka"
"Yaya don Allah kayi hakuri da abinda Yaya Adam yayiwa nafisa nasan bai kyautaba amma
kayi hakuri karkace zaka rabu dani wallahi ina sonka bazan iya rayuwa babu kaiba yayana
please katausaya min Yaya" takarasa tare da fashewa da wani kukan,
Jawota yayi jikinsa yara lallashinta yace
"Wayace Miki zan iya rabuwa dakeba nima inaso kisani laifin wani bazai shafi waniba don
haka nidake mutu karaba takalmin kaza kinji dear nah bar kukan nan"
Hakuri taci gaba da bashi akan abinda akayi musu tunda tasan Dole zaiji takaici cikin hakan
kawai ya hade bakinsu, nan suka lula wata duniyar,


********************


Murmushi baba yayi tare da fadin
"Inason magana dakaine kasameni yanzu agida Ina jiranka" Yana Gama fadar haka yajuya
yayi gida ikon Allah neh kawai yakaishi gida,
Mama na zaune taganshi yashigo zama yayi kusa da ita tare da dafe kanshi sannan yafara
salati don da Yama mance da yinshi saikuma yafara "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Allah
karabamu da mugunji da mugun gani, wannan musiba da yawa take Allah kabani ikon cinye
wannan jarrabawa data tunkaroni, dama haka duniya takoma ace kahaifi yaro amma yazo
yayimaka abinda bashike nanba" shiru yayi Yana dafe da kanshi kallonshi mama takeyi bakinta
cike da tunanin mezatace daurewa tayi yace
"Wai babansu meya farune haka naganka duk afurgice lafiya meya faru don Allah kayimin
magana naji" cikin sanyin murya ga hawaye ya fara Bata labarin abinda yagani dakuma abinda
yaji har zuwa karshe,
Itama salatin takeyi tana tafa hannu Tama rasa abinda zata fadi Sai kuka data fashe dashi,

Suna cikin haka saigashi yashigo yanata dukar dakai ya zauna daga gefe can nesa dasu Babu
Wanda ya kulashi har tsahon mintuna,

Sannan Bab yace "tashi kabani guri gobe da safe kazo wallahi idon har kayarda na nemeka
dakaina saina tsine maka nahuta kaji nafada maka"
Mikewa yayi jiki Babu kwari yakoma gida Yana zuwa sailuba ta mantar dashi damuwarshi don
batason taga Yana wani tunani Amma adaren suka Gama yanke shawarar gobe zaikaita
gidansu Sai abin yayi sanyi sannan zaizo neman aurenta, aikuw abin yayi mata Dadi sosai,

Washegari da sassafe yadauketa yakaita gida tare da kayanta sannan yayo gidansu don amsa
Kiran baba,
Samun mama yayi zaune itada baba sunsaka kayan Kari agaba suna kallo sunkasa tabawa ko
kadan tsugunnawa yayi tare da gaidasu Babu Wanda ya kalleshi balle yasa ran zasu amsa
Masa,

*******************

Bangarena kuwa zazzabi yayimin ruf Sai barin sanyi nakeyi gashi nasha maganin Amma
kamar banshaba ahaka nakwana da zazzabin bacci kuwa saidai barawo ban yishiba yadda
naga rana haka naga dare,
Da asuba haka nake kwance nakasa ko tashi gashi inaso nashiga toilet duk da ba sallah
zanyiba amma inason shiga don nagyara jikina, taimakamin tayi nashiga hakama dazan fito
Saida ta taimakamin hakan yasa tafita takira Yaya tace yazo yadan dubani,
Dubani yayi sannan yafira yace zaije yasiyo ruwa don saidai akaramin tunda jikina yayi sanyi
da yawa gashi ko tafiya bana iayawa,

Haka aka karamin ruwan nanne nasami bacci yadaukeni bansan me yakara faruwaba don nayi
bacci sosai bantashiba Sai wurin azahar,

******************


Mamace ta kalleshi tafar magana cikin fishi tace
"Kai yanzu abinda kakeyi kayi daidai kenan yanzu kasami yarinyar mutane kayi mata duka
sannan kasaketa Kuma saboda hauka saki uku, Koda yake banga laifinkaba tunda har kayi
girman da kake ajiye karuwa acikin gidanka Kuma na tabbata yarinyar Nan Mai hakuri tana gani
Amma Bata tanka mukuba shine duk da haka Bata yiba ka saka mata da saki, wallahi kabani
mamaki bantaba tunanin zaka iya yiwa nafisa hakaba kodan mahaifiyarta yadda ta daukeka, ta
maidaka tamakar danta batason abinda zai Bata maka Rai duk abinda tasamu Kaine kaitake
kawowa tunkafin ta haihu har bayan ta haihu Bata dainaba Amma shine kasaka mata da
wannan mummunan abun, wallahi kabani mamaki Kuma kabani kunya..." Batakai karshen
maganarba ya katse mata da cewa
"Mama wallahi wanna yarinyar Bata........." Ai baimakai karsheba taji ta wullo Masa cup din
dake kusa da ita daga gani kasan Wanda zatasha tea ne dashi.




*Comment*
*&*
*Share*



*By*

*Khadeejah (Ummu Fu'ad & Afnan)*
[9/21, 7:49 AM] Hayat: *ν ½νΉ†ν ½νΉ† RAYUWATA CE*ν ½νΉ†ν ½νΉ†


*Na*


*Khadeejah Sani (Journalist)*



*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*ν Όν΅Ώ43_44*



"Okay rashin mutuncin naka yakai haka dama bansaniba ina magana kana katseni lallaine
wuyanka ya isa yanka, to wallahi kaji nayi rantsuwa indai wannan halayyar ta banza kaga zaka
iya babuni babukai saina hakura dakai kwata kwata don bazai yuwuba ka doramin lalurar da
Allah bai halittoni da itaba, inbanda Kai sakaraine saika Duba kagani cikin gidan nanfa Kaine
babba abinda kannenka sukagaa kanayi shifa zasu dauka bandama dama Allah yayi ba halinku
Daya da babanaba datuni ka koya Masa wani mugun halin gashi Nan yaron arziki yanacan
yanata Sana,arshi baidamu da wani shashaciba, wallahi tunba yauba nake zarginka Amma
nabar abin acikin raina kawai don karna fada kace natakuraka duk da nasan kanama fada, to
inaso kasani insha Allah bazan sake saka bakina cikin wannan shashacin nakaba kaje kayi duk
abinda kaga dama, Kuma Ina Nan inafadawa Allah akan Allah ya sakawa wannnan yarinya
daka cuta ka saketa, kilama ka kulla mata wahala nasan dawuya idon baka cusa mata cikiba to
wallahi indai hakan yafaru dolenka ka dauki nauyinta komai har zuwa lokacin dazata yaye
abinda ta haifa, waima duk ba wannanba metayi Maka kayi mata wannan cin mutuncin saki
harda duka saboda hauka?"

Dafe yake da baki tun lokacin data wulla Masa cup,
Zare Ido yakeyi Yana rarraba idanu Yama rasa abinda zaice Saida ta Kara daka Masa tsawa
sannan yafara inda inda Yana fadin
"Ma...ma....umumum....mama dama....dama..tun..." Wata tsawar ta daka Masa tace banason
rashin mutunci inayi Maka magana kanawani kame kame to bari nakirata naji Kuma kaima kaji
agabanka" daukar ways tayi tare da Kiran Innarmu jin wayar tayi akashe don haka takira ta
Nafisa dauka tayi tare dayin sallama sungaisa mama tace

"Ke kaiwa mamana wayar zamuyi magana"
"To mama" dakin tanufa don dama tana kitchen din tsakar gida,
Samun Innarmu tayi tana gayaran dakin nan suka gaisa sannan tace
"Inna bacci anty takeyi?"
"Eh kinganta tunda aka saka mata ruwa don jiya Bata rintsaba kwata kwata shine take bacci ai
naji dadin yadda baccin ya dauketa"
"Ayyah Allah sarki Allah yakara sauki gashi nan kuwa harta rame" Inna na niyar yin magana
aka Kara kiranta dauka tayi tare da fadin
"Mama wallahi kinganta babu lafiya yanzuma bacci takeyi yayane yayimata katin ruwa, don
jiya haka ta kwana Babu bacci"
"Ayyah Allah sarki mamana Allah yabata lafiya ina innar taku?"
"Gata kusa Dani"
"Bata zamuyi magana" mikawa Inna wayar tayi tare da fadin ga mama,
Tana karba tajuya tabar dakin gaisawa sukayi sannan mama tadora da fadin
"Saikuma mukaji wannan abun Daya faru babu dadi, yaro ace kahaifeshi amma baka haifi
halinsaba Wal........." Saurin katseta Innarmu tayi tace
"Ai acikinsu baza,a iya banbance Mai gaskiyaba Sai anzauna Yaya, don Allah kidaina fadar
haka, wannan wata kaddarace da Allah ya dora mana saidai kawai Allah yabamu ikon cinyeta"
"Ameen ya Allah, Daman inason nayi magana da mamanane Kuma naji ance Bata lafiya
meke damunta haka?"
"Zazzabine dai takwana dashi amma yanzu bacci take Bari na tadata saikuyi maganar"
"A,a karki tasheta rashin imanin Sai yayi yawa yarinyar takasa bacci yanzu tasamu tanayi Sai
atadata barta kawai, amma nace tafada Miki abinda ya hadasu kuwa?"
"A,a wallahi banma tanbayetaba ita Kuma zata fadamin nace tabarshi Allah ya kyauta
nasandai itace tayi Masa wani laifin don mai sunan manya bazai mata wani abuba Sai takaishi
karshe, shiyasa nake rokon don Allah kuyi hakuri abawa babannasu hakuri yayi hakuri
yarinyarce akwaita da zuciya bansan meke damuntaba hartaje tayimasa abinda hakan ta......."
Katseta Mama tayi da fadin
"Wallahi tallahi kinji nayi ranstuwa nasan mamana keda gaskiya bakowa don na tabbabata
bazatayi Masa komaiba shinedai mugu azzalumi Mara inamani dayayi mata wannan
mummunan abun Wanda ko makiyinka baka fatan ayiwa haka, nidai inamai Kara Baku hakuri
akan abinda yafaru don wallahi da ace Adam yayi shawara Dani dabai aikata hakaba Amma
yaron yanzu halinsu saisu don Allah kiyi hakuri Kuma insha Allah anjima zanzo Naga yanayin
jikin nata sainazo"
Tana kaiwa nan takashe wayar tare dakai dubanta ga Yaya Wanda cikinsa ya duri ruwa don
duk atunaninsa za,a bani wayar nafadi abinda yayiminne Amma Sai yaji yadda innarmu ke
kareshi, Sai anan yayi nadamar yimin abinda yayi duk jikinshi yakara sanyi Yama rasa meke
Masa dadi gabaki Daya don haka yayi shiru Yana sunkuye da kansa, Mama kuwa takasa magana kawai Sai aikin kallonsa take babane ya daure yace
"Inaso kafadamin abinda ya hadaka da ita banason karya karkayimin ita don Dole naje naji
daga bakinta karka yadda naji abinda kafadamin karyane idon naji haka ranka zaiyi mummunan
baci"
Shirune ya ratsa dakin har mama tagaji tafara want sabon fadan don daman agidan tafi baba

fada sosai bama akan Tara ita Bata Wasa dasu sosai don batason sanyin da baba keyi musu,
Hakan daganine yasakashi fara magana yace
"Don Allah kuyi hakuri nasan nabata muku rai inamai neman gafararku daku yafemin, dafarko
bayan bikinmu natakura Nafisa na hanata sakewa acikin gidan none dukanta zagi hatta abinci
akwai abinda nake Bata akwai Wanda na hanata daukarmin saboda nayi la'akarine da gidansu
don haka nake mata abinda naso, hatta lemo na hanata daukarmin kullum idon zan fita saina
kirga abina hakama idon nadawo saina kirga"
Hakadai yayita Basu labarin kalar ukubar dayayita sakani Amma bai fada must maganar
karuwarshiba har yazo lokacin dasu Yaya sukaje yadda mukayi dashi akan lemon Dana Basu
sannan yadora da fadin
"Saboda nayi mata hakan shine jiya da yamma Ina dawowa nasameta ta fito da akwatinta
guda biyu falo tana zaune Ina shigowa tamike tare da fara zagina Wai idon na haifi cikin hafsat
da isah na saketa idon ba hakaba saitaga bayana a daren, nikuma danaga haka saina
wucewata daki nayi wanka nafito zan tafi masallaci takara tsaremin hanya harda marina shine
nikuma abin yabatamin rai nayimata duka nola saketa, Amma Ina Mai kara baku hakurin ku
yafemin don Allah"
Babane ya kalleshi tare da share kwallah yace
"To naji wannan tatsuniyar taka Amma baizama lallai na daukaba, Abu na gaba Kuma wannan
yarinyar dana gami agidanka wacece ita?"

Nanfa idon Yaya yayo waje yafara kame kame Amma saiya dake yace
"Baba wannan itace yarinyar da nakeson na aura"
"Wadda kakeson aurece Kuma zatazo gidanka da dare meya kawota?" Mamace tayi wannan
maganar don haka yakara tsorewa Akan nada yace
"Munyi wayane da ita tajini cikin bacin rai shine tazo donta .........."
"Don tayima uawarka nace don tayima uwarka mutumin banza mutumin wofi" kukane ya
kwacewa mama don haka tadaina magana tatashi tashige daki,
Babane ya kalleshi yace
"Kazo anjima zamuje gidan Adamun don Dole muje zamuyi magana Dani dakai da mahaifiyar
ku"
To yace tare da barin dakin ammafa cikinsa ya duri ruwa don baisan ya zata kasanceba,



**********************


Nikuwa bangarena Koda matashi naji dama dama bakamar jiyaba saidai ciwon jikin kamar
ankaro minshi haka na tashi,
Innarmu itace ta taimaka min nayi wanka sannan nasauya kaya nadawo nazauna afalonmu,
mahbub dake zaune don yau babu makarantar boko tahfiz kuma anyi hutu bina yayi da kallo
murmushi nayi masa nace
"My kani yau babu makarantar ne?"

"Eh anty babu anmana hutu Sai wani satin za,a koma"
"Jarabawa kukayi?"
"Eh gama report shite Dina can Bari nabaki kigani nayi ta biyu, dama uncle Yana Nan yazo
yagani harda na school Dina asiyamin kekena dayace zai siyamin" surutu kawai yakeyi nikuwa
tunda yace uncle hankalina yabar gunsa yatafi can.




*Happy jum'at Kareem to all my fans, friends, sisters & Brothers*


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login